Kaka ta ‘fada masa, sannan ya rubuta
a jikin
‘yar takardar ya mike ya shiga wani daki.
Daga ita har Haj iya Kaka babu wanda ke iya
magana, babu jimawa ya fito
ya sake haWa kan dardumar da yake zaune
dazun, ya dubi Hajiya Kaka ya ce
“Haj iya yarinyar nan babu matsalar aljani k0
sihiri a jikinta, matsalar dai daga masu zuwa
wajen nata yake musamman shi wanda na ga
kamar zuciyarta tafi so a cikin manemanta, akwai
Saminu da
Sulaiman, duk wadannan da gaske suke yi a cikin
binciken da na yi, na ga dukkansu a
shirye suke da aurenta.
Sai dai rashin samun 'goyon bayanta ‘ abin da na
gani zuciyarta ta f1 karkata ga shi Saminu,“sai
dai shi matSalarsa iyalinsa duk matar da ya so
da aure sai ta lalata maganar ta zama shiririta”.
Hajiya Kaka ta jinjina kai, sannan ta ce
“To Malam yanzu ya kake’ ganin za a yi? Su dai
yaran yanzu 'ba a-musu dole, kuma 'shi. zaman
aure da 'soyayya ya f1 dankO inda zuciyana ta f1
karkata kenan
Malam ya ce, “Haka ne”.
Yana duban Amira da ke ‘ta raba idanu tsakanin
Malam da Hajiya Kaka zuciyarta ciike da dumbin
mamakin abin da Malam ya fada tunda ya
bayyana sirin ' zuci’yarta ne da babu wanda ya
san da shi, ita kadai ta san samarinta da yadda
suka Zautu da son ta ba su damar turowa a
gidansu a yi maganar aure ta ke zullewa. Malam
ya ce “Duk wannan abu ne mai sauki Hajiya, za a
yi aiki a kansa, zai zo da maganar aure ba da
jimawa ba, za kuma ta. samu alkhain' a jikinsa
mai tarin yawa, wani nata ma zai ji dadinsa”. ‘
'ba Hajiya. Kaka kadai ba, har ita ma sai data yi
murmushi. Ya ci gaba da cewa. “Za ta dingazuwa
tana karBar rubutu tsawon kwanaki uku da kanta
za ta dinga zuwa, akwai‘ Wanda sai ta 20 '2a a
rubuta mata ta .shanye, akwai kuma wanda» za
ta
tafi da shi cikin dare ta sha ta, shafe jikinta da
shi”.
Hajiya Kaka ta ce, “Za ta zo ai ta ga gurin”. Ta
bude ‘yar Karamar jakarta ta zaro dubu biyu ta
ajiye wa Malam suka mike suna godiya: Malam
ya" bi bayansu da kallo, ya lashe“ busassun
laBBansa.
“TabbaS da ina ‘da wajen ajiye
wannan yarinyar da na ajiye ta, a gidana na more
da baiwar da Allah ya yi mata”; Abin da ya raya a
zuciyarsa kenan, sanin ba shi da sauran gurbi
domin matansa na aure hudu ne, cikon ta hudun
k0 shekara daya ma bai yi da aurenta ba.
Asha karatu lfy
Daga qaninnan naku
Bankada
Chapter3
Nuradden ya farka daga baccin da ya dauke shi,
yana kuma jin dadin baccin sai dai kiraye—
kirayen sallar la a'sar “‘ne ya ‘ farkar da shi, ya
mike jikinsa babu kwari
*** *** ***
sai dai ya rage radadin zuciyar da ya
kwantadashi.
Ya yi alwala a dakinsa, wannan karon jam’i yake
son bi tunda lokaci bai qure masa ba, don haka
ya fito daga dakin.
Yana fitowa suka hada ido da ita, da alama
dakinsa ta nufo. Ta sakar masa murmushi. Tare
da fadin. harka
“sha baccin yanzu nake shirin
zuwa na tashe ka saboda lokacin sallah ya
yi”. Duk yana jinta duk da gaba daya ya
mai da hankalinsa a kan saka takalmansa, amma
sai ya basar da ita tamkar ba da shi ta ke ba.
