leka dakin,Iklas da Ummi kwance gado daya suna ta baccinsu,karfin hali Omar yayi ya matsa kusa da Iklas,a hankali ya kama tashinta ta hanyar Sosa mata kunne,
Firgigit ta bude idonta,alama yayi mata da tayi shuru,saboda Kar ta tonawa Kansu asiri tayi luf tana kallon Omar,tasan idan Ummi ta gansu fadan har Ita.

a hankali yayi rada ki taso muje dakina,kafada ta noke tana masa nuni da Ummi, kara rada mata yayi ni zakiji tsoro,nine mijinki,itama rada masa tayi ummi zata kamamu.

Tsaki yaja a hankali ki taso kawai malama na fada miki,ni lokacin da kike zuwa kina taba min jiki hanaki nayi?lokacin ma fa ban San ke matata bace amma na kyaleki,murmushi Iklas tayi,harara Omar ya watsa mata,ki taso ki biyani jikina da kika dinga taba min,mijinki ne ni Allah ya konaki kinki bin umarnina kinji dai nasihar Ummi ko,
Tsorata Iklas tayi kar Allah ya konata fa,Omar ya kara da kizo ko na kwanta anan Ummi ta kamamu.

Da sauri Iklas tace a'a dan Allah zanzo muje ni,kar ka jawo min masifar Ummi dan laifina zata gani,muje kawai,mikewa tayi a hankali kamar barayi sadaf sadaf suka fara tafiya,Ummi kuwa dake bacci motsi taji kusa da ita ta farka, mikewar da Iklas tayi shine ya tashi Ummi da ga bacci,

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Iklas yanzu iya shegen da kika dauka kenan,nasan Umaru bazai aikata ba ke kika kirashj a waya,dawo ki kwanta ko wlh na saba miki,mu zaku mayar yan Iska, tuni Omar ya bawa Ummi hakuri yace Ummi cewa tayi nazo na dauketa tafi son dakina.

Salati Ummi ta kara saki jeka Umaru Allah maka Albarka ai nasan halinta,ficewa Omar yayi da sauri cike da kunya.wlh Ummi bani nace yazo ba cewa yayi.....rufe min baki Ummi ta kai mata duka dan ubanki kwanta ki rufe min baki,Iklas kija mutunci ki ina fada miki namiji ba dan goyo bane.

Rushewa da kuka Iklas tayi wiwi take kuka haushi takeji Omar ya kala mata sharri ya zame kansa gashi ya barta Ummi tana jin haushinta,shi kuwa ya wanke kansa tas wurin Ummi.

Gajia tayi da kukan ta shige toilet tayi Alwala ta fara nafila da adduarta Allah sawa Omar sonta,ya sota ita kadai a duniya,Allah bata ikon yi masa biyayya yasa su zamewa junansu Alkhairi.
Tana idarwa harda karantawa Omar suratul Yaseen Allah sa masa sonta,ita gani takeyi Omar baya sonta shi yasa yanzu yasa Ummi tayi mata fada.da yana sonta ai bazai zame Kansa ya kyaleta ba.
A ranta tace Allah kaimu gobe lfy Allah sai na rama zai San nice Gomnati.
Washe gari Iklas da fushi ta tashi cike da shirin ramuwa kan Omar shima sai tasa an masa fada yaji kunya.




Pls kuyi hakuri da wannan bazan iya forcing kaina nayi muku 2 pages ba,typing akwai wahala ga shi akwai schl ba time,Ku danci wannan tuwon Ku kora da ruwa kuyi bacci.
Tnx alot readers ..




