, Regular payment₦300 vip payment₦500 special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 ban yarda kika karan ta mun idan baki biyani ba , haka kema don Allah kar ki fitar mun ,duk wanda ya karanta bai biyani ba shida Allah._


Ina kuke masoya ga sabon littafi Mai ɗauke da darussa na rayuwa tare da nishaɗantarwa daga Alƙalamin Maman nusaiba...kunsan sunan littafin kuwa? A'a bamu sani ba ,nasan wannan shine amsan ku gare Ni, ABBA NE! littafin complete zaku same shi Inshaallh akan ₦300 masu buƙata zaku na iya tuntuɓar wannan Number +966599791573 domun ƙarin bayani mun gode!

***

Jin kalamin Hajiya babba yasa Jikin Umma yin sanyi ƙalau. Kiyi haƙuri Hajiya ba nufi na...Ni dai ya isa ya isa kawai jeki abinki kubar Ni da Sumayya. Umma ce ta tasa su Yusrah suna barin falon Hajiya babba yayin da Hajiya ta tada Sumayya da har a wannan lokacin kuka take yi sosai kaman ranta zai fita. Uwar ɗakin ta ta shiga da ita ,tana aikin rarrashin ta daban baki akan babu yanda zasuyi , an riga an ɗaura Auren nan haƙuri tayi ta ba Sumayya wanda a haka ta shawo kanta . Tun daga wannan yammacin har Washegari Sumayya bata fita ba ,a ɓangaren Hajiya Babba ta ƙwana. Sai da Safe ne ta tashi bayan ta kimtsa tayi karin kumallo ta nufi ɓangaren Mom Juwairiyya ta fara gaishe da ita , wanda har ila yau babu wani fara'a ko harka tsakanin su ...a haka ta nufi ɓangaren Umman ta , a falo ta tadda ita Khamal na gyefen ta sai fidda wani irin daddɗan ƙamshi yake ,yana sanye cikin ƙanann kaya , kallon Umma tayi tana gaishe ta ,wanda batare da ta nuna mata komai ba ta amsa kaman babu abun da ya haɗa su jiya.... Kaman ba zata gaishe da Khamal ba ,amma ganin Umma ya da Abba yasata don dole gudun kar ta ƙara shan wani marin tace " Yah Khamal Ina ƙwana! Lafiya lau Sumayya ,ashe yau a ɓarayin wancen tsohuwar kika ƙwana?... Gyaɗa masa kai tayi bata re da ta kalle shi ba ,a zuciyar ta tana mamakin ranin hankali irin na Khamal da yake mata. To kiyi a hankali kar tayi maki wayo ta ƙwace Maki Ni , don tayi tayi nine nace ina?? Sai mai jini a jika...dariya Umma da Abba suka sa suna cewa " Au shakiyanci n naka har da Hajiya babba? Koda yake kun fi kusa.


Dariya shima yasa yana miƙewa da cewa " Abba na tafi yau ina Son na leƙa Company na ,shigar baxata nakeson masu. Mashaallh Hakan ai yana da kyau ,don naji ka daɗe baka je ba ,kana can na Lagos . Eh Abba. Ai na Umma ne wancen . Amm Abba ? Ya kira sunan Abba yana koma tare da zama. Kallon sa Abba yayi yana cewa " Ina sauraren ka. Abba ina so ne mu tare a gidana na Lagos saboda Sumayya ta cigaba da kulawar ma Umma da Companyn can sai na rinƙa duba mata. Eh ƙwarai haka yayi ,kasanar mawa Hjy babba wannan maganan Ni xan zamuyi magana da Daddy. Hummm hummm bkmai ai bakomi shikenan Sumayya ke maganan tana ƙwatse Abba da ya nuna ya gamsu da tafiyar tasu. Kallon ta Umma tayi nan tayi saurin yin shiru sai taɓa baki take tana shirin kuka , wanda hakan yasa Khamal shagala da kallon ta , sosai yake jin Son ta a zuciyar shi , musamman yanayin wautan ta komai nata a tsiwace takeyi da yarinta. Khamal shiknn Allah ya dawo da kai lafiya. To umma . Yayi maganan yana miƙewa da dakatawa da kallon Sumayya yana barin falon . Da ido Umma kebin shi har ya fiche,wani irin tausayin Khamal take ji yana kamata ƙwarai ,tabbas tasan Allah ya jarabe shi da zazzafan Son Sumayya ,Wanda Shima faɗin da yake a baki na zuciyar sa tafi hakan . Muryar Abba taji yana kirar Sumayya da cewa " Mama na taho muje muyi magana. Cike da mai da ƙwalln idon ta tace " To Abba. Ta miƙe tare da bin bayan shi. Da ido Umma ta bisu duka , tana faɗin Khamal ne abun tausayi ba kya ba,ke naki shashanci ne don baki san So ba.
••••A falon Abba ne ya zauna sosai yana yi ma Sumayya magana da rarrashi akan auren ta da Khamal ,wanda goge hawayen ta tayi tana cewa " To Abba na shikenan na haƙura ,zan zauna dashi tun da ya Aure Ni, Amma ina Son Fahad Shima. Murmushi Abba yayi cike da girma yace " To ɗana Khamal Fah?. Kai tsaye Sumayya tace " Shima ina Son shi ,amma nafi son Fahad. To kiyi haƙuri Mama na ki zauna da Khamal Kinji. To Abba .