Sai dai ya dan kura mata ido~ kamar mai son
gano Wani abu a cikinsu, sannan ya juya ya hada
da sauri domin ya ji an tayar da sallar. Sai dai
yana jin zuciyarsa a washe tas, da ya fahimci
fushin na Bahijja yau ba‘ mai zurfi bane
Tsawon kWanaki biyun da Nuraddcn ya yi a cikin
gidansa ya yi su ne cikin kunar zuciya, saboda
fushi mai tsanani da Bahijja ta ke dauke da shi.
Abu daya ne yake dan lafar masa da zuciya ganin
raguwar yawan zuwan almajiran da ke wunin
musu a‘ gida. Yaran ne kadai ke zuwa, su ma
daukar abinci kawai suke yi su fita, hakan sai ya
sa ya dan ji sanyi har ya soma zargin Bahijja ta
fara gane kuskurenta
ta kore su ne Girman kai irin nata ya hanata ta
ba ‘ shi hakuri', k0 ta nemi sulhu da shi, hakan
ma ya yi Wa ' zuciyarsa dadi, domin ya samu
nutsuwa cikin hutun da yake shirin yi na kwanaki
bakwai a gidan sa ba tare da ya fita kasuwa ba,
har zuwa‘ lokacin da jirginsu zai daga zuwa
ka‘sar Dubai, domin sarin kaya.
Yadda gidan ya yi shiru ya yi masa dadi kwarai,
duk da da ma Sun rage shi cikin jin dadin
kwanakin, amma zaman gidan shiru ba hayaniya'
Shi ma yana da tasa babbar gudunmawar ta jin
dadinsa.
Yana cin abincinsa cikin kwanciyar hankali tunda
ya san ba almajirai bare su yi masa jagwalgwalo,
daga ci sai bacci sai zuwa masallaci.
Sai dai a ranar ta yau yana dawowa daga
masallaci suka hada ido da Bahijja, tana tsaka da
kwankwatsa attarugu‘a cikin
no“Yar rigima kenan, kin San gaskiya kike takewa,
yanzu gidan nan haka daga ni sai ke bai fi miki
dadi ba, ga shi har kin samu damar da za ki yi
wa mijinki irin ' kwalliyar da ya ke so. Kin ga
kyau da kayan suka yi miki kuwa?”
Ba ta tanka masa ba, ya janyo fatar gefen cikinta
a hankali, ta sa dariya.
. “Ka gani‘ ba na so”.
Ya rike hannayenta. ‘
“Kina so Bahijja, miskilancinki ne ya hana ki bin
mijinki ki ba shi haquri”.
Ta juya ido, tace ‘
' “Ni na yi maka laifi ka koreni daga dakinka, in
na sake shiga ai sai na yi wani...
‘Abin da yake ne ya sa ta kasa karasa abin data
ke shirun fada, sai dariya da kyar ta kwaci kanta,
ta soma gudu yana binta suna zagayen gidan. '
A yammacin nan ya samo cikon
farin cikinsa da jin dadi da ya rasa na kwana
biyun DA suka wucw
Ya manta da komai, lallai komai ya shafe a ransa
Kaunar Bahijja ke ninkuwa a ransa, yana girmama
son da yake yi wa Bahijja. Duk abin da ta ke yi
masa ba ya tunanin rabuwa da ita k0 sau daya,
burinsa ta gane irin rayuwa da yakeso su
shimfida ta ba shi hadin kai a burinsa na
dauwamman zamansu.
A cikin daren ranar ya baje tsarabar dinkunan da
ya yo mata a Abuja, atamfofi ne masu kyau da
tsada. Yana kallon yanayinta lokacin da ta ke
kallon dinkin. ’
Zuciyarsa ta ba shi ba za ta saka su kamar
yadda yake so ba, tunda ya ga tana kallon dinkin
tana yatsina baki. Cikin karfafa gwiwarta ya ce
mata.