Asmabaffa[4/10, 9:20 PM] El-hajj💥: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
â“‚â“‚â“‚

135-140



By
Asmabaffa




Jira kawai Iklas takeyi taga ta inda Omar zai bullo amma shuru,Mama ce ta fito cikin shiri,tashi maza dauko mayafi zamu fita,ba shiri Iklas ta fito dauke da mayafi,driver ne ya kai su Iklas wurin wani saloon,Mama ta biya kudin komai yanda za a tsantsare Iklas,
Komai da ya dace iyaye suyiwa yarsu Baffa da Mama sunyiwa Iklas kayanta babu banbanci da na su sadiya sai dai color daban,na Iklas Dark brown ne komai,haka kayan kitchen Mama tayiwa Iklas Wanda ya take nasu sadiya,kayan gyara Dana kamshi babu abinda ba a siya mata ba wadatacce,kayan yaji da sauransu du an shirya mata part dinta,

Allah ya taimaki frnds din Iklas da wasu dangin Mama har aka gama shirya kayan Sahar bata nan,kayan sawar Iklas du an kai gidanta an shirya mata lefe kuwa Baffa ya bada kudi Mama ta hada mata akwati 8 ba abinda babu masu tsadar gaske da kyau domin English wears kaf da wasu tarkace a Russia Mama ta hado su murna Iklas keyi za a sha wanka,Omar kuwa gagarumar walima ya hadawa frnds dinsa maza a wani katafaren waje,ranar kai Iklas ranar za ayi walima.

Omar kafin ayi jeren Iklas har ma'aikata yasa suka kara yin adon golden jikin ginin Wanda yafi na da iri iri,ko ina sai ka rantse adon zinari akaiwa ginin wajen Iklas, komai dark brown da Golden ne,har labile idon gari.tsayawa fada muku yanda part din Iklas ya hadu iya haduwa karshe ya zarta tunanin me tunani,sai na gama novel din nan kaf ban gama ba,
Iklas koda suka dawo ma Omar na busy bata Ganshi ba,Iklas manya tsabar gyara duk inda ta zauna kamshinta sai yayi kusan 1wk bai bar wajen ba,ko gidan mutane taje to sai tabar musu tsarabar kamshinta.

Washe gari dangin su Mama mutum biyar sunzo raka amarya gobe,haka dangin Baffa,ga frnds din Iklas zuga guda,Rana ta Uku ranar kai amarya,da wuri Iklas taje wurin Saloon da lalle,masu mata lallen mutum uku ne ,sai mai gyara gashi,Karfe 4pm Iklas driver ya dawo da ita,kunga Iklas kuwa yanda ta koma?tab zankadaziyya kenan,dama gata fara kwal,ga lalle yayi kyau over,
Tana shiga room dinsu mero lallausa tana jiranta,nan itama ta hau nata gyaran,gashi sai bata abubuwa akeyi ta shanye wannan ta cinye wancen,Lallausa da Mama sun koya Iklas harkoki sosai na mata da ake amfani dasu,Mama da Ummi sun hada mata wasu da yawa an kai gidan,store kuwa both na Iklas Dana Sahar an dankareshi da kayan abinci haka kitchen ma.

Karfe biyar su Omar suna can suna Walima,amarya an shiryata tsab jiran angwaye kawai akeyi,Ummi da Maman saleem sun sa Iklas gaba da nasihar bin miji,idon Iklas Kamas ko kuka babu tunda wajen Omar ne bata da Matsala.
Ummi tace to kinji dai abinda muka fada miki kishiya gareki wlh kija mutuncinki,ban son tsokana nasan halinki,kuma ba a dambe da kishiya jahilci ne,ki kiyaye,zaman aure ne ba jin dadi kikaje ba ibada ce,dole sai da hakuri da juriya,ki farantawa mijinki,komai ba musu,sannan kinji na rantse Iklas kikaje kika tashi hankalin Omar da fadace fadace da kishiya Allah sai na saba miki,
Ki rike mijinki nasan dole kin San dai dai da rashin dai dai abinda ya shige miki duhu ga Mama ga ni ki bugo mana waya,haka dai suka dinga yiwa Iklas fada,kawayenta ma sai nasihar iya shege suke mata,
Amarya banda rowa a wangalewa oga cinya etc.
5:30 yan daukan Amarya suka zo,motoci Jere na alfarma aka dauki amarya da yan rakiyarta zuwa gidanta,Iklas fa har yau idonta tarwai har hira takewa angel kawarta,,
Gida ya hadu kowacce sai kallon tsaruwar gidan sukeyi,gidan Omar dan gayu gidane na alfarmar gaske,upstairs kadai part uku ne,haka downstairs ma karshen haduwa ce,bare compound ba a magana,kayan da akayi ginin Omar wasu da yawa basu zo kasar mu Nigeria ba,domin turawa ne sukayi masa ginin gidan.

