Bankada
Chapter1
wai ana kiran amira inji wani yaro amira ce
kwance a kan tabarma tana danne-danne a
'wayarta tamkar ba ta ma san yana yi ba.
_Ummansu da ke cikin dakinta ta fito ta
duBi‘yaron. “Kai je ka ce masa tana zuwa' Amira
ta yi saurin juyowa ta ce da yaron. ' ‘ ' “‘Ka ce
waye yake sallama?” Ummansu ta kwada mata'
harara’. “‘Au. da kina ma jinmsa ki ka yi masa
shiru saboda ba ki san muhimmancin sallamar da
yake yi ba k0?”
Amira ta mike tana murtsike idanu. “Umma ban ji
shi ba ne, game din nan ce ta dauki hankalina”.
Umman ta-sake Watsa mata kallon rashin yarda,
sannan ta ce'. “Allah ya kyauta miki: Tayi kicin
tana duba miyar da Amira ta dora. Yaron ya
daWo ya ce “Wai Alhaji Saminu ne Amira ta dan
yi wani tsaki a‘ ciki, sanna tacewa yaron. kace ga
ni nan zuwa”. mayafinta ta tita. ta yafa' ta isa
soran gidan kamshin turarensaya mamaye ,wajen
Yana ‘tsaye tsadaddiyar shigarsa da ya saba yi.
Wannan karon blue din shadda ce mai daukar ido
'da' taushi ga sheki, ya: Sha‘ aiki da hula a.
kanshi,’ :kyakkyaWar fuskarsa mai dauke da
murmushi' a .koda yauShe na
' nuna Kuruciyarsa ko ba a fada ba za ka
gane yana‘ 'cikin ganiyar kuruciya ne da'
zaman dirshan da naira ta yi masa‘ Amira
Gimbiya; Amira ' zonan_sarauniyar mata”.
' Ya ’furta’ da salOn' Wake‘Sun'dukima suka yi
dariya, abin da ya; f1 komai barge ta; da shi
kenan,‘ Sanya mutum nisha'di ga barkwancinsa
yadda ta fito
' da ya yi dariya.
‘ Ta gyara tsayuwa hade DA bude masa; fararen
idanunta masu ta lumshe su. ‘ Kallonta Yake“Yi‘
babu KO kibtawa
'komai nata sake kidimashi yake‘yi
cikin wani‘yanayi ya ,ke amsa gaisuwar da
take yi masa.‘ Ita kanta ta lura da kallon da
yakeyi mata ta 'hadiye Wani ya tsaya' mata ta
mai da idanunta kasa. Ya Kara taku biyu 'zuwa
inda ta ke
motata kadai zai gani ya gane ina nan, kin ga
kuma hakan ba girmana bane a idon jama’a, ki
amince min mu shirya wajenda” za mu dinga
haduwa kawai, kinada ilimi ya kamata ki gane
cewa wannan zancen ya zama tsohon yayi ko
ince“ na talakawa ne, amma ga gurin hutawa
kala-kala, ki zabi ko’ina a fadin Kasar nan mu je
mu tattauna Amira in har kina kaunata; wannan
duk ba Zai gagara ba”; Tunda ya soma fadar
bukatarSa kanta ya soma daukar zafi tana
matukar son Alhaji Saminu a ranta,‘ amma .irin
wadannan wayayyun kalaman nasa. ke. bata,..
mata rai da Shi. . ‘ Ta hasala sosai, ta sauke
nannauyar“ ajiyar zuciya, sannan ‘tadago ido ta
dube' shi na tsawon Sakan biyu. Ya kasa 'dauke
nasa idon a kanta, yana binta,_.da kallon karfafa
gwiwa a kan manUfarSa..
“Alhaji ina ganin wannan ba shi ne - abu mafi
muhimmanci a tsakaninmu ba , saboda haka bai
kamata ka kira shi rashin
kauna ba”. Ya wani "Ware idanu yana fadin. . “Ya
ya za ki kira lokacin da za mu ’ samu damar
tattauna mara muhimmanci a gare mu? Lokacin
da za mu sake ne fa mu fahimci juna fa, haba
Amira
‘ Ta hade yatsun hannunta biyu har sukayi ‘yar
Kara.