“Kin ga irin dinkunan da ‘yammatan Abuja harda
na nan Kano ma ke yayi”. Ta yi sa ar tararsa da
cewa.
“Shi ne kuma ka kawo wa matarka ta aure, abin
da marabarsu da tsirara kalilance?
Ya dan yi murmushi, ya ce
“Ai ina ganin da ‘yammata ne kadai dinkunan ba
su dace ba, matan aure ya fi dacewa su mai da
su kayan saka wa mazajensu a gida. Idan kuma
za su fita sai su sanya sutura mai yalwa da duhu
mai rufe jiki domin dinkunan na da daukan
hankali musamman idan suka samu jikin
kyakkyawa kamarki”. “Oh na gane abin da ka ke
nufi, kana
so na dinga shigar da karuwanku suke yi?”
Ya dago da sauri daga kishingiden da ya yi, ya
Kankantar da idanunsa yadda ya ji maganar
kamar shigar mashi.
,“Karuwai?” Ya sake nanatawa kamar mai son ya
tabbatar.
Ta murguda baki.
“In ba karuwa ba ta ya ya aka yi har ka iya yi wa
mace kallon tsanaki a kaya na
jikinta?” . . .. '
“Bahijja ni ki ke gaya wa ina tare da ‘karuwa
saboda baki da mutumci, ba ki san qimata ba?”
Ta ja dogon tsaki, ta dauke kai tana
‘yan guna—gunin da ba ya jin abin da ta ke fada,
amma tafasa zuciyarsa take yi, yana jin kamar ya
’ faffalla wa fuskarta kyawawan mari yadda
zuciyarsa ta hasala, amma sai ya koma ya lafe
jikin kujerar da yake kishingide yace Bahijja duk
yadda ki ka fassara ni a ranki haka nake, duk
abin da za ki yi sai ki yi
Ta mike tsaye ta ce.
“To ni mai zan yi maka? Kaya ne dai
na ce bana so, ba ma zanyi irin shigar da 'zai
nuna tsiraicina ba sai akai kasuwa”. Duk da
fushin da yake ciki bai san
sanda ya kwashe da dariya ba, kalamanta na
karshe ne suka sa shi dariya, har da rike ciki
yana nunata da dan yatsa.
Duk da bai ce komai ba‘, ta gano kalamanta yake
yi wa dariya. Wani abu ya taso ya tsaya mata a
wuya na takaici. Ta juya ta soma tafiya, ya janyo
ta da karfi ta fada jikinsa.
A kunnenta yake rada mata.
“Bahijja ban da abinki wane dare ne kuma
Jemage bai gani ba?” '
Kai tsaye ta amsa masa.
“Sai ranar mutuwarsa mana”.
Ya ce “To shi kenan amaryata, duk yadda ki keso
haka 2a a yi, amma ina rokon alfarma a wajenki
ki daure ki dinga - tauna magana kafin ta fita
daga bakinki.
Idan ki ka yi haka za ki kara kima da
mutumci a wajen duk Wanda za ki yi magana da
shi”.
Ita ma ta hango kuskurenta, amma
kana ta saisaita murya.
“Nura ai kai ne wani lokacin ka ke tabo ni, ka san
yadda kuwa na ji. da ka ambaci kana ganin
kayan nan jikin wasu mata? Abin da ka fada fa
yana nufin sun ba ka sha’awa kenan?” '
Ta yi masa tambayar tana kallon tsakiyar idonsa;
Ya sauke ajiyar zuciya.
' “Ba zan yi miki karya ba Bahijja, ni : din nan da
ki ke gani ina miki kaunar da ba na hada ta da
duk wata diya saboda kaunarki ta gauraye da
girma da martabar Malam da nake gani a idona.
Ban Boye miki komai ba, ina sha’awar dinkin a
cikin idona, amma ina SO na yi masa kallon
sha’awa a jikin iyalina shi ya sa na yi na kawo
miki da ina da wadanda zan yi wa kallon'
sha’awar da zan gan .su da ban kawo miki su
ba”.
