shigo da dan kofi a hannunshi tareda Modibbo ya duka ata bayanta yakai hannu yana bude kyallen kan yakai cup din yanaba matan ta karba tace "ungo sha maganin zafin zai dena" bakinta takai kofin tana lekawa datagani baki saikuma tace "menene shi?" Dasauri matan tace "magani"? Dasauri Rashida tace
"menene magani?" Dasauri dukansu suka kalleta saikuma matan tace "shine zaisa kan yadena zafi"
Dasauri tabude baki aka samata kofin ta kurba kadan tacire fuska tana yatsine fuska sabida daci daidai lokacin Hawaro yashiga kankare maganin daya shafa akanta daya bushe, ihuuu tayi zata yunkura ta gudu, da idanu yamusu alamu su riketa suka riketa yahau cirewa tana ihu sosai tana kuka, haka yacire ya maida wani madani wajen sannan suka saketa yadauki wani kyalle ya zagaye kan dashi, Modibbo yabata nono a kwarya yace "sha" kallon nonon tayi saikuma tana goge fuska tace
"menene shi?" Ahankali yace "nono sha" karba tayi takai bakinta ta kurba kadan saikuma ta ijiye ta shiga kallonsu yanda suke kallonta suma kaman sun sami tv zafin kan yasoma rayuwan mata, ahankali Modibbo yace "ya sunanki?" Bakinshi take kallo saikuma ahankali tace "sunana?" Saikuma tashiga kallon jikinta tanabin fararen kayan fulani dake jikinta da kallo takai hannunta ta taba kanta kafin takara kallonshi tace "sunana" saikuma tace
"sunana" ijiyan zuciya Modibbo yayi yace "kin manta sunanki" dasauri tace "sunana" tashi
Modibbo yayi kawai yafice waje dasauri Hawaro yabiyoshi, Modibbo yakalleshi yace "zan dauki Liti, da Anas mutafi binni muje wajen yan sanda mu bada sanarwa, banson na je da ita, amman kai ka zauna dasu sabida kar jikinta ya rikice bari muje" gyadamusu kai yayi yawuce su uku suka tafi daga kauyen zuwa wajen gari kusan tafiyan machine awa daya, sannan sukahau mota dazai kaisu Kano about 2 and half hour journey in total, the nearest police station dake nan tashan dasuka sauka suka shiga, ihu yan sanda suka musu ganin su wani kala. "Me kukezo yi nan"? Ahankali Modibbo yace "munzo fadan wani abune daya faru sirri ne gaskiya opisa" wani kallo dan sandan yamusu yace "fada ina jinka" kallon wajen Modibbo yayi saikuma yace "gaskiya muje daga ciki" dan jim dan sandan yayi saikuma yace "okay muje" sukai ciki wani office yabude musu suka shiga yazauna yace "ina jinka" anatse Modibbo yashiga koro bayani sannan yace "yarinyar ina kyautata zaton likita ce tana sanye da fararen rigan likitoci mun batta chan kauyenmu sabida kanta dakuma bamusan ko za'a sami mijin nata ba Ambato rigan likitoci dayayi yasa dan sandan yace
"kujirani" yawuce yafita office na ogansu yawuce ya sanar dashi komi da sauri yasa akawosu office nashi, shigo dasu office na Ogan yayi exact bayani sukamai wayanshi yaciro dasauri yaciro hoton
Rashida yanuna musu yace "itace?" Atare dukansu ukun sukace "eh" wani bala'in farin ciki dan sandan yayi promotion guaranty kenan, dasauri yashiga kiran asalin ogansu kwata kwata ya sanar dashi komi.
Daga Ammi har su Buba dasu Gwaggo da Muji duk an taru ana kan Riyad da aka kasa gane kanshi
Sarkin gida yabuga uwar sallama.
