tsawon 23yrs data taso tana gani it takes time, cikin kuka tace “Maimoon I want to see those 2 women sun rike cikinsu suna kuka suma just like Mama! I want to see them having sleepless night! I want to see them having HIV suma, Maimoon even if it’s one quarter of Mama’s pain inaso Allah ya jarabesu dashi and nagani da idanuna idanba hakaba I don’t think zan taba iya mance rayuwan da Mamana tayi and move on nayi letting go of the hate in my heart” tana maganan ta tashi da gudu tadauki jakanta tayi kofa tabude tafita. Fitowa tayi tana goya jakanta abaya tafito daga building din gabaki daya she just feel like taking a walk fitowa tayi tana tafiya tana goge fuskanta hartakai wajajen bayan hospital nasu ta inda babu mutane tasan wajen sabida yawanci tana zuwa karatu awajen kasan bishiya ta shimfida dadduma tazauna gabanta sai faduwa yake she’s angry with herself sabida tasan all maganganun da Maimoon ta mata is true, tsugunnawa tayi awajen bishiyan ta duka tareda kifa kanta akan kafafunta tana kuka sosai, jitayi kaman akwai mutum a inda take dasauri ta dago kanta daidai taji saukan kaman karfe akanta kawai idanunta suka kulle ta sheme awajen a sume jini nafitowa daga kanta!!!!!
Yana zaune a fada kawai yaji gabanshi na faduwa hannunshi yadaga yakalli agogon hannunshi yaga 11:45AM there’s still 1hour plus kafinsu tashi, kasa natsuwa yayi sai fadomai Rashida take arai which is so unusual sallaman mutane fada yayi yafito fadawa na binshi abaya wayanshi yaciro kawai sai yayi dialing number Ammi dake wajenta amman har yagama ringing ba’a dagaba, wucewa flat din Ammi yayi yashigo falon Ammi na magana da Munir suka ganshi zama yayi yanayinshi yasa Ammi ta taho wajen tace “lafiya naganka wani iri ko bakada lafiya ne”? Kallonta yayi kafin ahankali yace “Ammi I feel uneasy wlh, I don’t know why” anatse tace “kayi azkar na safe?” Gyadamata kai yayi yana kai hannu yana bubbuga heart nashi dasauri Ammi tace “bani ruwa Munir kaga” da dan gudu Munir yakawo ruwa daga dinning karban ruwan Ammi tayi tabude tana kallon Riyad din still da yanda yakeyi kaman zuciyansa zai fashe yafito, fatiha kawai ta iyayi cikin ruwan takai bakinshi tace “sha” ahankali yakai ruwan bakinshi yadan kurba saikuma ahankali yace “Ammi Rashida!” Cikeda damuwa Ammi tazauna kusada shi saikuma ta rungumeshi da sauri ajikinta tana shafamai baya tace “Riyad calm down calm down, kace Innalillahi wa innailaihi raji’un” ahankali Riyad yace “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un” sai alokacin yaji natsuwa ya shige shi Ammi ta dauki dayar wayanta tai dialing number wayan dake hannun Rashida kafin tace “tashi kuje school din kaida Munir tunda you feel troubled, Munir kuje” tashi Riyad yayi yabi bayan Munir Ammi tabisu da kallo kafin ta zauna sai itama kawai taji tadamu tacigaba da kiran numberta but still Rashida bata dagawa. Wuraren 12:20 sukakai hospital din gaban hall daya ijiyeta dazun yayi parking daidai student na fitowa Maimoon itama tafito looking so worried ga waya a hannunta tana karawa a kunne alamun kira take da sauri Riyad yabude kofa bai damu da daliban dake fitowa ba yayi wajen ganinshi yasa tacire wayan daga kunnenta da sauri tace “laaa ina yini” bai amsa maganan ba yace “where’s Rashida?” Dasauri tace “wlh nima ita nake kira na nemeta har mosque bata wajen gashi test din nan damukayi batai attending ba” faduwa gabanshi Riyad yashigayi da sauri Munir yace “but when last did you see her” cike da damuwa tace “after 10 bayan mun fito daga last test munje common room ni da ita, we spoke