Wani almajiri-ne ya yi sallama, sun shagala da
tattaunawa ba su amsa ba, shi
kuma ya shigo falon nasu. Ta mike da sauri ta ji
kunyar yadda yazo ya same su sosai, shi ma
yaron ya juya da baya. Ta kasa k0 magana,
Nuradden ne ya ce“Kai mene ne?”
Yaron ya ce, “Na zo kawo allona
ne
Nuradden ya ce, “To ajiye shi a nan”. .
Sai da ta ji fitar yaron ta sauke ajiyar zuciya
idanunta har sun kawo Kwalla saboda wani irin
takaicin Nura da ta ji, duk shi ya janyo mata
tunda ba ya iya zama sai ya Kwakume jikinta duk
yaran da suke zuwa yi mata aiki, da wadanda
suke taya ta hira duk zuwansa ya sa sun daina
zuwa gidan sai ya yi mata shiru. Duk ba dadi a
take ta soma‘addu’ar Allah ya sa Nura-ya tafi ko
sa wataya.
Ta dube shi,’ “Ka gani k0?”
Ya dauke kai, ya ce.
Na gani duk kin wani diririce kamar
wadda aka kamada kwarto. Ni mijinkinefa ‘
Ta ce, “Amma ko k mijina ne
bai kamata ya ganmu a haka ba, sai ya rage
ganinmu da kima”. Idan wannan ya dame ki, to ki
koyi rufe fadarki, wai ma allunan me ya zo kawo
miki cikin daren nan?” “Rubutu na sa shi ya yi
min”. Ya gyada kai, “Ya yi kyau”.
***
Tun lokacin da Amira suka bar gidan Malam ta
gama aminta ‘da lamarinsa- ta yadda ya gama
sanin bayani game da sunan samarinta ba tare da
wani ya gaya_ masa ba.
A hanyarsu ta komawa gida sai ya zamana Amira
ta ke damun Hajiya Kaka da tambaya, saBanin
lokacin zuwanta da ta,
*** ***
ke jin matsa mata Hajiya Kakan kawai ke yi.
Karin bayanin da Hajiya Kaka ke yi mata game da
ayyukan da Malam din yake yi shi ne ya ke dada
sa ta aminccwa da aikin da zai yi mata a kan
Alhaji Saminu.
Tana jin kamar ta same shi ta gama 'ta hanyar
auren da ta lura ba ya so, ba ta Bangaren
shashanci ba.
_ Ta dauki ‘yancinta da martabarta ta ‘ya mace a
matsayin abu mafi daraja a tare da ita, shi ya sa
k0 Kuwa wadda kanta 'ya waye da soyayyar
zamani ta rage zafin k0 shan minti ba ta yi, duk
kuma yadda ta dauki yarinya da daraja a idonta
da zarar ta samu labarin tana irin wannan harkar
shi kenan ta daina ganin Kimarta, haka za ta
dinga jin kyamarta da tsanarta a zuciyana, irin
yadda k0 a hanya ba ta son haduwa da ita bare
kuma da namiji. ‘
Ba ta taBa yin saurayin da ta zarge
shi da manufar nuna mata soyayya- irin ta
zamani ba ta sake saurarensa, wani ma ba
nufinsa ‘ kenan a kanta ba, amma wayewarsa da
zakewa a kan soyayyarta idan ya yi mata yawa
tana musu kudin goro tace duk ‘yan iska ne,
mayaudara.
Alhaji Saminu shi ne kadai mutumin da ya nuna
mata maitarsa a fili ta kuma ji ya yi tsayuwar da
ta kasa cire shi daga ranta. Hangen samun
nasara a wajen Malam na sauya manufarsa daga
mummunar manufa ‘ zuwa kyakkyawa ya sa ta ji
a yau zuciyarta ta yi wasai tamkar an sauke
mata wani nauyi daga Kirjinta.
Sun rabu da Hajiya Kaka tun a hanyar da zata
:shiga mota tana jaddada mata, kada ta yi
sakaci‘ gobe, ta yi sammakon zuwa wajen
Malam.