Sahar da kawayenta yan magaa tantiran yan banaline da codine ne suna Palo sai shewa sukeyi hade da habaici kala kala,idan suka ga wata cikin yan kawo amarya sai kaji zagi da ashar na tashi.

Kowa tausayawa Iklas yakeyi sabo da Sahar da suka ga abinda takeyi,ita kanta Iklas ta shiga damua sai taji duk ta tsorata,gwiwowinta sunyi sanyi,gashi bata San ya Omar zai karbeta ba tunda ba sonta yakeyi ba,
Ummi na kusa da Sahar sunyi jugum jiyo muryar Sahar da sukayi tana ta zunduma Ashar.Iklas ji tayi dama bata yarda an daura aurenba,tasan Sahar watarana maybe kasheta ma zatayi.tsoro ne ya kama Iklas,amma har yau zuciyarta bata yi raunin da zatayi kuka ba,

Yan kawo amarya duk sun mata sallama sun tafi har Ummi amma still Iklas ko kuka babu.
Tana zaune tana tunani 9pm Omar, sultan,Raj sai Usy suka shigo dakin amarya Iklas,tana ganin Omar taji wani sanyin dadi,idon amarya kiri kiri mayafinta a kai amma bata rufe ido ba,haka aka bude da addua,sukayi musu nasiha da barkwanci,suka ajiye mata kudi Omar yaje ya Rakasu sannan ya dawo wajen Iklas fuskarsa a sake,ita kuwar gogar ji takeyi kamar ba aurenta akayi ba,normal tunda ta saba da Omar dama

Gyalen kanta ya cire mata yanmata Amarya,ya kk,a hankali tace lfy,yau najiye miki dadi abar da kika Dade kina kallon shape dinta a boxers ko a towel gata yau har gida,sai kin gaji,yau zan baki ita,tunowa Iklas tayi da kallo tabi Omar kamar zatayi kuka,
Cike da shagwaba tace ban taba kallar maka abu ba,kawai bangon dakin nake kalla amma kake ganin kamar idona a kanka yake, murmushi Omar yayi ganin yanda Iklas ta tsorata,bai taba sanin tana da tsoro haka ba sai yau,dama tsokanarta yayi.
Tausayinta yaji ganin bata San kowa ba sai shi,bata saba da kowa ba sai shi,kwantar da hankalinki amaryas tsokanarki nakeyi,da Sauri ta rufe idonta tana daria,tare da furta ai nasan Sir dama tsokanata kakeyi,

Omar a ransa yace zakiga tsokana yarinya nan da wasu kwanaki bazan iya jure kallonki ba ga sonki da ke ragargaza min zuciya,a fili yace dama ni salihi ne uztazu kece kike Neman lalatawa Mama ni,
Je kiyi wanka muyi Sallah,ko na miki?murmushi tayi ba yanzu ba sai watarana,zaro ido Omar yayi yau ga amarya Mara kunya wai Iklas yar yarinya amma tasan zasuyi wanka ma wato nan gaba,inda take birgeshi ba boye boye irin na mata dan a kallesu a nutsatsu, abinda ke ranta zata fada koma wanne kallo kayi mata kai ka sani.

