ya tuna bai karya ba, yaCe
“Ki dafa min ‘shayi da indomi sun isa”. "
Tace, “To Nura, sai ka 20”.
Ya kashe wayar zuciyarsa ta narke da tausayin
Bahijja, wato duk abin data ke yi masa na rashin
da’a da tarbiyya ilimi aka ba ta, ba a koya mata
yadda za ta yi aiki da shi ba.
Tabbas duk halin da ta tsinci kanta a ciki ba.
laifinta ba, laifin iyayenta ne, tunda Allah ya
Kadarta masa Bahijja matarsa ce sai ya‘ bi ta
a'hankali ba da Karfin ikon tursasawa ba, ya
koyar da ita ilimin da 2a ta yi aiki'da shi bisa
koyarwar Manzo (S.A.W). idan ya yi haka ya'san
ya yi jihadi mai girma, Wannan shi ya ke kallo ya
sa shi a gaba sama da bukatar haihuwa tunda
da‘ irin tarbiyyar ta zata tarbiyyantar da ‘ya’yan
da‘zasu haifa.
Ya kuma ajiye abin da ya faru a Bangaren
RUFAFFEN SIRRIN zuciyarsa.
Duk da babu girma da Kimar da yake
ganin Malam da shi warwar sun zube a idonsa.
'Duk wani barbade-barbade‘tuni ta yi a _cikin
indomie din data dafa masa, haka shayin da ya ,
ji kayan kamshi duk da ruwan rubutu aka dafa
shi.
Mallakarsa ta ke son yi fiye da dan cikinta, shi ya
sa ta dama 'damara hatta hanyar da zai bi ya
shigo sai ‘da‘ta yayyafa ruwan rubutu.
*** *** ***‘
Har yammaci Amira na kwancc a ‘cikin dakin
Ummansu, tunda ta sha maganin zazzaBin ya
sauka .sai dai kuncin zuciya da sanyin da jikinta
ya yi ya hana ta mikewa daga kwanciyar da'ta
keyi, ga shi ‘duk tsawon wunin da ta yi a kwance
bacci ya kauracewa idanunta, k0 gyangyadi ya
kasa dibarta. Duk hayaniyar da kannenta keyi
tana jinsu, har zuwa lokacin da suka tafi
makaranta, Ummansu 'keta kaiwa da kawowa
tana ayyukan da ta saba tayata na‘ ' tsakargida
_ Karar Wayartace ta dame ta, wadda a wunin na
yau duk wanda ya kira ta bai samu ta daga
wayar ba, sai dai ta yi rurinta ta gama, kuma ba
dama ta kashe saboda wani kiran ma k0 jinsa ba
ta yi saboda abin da ke damun zuciyarta, ‘ wanda
ta lulluBe shi, ya ke kuma shirin tarwatsa
kwanyarta saboda zazzafan tunani dadamuwa.
Sai a wannan karon ne ta yanke shawarar ta
kashe Wayar domin Karar ta soma damunta. A
kasalance 'ta kai hannu ta . dauki wayar, sai dai
sunan wanda yake kai ne ya sake. girgiza
zuciyarta," Alhaji Saminu-ne
Wani irin abu mai kamada tsanarsa ta ji sam k0
muryarsa ba ta son ji,‘ ta yi
sauri ta kashe wayar, -ta wurgar da ita a gefenta,
ta juya mata baya tana ’sharar kwallar da ta cika
mata ido yanzu ta samu sararin zubowa. Ta
lumshe‘ idanunta.
, , “Kada ki dorawa kowa laifi sama da
ke, Alhaji Saminu sonki ya ce yanar yi kadai, ba
shi ne ya kai ki gurin Malam ba, zuciyarki da ta
Ki .yarda .da kaddara ita ce ta ja ki zuwa inda
za‘ a cutar da ke Tabbas da iyayenki Sun san
halin . Malam Balarabe da ba su turAki ba, ke ce
da laifi tun farko da kika ga ya yi miki abin da‘ ya
saBa wa shari’a da ba ki guje-shi ba. Laifina ne!