Ta‘ shigo Ummansu na kicin, sai Umar fake
tsakar gida yana rarrafe, ta dauke shi ta daga
sama, tana cilla shi ~suna‘ kyalkyala dariya daga
shi har ita. Tunda
Ummansu ta ji muryarta ta ke tai sauri ta.
kammala da zuba abinci dan ta zo ta ji abin da
ya faru a gidan malam, domin tun fitar Amira
hankalinta ya kasa kwanCiya, musamman idan ta
tuna da» kalaman Amirar kafin fitarta.
Ita ma sai nata gaban ya dinga" matsanancin
faduwa, jikinta ya yi sanyi Kalau, ta ke ta sake-
saken abubuwa da dama har ta soma bawa
kanta laifi
Sai dai jin yadda Amira ké Kyalkyadariya ya‘ sa
ta sauke ajiyar zuciya, ta ‘ fahimci ba a yi mata
wani abu da zai dami zuciyarta ba.
Amira ta nufi hanyar kicin din, ita ma Umma
nakokarin fitowa ta. tsaya tana
mai da numfashin daga Umar saman da ta
yi ta yi.
“Umma sannu da aiki”.
“Yauwa Amira, kun dawo?”
“Mun dawo Umma, ashe wajen da kafa ma ake
zuwa daga gidan Hajiya Kaka? Lunguna dai muka
yi ta bi can wani waje wai shi Saran ban taba
zuwa wajen ba sai
yau . .Uma ta ce “kun same shi dai k0?” “Yana
nan Umma, yace‘ matar Alhaji Saminu cekeyin.
asiri a kan duk matan da ya ke cewa yana so ya
janye”. Ummanta ta sauke ajiyar zuci’ya har
lokacin da Amira ta gama ba tar labari hankalinta
bai kwanta sosai da, ita abin da ta tsorata da shi
tun kfin ma a shiga gidan sai an soma bin
malamai a kansa, idan an shiga kuma sai ya ya?
Haka za a ai ta biye-biye saboda kawai ana son
zama da shi? Sai dai yadda ta ga Amira na ta
_farin ciki wanda rabon da ta yi irinsa har ta
manta a gidan, ya kure duk wani abu ta ke hange
a zuciyarta, burinta na son ganin auren Amira ya
sake ninkuwa.
Washegali da wuri Amira ta shirya zuwa wajen
Malam, tun da Aminatu ta yi ' wa Babansu
bayanin duk abin da Amira ta" fada mata, saboda
haka da ta shiga ta gaida shi da safe ya ce
,“Amira ga kudi ki shiga mota,Ki tafi wajen Malam
ki kuma tafi da wuri bana son biye- biye gidan
kawaye kin ji na fada miki”.
Tace “To Baba insha Allahu ba zan jima ba zan
dawo”.
Ya dauko dari biyar ya miKa mata.
“Ga shi”.
Ta karBa ta duke domin kudin ya zarta na mota
kadai.
Amira ta isa gidan Malam a yau mutum daya
kawai ta tarar a shimfidar da ta ke soron gidan,
ta yi wa matar sallama ‘ suka gaisa ta zauna,
matar ta dube ta. ‘
“Yau Malam din, ya yi jinkirin fitowa da tuni ma
na tafi dan na dan jima da zuwa”.
Amira ta dubi kofar 'dakin‘ da'yake zama din,
ashe bai ma fito ba, motsin fitowarsa ne ya katse
musu hirar‘ tare suka dubi kofar fitowar daga
gidan, shi din 'ne kuwa yana sanye da manyan
kaya.. Ya yi yafe da farin mayafi kansa da hula,
fuskarsa cike kwarjini. ‘
Suka soma-‘rige rigen gaishe shi yana amsawa
idanunsa na kan- fuskar Amira. Ya sakar mata
murmushi ya shiga dakinsa, bai jima da shiga ba
ya'yi‘ gyaran ‘murya ya ce
a shigo da wadda ta soma zuwa. ' ‘ Ta tashi ta
shiga, ya rage Amira ita kadai. Ba ta jima sosai
ba ta fito, Amira ta shiga. ‘ Ta durkusa ta. sake
gai‘she shi, sannan ta zauna ya daukowani
madubi da aka yi wa rubutu a kai, ya ce.