“Babu wani abu da baki zai furta wanda ba zamu
iya yinsa a nan ba... ba mu tSaya bata lokacinmu
zuwa wani waje. Wanda waje ne da addininmu da
al’adarmu basu koyar‘ da mu ba...”
motsin shigowar da suka ji ne“ya sa . shi'yin
shiru daga abin’ da yake shirin fada mata,
mai'Shigowar ta shigo soron ‘ sannan tai
sallama. Dukkansu' Suka amsa mata Alhaji
Saminu ya gaishe ta ganin‘
tana kallonshi.
Ta amsa, ta shigesu, Alhaji Saminu ya ce.
“Kun yi kama sosai, yayarki ce?”
Ta girgiza kai, tace
“Kanwar'Babana ce”, "
Ya ce, “Ya yi kyau”. ’
Sannan ya gyara tsayuwa ya ci gaba.
“Kin ,kasa fahimtata saboda ba kya sona, kina
son yi min kora da hali ne kawai, amma ya dace,
ki gane bambance-bambance masu yawa a
tsakanin tsayuwarmu a nan da samun -
keBantaccen waje na musamman, amma' zan ba
ki lokaci ki yi shawara, sai dai ni daga yau din
nan idan har ba ki sauya
ra’ayi ba ba zan sake zuwa na tsaya a nan ba.
Irin ‘zamanin da ki ke fada‘tuni ya jima da
wucewa; komai ai tafiya yake da .zamani, ki yi
shawara da ,zuciyarki ni
zan wuce. Duk abin da kika yankesai na ji ki a
waya
Ta bi shi da kallo, ya fice ba tare da ya
waiwayota ba. Ita ma sai ta juya ta shiga gida,
ita kam ta dauki wannan rana ranar rabuwarsu ta
har abada, domin ba za ta taBa yarda ta bi abin
da yake nufi din ba.‘
Tana shiga tsakar gida ta tarar da Aunty Ummce
da. Ummanta a kan tabarmar da ta tashi, » suna
hira har da Kyalkyala dariya'. Abin da ya sata
cikin mamaki kenan, domin Aunty Ummee idan ta
zo gidansu ban da harara da tsaki babu abin' da
ta keyi wa Ummansu ita din ma ba haka ta ke
shiga ba, daga gaisuwa za ta shiga sabgar
gabanta.
:‘Ba ta gama wannan mamakin ba Aunty Ummi
ta Kwala mata kira. ‘
“Zo, ya ,‘yar nan mai Kashin . . arziki, ashe Alhaji
Saminu ne yake Zuwa Wajenki?”
Yarinya kin yi gadon arziki”.
Ta soke kudinta~ a, jaka, sannan ta soma duba
kayan kwalin atamfoii ne super guda biyu, da
leshi guda biyu, kowanne da kalar mayafinsa. Sai
takalmi da jakunkunansu guda biyu hade da kudi
dubu ashirin a kai.
. Daya kwalin kuma mayukan shafaWa ne da na
Wanke gashi da turaruka,
komai saiti. Ta dubi Umman Su Amira, ta ce
“Wannan lefe kuma sai, ya ya?” Murmushi
Umman tayi tare da godiya ga'Allah a
cikinzuciyarta, da Allah ‘ ya kawo ranar da za a
ga wani abu a yaba a
tare da ‘ya’yanta. Malam Bashir ne ya shigo da
sallama. Hayaniyar me ku ke yi haka?”
Aunty Ummee ce ta dago kai fuskarta cike da
mujrmushi.
“Kayan da aka kawo wa Amira muke gani
Malam Bashir ya sauke ajiyar Zuciya, domin ya
dauka fada ake yi da Umman kamar yadda aka
saba.
Kallo daya ya yi wa kayan ya dauke kai. Can ya
zauna a kan wani tudu da ya
saba‘ zama, Ummansu ta tashi ta shiga kicin dan
ta ba su waje Yaya, Amira ma ta mike ita ma ta
shiga daki.
