‘yadda ya dace. “ Cikin kwana biyu wanda
ya ke wajensa ya tura shi zuwa Dubai zaBo musu
wasu kaya da ake so. ‘
Komai na tafiyar nawa Nura ,daidai har yaz0 shi
ma yana zuwa ya dauki karatu a
wajen malam in yana gari.
Sun shaku Kwarai da Malam har ya zama Nuran
kan yi 'Wasu shawarwari da Malam don shi ma
haka ya zama ba shi da shamaki a ko’ina gidan
Malam tamkar dan cikinsa haka ya dauke shi
wani yammaci bayan sun gama karatu da Malam
ya dubi Nuradden ya ce
“Kai ma fa kana daga cikin angwayen wannan
shekarar, zan aurar da kai tare da ‘yan uwanka,
amma ba dole zan yi maka ba idan kana da wani
hanzari sai ka fada min shi, idan kuma babu ni
na zaBar maka matar da zata dace da kai”.
Duk kunya ta lulluBe Nuradden, kansa na kasa ya
ce.
“Malam ba ni da wani hanzari a kan abin da ku
ka zaBar min”.
Malam ya yi mumushi har ya dafa'
kafadarsa, ya ce. , “Allah ya yi maka albarka
Nuraddcn."
Bahijja ita Ce yarinyar da na“hada ku
Isyaku kuma Maimuna, Basiru kuwa Hamida”.
Nuraddcn cikin zuciyarsa ya soma laluben wacece
Bahijja cikin yaran gidan, duk da yawan shigarsa
gidan bai tantance ‘ da sunan ‘ya’yan Malam din
mata ba, domin babu wani abu da ya ke hada su
duk Shigar da yake yi yawanci saman malam din
yake hawa, sai dai k0 shi ya aike shi wajen
matansa k0 ‘ya’yansa maza, da ya . fadi aiken
ya ke fita ba ya zama cikin gidan.
Zuciyarsa ta soma hasko masa wace ce Bahijja a
cikinsu, ya dinga addu’ar Allah. ya sa ‘yar gidan
Hajiya Kaltume ce, domin yana son matar tana da
kirki sosai, sai dai ya kasa samun zaBi a cikin su
ukun, k0 wace ce ma a hada shi da ita, ya san
bai yi zabe tumun dare ba.
Iyalan Malam zasu zamo ababen
alfaharin mazajensu, duk da ba lokacin ya
zabarwa kansa aure ba, amma ya ji dadi kwarai
da ganin Bahijjarsa ta kwanta" a ransa sosai,
musamman da ya luratana cikin farin ciki, ta
karBe shi a matsayin mijin aure. A taKaice tana
sonsa.
Yadda ya tsara wa kansa, zai soma gininsa-kafin
lokacin biki, amma Malam din ya ce kada ya
daga hankalinsa, ya yi gininsa a sannu domin ya
tanadar musu gidan zama a bayan gidansa ya
kuma ce ya yafe duk wani kaya da za a yi na
bidi’a, sadaki kawai yake bukata.
Mahaifinsa tamkar ma yaf1 shi murna da faruwar
wannan lamari, domin son da yake nuna wa
Nuradden ya sake kusanta shi jikin Malam din, ga
shi kuma yau suna shirin hada zuri’a da shi, duk
nasiharsa da Nuradden‘ ba ta Wuce ‘ya rike
Bahijja da kyau, domin ita wata baiwa ce a
tare da shi Allah ya ba shi‘
'Shi ma 'haka ya dauki lamarin da ' girma a
ransa shi ya sa bai taBa jin wani abu na kin
hadin ba, duk da akwai irin type dinsa da yake ta
kissimawa zai ajiyc a matsayin matarsa ba irin
Bahijja ba.