she remembered Mama and went out” nima nabita na dauka mosque ta tafi but bata mosque duk inda nasan zan ganta ban ganta ba so I thought ta koma gida nema since ina kiranta bata dagawa” bubbugawa kan Riyad yafara sai kawai yajuya kaman wanda yasami tabin hankali yace “Munir I need to see the chief security na this hospital, I need to report my wife missing, she might be in trouble, she’s a small girl she’s…..” dasauri Munir ya rikeshi yace “Riyad calm down” “don’t tell me to calm down!” Riyad ya dakama Munir tsawa da saida attention yadawo kansu yace “I told you she’s in danger you’re asking me to calm down banga matata ba” taruwa aka farayi awajen wasu security suka fiffito da uniform ajikinsu harda mutane ana tambaya meya faru Munir ya sanar dasu Riyad yawuce sama direct CMD office. Dudda baisa kayan sarki ba normal kaftan ne ajikinshi direct yashiga office din CMD yace “ranka shi dade barka da safiya” muryanshi na rawa sosai yace “i want to check CCTV naku ina neman matana” CCtv room aka wuce suka shiga harda Munir da CMD na hospital din da ko’ina daga hall da Rashida tafito aka fara tracing nata zuwa dajin dataje wajajen babu camera amman wani van dake binta abaya gray Riyad ya nuna security yace “I think muje inda mukaga tayi” duka su fitowa sukayi sukai wajen dajin suka shiga hango jakanta akasa awajen yasa Riyadh yayi wajen da gudunsa ya taugunna daidai zai dauki jakan natane yaga jini akasa ga pen nata guda biyu datake makalawa jikin aljihun lab coat nata rawa hannunshi yafara CMD yace “call the police”Yanda Riyad kawai yaduka jikinshi na shaking yasa hannu ya dangwalo jinin ya kalla jikinshi na bashi jinin Rashida ne yasa jikinshi yafara rawa idanunshi har kukkulewa suke, dasauri Munir yayi kanshi yana dagoshi idanunshi juyawa suke kawai hakan yasa Munir yayi gefe dashi yana kokarin yama dagashi but kawai ya sumema Munir, arude Munir yace “help me” dasauri aka dawo kansu tayashi rike Riyad sukayi har zuwa wajen mota yasashi a mota yana watsamai ruwa yadau wayanshi yashiga kiran Ammi yana sanar da ita kai tsaye Ammi takira Muji ringing daya yadaga ahankali Ammi tace “something happen Rashida is in trouble” zumbur ta mike tace “meya faru Munir”? Fadamata komi Munir yayi dasauri ya katse wayan Ammi tashiga kiran Buba shima kafin itama tafita tashiga mota sai hospital din.
Ahankali yake bude idanunsa kanshi na daukan ringing yana kallon saman dakin da drip daya gani yana shiga hannunshi da sauri yatashi yana cizge ruwan hannunsa baidamu da jinin da hannun keyi ba yawuce kofa da sauri Ammi ta sallame salla ta tashi takama hannunshi tace "Riyad ina zaka?" Juyowa yayi yace "Rashida Ammi" dasauri Ammi tace "zoka zauna kaji" kasa motsi yayi jawoshi tayi yabiyota ahankali zaunar dashi kan gado tayi tace
"Riyad kasan karfe nawane yanzu is 3:00AM nadare tun Rana you were unconscious" Ammi tai dan shiru tace "ka tattara hankalinka kabani cus kowaye yayi aika aikan nan anaso aga kadawo haka ne kaman wanda baida cikakken lafiya" still kallon
Ammi yake anatse tace "da su Baffan ka, harda yan uwanka ma da Buba da yan sanda da hospital din at large are on the case, an dauki number license plate din don tracking but it's fake, duk wani investigation da za'ayi anyi babu wani lead" runtse idanunshi Riyad yayi sosai jikinshi yafara rawa Ammi ta rirrikeshi tace "police sunce suna suspecting kidnappers ne wai sabida anga matarka ce da kalan motocin dake kawota school, but ajira within 48hrs for calls na kidnappers din idan basu kiraba sai anemi next course of action".