Aunty Ummee sun gaisa da Alhaji Bashir ta fada
masa sakon da mahaifiyarsu ta turota ta fada
masa, wato zuwa gaisuwar mutuwa a can garin
mahaifisu da ke karamar hukumar "‘Kura gobe da
safe, sannan suka yi sallama ta tafi
Malam Bashir mahaifin Amira su shidda iyayensa
suka haifa, daga babbar yayarshi Halima, sai
wanshi Alhaji Musa
sannan shi da sauran kannenshi duka duk da
mala bamai hali bane
Yana da rufm asiri domin gidan da suke ciki
gidansa ne na kansa. Yana sana’ar sai dakayan
masarufi a kasuwar Kurmi, Allah ya ‘azurta _shi
‘da ‘ya’yanshi takwas Wanda matarsa’ Amina ta
haifar masa Amira ita ce babba, sannan Saifullahi
da Mukhtar, Hauwa, Aina’u, Mahmud Fatima tana
goyon Umar.
.Rayuwar gidan rayuwa ce wadda iyayensu suka
shimfida musu ita bisa‘ doron tarbiyyar addinin
musulunci musamman 'Amina da ke kula da
mijinta da ‘ya’yanta cikin rufon asiri da
mutumtaka wannan ‘ne 'ya janyo mata
kyakkyawar tsana wajen dangin Malam
Bashir.
Suna ganin ba ya shawara da su bisa dukkan
lamarinsa .sai matarsa. Kalmar nan ta ta shanye
shi. ta dora daram akanta. _
‘ Shi‘, kam ~hankalin Aminatu da nutsuwarta shi
neya fizgi hankalinsa, su
duk sun yi bacci, tunanin da ya addabi zuciyarta
shi ne ,ya hana idanunta runtsaWa.
Hakika tana matukar son Alhaji Saminu tana
kuma mafarkin ace shi ne mijin aurenta, domin ba
ta hangi makusa a tare da shi ba, sai dai a yau ta
gama tabbatar da zargin da zuciyarta ta ke yi a
kan irin son da Alhaji saminu yake' yi mata ya
sauya tunaninta a kansa na son ya Kulla
kyakkyawar alaka ta aure a tsakaninsu.
A yau kam ta tabbatar da Alhaji Saminu yana son
ya bude idonta ne da soyayyar zamani, yana
neman ya yi mu’amalar banza ne da ita duk
bayyanar soyayyarsa gare ta sha’awa ce kawai!
Babu batun. so na gaskiya a tare da shi, ta
matso wasu guntayen Kwalla daga idanunta
lokacin da ta tuna da _irin farin cikin da Ummanta
ta ke ciki a ,yau tun zuwan Alhaji Saminu wajenta
yadda
Aunty Ummce ke kwarzanta dukiyarsa da
kyawawan halayensa tare da iya rike iyalinsa.
Sai dai duk wannan ya zamo ta baya ta rago- a
gare ta, domin tana ganin yau rana ce ta karshe a
tsakaninsu, rabuwarsu tazo
Ta sake yin juyi tabbas tana son ta zame wa
mahafiyarta mai share mata hawaye a kan gorin
da dangin miji keyi mata, musamman a ‘ cikin
‘yan kwanakin nan a kanta wai su yarinya ba ta
taBa gama sakandire ba mijinta a hannu ba, duk
cikin danginsu sai dai ita suna ganin nauyin jinin
da ta yi ta kwaso shi ne a dangin uwarta, su kam
farin jini gare su.
Ba Ummanta kadai ba har ita kanta maganar ta
daki qirjinta, kuma sanadiin furucin ne ta warware
duk shirin da ta yi na ci gaba da karatu. Wannan
shi ne dalilin da ya‘sa ta Ki ba wa samari fuskar
da 2a su
zo da maganar manya gidansu, ba wai rashin
manema ba kamar yadda suka zata.
' Mahaifiyarta ta san burinta na son karatu mai
zurfi tun tana ‘yar Kankanuwarta, sai dai ta kan
gargadeta a kan kada ta mayar da wannan
buquta fiye da yin aure, sam aure ba ya hana
neman ilimi. . ’ - “Amira kada ki kori manemanki
idan Allah ya sa kina da rabo a karatu sai ki yi
shi a dakinki”.