Ni ce da laifi
‘ , Ta amsa wa wani sashi na zuCiyarta da yake
tunasar da ita abin da ta ke son shigar da shi
cikin ranta, wato soyayyar Alhaji Saminu ce ta ja
ta zuwa ~gidan malam mai‘bakar aniya.
Tana nan kwan ce tana sakar nadama har ba ta
san lokacin da Ummansu ta shigo ba
ohhhh may god
Frndzz wato chapter din yau ya ban whl sosoi
SBD printers din DA sukai print din book din
basuyishi DA kyau ba wlh wasu pages din
tsallakewa kawai nake SBD damege din DA suke
hakan yasa nace Bari na nemi shawararku zamu
tsaya hakane har mu samu wani book din KO
kunaso muci gaba a haka
ur opinion plz
Bankada
Chapter5
ba, sai muryarta ta ta ji tana cewa.
“Amira in za ki iya fita ki je Alhaji Saminu ke
sallama da ke, na ce a fada masa ba ki da laflya,
amma ya sake aikowa wai dan Allah ki daure ki
fito minti biyar ’wani sako yake son fada miki”
Amira ta ce, “Umma a fada masa ya yi haquri
kawai, wani lokacin ya leko”.
Umma ta ce“Ai kuwa ya zame miki dole ki tashi
kije ki saurare shi, domin ni ba zan yarda da
wannan ba, kin san ba zuwan kansa ba ne janyo
shi aka
y1 . Amira da ta rufe kanta da bargo ta yi
saurin budewa.
“Janyo shi Umma?”
Eh mana janyo shi aka yi, kema kin san akin da
malam ya yi a kansa ne ke aiki a jikinsa. Ta ya
ya kuma ya zo za a dinga cewa ba za ki jeba?
Tashi za ki yi, ba za ki dauki alhakin mutumin
nan a banza ba
Tunda ta ji Umma ta fadi haka ta shiga tunani a
zuciyarta, tabbas duk abin da Alhaji Saminu ya yi
a yanzu a kanta ita ce ta janyo shi ta yaye
bargon. Tunda ta ji abin da Umma ta fada ta san
ba za ta taBa barinta ta Ki zuwa ba, ita kam da
2a a kyale ta maganar aure Sam ta fita daga
ranta, sai dai babu yadda za ta yi ya zama dole
ta ba .Wa Alhaji Saminu hadin kai idan har tana
son asirrinta ya Ci gaba da rufuwa, domin
bijirewarta na iya sake daga hankalin
iyayenta su yi tunanin akwai wani abu a
kasa, k0 ma su sake kokarin kai ta zuwa ga
Malam Balarabe, wanda ta‘ kejin da ganin
wannan ranar gara ganin mUtuwarta
A soron gidan ta hango Alhaji Saminu, yanayinsa
ya nuna damuwa, kuma yana hangota ya soma
murmushi.
“Amira gimbiya”. Ya fada a sarari. Ta yi karfin
halin sakar masa murmushi.
“Da ma ana ganinku?” Ta fada.
Ya ce, “Ga mu kuwa Amira”.
Suka yi murmushi gaba daya, ta soma gaida shi
yana amsawa yana kuma sake kare mata kallo,
ya ce
“Da na yi zaton irin yangarku ce ta mata, amma
alamu sun nuna min da gaske. ba ki da lafiya, me
ya faru da ke haka?”
Ta dan gyara zaman mayafinta ta juya ido na
halitta, sannan ta ce
“Ciwon ciki da zazzafi ne -yau na wuni da su”.
Ya tsareta da idanunsa da ke mata kallon kurilla,
ya ce
“Kin je asibiti?”
‘Ta yi kasa da kanta cikin Zuciyarta kamar ta
zagwanye saboda zafin da ta ke ji. Kallonsa ba
shi da maraba da irin‘wanda Malam ke yi mata.
Muryarta a sace ta ce
“Banje aSibitin ba, amma nasha magunguna”.