Runtse idanunshi yayi da karfi yace "Ammi I can't sit still for 48hrs she's hurt Ammi, l've seen her blood, Ammi Rashida is in danger how can I stay still" tashi zai sakeyi dasauri Ammi tarikeshi tace
"tsaya to kaga nakira Buba" dasauri tadauki wayanta dan bataso yafita he doesn't look okay, ringing daya Buba yadauka cikeda damuwa tace
"Buba kaga ya farka yakijin magana na" dasauri Buba yace "bashi wayan" karban wayan Riyad yayi anatse uba yace "Riyad idan har ayar Al'Qur'ani gaskiya ce! Rashida zata kubuta daga hannun duk wani mugu dayake nufinta da bakin nufi ina mai tabbatar maka, wih wih ko sunso cutar da ita bazasu iyaba, ban runtsa ba addu'o'i nake, abinda nakeso dakai kaima jekayo alwala kahau kan dadduma ka gayawa Allah bukatunka Rashida zata fito" gyadama Buba kai yayi ya ijiye wayan yawuce bayi kayan jikinshi yacire ya kunnama kanshi shower kaman zai haukace yakeji kaman yayita ihu wanka yayi yadaura towel yayi alwala yafito ganin baiga
Ammi a dakinba vasa vashida closet nasho ya sakajallabiya yazo yahau kan dadduma.
Gently take bude idanunta dake juyawa sosai tanajin gaban goshinta lema lema na jini, inda take duhu sama sama takejin magana dudda bata ganin daga inda ake maganar ko inda maganan ke tashi.
"Mom, Mom dan Allah kar akasheta kawai dai aje a wurgar da ita chan wata uwar duniya" sai kuma chan taji maganan namiji yace "kashe wayan Haleema batada hankali" sai kuma taji wata muryan mace again tace "wat do we do with her"?
Daidainan idanunta suka kara lumshewa.
Ahankali ta zare P-cap din dake kanta Waziri yace
"wai ya akayi aka sako ki ne Hajara"? Murmushi Mom tayi tazauna akan plastic chair dake wajen tace "idan ba'a sakoni ba ai Babana baicika attorney general na Nigeria ba, banyi any crime ba, sannan banyi confessing anything kaman Jummai ba, sun duba footage din, basu da wani abu to hold me for, no evidence, law works with evidence, abinda Jummai tace game dani were baseless accusations, itako Jummai har cleaner data bama poison an ganota, cus police sun bincika every single mutum daya shiga dakin matan that day, akaga cleaner itane last person and tafito dawani bottle water a hannunta aka kawota tayi confessing poison ne, aka sake tracking abun back to car parked inda tafito daga motan Jummai ga plate number da komi, next week za'a kaisu court niko 2days nayi aka bada belina Papi paid everything nafito muka wuce Abuja since, I'm sure yaronchan (Riyad) bai saniba cus he was busy da amaryansa da uwarsa" Mom ta kwashe da dariya tace "but I promise he will lose everything that is important to his life starting from this girl" duk kallon Mom suke tace "I wanted na samata HIV kaman mamanta but mai HIV nan dana sani na nemeta wai tarasu" ta yatsine fuska sannan takallesu tace "the only reason yasa zanbar Riyad sabida ku da diyarku ne Wallahi!" Ahankali Waziri yace "godiya muke Hajara" ahankali tace "zan kashe yarinyar nan, na kashe Ammin sa! Na kashe Munir! Ta yanda dolensa yadawo dani mamarsa na zama mahaifiyar mai Martaba daya tak!" tai murmushi tace "ku shigo!" Wasu manyan gardawan maza ne guda biyu suka shigo wajen ta nuna musu wani lungu dasuka zubar da Rashida tace "jeku duba idan ta margaya ku dauketa kuje ku zubar idan bata margaya ba ku karasata" wucewa wajen sukayi
Sukasa hannu suka jawo kafafun Rashida da labcoat dinta da yariga yakoma blood sukakai hannuwansu hancinta jin bata numfashi yasa suka dago suka kalli Mom dasu Waziri sukace "ta mutu Hajiya" wani kalan hatsabibin murmushi Mom tayi tace "ku kawo tabarma ku nannadeta aje a zubar" dauko tabarma daya yayi yakawo wajen ya warware suka daga Rashida da hannunta ke lilo suka sata aciki suka nannade daya ya dauketa yasa awuya sukai waje da ita Mom ta kalli Waziri tace "I hope I've solved problem naku" Waziri yace "kinyi Hajara" Mommy Haleema ta zube awajen tace "uwar dakina Allah dai yajamiki tsawan kwana, kin share mana hawayen mu kin tsayama Haleema, godiya muke" murmushi tayi tace "kuwuce kutafi" wucewa sukayi.