Duk lokacin da ta ji Ummansu na fadan haka
tana jinta ne kawai, amma Kudirinta na sai ta yi
digiri ta soma aiki sannan za tayi aure yana nan
a cikin ranta. Tunaninta na nuna mata mazan
yanzu mayaudara ne :zasu' iya amincewa da
maganar karatu sai kun yi aure ‘su Ki amincewa,
ita kam ba ta son abin da zai hana ta cikar nata
burin na karatu
Lokaci daya ta sassauto daga nata burin zuwa
namahaifiyarta, domin gorin da aka yi wa
mahaiflyarta gori a kanta‘ sai da ta zubar 'da
hawayen baqin ciki, sannan ta sha alwashi za ta
yi aure aure kuma na nunawa sa’a domin a can
ma ba ta taBa yin ragon saurayi ba, rashin
amincewane kadai ya sa 'suka kasa gane tana da
farin jinin masu hali ma kamar‘yadda Kawayenta
ke fasa mata kai da cewa, ita matar manya ce
Kamar ba su yi Karya ba, idan ka dubi diri da
kyan surar da Allah ya ba , Amira sunan- da mafi
yawancin jama’a ke kiranta da shi, amma usulin
sunanta Khadija. Ta ci‘sunan kakarta ta wajen
uba ne shi ya sa ake kiranta da‘ ‘ Amira.
- Fara ce tas, mai .matsakaicin tsawo,‘ tana da
dirin jiki mai daukan hankali ba ta” da kiba can,
jikinta a murje yake, Tana da dara—daran
idanu wadanda ke kara fitar da sirrin kyan :
fuskarta.
Hancinta bai fiya tsawo can ba, _ amma ba gajere
bane tana da dan karamin baki, kallo daya za ka
yi wa Amira ka gane " kyakkyawa ce.
Tun tana ‘yarinya Karama mutane da dama ke
cewa, kamannin kakar Babanta ta dauko Ladi
buzuwa, har ‘tsayin gashinta Usulin Ladi Buzuwa
a can Agadaz kakan Babanta ya auro ta k0
‘ya’yanta ba su yi kama da ita kamar Amira ba,
inji wadanda suka yi wa Ladi Buzuwa farin sani
Amma dirin jikin na mahaifiyarta ne. domin ita
Ladi siririya ce matuqa, tun Kuruciya har tsufanta
ba ta yi kiba ba.
Sun hadu da Alhaji Saminu a wajen bikin kawarta
Nafisa,ne yana daya daga cikin ', abokan ango,
ya kuma ziyarci 'wajen
dinner din da ake. Tun da ya kyalla ido ya
ga Amira hankalinsa ya gaza kwanciya, ya yi
dace da ta amshe shi hannu bibiyu karo na hudu
kenan yana kawo mata ziyara bayan waya da ya
ke kiranta sau hudu k0 sau uku a kowacce rana.
Komai na Alhaji Saminu abin burgewa ne shi ya
sa cikin kankanin‘ lokaci ya shiga ranta sai dai a
zuwansa na biyu kadai ya soma rikita lissafinta
da buqatunsa da suka yi wa kanta girma, har ta
ke nazari a kansu.
Daga karshc ta ajiye shi a matsayin ba abokin
tafiyarta ba, domin ita aurensa ne burinta. '
Dukkan yadda zuciyarta ke azalzalarta da tunanin
Alhaji Saminu ba ta taBa sha’awar kiransa a
waya ba, haka shi ma bai sake bi ta kan tunanin
sake zuwa wajenta ba, musamman a halin yanzu
da ya sake haduwa da wata yarinya Sa’adatu
da ta mallaka masa komai nata su ke
sheqe ayarsu kaman ba gobe
Bankada
Chapter2
watsewarsu gaba daya ma ya manta da batun
Amira a rayuwarsa
Tsawon watanni. biyu ba ‘kira ba sakon Alhaji
Saminu, a gidansu‘duk saurayin da Amira ta
kwatanto sai ta ga bai kai Alhaji Saminu dacewa
da‘ ita ba, saboda haka ta dawo da dabi’arta ta
Kin "
kula samari k0 an yi sallama da ita ba ta fita. “
Wannan lamari ya dami Umnmnsu tana ta saka
da kwancewa a kan ‘yartata na abin da ya sa ta
ke korar samari ita tafi son ‘karatu
kuma,.Babanta ya ce ba a ‘gidanshi ba sai dai
gidan mijinta. Abin ya'dame ta sosai, har wata
‘rana suna tsaka da ninke kayan kannen Amira
Ummansu ta‘dube ta. ‘
“‘Amira Wai ina mutuminnan na na kwanaki da
yake zuwa "wajenki, ya daina zuwa? K0 shi ma
korar tasa kika yi. ne?”