Ya yi yar ajiyar zuciya, ya ce
“Amira kina neman ki yi min wasa da lafiyarki
ko? Ki shiga yanzu mu je likita ya duba ki”.
Idanuma har sun kawo Kwalla, muryarta a sarke
ta ce
“Ai ka san ba za a bar ni mu tafi tare a gida ba”.
Ya ce, “Haka ne, duk na rude ne da ganin halin
da. kike ciki Amira, amma bari na bar ki ki huta
sosai zuwa gobe idan ba ki ji sauqi ba ki je
asibiti, amma ki daure ki bude wayarki dan na
samu damar jin ‘yadda ki ke?” '
‘ Ta ce “T 0 shi kenan, zan bude
‘ Ya ce “Allah ya baki sauki Sai goben zan shigo”.
‘ Ta ce, “To”.
‘ Ta soma tafiya, yana bin bayanta da
kallo, ya hadiye ragowar yawun da ke bakinsa.
“yace da na bar yarinyar nan da na yi asara mai
girma"
Ya fada a zucnyarsa, sannan ya juya ya koma
wajen motarsa ya dauko kudi ya sa cikin
ambulan ya kira Kaninta ya ba Shl, ya ce ya kai
mata,‘ shi kuma ya shiga motarsa zuciyarsa cike
da sha’awa da begen Amira.
Ta yi masa kyau yau fiye da yadda ya santa,
burinsa na son aurenta ya ninninku a zuciyarsa.
Washegari Amira ta kasa' samun nutsuwar zuciya
bare karfin jiki, tunda safe da Abbansu ya shigo
duba ta yace ta shirya ta je asibiti, ta ce
“Abba gudawar ma ta tsaya, Karfin jikina ne
kawai ba na ji”.
Ya ce “To shi kenan, Allah ya sauwake
Ya fita, ita kadai ta san ciwonta ba
na zuwa asibiti bane, magungunan da shansu
kawai ta keyi tana da maganin ciwonta. ta mike
ta yo wanka ta gasa jikinta dan Kara samun Karfi
da saukin zafin kasanta, duk da tana ji yana sauki
ba kamar wunin jiya ba hakan ya sa ta dan ji
dadin jikinta har ta shafa mai ta gyara fuskarta,
ta saka atamfa dinkin riga da siket ta fito tsakar
gida inda Ummansu da qannanta ke gyaran
ganyen zogala.
Ta zauna ita ma ta soma taya su, kanwarta ta ce
“Yaya Amira har kin rame fa?”
Ummansu tana murmushi, ta ce
“Ai sauki ya samu, ni kam jiyan nan
ai har ta fara ba ni tsoro”. Ta “Tsoron me Umma.
k0 kin
dauka mutuwa 2a ta yi. “Shi mutum ai ba a bakin
komai
yakeba, amma kin dai santa da dauriyan ciwo,
don jiya har zubar da hawaye naga tanayi ai na'
san ciwon ba karami ba ne, ga shi kuwa duk ta
zabge kwana daya
kawai”. Amira ta ce, “Umma ni kadai na san
abin da nakeji, Allah dai ya kiyaye gaba”. Hauwa
ta tuntsire da dariya. “Allah ya sauwake gaba ake
cewa”. Sannan Amira ,ta tuna a fili ta fadi
maganar ba a zuci ba, ta ce. “To sarkin iya
magana k0 me aka
fada ba daidai ba ne, ita ta iya ai duk daya
ne k0 Umma?” Ummansu ta ce, “Daya ne mana,
ai
duk addu’a ce”. Zaman da suka yi a yanzu ya sa
Amira ta ji saukin damuwa yadda kannenta suka
baibaye ta suna ta hira, suna sa ta dariya, yanzu
da sun san abin da ta aikata da sun tsane ta,
tsanar da za su yi kamar da ba a halicce ta ba a
cikinsu. Tunanin da ya fado ranta kenan.
Ta tsayar da duk wata walwalalta, ta zabga
tagumi kawai tana ‘ kallonsu, har Saifullahi ya
fuskanci sauyawarta, ya dafa kafadarta ya ce
“Menene Yaya Amira kika yi tagumi?