Nuraddcn mutum ne wayayye, yana kuma
sha’awar auren mace mai wayewar addini da ta
zamani, musamman Bangarcn ado da kwalliya shi
kam mace mai yawan ado tafi daukar hankalinsa
fiye da mai kyau
Abin da ya lura Bahijja bai dame ta ba kenan k0
ma yace irin tsarin gidansu . babu bayyana
kwalliya a wajen kowacce budurwa. Girman
lamarin Bahijja ya sa bai dauki wannan a bakin
komai ba, abin da zuciyarsa ke gaya masa
saukakken lamarinc idan ta zo hannunsa zai
tafiyar da ita yadda yakeso. _ :
Anyi komai. cikin farin' ciki da karamci da
mutumci, sai dai tun farkon aurensu. ya ,soma
haduwa da matsaloli
masu tsayawa a rai. Ya danne, ya kuma hadiye
yana kuma Kokarin nusar da ita irin: yadda ya ke
so har zamansu ya kai tsawon; shckaru hudu,
inda k0 'da yaushe abubuwan ci gaban rayuwa
keta Samunsa, kasuwancinsa na tafiya sosai. Ya
mallaki abubuwa da dama na ci gaba tuni ya bar.
KarKashin wani yana cin gashin kansa ne.
Sai dai abin da yake dakusar da ci gaban nasa
Bahijja wanda ya lura har yanzu babu wani sauyi
daga nata Bangaren har yanzu duk yayin da yake
son kawo gyara na ci gaba irin wanda yake so, to
sai ta kawo masa wasu shirmammun dalilai da‘
za ta kafa hujja dasu ta Ki amsa gyaransa.
Idan ya ji‘ kamar ya ‘kai karanta gurin
mahaifinta, sai ya ji nauyin yin haka ba ma ya iya
tattauna matsalarta da‘ kowa, hadiyewa kawai
yake yi yana tunanin duk; wanda "ya ji zai ce
bata samu kyakkyawar tarbiyya ba ne, a rage
ganin Malam da,
’Kima. Yanzu ma haka ' ya ke ta hadiye
fushinsa‘, duk da tunzurar zuciyarsa da ta ke yi,
yana ji kamar ya mike ya bi ta har cikin dakinta_
ya lakada mata duka, domin shi' ne kadai abin
da'ya' rage ya yi mata horon da za ta hankaltu
ta gane _ abin da - yake so; da wanda ba ya so.
‘
Ya ci- gaba da nanata hailala tunda da ma idar
da sallarsa kenan, har ya kammala a hankali
komai ya soma lafa masa, take yunwa da gajiya
suka bijiro masa, jikinsa babu Kwari ,ya mike
yana tunanjn mai ya kamata yaci da alama ba a
k0 kammala girkin gidan' ba, k0 ma da sun
kamala ba ya jin zai iya cin abincin da almajirai
masu tarin Kazanta irin wadannan suka 'yi
hidimar girkawa ba. ' ' " Ya fito ya nufi kicin dan
har lokacin suna tsakar gidan sharar tsakar gidan
suketayi
tana tsakikyar kicin tana. kokarin dora Katuwar
tukunya a kan cooke.
Kallo daya ta yi masa ta dauke kai kamar yadda
ya yi mata, butar shayi ya dauko ya wanke da
ruwan roba da yake hannunsa, sannan ya kunna
cooker ya‘ dora lokacin har ta fice daga kicin din,
yana jin tafasar tattasai kamar 'zai yi amai Sai
dai ya Ki fita daga kicin din ne gudun kada wani
yazo ya yi masa kazanta a cikin shayinsa.
Har ya tafasa ya juye abinsa, ya fita zuwa
dakinsa ya debo kayan shayi ‘ya yi hadi mai
kauri, sannan ya dauko kek din
da ya yi 'mata tsaraba yasoma ci,_shi kam kayan
zakin nan ba cimarsa bane'sai ya zamo turawa
kawai 'yake yi, da haka cikinsa ya daga bai san
lokacin da bacci ya kwashe shi a wajen ba.
***************
Umman su Amira ne a tSakar gida
tana tankaden garin tuwo ta ji sallamar surukarta
Hajiya Khadija da sauri ta ajiye rariyar tana mata
sannu da zuwa, har suka isa falo ta zauna tana
dai 'cike da mamakin ganinta, domin ba kasafai
ta ke Zuwa gidan ba. , Bayan sun gaisa Hajiya
Khadija ta ce. ‘ ‘ ' ‘
‘ “Wai 'ina yaran. ne na ji gidan- shiru Sai
wannan sarkin rigimar?” 1
Ta mika hannu' za ta dauke shi,’ ya ki
yarda Umman ta ce “Suna makaranta”.