****

Kallon shi Daddyn nashi yayi yana cewa " Fahad me kace?? Eh Dad ka bar zuwa gidan su Sumayya ka dakata , na haƙura a baki da Son Sumayya ,Amma azuciya ba xan taɓa daina Son Summayya ba har numfashi na na ƙarshe Momy Kar dad yaje , Aminina ya Auri Sumayya. Fiddo da ido Mom tayi waje tana cewa " Khamal? . Gyaɗa mata kai yayi kawai sai wani irin zazzafan ƙwallah ya fara bin kuncin sa. Dad ne yakai hannu yana bubbuga kafaɗan sa alamun rarrashi kamin yace" Kayi haƙuri Fahad taka ƙaddarar kenan. Yanda nake jin yawon Amboton sunan Sumayya a bakin ka , nasan ba zaka iya zaman Nigeria ba , ko ka zauna ba zamu ga kan gadon ka ba. Don haka Ka shirya gobe zaka bi jirgin ƙarfe 2:00pm zuwa saudi Arabia kaje ka zauna da Ammien ka Nauwara (matar Sheikh mufti😜😂 ) tare da iyalan ta nasan xasu fi ɗebe maka kyawa kusa ,ka manta da komai... Ɗaga mawa Dad kai yayi yana cewa " To dad zan tafi , xan dawo a lokacin dana manta da raɗaɗin da kuma zugin Son Sumayya a zuciyata ,a wannan lokacin xan fara sabuwar rayuwa tamkar wanda a ranan ya buɗe idon sa yagan sa a duniya...amma Momy xanyi iya mantawa da Sumayya ba! Dafa shi mom tayi tana goge hawayen dake sauko mata. Sorry my Son Kayi haƙuri kaji Fahad , tun kana yaro nasan ka da jarumta yanxu ma ina so ka ƙara plz . Miƙewa yayi yana cewa " Dad kasa Amun ticket na tafiya bana son na ƙara ƙwana a Nigeria .


****

Tun safe Sumayya take kai kawo a gidan , don tun yanxu tafara ganin shiga da ficen gidan yayi yawa alamun an fara shirye-shirye. Burin ta a yanxu bai wuce taga Fahad ba , wannan yasata tunani barkatai , ciki harda tunanin ko ta samu Khamal yakai ta gidan su Fahad ne? Sai kuma ta girgiza kai tana cewa " No baxai yiwu ba hakan. Burin ta kawai tagan ta gata ga Fahad. Brk da sfy Ranki yadaɗe . Jin Muryar kaman bana cikakkiyar bahausa ba yasa Sumayya juyowa ...yowa tace tana kallon Oruma. Am Jidda don Allah wani taimako nakeson kiyi mun . Ohk Inajinki . Amm kinsan Yah Fahad ko? . Eh nasan shi Abokin Sir Khamal. Yowa eh shi ,don Allah kin san gidan su ki kaini. Buɗe baki Jidda Tayi tsoro ya kamata , cikin wani irin gurɓatacciyar Hausan ta tace " Sumayya xaki sani a matsala ,kar ki sa a koreni a aiki na pls.
Hi haƙuri Jidda Wallh bBu Mai korar ki ai baxan bari kowa ya sani ba.pls inkin sani ki taimaka mun ki kaini. Yanxu mu samu mai adaidaita. Eh na sani a G.R.A suka zaune. Ɗauko bayafi mu tafi. Juyawa Sumayya tayi tana nufar Apartment ɗin Umma ,haka itama Oruma tayi ,a tare suka fito kaman sun haɗa baki duka hijab jelbab suka saka. Ficewa sukayi daga gidan ba tare da Sanin kowa ba.