Iklas ta saba da Omar bare ace zata ji kunyarsa,dama kuma ita bata cutar kanta da kunya a cikin arna ta taso shi yasa ba komai ke bata kunya ba,gogayya da mutane bata tsoro da Shakkar mutane bare ta bari a cuceta tayi fa talla a kwalta readers kar a manta.Iklas kwai wayo sai ta siyar da mutum a gabansa bai san anyi cinikinsa ba...
Mikewa tayi ta tube gaban Omar daga ita sai towel ta Shiga wanka,ta dan jima ta fito,Omar ya fita yana Room dinsa ko takan Sahar bai bi ba,tunda ya shigo shi da frnds dinsa ta kama zage zage,shi Sam bai dauki Sahar a me hankali ba,baya sata cikin jerin mataye,duk yasan irin bin mazan da Sahar ke yi,yana da labarin komai,shi yasa yanzu bazai iya hada makwanci da ita ba koda sau daya,

Shuru kawai yakeyi sabo da Baffa kar yayi laifi,kuma yana so lallai ya koyawa Sahar hankali ta gane aikin Gomnati ba shine gatan mace ba.
Sahar kuwa frnds dinta ta Sallama,ta shige dakinta tana hucin kishi,sai yau tasan lallai tana son mijinta,ga kudi ga kyau ya hada komai da ake bukata,

Tunowa tayi sanda Omar ya taba saduwa da ita,duk da ita keyin komai tayi enjoying fiye da mazan da take harka dasu,akan tayiwa namiji biyayya ya biya mata bukatarta gwara ta rike aikin Gomnatinta ta nemi maza ta biyasu kudi suyi mata abinda take so.cewar Sahar.
Haushin Iklas ne ya tasowa Sahar,har akwai wacce ta isa tayi kishi da ita ta kwana lfy,wlh yau babu Wanda ya isa yayi bacci a gidan.
Omar wanka yayi ya shirya cikin rantsatsun fararen kayan bacci na maza marasa nauyi sannan ya dawo Room din Iklas, a gaban mudubi ya ganta tana tufke gashinta,sanye da da wata rigar bacci kadan ta wuce pant dinta me siririn hannu tasha kyau,sai cinyoyi santala santala lumi lumi dasu farare tas,Omar da kyar ya danne zuciyarsa a ransa yana yabawa Iklas wurin kula da kanta,tasan kanta basai an koya mata ba,

Jikin mudubin Omar ya taka har bayan Iklas, tallafota yayi ya kwantar da ita a jikinsa,cikinta ya shiga shafawa tare da warware jelar gashinta data tufke,sai shinshinata yakeyi tayi mukui da ita tana zukar kamshinsa tare da yaba taushin fatar omar.

Bakin gadon ya jata suka zauna da kyar ya fisgo tunaninsa murya a dishe,idonsa yayi wani ja,tashi muyi nafeela,skert tasa tare da hijab sukayi Salla raka'a biyu da addua,
Suna idarwa tace ya Omar yunwa nakeji ina kazar tawa?daria yayi sosai wlh ban taba ganin amarya irinki ba.
Baki ta cokalo ni ka bani abinci naci Dama ina jin haushinka ka daura min laifi wurin Ummi rannan ka tafi,murmushi yayi tare da kallonta yana mamakin wai bata manta ba,shi ya Dade da mantawa,

Leda ya jawo mata gashi kici ki ture,Indai kazace akwai ranar da sai kin biya ni bashi kika ci,daria Iklas tayi Ai Allah bazan Biyaba Sam bata gane nufin Omar ba,bude mata yayi ledar kaji dakwa dakwa,yogourt da juice sai sauran kayan ciye ciye,kafada ta make haka ake bawa amarya kazar? To ya akeyi cewar Omar nifa kin San komai sai kin koya min,haka kakewa Sahar din?kai ya gyada mata wai ae,tabe baki tayi tab haka ake love din?shi yasa ta gama rainaka in zaka mike ka mike kayi maganinta ka nuna mata namijine kai,ka zauna lalaci,jifa sunanka wurin Sahar wai Holoko.hmm maganar nan tana kona min rai,amma kai ko ajikinka,ka tabbatar kayi maganinta ato rai bace Iklas tayi maganar kamar itace Mama.