Suna fitowa wajen cikin tsakiyar dajine da babu kowa sai machina dasukai parking gaban yar gidan dasuke ciki tafiya suke da sauri da sauri daya yarike kasan tabarman daya yarike sama har sukakai wajen wani babban kogi dayan yace "mesa zamu aka kira da Baaba yace "dayake kanada shovel dole kahaka" yayi maganan yana fincikan tabarman daga hannunshi kawai ya wurga cikin ruwan duk suka tsaya suna kallon rafin ganin tabarma kadaine yadawo saman ruwan babu yarinyar yasa suka juya sukace suka wuce.
Dirkowa wani bafulatani yayi daga daya daga cikin bishiyoyin dake ta dayan side of the river, dan tsohone haka dayar sandarsa a hannu hakama wani dan yaro ya dirko daga wata bishiyan wanda bazai wuce shekara goma ba yace "Bap...." hannunshi tsohon yasa dasauri yadaura kan bakin yaron alamun karyayi magana, sannan suka shiga tafiya suka gangara kasa wajajen rafin kafin Baban yabashi sandar yaron ya karba yarike, Baban yayi tsalle yafada cikin ruwan kusan 2min yayi saigashi yafito rikeda Rashida da ruwa ke tsayaya daga ko'ina na jikinta tsohon yajawota bakin rafin yana duddubata saikuma yashiga bubbuga mata ciki amman ko gezau kafin yarike hannunta gam na kusan minti daya sannan yakalli yaronshi yace
"kwabe riganka kabani Iro" dasauri yaron yacire yakawo yabama Baban ya karba ya yaga sannan yadaga kan Rashida ya daure kan gam gam sabida jini yadaina zuba, sannan yadauketa da kyar yana nishi dan ya tsufa ba karfi yafito yayi wajen shanayensa yadaura Rashida akan daya sannan yashiga kadasu suna tafiya yaron yace "Baba bata mutu ba"? Dasauri Baban yana gudu gudu yana kada shanun yace "jijiyoyinta na motsi" da sauri sauri gudu gudu suke kada shanayen, kusan tafiyan awa daya sannan sukakai wata karaman karkara ta yan fulani, ga bukkokin su ahaade in circles dabazasu wuce 30 ba, duk inda zasu wuce yangarin biyosu suke ganin sun kawo wata akan shanu har zuwa kofar gidansu duk suka taho suka tayashi aka sauko da ita aka shimfide kasa, Dattijon yace
"ina Hawaro"? Da sauri aka hau kwalama Hawaro kira. "Hawaro, Hawaro" chan saiga wani dan matashi yataho yana sanye da kayan Fulani harda hula da sanda a hannunshi ya bullo daga daji, mutumin ya nuna Rashida dake sheme a kasa yace
"kaga yanzu mukaga wasu miyagu na jefata a rafin buluduwa, naga kaman likita ce kaga kayansu ajikinta, kaga tasamu lafiya kaida ita saiku zama likitocin garinmu" dukawa matashin yayi ya dago kan Rashida yana warware daurin da Dattijon yamata, yadaga gashinta ya kalli ta wajajen keyan dayaga ya tsage sosai da sauri ya maidata ya ijiye yatashi saiyahau gudu kaman tsuntsu ya shiga daji yana ihu a izamin garwashi akawomin, wasu ganye ya tsinko sannan yafito ya shiga daki yafito dawasu kananun wukake da allurai da zare yana zuwa ya jiyesu acikin gareashin da aka kawomai dan su
kone alluran sannan yaduka yadauki dutse yana daddaka ganyen yana gamawa yatashi yadauki alluran dake wutan ya goga a jikin dutse mai tsafta sannan yasake warware zaren yace "riketa Modibbo" dago Rashida Dattijon yayi yarike shikuma yazo ya dage gashinta yasa wata wukar da itama ya kona awuta ya aske gashin wajen kadan sannan yafara mata dinki kusan stitches guda 6 sannan yadauki ganyen daya daka ya mammanna awajen sannan yakoma daki yafito dawani kyalle yashiga daurawa a kanta yana zagayewa ya daure tamau sannan yakama tafin hannunta yasa yatsushi biyu aciki ya kama sannan yafito da yatsun yadaura a julyan gefen wuyanta saikuma chan yabude kwayan idanunta ya kalla kafin yakalli Modibbo da sauran mutanen garin dasuke tsaye sun zagayesu yace "juna biyu ke gareta ai Modibbo da bazai wuce kwanaki sha hudu ba!" Shiru duka mutanen karkaran sukayi kafin yace "sa mata su kaita daki achanza mata kaya kar sanyi yashiga kasusuwanta kar abin cikinta ya shiga hatsari ruwan rafi baida kyau ga mai karamin danyen gudan jinin ciki" dasauri kafin Modibbo yace wani abu da matansa da sauran matan garin sukazo suka dagata cikeda care sukai ciki da ita Mazan kuma suka jaye gefe dan shawara da maganan yanda za'ayi.*SANYI DA ZAFI*

*EPISODE 67



Duk tsaitsaye sukayi kusan Moddibo shine babba agarin, so ana jin maganansa sosai, shi likitan Hawaro ne yace "Modibbo yaya za'ayi yanzu?