***

A bakin gate ɗin gidan da tun daga farko CCTV ke masu sallama suka tsaya ,kai tsaye gidan suka shiga ,wanda sai da security sukayi laccesu kaman wasu ɓarayi....kana su bar su suka shigo...a farfajiyar gidan ne suka ci karo da Mom da Fahad dake saukowa da briefcase a hannun sa cikin shigar sa ta suit oh my God yayi matuƙar ƙyau ,dama shi Allah yayi sa ɗan gayu ne ƙwarao kuma sosai yake ɗaukar wankan. Shi yasa ƴammata kebin sa basa nadama don yayi lalata dasu ,su suka fi Son yin hakan fiye dashi.

Sauke baƙar gilashin idon sa yayi yana kallonta kana yace "Summy ta! Hawaye n da tayi ta dannewa ne suka fara mata ambaliya. Fahad Ina kuma zakaje?. Juyowa Mom tayi tana kallon wacce ya kira Da Summy.Ohk kece Sumayya n kenan?". Gƴaɗa mawa Mom kai tayi ,wanda Fahad Kallon ta yayi idon sa na sauyawa zuwa jah sosai . Sumayya a yanxu ke matar Khamal ne ya akayi kk fito har kika zo nan?. Garin Baya nesa , kamar yanda kace kana Sona nima Ina Son na Fahad. Kuma baxan daina Son ka ba ,yanda kayi haƙuri ka rungume ƙaddara ,nima hakan xanyi don bayan da xanyi ,ka tafi kayi nisa dani , amma ka sani baxan taɓa mantawa dakai ba ,ka nuna mun so a sa'ilin da nake ba kowa ba. Na gode ƙwarai da hakan ina Son ka Fahad har Abada abadan Abada har iya numfashina na ƙarshe ,na Barka lafiya Allah ya kiyaye hanya. Juyawa Sumayya tayi cikin sauri tana barin gidan ,wanda yasa Mom bin su da kallo.wanannan wani irin so ne? Khamal , Sumayya , Fahad? To Allah mun bar maka komai. Shine abun da Mom tace tana gani Fahad ya shiga Moton yanasa hankie yana goge ƙwallah. Oruma ne ta juya tana bin bayan Sumayya da suna shiga me napep ɗin yajah su zuwa TK road. Mom kuwa shuga tayi moto don yima Fahad rakiya zuwa aviation.

***


Abu kamar wasa yau kusan kwana baƙwai kenan da faruwar komai , wanda a ranan ne Sumayya dasu Billy suka shirya don tafiya garin su Billy komawan ta gida. Wanda mahaifin ta yayi farin ciki da ƴan uwa ,kwana ɗaya sukayi suka nufi gidan su Diyana ,itama nan sukayi kwana ɗaya , sannan daga ƙarshe suka nufi garin Bauchi zuwa gidan su Laurat .zokiga farin ciki wurin mahaifiyar ta sa masu Albarka marar iyaka ,ta tsine mawa ɗan Asabe ba iyaka. Lagos suka nufa , wanda Gidan Ƙanin mahaifin Safna suka je , da har kotu yakai Barau faɗa sosai ke tsakanin su , mutum ne babba da Allah ya azurta shi a dangin nasu ƙwarai kuma shine ƙaramin su. Ganin Safna yayi matuƙar farin ciki tare da iyalan shi ,nan abu ya dawo sabo ,daga masu kuka sai kuka. Nan Hjy Juma ta amshi Safna tare da haɗata da iyalan ta....basu kwana ba suka dawo garin Zaria ,a gidan Hjy Adiyya suka kwana a ranan Sumayya da Yusrah ,kana washe gari suka dawo gidan Umma. A cewan su zasu sa rana bayan tarewar Summy su taho Lagos..wannan ya faranta ran Safna don ita tasan gari guda zasu zauna. Yusrah ce da Sumayya kaɗai suka dawo gidan ,wanda a ranan ya kasance saura kwana uku tarewar su.