Hajiyar ta ce
“Ni ma wucewa nazo yi ta nan na ce bari na leko
biki naje gidan- Alhaji Mamuda’
Umma ta‘ mike, “Bari na kawo miki ruwa
A“A’ bar shi yi 'zamanki, na' cika Cikina da lemon
gidan biki”.
Sun ' dan‘ yi shiru’ na ‘yan daKiKai
Haj iy‘a Maryama ta ce.
- “Ya ya maganar 'takwarata (Amira), har yanzu
babu wata : magana tsayayya? Auntynsu Umme
ta zo min da maganar Alhaji Saminu yana zuwa
wajenta, har ya, . yi mata kyautarkudin mota’
‘ Aminatu taja ajiyar zuciya, ta ce. “Haka ne Inna,
amma ni lamarin yarinyar nan ne na kasa gane
mata, ina tsammanin da kanta ta ke korar
samari, da mutum ya yi zuwa daya biyu wajenta
sai ta daina fita, k0 da ya 20 idan kuma na
matsa mata ta fita, to ba zai sake zuwa‘ba Alhaji
Saminu ne ma nake dan tsammanin ta amince
masa sai-"gagashi ma tun daga ranar da ya zo
har‘Ummee ta ganshi bai sake zuwa ba, da na
matsa mata da .tambaya, sai cewa ta yi ya yi ta
fiya ne, ba ya Kasar”. ‘ ‘ salatin da.Hajiya Khadija
ta ke yi
ya katse wa Aminatu maganar da ta keyi, jikinta
ya yi sanyi tana zaton ba karamin - laifi ta yi ba
dalilin fadar hakan. Ita dai ta san manufarta guda
daya ce su gane ba wai rasa manema Amira ta yi
ba, ita din ce ba ta damu da kula su ba.
Bayan' Hajiya Khadija. ta karasa sallallami ta
sake duban Amina ta 'ce
“Ai gara da ki ka fada min, , wannan lamarin ba
na zama ba ne
Aminatu ta sauke ajiyar zuciya da ta' ji ba laifi ta
yi ba.
“Yaushe ne za a‘ zauna da yarinya irin haka na
faruwa, _ ba a~ san dalili ba? Arzikinki na zuwa
tana hamBarar da shi da
kanta”. Hajiya Khadija ta mike tana cewa- '
“Nizan tafi amma ki turomin
Basiru gobe mu tattauna abinda‘
yadace
Aminatu ta yi mata rakiya ta
ta dawo cikin zuciyarta tana . juya maganganun
Hajiya Khadija, ita kam ba ta taBa rainon
budurwar ‘ya‘ ba sai a kan amira tabbas akwai
yiwuwar akWai matsala a tare da' Amira don, ita‘
ceta kasa ganeWa, amma yanzu sai ta ji dadi. da
Hajiyar ta sanya ' baki, ta kuma ce za ta binciki
matsalar. Hankalinta ya kwanta da hakan, duk
da- ba ta san ta hanyar da za su bi a warware
matsalar-ba, ' ’ ’ ‘Haka Amira ta dawo daga
makaranta ta same ta, kallo daya ta yi mata ta
fahimci akwai damuwa a tare da ita; ta ajiye
alkur’aninta a inda ta ke ajiye ,shi.. K0 hijabi ba
ta cire ba ta zauna gefenta. ‘ “Umma lafiya na
ganki kamar kina tunani?’:’ Aminatu ta dago kai
da murmushi a fus'karta. . . , . “Lafiya Kalau nake
Amira, yanzu Hajiya Kaka ta zo”. "
Sunan da jikokinta ke kiranta kénan. Amira ta kau
da fuska. mtws
“Ni gara ma da bana nan ta zo me ta
fada miki Umma?”
Ta mike, “Babu komai gidan biki ta je ta biyo ta
dai tambaye ku”
“ “Uhum”. Kawai Amira ta ce, ta mike ta soma
cire kayan makaranta.
‘Mama ki daina damuwa da surutun mutane a
kaina, duk abin da Hajiya Kaka za ta fada kada
ya dame ki”.