“Abin abinda ke damuna ba zai fadu ba. . Sai dai
ya zauna yaita con zuciyata alhaji saminu ne
zaune a falonsa ji
tamkar ya janyo lukaci da ya yi alkawarin zuwa
wajenta ya yi, saboda dokin zuwa ya ganta k0
‘ya ji sanyi daga irin azalzalar da zuciyarsa ta ke
yi masa a kan Amira ya fahimci a yanzu muryarta
kadai idan ya ji yana jin sanyi daga kewarta da
yake ji, bare ya dora ido a kanta, shi ya sa ya
kagauta domin ya ajiye ganin a matsayin cikar jin
dadinsa.
Amira na kan dardumar sallah tun bayan da ta
idar da sallar ba ta tashi daga kai ba, wayane ta
yi Kara. Ta daga, Alhaji Saminu ne, ya ce ga shi a
kofar gidansu.
Ta yi mamaki domin ba ta tsamamci Zuwansa a
daren nan ba tunda mafiya yawan lokuta ya fi
zuwa da yammaci. Ta ce da Ummansu.
“Alhaji Saminu ne yaxo
Umma ta ce, “Sai kije
Ta mike ta dauki mayafinta ta yafa
yana: tsaye yana sauraronn fitowarta ta yi masa
sallama, ya amsa tare da fadin
“Amira gimbiyar mata'
Ta dan yi murmushi.
“Duk kin hana min sukuni tunda na barki jiya
cikin halin jin jiki k0 me na keyi tunaninki na ke yi
to ya yajiki?”
Idanunta na kallon ka'sa ta amsa.
“Na samu sauki”;
Ya ce, “Na ga alama Amira, amma fa har kin dan
yi rama”.
Ta sake yin murmushi ba tare data dube shi ba.
shi kam nasa idanun yana kan duk wani motsi
nata.
“Amira zuciyata ba mai iya hakunri: da ke ba ce,
shi ya sa na samo mana mafitar da ta f1 wadda
na kawo a baya‘
inganci, da muhimmanci. Mafitar kuwa ita ce turo
magabatana su nema mini aurenki tare da saka
ranar bikinmu cikin watanni biyu kacal
Gabanta ya yi wata irin faduwar da ba ta san
dalilin yinta ba.
Ta dago idanunta da sauri ta dube shi, ba
mamakin abin da ya fada ta keyi ba, kalamansa
sun daki zuciyarta ne fiye da zatonta. Yana nufin
za ta fuskanci aure kenan tsakanin watanni
qalilan da ta yi asarar budurcinta? Me za ta kai
masa, .me Za ta shirya fada masa ranar da ya
fuskance ta ba cikakkiyar mace ba ce?
Tunanin dake zarya kenan a zuciyarta, ya ke
kuma tsananta faduwar gabanta. Tana jin Alhaji
Saminu na cewa. ‘
“Yardarki kadai nake nema Amira, wannan ita
kadai ce hanyar da ya dace in bi dan na gujewa
saka idon mutane a kan zaryar zuwa gidanku, k0
hakan ma bai yi miki ba?”
Amira ta yi nisa cikin tunanin da take karyar mata
da zuciya, dan haka ta kasa cewa komai, har sai
da ya kwantar da
inaa ganin ta ishe mu amincewa juna na zama
ma’aurata a nawa Bangaren ina ganin na yi
dacen samun mace mai kunya, mai
‘ hakuri, mai addini, mai kamun kai. Ke
; kuma a naki Bangaren wane irin dace ki ke
ganin kin dace da miji a iya fahimtar da ki ka yi
min?”
Maganganunsa tamkar zubar ruwan zafi a
zuciyarta, da da halin da za ta hana shi ambata
mata su da ta yi, duk da kyawawan yabo ne
yakeyi mata, amma ba ta cancance su ba a
yanzu.
Da hannunta ta lalubi bango ta jingina bayanta,
domin kafafunta ne ta ji suna yi mata sanyi
kamar ba zata jure daukanta ba, ta ce
“Na yi dace Saminu da samin namiji
mai juriya da rukon amana”.