****

Binafa kinga wannan hayaƙin da kike turara gabanki dashi , to wallahi ko shine Meye bazai gane kin taɓa gantali ba , don ko baki faɗa ba nasan kin san namiji...Shi kuma wannan da kike hayaƙe fuskar ki na mallakar Hjy Juwairiyya ne, don kin san inba don aikin wannan bokan ba ,yanda take Son Khamal baxata taɓa yarda ya aure ki ba...tun da itama tana da Son kan ta. Shi yasa nasa boka ya mallake mun ita , komai sai abun da nace mata. Kuma ina maki albishir da kinga wannan zoben da boka yace kisa, tsawon wata guda ,a ranan da kika cire a wannan rana Khamal zai saki wannan shegiyar yarinyar.... Hjy naja'atu ta ƙare maganan tana kallon Binafa da ke ta murmushi tana gyaɗa mata kai...............






*AUNTY AISHA MMN TEDDY*
[9/27, 11:27 AM] ANTY AISHA MMN TEDDY: _🕊️MY LADY BOSS🕊️_
_42-43_


_Littafin my lady boss na kuɗi ne , Regular payment₦300 vip payment₦500 special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 ban yarda kika karan ta mun idan baki biyani ba , haka kema don Allah kar ki fitar mun ,duk wanda ya karanta bai biyani ba shida Allah._


Ina kuke masoya ga sabon littafi Mai ɗauke da darussa na rayuwa tare da nishaɗantarwa daga Alƙalamin Maman nusaiba...kunsan sunan littafin kuwa? A'a bamu sani ba ,nasan wannan shine amsan ku gare Ni, ABBA NE! littafin complete zaku same shi Inshaallh akan ₦300 masu buƙata zaku na iya tuntuɓar wannan Number +966599791573 domun ƙarin bayani mun gode!

***

"Ammie Wallahi ada ban kawo aikin wannan bokan zaiyi tasiri akan Momyn Khamal ba ,don sau tari gautsin ta ya biyo , kinga ko tun da yayi aiki akan ta ,shima ina shiga gidan sa zamu tabaybayo sa. Ƙwarai kuwa da gaske , Khamal ɗin wa? Shi har ya isa ,ai tun da yayi tasiri ma uwar sa to shi zuwa ɗaya xamuci nasara akan sa bama ita ba da mukayi mukayi sai da ƙyar... Humm nisawa Binafa tayi tana gyaɗa mawa Hjy Naja'atu kai kana tace " Mom zuwa Anjima zanje MMT COLLECTION tana da magunguna da dama ,kaman na buɗewar gaban mace , wata daga haihuwa shikenan , wata kuma ta rasa budurcin ta ta hanyar fyade ko sharrin yaudarar ɗanamiji , aƙwai na tradition da kuma na bature , supliment da zai ciko da gaban mace a nan take kina sawa xaki koma gam. Allah ko Binafa ? Yanxu wurin ta xAki je kenan.


Eh Ammie don yaro Khamal wanda idon sa yake a duniya dole sai nayi gyara kaman banayi. Ai yana da kyau hakan maza jeki sau ra kwana kaɗan ...Kuma Binafa bance ki raga mawa wannan yarinyar ba, indai kika raga mata har kika bari wani abu ya shiga tsakaninsu to gaskiya baki biyoni a kissa da makirci ba. Humm Ammie kar ki damu nice fah dai Binafa. Dariya Hjy naja'atu tasa tana faɗin Allah yayi maki Albrka.