"Assalamuuuuuuuu Alaykum, nazoma da sarkina babban gagaruman sako amin izini" kallon kofan Muji yayi yace "shigo" dasauri yashigo yana gyara malum malum yayi wajen Riyad dake kwance kanshi akan cinyan Ammi gashinan ne kawai ya rame looking sick sosai, zubewa yayi inda Riyad yake da waya a hannunshi ya nuna wayan yace "yanzun nan commissioner na yan sanda yakira masarautan nan" da kyar Riyad yajuyo da kanshi yakalli sarkin gida, sai kawai sarkin gida yafashe da kuka yace "Mai Martaba ana kyautata zaton anga Sarauniya Rashida!" Wani kalan zabura Riyad yayi yatashi yazauna yana kallon Sarkin gida yana kokarin kara gasgata abinda yaji, Muji yace "mene mene? An ganta? Anga Rashida? Aan ina"? Sarkin Gida na kuka yana kallon Riyad yace "wasu bafulatanai guda uku sukazo offishinsu na tashar riya sukace sun tsinceta sany da kayan likitoci ajikinta an nuna musu hotonta sunce itane" wani irin tashi da Riyad yayi sai kawai yadauki key mota daya gani kan table yayi waje da gudu biyoshi kowa yayi harda sarkin Gida da Ammi dake neman lullubi da Gwaggo da Muji yarike tana kuka sosai duk aka wuce aka shishiga mota Sarkin gida na nuna hanyar police station din da akace suke, suna kaiwa parking sukayi Riyad yasauka ya shiga police station din da gudu kowa yabiyoshi Sarkin Gida na ihu "gafaradai gamai Martaba" ana kallon Riyad da babu rawani ko alkyabba ajikinsa.
Babban su ne yataresu yanuna yan fulanin yana farin ciki yace "gasunan mutanen Ranka shi dade dasukazo mana da bayanin" kallonsu Riyad yayi dasauri yayi wajen babban cikinsu bakinshi har rawa yake yahada hannayenshi biyu yace "dan Allah ku kaini wajen Matata!" kallonshi duka suke
Moddibo ya gyadamai kai yace "bismillah mu, muje Alhamdulillah tunda an sameku" yan sandan ma suka dauki mota guda, Modibbo yashiga motan Riyad, sauran suna motan yan sanda aka dau hanya Allah yasa Munir ke tuki cus Riyad can not even drive 2hrs suka bata a hanya motocin nasu ma basu karasa shiga kauyenba haka duk suka sassauka akahau machine harda Gwaggo tace baza'a barta a mota ba.
Har kauyen nasu kafin sukai wajen bukkan duk akai parking suka sassauka dagakan machine yara da manya na zuwa suna kallonsu ganin fuskokin baki, chak Riyad ya tsaya yana kallon Rashida dake zaune kan tabarma agaban bukkan matan Modibbo tana sanye da kayan fulani farin rigansu da zani, babu dan kwali akanta amman an nannade kanta da kyalle har zuwa goshinta, ga kwarya daban daban na abinci agabanta kusan guda biyar wayanda matayen kauyen duk suka kawo mata ganin takicin abinci har yanzu gashi tuntuni ta tashi kuma yunwa takeji, daya tuwo da miyan kuka, daya usulin awaran nono, daya kuma shinkafa da miyan ja, daya namomi cike ne da aka soyamata da manja, sal dayan kwaryan kuma fura, sai kallon abincin take,ayanda take kallon abincin kasan kaman batada lafiyan kal.
Nunata Moddibo yayi da hannu daga inda suke tsaye wajen masu machina da akace su jirasu yace
"gatachan" kowa kasa motsi yayi har Buba, cikin muryan kuka Gwaggo tace "meya sameta naga an daura mata tsumma aka?" Ahankali Modibbo yace
"dana cirota daga ruwa kanta afashe jini na zuba daga kanta, to tafarka muna tambayanta ya sunanta kaman ta mance komi banda haka kuma akwai juna biyu ajikinta yanzu zaiyi sati uku!" Dawani irin sauri Riyad ya kalleshi hakama kowa ke kallonshi jin abinda ya ambato ganin yanda suke kallonshi yasa Moddibo yadaga hannu yakira Hawaro dake cikin tarin jama'an yan kauyen dake kakkallonsu yace
"Hawaro taho" dasauri matashin yazo Moddibo ya nunashi yace "ni kawai na cetota daga ruwa ne amman ga asalin wanda ya ceci rayuwarta dana halittan datake dauke dashi nan Hawaro" yadan sauke ijiyan zuciya yana dafa Hawaro yace "yasan magunguna shine ke bamu magani idan muna ciwo, ya gaji magani daga kakanninsa, Hawaro gayamusu meke damunta".
Cikin hausansa da bata fita sosai yace "¡iee to!