“Na fada miki ta ce min wani abu ne, da za ki sa
ni a gaba da surutu‘? Ni lafiya muka rabu da ita”
. Amira ta raunana murya,‘ta ce.‘Yi hakuri Umma
gani ‘na yi da naa shigo kin yi jugum...” '
Umma ta katse ta da cewa.
“To babu komai, ni ba mu. taBa yin hira mai dadi
ba irin na yau”. “To Shi' kenan Umma, ' me ‘ake
dafawa Yunwa nake ji yau sosai”.
Umma ta ce “Tuwo ne, Sai ki Shiga kicin din ki
kwashe? '
Washegari Alhaji Basiru ya je wajen mahaifiyarsa'
do’min ya sami sakonta Wajen Aminatu. '
Bayan sun gaisa Hajiya Kaka ta gyara zama, ta
ce
“Da ma a kan maganar yarinyar nan ne Amira”.
Duk ta fayyace masa abin da ta ji daga Bakin
Aminatu, da labarin Alhaji Saminu da Ummce ta
ba ta. Sannan ta dora ' da cewa. '
“Irin wannan idan ha a lura ba sai tafiya ta yi
nisa a." gane aljanune suka shiga jikin yarinya
budurwa ta dinga tsanar duk wanda ya‘ ce yana
sonta, suna korarsa..To shi ya sa na ce ’kaZo mu
yi shaWara”.
Shima "jikinsa ' yayi' sanyi, hankalinsa- ya tashi
dan bai dau wannan a
matsayin matsalar da mahaifiyarsa ta hango ba
sai yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya. “Kan wannan
Hajiya har sai kin
nemi shawarata kiyi abin da ya dace a kan Amira
duk abin da kika yanke ya yi daidai”;Hajiya
Kaka‘tace. “Eh haka ne. Basiru,‘amma shawarat
ma ai tana da dadi, ni abin _da nake ganin ya
dace a yi shi ne, a kai ta wajen 'Malam Balarabe,
na lungu biyu’ ya duba lamarin nata ya gani, idan
tana da matsalar aljanu sai ya korar matasu.
Idan kuma babu sai a yi mata addu’a har Allah
ya kawo manemi da wuri’
Alhaji Basiru ya ce
“ai wannan babu -laifi,:yaushe ya _ ka mata ku je
sai na turo ta?? Hajiya Kaka ta nisa, tukun ,ta ce
“Ina ganin gobe ma za mu je saboda
jibi za mu bikin ‘yar wajen Lantana”_
Ya ce “To sai ta z0 da safe kodan kuji saukin
samunjama’a. - '
Ya zura hannu a alj‘ihunsa ‘ya 2aro
dubu daidai guda uku, ya ce ‘ '
“Ga shi ku rike a hannunku”.
Haj iya Kaka ta amsa. '
“To sai goben duk yadda aka yi kuma idan ka zo
sai ka ji”.
Yace“Ba damuwa”.
Ya fita, maganar ta kwanta a ransa sosai, domin
ya 'san Malam Balarabe shi ma ya taBa zuwa
wajensa ya kuma yaba da .Kokarinsa; domin
matsalar da ta kai shi wajensa tuni ta zama
tarihi. ‘ ' ,
. Lokacin da ya koma gidanshi ya kammala' ‘cin
abinci, Aminatu na zuba masa ruwa yana wanke
hannunsa, ya ce
- “Kin ji' shawarar da Inna 'ta. yanke game da
Amira?” ' Aminatu ta buds idanu na razana,
sannan ta ce‘
“Me ya faru?”
Ya yi murmushi, “Babu komai, ta dai yi min
maganar korar samari da Amira ta ke yi, ta ce‘sai
an taimaka mata da ' addu’a saboda haka gobe
za su je wajen Malam Balarabc tare da ita”.
Aminatu ta zauna, tana fadin
“Kayya Malam, ni bana zaton tana da wata
matsala illa iyaka hangen wani abu ta. ke yi ya
sa ta haka, da a hadu ayi mata fada ta daina k0
a bata duk wanda aka ga dama da ya f1”
Alhaj i Basiru ya Bata fuska.