Yau da gobe ba wuya ga mai yawancin kwana , gashi yau gida dangi da ƴan uwa sun cika gida , ana bikin ɗaura Aure tare da tarewaa. Tun safe Sumayya bata bude ƙofan ta ba har wuraren hantsi don sha biyu tayi ...kana su inna tani da Aunty jummai suka nufo bedroom ɗin nata don tafe suke da mai kimtsa amarya. Haushi ne duk yabi ya ishe sumayya , ganin irin magani da dafedafen da ake bata...Aunty jummai faɗi take " Ku biyu ne Sumayya gwara ki saki jiki kici wannan dahuwar kema yajiki zam-zam don mazan yanxu ba irin iyayen ku bane. Inda suka fa jin daɗi nan zasu manne. Haushi ne yasa Sumayya cuno baki a zuciyar ta tana faɗin to ya manne mawa ne?. Haka tayi ta cin komai ba musu. Sai a wurin makeup ne tace ita sam bata san wannan ba . A bar mata fuskar ta a haka. Kaya ma da xa'a sa mata namu na Hausa cewa tayi ita sam bata san wannan ba. Haka suna gani tasa jallabiyar ta tana naɗe kanta da mayafi ,yanda kasan ba amarya ba ....sai dai tayi kyau sam batayi shigar amare ba ,acewan ta ita wannan ba Aure ba ne , dole ne akayi mata. Ƙarfe ɗaya aka ɗaura Auren Khamal da Binafa ,wanda jin haka yasa Hjy naja'atu kaman ta zuba ruwa a ƙasa tasha...Nan aka sanar da cewa " amare zasu bi jirgin ƙarfe biyu zuwa Lagos ...nan Fah take aka fara shirye-shirye. Khamal mai mutane sunan dai ba kirki ne dashi ba ,amma Allah yasa masa Farin jinin Mutane kowa Khamal wannan dalilin yasa Su manager Mubarak Al-mustapha da Su PA tun ana gobe suka taho Zaria..Haka sauran mutanen sa,abokan nan sa kuwa na taƙadirin shi na Malesia a ranan tarewar suka sauka a gida Nigeria , wanda a cewan su Har Lagos sai sunje. Kasancewar duk wata nasiha an yi mawa Sumayya yasa Umma bata kuma cewa komai ba sai hannun ta data kama tana mata addu'a , wanda nan take Sumayya tasa kuka harda jijjiga wani irin Haushin Khamal take ji a zuciyar ta cewa take " Tun da kazo kake mun yankan ƙauna ,ka rabani da Umma na na ɗan ƙanƙanin lokaci ...ka rabani da masoyi na kuma. Sai kuka ƙanƙame Umma tayi sam taƙi sakin ta ,wanda Umma duk kawaicin nan nata a wannan karon itama rungume ɗiyar Tata tayi. Sumayya kiyi hakuri banda faɗa nasan halayyar ki. Umma baxanyi ba ai na faɗa maki kuma nayi Maki alƙawari baxan nema ba ,sai dai idan an taɓoni baxan yi haƙuri.... Ta ƙare maganan tana raba jikin ta dana Umma da jikin ta yayi sanyi qlau. Hajiya babba kuwa irin turarukar da tayiwa Sumayya guxuri don tasan Jikan nata da Son Ƙamshi shiyasa Sosai tayi mata haɗi har da na ƴan mai duguri...


A airport ne ko wacce moto aka iso tare da Amaryar ta. A ɓangaren Sumayya Aunty jummai ce kaɗai xata bi su ,saboda irin tafiya mai nisa ba aɗeban dangi. Haka a ɓangaren Binafa innan ta ɗaya ta biyo bayan su. Airport kuwa Khamal da Abokan sa sun cika sunyi tanƙam kowa na jirar isowar Amarya. Binafa ce ta fito cikin wani irin tsadaddan kace maroon , Jikin ta ya sha adon gwala gwalai....fuska kuwa make up ba'a magana dagani kaga Amarya. Wannan ce amarya ? Tambayar da Abokan keyi kenan. Ganin ta ɗan rufe kantata da mayafi mai sharashara. Mashaallh babban mace kenan ,abun da suke faɗi kenan. To wai ina Uwar gidan? Tahir ne ke tambaya ganin Tun da moton ya tsaya Sumayya ta tirje sam taƙi fitowa. Aunty jummai tayi har
Showing 21001 words to 24000 words out of 42765 words