Kanta ya bugu sosai, ta zubar da jini sosai dudda ina bata ruwan ganye dake kara jinin amman dudda haka bai ishetaba jinin sosai batada karfi zatana dinga yawan sumewa, buguwan da akama kanta yasa ta mance komi amman bazata dauki lokaci ne zata warke, komi zai dawo mata, ruwan data shiga ciki yasa sanyi ya taba abin cikinta amman tagama magungunan danake bata za'a dace, shima kan za'a dace da izinin Allah" kowa shiru yayi suna kallonta barin Riyad daya tsareta da idanu yana kallon yanda tadauki naman takai bakinta ta tsotsa tafito dashi kuma ta ijiye sai chan tasa hannu ta dauki wara tana kallo sai ta ijiye saita dangwalo nono takai bakinta tana tsotsan yatsanta, ahankali Riyad yafara tafiya kowa binshi yake da kallo har zuwa inda take gently ya tsugunna gaban tabarman yana wani irin kallonta, wasa take da abinci but jin mutum agabanta da kamshin turare mai dadi daya daki hancinta yasa tafara kallon tundaga kafanshi yana sanye da bakin crocs da dark brown yadi mai bala'in kyau sannan tadago kanta ta kalleshi hada ido sukayi ta tsareshi da idanu kaman yanda ya tsareta shima da idanu, wani irin lankwasa kai tayi tana kallon fuskanshi kaman taga abinda bata taba ganiba tanabin tundaga idanunshi har zuwa dogon hancinshi da kallo down to his lips, wani irin kyau yamata wanda ya banbanta da sauran mutanen yan garin har kayan jikinshi ma, saikuma tadauki kwaryan naman dasauri tasa hannu taciro nama daya ta mikamai, kallon naman yayi sai kawai hawaye ya cika idanunshi, ahankali yasa hannu ya amsa murmushi tamai daya bayyana duka hakoranta jin sahun tafiya yasa dasauri tajuyo takalli sauran mutanen dasuka taho, Muji ta hango yana kallonta shima rikeda soda a hannunshi na Gwaggo dawani irin sauri tashiga kokarin tashi tasa hannunta duka biyun tana kama kanta alamun yana mata zafi tana yatsine fuska dasauri Riyad yatashi wucewa tayi dasauri tana tafiya ahankali kowa na kallonta har gaban Muji hannunta tasa da sauri ta karbi soda a hannunshi tashiga kokarin budewa takasa saikuma tasake kallonshi tabashi, karba yayi ahankali muryanshi har rawa yake yace "nabude miki? Okay zan bude miki" dasauri yabude mata karba tayi takafa abakinta tass ta shanye tana lashe baki tasake saka empty bottle din abaki tana girgijewa saikuma ta kalli Muji dayakai bayan hannu yana goge idanunshi ahankali tace "bani" da sauri takai hannunta takama nashi tana budewa tana neman drink din ashagwabe tace "banimmili" wih duk yanda Muji yaso yadaure saiya kasa yafashe da kuka, he can't believe for the first time yau yanajin dumin hannun yarsa da tun tana ciki ya kada uwarta, ganin yana kuka yasa ta tsaya tai shiru tana kallonshi saikuma tafashe da kuka takai nata hannun tana gogemai hawayenshi Buba yataba bayanshi alamun yayi shiru, daurewa yayi yadena yace "nadena kuka to kinason soda?" Yanuna goran hannunta gyadamai kai tayi da sauri tana dakatar da kukan yace "to mukaje mota zan baki" ahankali tace "mota"? Gyadamata kai yayi yace "eh mota" juyawa tayi tana fadin mota mota mota mota mota tawuce wajen tabarman taxauna ahankali, tana kallon Riyad data sakemai murmushi tace "mota, mota, mota, mota" saikumai tamai murmushi again, kafin tazo dasauri takama hannunshi tarike tana kallon agogon dake writs dinshi saikuma takalli fuskanshi tace "mota?" Hannunshi Riyad yakai ahankali for the first time yadaura akan fuskanta dasauri takalleshi ta tsare idanunshi da kallo dataga suna tara hawaye, tace "sunana mota"