“Yarinya ai tun jiya na kammala da rubutunki”
Ya dauko tawada yana'Wasu rubutun a kan
wanda ya‘yi a jikin madubin wanda ba ta fahimci
abin. da yake rubutawa ba. Kalmomin ba Shi yi
mata kama da wasu ayoyi na cikin alkur’ani
amman zaif1 kyau a ‘ kira rubutun nasa da
jagwalgwalo ba don kada na yi saBo ba. Abin
data ke ta fada azuciyarta kenan lokacin da ta ke
kai mafara wajen hada baki ba larabci k0 2a ta ‘
gane wani abu mai ma’anar da ta sani, ba ta
gane komai ba har ya kammala, sannan ‘ ya ce
ta miko masa hannunta. .
Ba tare da musu ba ta miko hannun nata ya
dangwali tawada ya dora alkalami a kan tafin
hannun nata ya soma rubutu.
Wani irin abu ta dinga ji yana yawo a .jikinta
tamkar wadda ake‘ yi wa tafiyar kadangare,
amma haka ta sa wa kanta
juriya har ya gama ya dubeta.
“Amiran tauraronki mai haske ne aikinki zai 20
min da sauki k0 da kuwa shi saminun ba sonki
yake yi ba, idan har na soma aikin da wuri zai ci,
tunda kina haska idanun duk wani da namiji”, Ya
mika mata madubin da yayi rubutun a kansa.
“KarBi wannan”.
‘ Ya tura mata wata roba da ruwa a cikinta, ya ce
“Ki wanke madubin nan da hannun da na yi miki
rubutun nan daidai yadda za ki iya shanye ruwan,
ki shanye”. ‘
Ya jingina da bango yana lumshe idanu kamar
mai bacci, jikinasa_ ya gama mutuwa ido yasa
mata yake sake kare wa Amira kallo tana .wanke
rubutun.
Tun zuwansu Amira jiya da ya dora ido a kanta
babu matar da yake iya tunowa sama da ita.
Babu tunanin da yake illa nata. Wuni ya yi yana
sakawa da
kwancewar yadda zai yi ya mallaki Amira, sai dai
duk tunanin da yake yi a kanta yana saurin
warware shi da kansa. Yana ganin ba abin ma da
zai yiwu bane, sai ya watsar. ‘
A yanzu da ta ke zaune a gabansa- ’tana wanke
rubutun da lallausan hannunta da ya gama
kidima lissafinsa tun a jiya komai ya gama
kwance masa, yana ji kamar a zabce shekarunsa
a kan wanda yake da su Yana laluben
maganganun; da ya dace ya soma da su dan ya
sace zuciyarta sai dai yana ganin kada ya fada;
mata Wata maganar da za ta daina zuwa ya
kuma zubar da damarsa a wajenta ba tare; da ya
ci gaba da samun wani abu daga gare ta ba, k0
da na xaman da ‘ya yi ne yana kare mata kallo.
ne
Saboda haka ya ja bakinsa ya yi‘ shiru, ita kam
hankalinta na kan abin da ya sa ta bata kula da
kallon da yake yi mata ba
Ta yi tsammanin ma gyangyadi yake yi, shi ya sa
da ta gama ta ce masa.
“Malam na gama”.
Ya dago kamar mai baccin gaske.
“Yauwa kin shanye? To sake wanke ki dura
ruwan a wannan ledar, idan kin je gida sai ki
shafe gaba daya jikinki da shi”.
Ta zuba rubutun kamar yadda ya ce, ,' sannan ta
daga ‘yar karamar jakarta, ta mike tana ce masa,
to ta tafi.
Kasa magana ya yi, kai kawai ya daga mata
saboda irin abin da yake fama da shi
Showing 6001 words to 9000 words out of 79369 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3 Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27