“Kina ganin kinf1 Hajiyarmu sanin abin da ya
dace kenan k0 kina son ki nuna mata iko a kan
Amira ne?”
Amina ta yi murmushi, ta cc.
“Haba dai duk bana nufin abu daya daga cikin
wanda ka fada, ina dai ganin kamar matsalan ba
a kai ga zuwa
wajen wani malami ba ne, amma na san Hajiya
tafini hangen nesa da sanin halayyar mutane,
yara nawa ne suka girma ta aurar da su a
gabanta”.
Ya Ce,‘ :“Yauwa, ke ma kin fahimta idankuma aka
samu' wata matsala ta Billo a kan maganar nan
to ke ce tunda tun farko kin nuna Kin
amincewarki za kuma ki iya zuga ta ta ki bin
umarnin mahaifiyata”.
Aminatu' taji' zafin maganganun,
domin ‘ba su kai ‘yadda zai dinga sauya mata‘
manufa haka ba, ta dai dake kawai ta
ce ‘ “Insha Allah ba za- ka ji bakina ba,
Allah ya tabbatar 'da alkhairi”. -;‘Amin’~~ Ya
fada tare da mikewa ya dauki buta yayi bandaki.
Washegan' da safe, Amira na sharar dakin
Ummansu ta ji kiran mahaifinta. - Da sauri ta
ajiye tsintsiyar ta nufi dakinsa da sallama.
Ta durkusa a gabansa, yayin da ya ce. “Amira za
ku je unguwa da Hajiya yanzu, saboda haka ki yi
sauri ki shirya ki jeki same ta kuje da wuri kafin
mutanc su cika”. . ‘
“To”. Kawai ta ce masa zuciyarta na tunanin ina
zasu je da Hajiya Kaka haka da har Baba ya
sanar da ita da kansa, ya ke kuma gargadinta da
ta yi sauri?
Tana shiga dakin ta dauki tsintsiyar ta ci gaba da
sharar da ta ke yi. Tana sharar zinccn zuci ya yi
mata yawa. Nan da nan ta ji tana cikin-
matsananciyar faduwar gaba. Harta gama ta
shiga can dakin Umma; ta tarar da ita a zaune a
bakin gado tana lallaba Umar da ta ke so ya yi
bacci, ta ce
“Umma yanzu Baba ya ce na shirya za mu je
Wani-waje da Hajiya Kaka, ina za mu?”
Ta fadi hakan ne dan ta kwantar mata da hankali
daga wasu-wasi k0 firgici, amma Amira sai ta
Zauna. " a
“Kai Hajiya Kaka da'rigima ta ke, ni ‘ kam bana
son yawan shige—shigen nan”. '
Aminatu na jinta ta dai tayi shiru, dan kada Amira
ta fadi wani, abin a ce ita ce ta saka ta.
Amira tana shiryawa amma sai mita ta kce yi, da
jan dogon tsaki kuma har
lokacin gabanta faduwa yake yi. Amma ta‘“ san
babu yadda za ta yi'ta guje wa zuwanta tunda
Babansu da kansa ya kirata ya fada mata.
' Har ta kammala shirinta ta nufi gidan Hajiya
Kaka. Ba ta jima a bakin titi ba ta samu mota"
Wannan ya ba ta damar kai wa gidan da wuri, -
Amma ga mamakinta Hajiya Kaka
har ta kammala nata shirin, tana zaune a tsakar
gida kan kujera ‘yar tsugune Ta
“Kin san shirin namu sai a hankali
Hajiya Kaka ta amshe da cewa.
“Ana ta kaKalen saka hoda da jambaki ba,
kwalliya ba miji”.
Amira ta mike daga tsugunnen da ta yi. _ “Haba
Hajiya Kaka, yaushe na isa . ~auren da za ki kira
min miji?” '
Haj iya Kaka ta watsa mata dakuwa. “Un go
wannan, ja’ira kawai Shekara sha taran ki ce ba
ki isa aure ba, kin zama uwar mata a gida?” .
Amira ta ce, “Hajiya a birni fa muke . ba a kauye
ba, kamar ni a dinga yi min zancen aure, ga masu
shekaru arba’in nan ma a gida, ai ina da sauran
lokaci”.