Yanda takeda juna biyun nan da mijinta kenan yakamata anemo yan uwanta" dasauri daya daga cikin jama'an yace "binni zamu shiga muje wajen yan sanda mu fadi abinda yafaru" dasauri wani daga cikinsu yace "amman kuma likitoci nada amfani ga al'umma mesa bazamu barta taji sauki ta taimaka mana ba da likitancin zamani, takoyama Hawaro abubuwan zamani na lafiya amatsayin tukuicin cetota da mukayi saita tafi, yanzu rayuwanta na cikin hatsari idan mukaje muka fada mutanen sukazo har nan suka kasheta fa"? Sai abun yakoma wannan yafadi nasa wanchan yafadi nasa gyaran murya Modibbo yayi yace "ku dakata" duk shiru sukayi suna kallonshi, cikeda dattaku yace "na farko dai rayuwan yarinyar nan nacikin hadari gata da kankanin ciki tareda ita, idan kunga gardawan dasuka daukota a tarbama a hadamu mu goma sannan za'a samu daya" yasake yin shiru sannan yace "abarta tafarfado muyi magana da ita da kanmu sannan tafadi mana waye mai gidan nata saimuje da kanmu mu shiga binni mu nemosa yazo ya dauki matarsa gudun kar miyagun su biyota, idan tanaso zata iya koyama Hawaro likitancin zamani saitayi idan bataso saisu tafi kun yarda?" Atare kowa yace "eh" hakan yasa suka zauna suka shiga zantawa yana kara basu labarin yanda yafada kogin.
**
Wasa wasa yau kwana 7 babu Rashida babu labarinta kowa yakasa gane kan Riyad, labari yabi ko'ina afada Sarki na neman haukacewa sabida anyi kidnapping matarsa haryau kuma kidnappers sunki kira, Haleema karan kanta saita fara regretting komi cus attention datake nema wajen Riyad ma tarasa, he's not even himself, komi ya tsayamai chak baya baya gane komi, sannan komi no fada ya tsaya allbecause of shegiyar Rashida.
Ammi dasu Buba da Muji da babu inda bai shigaba har wajen yan sanda saida yaje yaga koto Jummai ce yaga tana kulle but ansaki Mom yazo yafadi Riyad kanshi baya wajen su Ammi ke mamakin yanda aka saki Mom, an baza hotunan Rashida ko'ina da news da tv ana cigiyanta, Riyad yadawo abin tausayl.
Ahankali take bude idanunta dasuka mata shegen nauyi tana kallon saman bukkan dakin kafin gently tayi yunkurin tashi taji sharp pain akanta dayasa ta daddage ta kwala uban ihu. "Wayyyyyoo kaina" da gudu aka shigo dakin wata yar matace sanye da kayan fulani yaro goye abayanta tana kallon Rashida dake ihu sosai tana kokarin cire kyallen da aka daure mata kan dake mata shegen azaba, da sauri matan takama hannunta tarike tace "yakuri, sannu sannu, Hawaro yace kar abari ki kwance idan kin tashi saiya zo dakansa yakuri" fashewa da kuka sosai Rashida tayi tana rawa da fuskanta tace
"kaina zafiliiii" daidai nan Hawaro ya
Showing 123001 words to 126000 words out of 139355 words