Buba ne ya iya katse shiru da akayi ana kallonsu yace "yamma na gabatowa, Mun gode da taimakon dakuka mana, baxamu taba mantawa da taimako da hallacin ku ba" duka kudin dake aljihunshi yaciro, shima Muji haka, duk suka ijiye Moddibo yace "a'a" Buba yace "dan Allah ku amsa" Modibo yakalli matarsa yace "kawo kayanta Hawaro kawo magungunanta" shigowa sukayi suka kawo Ammi takarbi maganin Hawaro na mata bayani, gently Riyad yakama hannunta vace "muie gida" "gida?"Gyadamata kai yayi yatashi amman taki tashi, ganin haka yasa Muji yace "muje mota nabaki soda" yanuna mata goran sodan, da sauri ya tashi ta kalli Riyad tace "soda" gyadamata kai yayi yace "muje mubaki" yana rike da hannunta suka taho har zuwa wajen machine, ahankali Riyad ya kalli Mai machine yace "bani key saika hau na wani kabiyomu" dasauri Mai Machine din yabashi sukuma yan sandan sukace muje ku nuna mana inda kuka ganota, hawa machine din Riyad yayi yajuyo yakama hannunta yarike kafanta yayi guiding nata tahau hannayenta yakama yasa ajikinshi dasauri tai lamo abayanshi kamanyar baby tana shakan kamshin dayake dakemata dadi har zuciya, yadan kallonta sannan ya kunna machine din duk sukaja har zuwa wajen motocinsu suka sassauka da sauri Muji yabude mota yadauko drink yabata karba tayi sai tahau tsalle tace "yayyyyy" riketa dasauri Riyad yayi dasauri ta kalleshi saita bashi drink din karba yayi yana mata murmushi yabude bayan motan yace
"shiga" shiga tayi yazauna yabude yabata sannan yashiga shima ya zauna Munir da Sarkin Gida suka shiga gaba akaja motan sai Kano.
Ko nisa basu yiba ta Shanye drink din takalleshi tareda bashi goran tana turo baki kaman zatai kuka alamun she wants more, cikeda so yace "I will buy for you soon" tsayawa tayi ta kafe fuskanshi da idanu sai shima ya tsaya yana kallonta ahankali tasauke idanunta takalli agogonshi da sauri tadaura hannunta akan agogon tashiga shafawa hannunshi yasa sai ya kwance Rolex din yakama hannunta yashiga samata wani tsalle tayi tana kallon agogon sai rawa take da kafa chan kuma saita kwanto jikinshi tana hamma kallonta yayi yace "kinajin bacci?" Lumshe idanunta tafarayi, ahankali yakai hannunshi kan waist dinta dasauri ta kalleshi jinjikinta yamata wani iri daban da yanda takeji since, batare daya damuba yasata ajikinshi kaman yanda ake daukan babies da za'a shayar sai kallonshi take kafin gently ya rungumeta a kirjinshi ya kankameta yana sauke ijiyan zuciya lamo tayi ajikinshi within few minutes bacci yayi gaba da ita. Kiss Riyad ya manna mata gently a forehead kafin ahankali yadaura hannunshi saman cikinta Hakkika Allah shine mai azurta bawansa da haihuwa aduk sanya yaso yakumaga dama! Sex din dayayi da ita that was unplanned and out of anger but Rashida got pregnant dashi, he slept with Haleema on so many occasions cikinsu harda ranakun ovulation nata but shiru babu ciki. Allah is the greatest of all mankind!!!
Babban private asibiti suka wuce da ita har lokacin da sukakai bacci take, daukanta Riyad yayi zai daura ta kan gado da aka kawo musu tabude ido, rirrikeshi tayi tana dirkowa daga gadon tafashemai dawani irin mugun kukan shagwaba tana shishigemai jiki shikuma duk yawani daburce wucewa kowa yayi suka shiga asibitin aka barsu ganin da Riyad kawai jininta yahadu.
Ganin haka yasa Riyad cikeda lallabawa yace "why are you crying" kallonshi tayi saikuma tasa kanta a kirjinshi tana rike riganshi tashiga makemai kafada, ahankali cikin lallashi yace "let's go inside kanki za'a duba dake miki ciwo" yakai hannunshi yataba kanta wajen ciwon hakan yasa itama ta taba kan nata tana kallonshi gyadamata kai yayi yama nurses din alamu da hannu sutafi sannan yarike hannunta tabishi ciki har lokacin tana taba kanta yanda yayi har office na
Dr dayasa kawai suka wuce wajen MRI nan ma da ihu da kuka ta shiga akayi aka fito da ita aka debi jininta akakai lab, daza'a taba kanta nanne Riyad yaga tashin hankali ba karamin zafi kan yake mata ba tadinga inu ahaka aka cire all magungunan aka mata proper dressing dan local stites din yayi aiki nan da nan aka kawo result her head its fine kawai short term memory loss ne dazai dawo with help na medication saikuma she's truly pregnant Riyad sai kallonta yake tana wasa da agogonshi daya daura mata a hannu, she's truly pregnant!.