Hajiya Kaka ta sake watsa mata
dakuwar tana fadin.
“Ungo wannan rasa kunya beran tanka. Idan ma
shekara dari aka yi to ba a gidan nan ba, ni ba,
k0 kin taba ganin yarinyar cikin gidannan da ta
kai shekara sha biyar ba ta yi aure ba?”
’ “Zamaninsu daban 'nawa daban’; .. Amira ta
fada murya.KaSa'Kasa
Haj iya Kaka tace me "kike cewa?”
Amira ta ce, “Ba komoi
Dan ta .kawo KarShen fadan Hajiya,‘ Kaka ba don
tsoron fada mata' abin da ta" fada din ba. ‘
Hajiya Kaka 'ta lulluBa mayafi‘- a kanta, ta ce
“Mu je kin ji, ke yarinya ce har yanzu ba ki' san
abin «da yake yi miki ciwoba, aure shi ne
mutumcin duk' diyar da ta kai minzalin yinsa,
Amira ta yi shiru kawai: tana
sauranon Hajiya Kaka duk rabin hirarta a ‘ kan
hanya a kan nusar .da ita ne
muhimmancin kama mijin. aure a hannu da yadda
iyaye ke fadi—tashi a~ wajen ganin ‘ya’yansu
sun‘sami gidan daular da za -a rike musu ‘ya. a .
Shiga wannan lungu, fita wancan sai " ga su a
gidan Malam Balarabe, Hajiya Kaka ta ce.
' “Yauwa”. Ganin mutum daya, biyu suka tarar.
'Dayar na zaune a kan benci, daya kuma na‘
-ciki suma suka ‘zauna a kan bencin sama masu
jira.
Bugun zuciya da fargabar Amira ya tsananta
lokacin‘ da’ layi ya zo kansu, wanda ita kanta ba
2a ta iya cewa ga dalili ba, tunda wadanda suka
shiga suka fito da fara’arsu suka yi musu
sallama.
Babban mutum ne mai girman jiki, tsawo da Kiba
sosai,.fari za a kira shi. Yana da ‘dogon gemu da
'yaWan saje da suka hadu da gemun suka kame
masa Shekarunsa kuwa ba za su‘ gaza hamsin
ba, yana sanye da manyan 'kaya ya dora ‘mayafi
a kafadarsa da hula a kansa, duk yawan
Kasumbar da ta 'mamaye ‘ fuskarsa ba ta Boye
dogon hancinsa da manyan idanunsa masu
kwanrjini ba. ' '
,Kallo. daya ta yi masa ta lura da wadannan
abubuwan da ke tare da shi, sai dai lokacin da ta
durkusa idanunta nakasa ba ta son sake hada ido
da shi, tana ji suna gaisawa da Hajiya Kaka,
sann‘lan ita ma ta
dago ta soma gaida shi,
Idon da ya zuba mata ya tsananta faduwar gaban
da ta keji, ta sauke 'nata idon tanaji Hajiya Kaka
na cewa
Wannan jikata ce malam’ yar
wajen Alhaji Basiru ce ita ce babba”. Malam ya
shafi gemu tare da cewa.
. ,“Masha Allah”,
TaCe, “TO malam wata ‘yar matsalace ke tafe da
mu game da wannan yarinyar. . . Tana da tarin
manema manyan mutane, sai dai har yanzu a
cikinsu babu wanda ya zo da batun maganar
aure, shi ne nake so ai mata addua ta samu
gwani daya ya tsaya”. " Malam ya‘ ce “Kin yi ’
tunani .mai kyau Hajiya, za kuma a bincika
lamarin ’ Ya dubi Amira, ya ce, ,“Ke yarinya ya ya
sunanki?” Ta fada masa, ya ce ” “Mu ga
hannunki
Ta bude masa tafin hannunta, ya matsa sosai ya
sa 'nasa yatsan ya soma yi mata Zane a ciki.
Amira ta dauke numfashi saboda wani irin abu da
ta ji yana yawo a jikinta.
Ya. dauke hannunsa ya koma kan wata takarda
ya tambayi sunan mahaifiyarta da mahaifinta.
Duk Hajiya
Showing 3001 words to 6000 words out of 79369 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2 Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27