Amira ta 'dago ‘kai kamar Ummanta
san zanccn data ke yi kenan a zuciyana, ta ce.
“Umma kina nufin Alhaji Saminu?”
Ummansu ta ce, “Eh ina ga shine mutumin da
Umme ta ce ta sanshi”.
Amira ta dame fuska ranta ya sosu, domin yanzu
nadamar haduwama da Alhaji Saminu kawai ta ke
yi, ta ce
“Umma tafiya ya "yi, ba ya Kasar ba korarsa na
yi. ba”
' -- Umman ta‘ ce “Eh to Allah ya sa da gaSke ki
ke yi 'Amira, domin lamarinki mamaki ya ke ba
ni. Abin da yasa na yi miki maganarsa‘ na ga
kamar kin fi sonsa a cikin. manemankine, ba
kuma dan kudinsa ba, domin idan kudi ne baa
kya Ki Alhaji Auwalu ba, abin da nake so ki gane
Amina, aure shine mutumci' da martabar duk diya
' mace, idan ba da gaske shi Saminun yake ba, to
ki daure ki amshi maganar Sulaiman
a yi auran nan naku hankalina mayafi
kwantawa dashi. Tace “To Umma’.
. NURADDEN
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, san‘nan ya yi
miqa tare da salati ya murza _ yatsun hannunsa
ya dora su a kan sitiyarin' motarsa tare da
hamdala. Ya dubi agogo Karfe biyu da rabi na
rana, ya yi sauri ‘kamar yadda ya So, amma ya
gaji liKiS tunda ya dauko hanya daga Abuja k0
sau daya bai‘ tsaya hutu a hanya ba, har ya iso
garin na Kano ta dabo tumbin giwa. '
Yunwa da gajiya, babu abin da babu a jikinsa,
uwa~uba kewar matarsa da ta
hana zuciyarsa sukuni, har sai da ya yi asubancin
zuwa gare ta. Ya shafi tsakiyar kansa yana
tunanin
irin yadda zai gan ta, da irin farin cikin da. za ta
yi idan ta gan shi da wuri haka,
saBanin yadda ya saba zuwar mata da la’asar.
Ya tsaya a wani store ya siya mata cake da ice
cream sannan ya jidar mata turaruka masu tsada
ya hada a cikin sauran tsarabar da ya yi mata
tun a Abuja ya nufi hanyar gidansa. _
Samarin da ke zaune a kofar gidan suka yi masa
barka da zuwa, ya amsa ciki- ciki domin shi ba
don Son ransa suke tare masa a gida ba.
Ya ajiye motarsa ya nufi ciki, sai dai tunda ya
doshi Kofar shiga ciki yake jin hayaniya kamar‘
ana ‘wani sha’ani‘ a gidan ya sa kai da sauri dan
idonshi ya gane masa abin da ke faruwa.
. Wadansu yara ‘yan samari- ne a kofar kicin din
suna ferayar doya su biyu, daya kuma na gyaran
kayan miya.
Duk da bai san sunan yaran ba, ya san
fuskokinsu almajiran malam ne Ya bi tsakar gidan
da kallo ledar ' pure water, bawon rake da na
gyada ban da na doyar duk ya tsallake su ya
shiga tsakar gidan. Hango kofar dakinsa a bude
DA yayi ne ya hana masa amsa sannu da zuwa
da ' yaran. suke yi masa. Ya hada da sauri har
da sassarfa domin ya shiga. ‘
Sabi’u ya gani tsaye da tsintsiya a hannunsa da
alama motsin shigowarsa ne . ya sa shi dagowa
daga Sharar da yake yi.’ . '
Ya daka masa tsawa.
.“Kai malam fita ka ba ni waje”
" Sabi’u na kokarin gaida shi ya juya gwiwarsa a
sage ya fita' da tsintsiya a hannunsa.
zuciyarsa ta gama hasala yanzu wannan jibgegen
katon ne baligi a dakin baccinsa da sunan yana yi
masa Shara? Yana da iyali ba babu ba. .