Ta yi furucin da murya na sarkewa.
Ya kula da yanayima amma
kalamanta sun sanyaya Zuciyarsa matuka,
ya ce
“Na gode da irin kyakkyawar fahimtar da kika yi
min amaryata. Da wannan zan sami karfin gwiwar
turo da nawa iyayen gobe idan Allah ya kai mu da
daddare kamar wannan lokacin, za su taho
da. komai su saka anan gaba daya”. Ta ce “Da
wuri haka?”
Ya ce, “A’a Amira kada ki ce komai tunda na nemi
amincewarki ~kika kuma amsa min zan turo a yi
komai da wuri, tunda ni ba yaro ba ne da za a
dauki lokaci ‘ ana yawon soyayya. Mu tamu
soyayyar a cikin gidanmu za mu yi ta. Duk kuma
ranar da ba mallake ki Amira duk dokin da nake
yi a kanki za ki gane ya, zama‘ dole na yi shi,
tunda na matsu da ke
Wata irin kunya‘ ta ji kamar ta nutse, ta rasa
abin da ya sa Alhaji Saminu ba ya jin kunyar
furta irin wadannan kalaman,
duk da ta gama sanin sha’awarta ta rinjayi sonta
a zuciyarsa, ba tun yanzu ba ba ta yi sammanin
zai ci gaba da nuna mata hakan ' ba a lokacin da
yake shirin aurenta.
Yace “Amira kenan sarki kunya, kin yi shiru kamar
ba kya magana,. Duk 'saboda na zo miki da
maganar da ta ke sa ‘ki jin kunya k0 kuma na
lura cewa, har yanzu kamar ba ki warware sosai
ba, bari na barki ki je gida ki huta, amma zan zo
miki cikin bacci na ba ki kadan daga cikin sirrin
dadin da ake ji a cikin aure
Ta juya masa baya tare da cewa.
“Kai ni dai bana so”.
Ya yi dariya yana fadin. ’ “Na ji ba kya So, amma
na yi miki alkawarin nan da watanni‘ uku sai na
koyar dake yadda za ki ninka ni a irin wannan ra
shin kunyar...”
Ba ta jira ya gama fadar maganar ba ta shige
gida da sauri, shi kuwa ya ci gaba
dayi mata dariya. Cikin zuciyarsa ya ce
“Farin shiga kenan, Ni dai ba ruwana da
sassauci,‘ domin duk wanda ya ci ladan kuturu
sai ya yi masa aski”.
Amira na shiga gida ta nufi dakin Ummansu tana
kishingide tana sauraron radiyo, ta zauna a
gefenta, sannan ta soma yi wa Ummanta
maganar da suka yi da Alhaji Saminu na turo
iyayensa gobe.
Umman da ke kishingide sai ta mike zaune tana
murmushi.
“Ke Amira wannan lamari da ban mamaki yake na
wannan malamin. Yau k0 sati daya ba a yi da
zuwa wajenSa. ba, amma maganar aurenki ta
taso gadan- gadan, irin wadannan malamai bayin
Allah da ba sa aikata sabo suna sane bakinsu ,
yake ambaton Allah a koyaushe,da sun roki Allah
bukatu da wuri yake amsa musu, ga
shi dai lamarin kamar a mafarki dun mutumin nan
da ya ce zai yi miki addu’a a kansa ga shi nan
duk hankalinsa ya dawo gare ki. Jiya ma bayan
kin shigo ya aiko da ‘ wata takarda da na yi
zaton kudi ne a ciki, ' mantawa na yi shaf ban ba
ki ba sai yanzu
da na ji zuwansa na tuna”. Ta tashi inda 2a ta
dauko takardar, Amira a cikin zuciyarta ta ce,
“Wato in dai malamai bayin Allah masu gudun
duniya da gudun aikata saBo Ummansu ke nufi,
Balarabe ba ya cikinsu. Mugun aikin sason da ya
aikata mata shi ne abin da ya haska mata
kwanyar kanta ta gane zaifi
kyau a kira shi . da sunan BOKA ba
MALAM ba, domin dukkan abin da ta ga
ya yi mata bai yi kama da koyarwar ilimi ta
addinin islama ba.