Anatse Riyad yace "why is she acting like a baby?"
Dan murmushi Dr yayi yace "kowa da yanda memory loss ke zuwanmai, tamanta ita kanta wacece, yanda ake magana da sauransu, just manage her and make sure tasha maganungunan ta, zaku dawo next week, and make sure she's eating healthy she needs blood harda blood tonic a magungunan dana rubuta mata, she will be fine in sha Allah, zaku iya tafiya" gyadamai kai Riyad yayi yatashi daga kujera dawani irin gudu itama ta tashi takai hannunta takama nashi wannan karan ya kalleta ahankali itama haka, wucewa sukayi suka fice zuwa inda kowa yake ganin sun tattashi yasa dasauri tashiga bayan Riyad ta labe tana bubbuga kafa akasa tafara bori, magana yakeso yayi but yanda tahau buga kafa akasa yasa dasauri yajuyo ya kalleta wata patient dakecin indomie a takeaway rubber ta nunamai tana kuka tana rike cikinta bala'in rudewa Riyad yace "zakici indomie? Stop crying, stop stamping feet naki akasa haka is not good you are not alone, you want indomie wanchan?" Yanuna abincin, Gyadamai kai tayi, dasauri yace "let's go home namiki toh stop" yakama hannunta tabishi still tana waigawa tana kallon maicin indomie, mota suka wuce suka shiga Munir ya karbi takardan pharmacy yawuce saida a karbo sannan yadawo sukaja motan suka tafi gida suka dawo duka a side na Ammi suka sassauka
Ammi tashiga kwalama jakadiyanta data kira ta dafa indomie tun suna hospital da sauri tafito da plate mai kyau da indomie ke ciki hannu Riyad yasa ya amsa he hardly eats indomie amman yau yadeba yafara kaiwa bakinshi sannan yabata dasauri tasa hannu ta amsa tana daukan spoon ta deba indomie dasauri zatakai baki dasauri Riyad yarike hannunta yace "ita hot wait" raurau tayi da fuska zatai kuka dasauri Muji yace "akwai fanka agidan nan Munir?
AC nan kafin yasa abincin ya huce an dauki lokaci, she seems hungry"
Dasauri Jakadiyan Ammi tace "akwai wata yar fanka a dakinmu amman bama amfani da ita bari nakawo"
Dasauri tawuce takawo aka kunna aka saita a abincin sannan Riyad yasaki hannunta yace "ci to" dasauri ta debi indomie takai bakinta da sauri sauri takecin abinci sai yanzu takecin abinda cikinta keso kowa sai kallonta yake, kwai tadauka takai hanci dasauri tadauka tabama Riyad ahankali yasa hannu ya amsa tacigaba da ci, tasake daukan second boiled egg din daga zaunen tamikama Muji, dasauri yataho yasa hannunshi biyu ya amsa ahankali yana kallon fuskanta yace "Allah baki lafiya Rashida" murmushi tamai tacigaba da cin indomie ta tana kallonsu ganin duk sunacin egg din tasake musu murmushi, da Riyad da shi kawai takeso acikin duka mutanen, Ammi tabude magungunan dazata sha taciro mata tazo ta tsaya gefen Riyad dasauri ta kalli Ammi ganin Ammi na mikama Riyad abu yasa da sauri ta ijiye plate na abincin takama duka hannayen Riyad tarike tana makema Ammi kafada wai bazai amsaba, sosai abin yasa Ammi tai murmushi tace "to gashi ke amsa kisha" Ammi ta mika mata maganin kallon maganin tayi saikuma tajuyo ta kalli Riyad ya gyadamata kai alamun ta karba dasauri ta amsa takai bakinta tasa Riyad yasaamata bottle water tahadiye tana bata fuska duk sukai dariya Ammi tace "cinye indomie to" daukan indomie tayi tacigaba da ci atsaye kusada Riyad taki xama sabida kar Ammi tasake dawowa kusadashi, tass ta cinye which is not like Rashida that hardly eat, Ammi tace "zo muje kiyi wanka kiyi salla" sake makemata wuya tayi tana shigewa jikin Riyad da ahankali yakama hannunta yace "let's go" binshi tayi sukai stairs suna hawa sama Ammi na binsu abaya.
Da kyar ta yarda Ammi ta tayata yin wanka ana gamawa tafito daure
Showing 126001 words to 129000 words out of 139355 words