Ya‘ ajiye ledar hannunsa, sannan ya juya
zuciyarsa na tafasa. Falonta ya nufa,
sai dai ta tarar da shi har ya shiga bandaki jikinta
ya yi sanyi ta zauna bakin‘ ‘ gadonshi tana sake
—saken yadda za' ta yi'ta taushi zuciyarsa daga
dukkan zafin donta lura ya yi. fushi Ya turo Kofar
ya fito da alama alwala‘ ya yi bai k0 kalli inda ta
ke ba ya shimfida darduma ya tayat da sallah. ‘
'- Tana nan a zaune ta rafka tagumi wasu
addu’o’i ta ke karantawa a zuciyarta, har lokacin
da’ ta fuskanci ya idar da sallar‘ ~
Ta mike tSaye zuwa inda ya ke. “ “Nura kayi
hakuri, ban san. zaka dawo yanzu ba..” ' Ya
katse ta,“‘Sai zan dawo za ki san ” abin da ya
dace da ke da wanda bai dace ba? Ina ilimin da
kike da shi yake k0 dama ba‘ don ki yi aiki; da
shi aka koya miki shi ba da za ki dinga kawo min
Katti gida ' kina. zama a cikinsu‘!” Nan da nan
"ta'hade fuska, ‘abin.zuciyarta
ta raya mata so ya ke yi ya raba ta da kowa ba
ya kaunar wani ya rabeta idan kuwa ta sakar
masa fuska haka zai - korar mata duk ja‘ma’a ya
tafi can wani gari ya bar ta a gida ita kadai
kamar mayya.
Ta sake hade fuska, ta ce.
nura su Sabiun ka ke kira Katti'sai ka ce baka
sansu ba? Ni fa ba za ka raba ni da su ba tunda
tare ka ganni da su...”
“Shut up!” ya yi furucin da har sai da hantar
cikinta ta kada. _ ’tafi ki bani waje_,>bana son
irin wannan shirmen naki
"“Zan bar. maka. daki amma ka sani yadda ka
ganmu da su haka za ka bar ni da su”. Ya dauke’
kansa.kawai .._yana ‘ maimaita hailala, domin
yadda ~yake ji- ‘ a, ‘ zuciyarsa' ba‘don girman
mahaifinta a , WAjenshi da babu- abin" da zai
hana“ shi
sakin aurenta k0 ya lakada mata dukan da .‘ za
ta kasa tashi, sai dai, kash 'tana da matsayin
‘yar malaminsa da yake da girma da kwarjini a
idonsa, ai k0 kare ya ba shi ba zai dakar masa
shi ba bare mutum mai darajar mace kuma ta
aure
Yunwa da gajiyar da ya yi duk sun kau, sai dai
bacin Bacin ran 'da ya keji a cikin‘ kirjinsa. .
Malam Balarabe mahaifin Bahijja malamin
mahaifinsa ne domin duk 'a yammaci yana zuwa
wajensa karatu. Babban malami ne da
shahararSa ta? mamaye Bangarenssu, ' yana da
yawan dalibai‘ almajirai amma , ya daina ‘
karantarwa, sai dai har zuwa‘ yanzu ana'
karantar da almajirai a wani fili nasa da ke: kusa
da gidanshi yana dai zama a dakin soron gidan'
yana’ kar‘Bar bukatu na maza da mata masu
neman bukatu na neman, taimako da addu’a.
Yana da matan aure har hudu da tarin ‘ya’ya
maza da mata nasa da na ruKO.
Yana da matukar girma a idon jama’a sosai, ana
ba shi girma domin idan yana tafiya da Wiya ka
ga mutum sama da biyu a bayansa, sai abin da
ya zana hakan.
Yadda mahaifin‘ Nuraddcn Alhaji Lawan ke
girmama Malam Balarabe shi ya sa Nuradden shi
ma bai dau lamarin Malam Balarabe da‘ sauki ba.
Bai dada ganin girman lamarinsa ba, sai da
mahaifinsa ya kai shi akan buKatar yi masa
addu’a a kan neman aikin da yake yi domin
lamarin yake tafiyar masa
daidai
Showing 1 words to 3000 words out of 79369 words