Surkulle ne irin nasa daga abin da ya
"kauce wa hanyar koyarwar Allah Ta’ala da
ManzonSa ya hada kai da wani shaidanci
irin nasa wanda ba ta san k0 mene neba yana ci
da addini ne kawai, wanda ta fi ganin a kira shi
da bokan ba malam ba, domin ba ya aiki da sanin
da Allah ya ba shi, ayyukansa a Boye na bokaye
ne kamalarsa a sarari da saninsa na malamai ne.
Ta dinga jin zuciyarta na ingiza ta ta sanar wa
da mahaifiyarta abin da Malam din ya yi mata, k0
ta daina yi masa kallon bawan Allah na gari da ta
amincewa, sai dai tsoro da fargabar bayyana
mata ita diyarta da ta sha wahalar yi mata
tarbiyya da nuna mata ta yi gudu da halin bin
maza tun ba ta san me ta ke nufi da hakan ba ta
sha nuna mata k0 hannunta kada ta kuskura ta
bari wani namiji ya rike
Ta tsoratar da ita da cewar idan namiji ya rike
hannunta 2a ta yi ciki har zuwa lokacin da ta
mallaki hankalin kanta ba ta gajiya da tunasar da
ita da kare
mutumcinta da na su iyayenta ta hanyar
' tsare budurcinta.
To yanzu idan ta gaya mata dukkan aikin da ta yi
a baya ya rushe kenan , wacce irin dauka za ta yi
wa lamarin?
Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta ta bayyana
wa mahaiflyalta k0 ma ya ya 2a ta dauki lamarin
yaf1 shirun nata saboda gudun sake faruwar abu‘
makamancin
wannan a kan kannenta a baya.
Amma bakinta ya yi mata matukar nauyi, ta kasa
furta kowacce' irin kalma har Umman ‘ta miko
mata kudin da Alhaji
Saminu ya aiko mata da su " a cikin ambulan. Ta
farke ambulan din ta soma ‘ Kirgawa dubu goma
ne cif. Ta sake mayar
wa da Ummansu. “Ki ajiye a wajenki Umnm”. Ta
, fada.
Alhaji Saminu tun bayan da ya bar . gidan su
Amira zuciyarsa cike ta keda
farin cikin yadda ya samu. ammcewarta, Gidansa
kawai ya nufa, saBanin da da yake raba dare a
waje, tun sanda mafarkinsa ya BANKADO masa
zahirin surar Amira bai sake yi wa' wata mace
kallon sha’awa ba sama da ita, shi ya sa ma ya
yanke shawarar komawa gidanshi da wuri, domin
ba shi da appointment da kowacce yarinya a yau.
'
Na’ima tana zaune a falo tsakiyar yaranta da
suke yin home Work ta ji an bude Bangarensa
alamun ya shigo.
Ba ta yi ‘yunkurin tashi ta bishi ba saboda ta san
halinsa, minti biyar ba ya yi a gidan ya ke sake
komawa idan dai ya yi irin wannan dawowar ta
wuri. '
Kasan zuciyarta cunkushe da jin haushin irin
wannan; dabi’a tasa ta raba dare waje,
Ga mamakinta sai ta ga ya turo kofar' falon ya
shigo yara suka mike dukkaninsu
suna murnar ganinsa daya cikinsu ya rungure.
Mahmood.
Na’lma ido kadai ta zuba musu har ya zauna a
gefenta, sannan ta ce
Sannu da zuwa”.
. . Yace:‘Yauwa maman yara, na fahimci daga ke
harda da yaran nan kowa ma mantawa yakeyi
dani
Ta yi murmushi, ta ce
“Ta ya ya zan manta da kai?”
Ya ce, “Ga shi kuwa har na shigo gidan ba,a san
na shigo ba?”
Ta ce, “To
Showing 15001 words to 18000 words out of 79369 words