Omar yasan maganar Iklas gaskia ce fa,dama tun farko ya samu Sahar yayi maganinta yayi mata kaca kaca,amma yanxu bazai iya hada jiki da ita ba tunda ta koma Neman maza.baya sonta,tana masa rashin mutunci amma yana iya kokarinsa ya biya mata bukatarta da abinda takeso shi ba wani karuwa yakeyi da ita ba amma kullim burinta ta yanka masa rashin mutunci.

Iklas ce ta katse masa tunani ta hanyar riko yatsun Omar tana wasa dasu,never mind idan tafi karfinka ni zan gyarata.kajifa karfin halin Iklas,murmushi me tsada Omar ya saki yace ko ta gyaraki ba,ki dai kiyaye dan zaneki zatayi idan bana nan,ban son abu ya sameki,a ransa yana jin dadin yanda Iklas ke damuwa da damuwarsa, jawota jikinsa yayi ya dinga bata naman a baki,yanko naman yayi shima zai sa a bakinsa hannunsa ta rike,ta sa bakinta ta kwace a hannunsa ta cinye,daria yayi sosai,da hannunta itama ta fara bashi yana ci itama yana bata,abin shar fa,
Sunci sun koshi sosai,lemo Omar ya kurba a bakinsa ya tallafo fuskar Iklas da hannayensa biyu bakinta ya nufa da nasa bakin,ya dan dago da kanta a hankali sannan a nutse cike da nishadi da shaukin so ya hade bakinsu wuri daya da harshensa ya bude bakinta ya juye mata juice din daya kurba a bakinta,ji kake makwat Iklas ta shanye tare da lumshe ido,
Kallon juna sukayi kowanne dauke da murmushi a fuskarsa,a sigar rada Iklas tace ya Omar kafa hadu ai ka fi kowa iyawa ma,ko novel ban taba karantawa ba,ai a karatuna na theory banzo nan ba.

Daria Omar yayi tare da yi mata wani arnen kallo na nuna mata zallar son da yake mata,idonta ta janye dan taji kunya yanzu,a ranta tace tab yafi karfina wannan uhm mutumin da yake rayuwar turai dama,
Do u need more?Omar ya tambayeta,da sauri ta dage kai sama yeah,Allah ya Omar lips dinka laushine dasu har da zaki zaki naji,a kara min.yau Omar har ya gaji da dariar Iklas,shiko Omar dama abinda yakeso kenan da haka ya dinga tsotsewa Iklas lips amma bata gane ba.

Wurin Iklas ta gyara ta kai komai kitchen,brush suka karayi Iklas harda kuskura ruwan zafi na kaninfari da citta,ta jefa wata sweet ta ginger a bakinta,Omar yana kallon iyayi wajenta.

Omar ya Riga Iklas kwancia a bed din,ya matsu tazo su kwanta ko zai samu saukin abinda yakeji yana masa yawo a jiki,hannu ya miko daga bed din ya jawota,karasa hawa bed din tayi da kanta,yau za a mori skin din Omar a ranta sai dadi takeji zata kwanta a kafi katifa.

Mahaukacin bugun kofa sukaji kamar za a balleta,tare suka karasa jikin kofar Iklas na bayansa,waye pls Omar ya furta cike da jin haushi zai murje jikin Iklas an zo kawai an cuceshi,Iklas kuwa ita ta samu kafi katifa an mata bakin ciki ko waye zai ci ubansa hhh cewar Iklas a ranta.

A bude Sahar ce tayi magana,kamar Mara lafiya wai don a tausaya mata,wani wawan tsaki Iklas taja, kafin omar ya bude kofa Iklas ta rungumeshi ta baya,jikin Omar ba Riga sai boxers Iklas daga ita sai fingilar rigarta,

Bude kofar Omar yayi tare da cewa mene zaki dinga buga kofa haka,Sahar juwa taji na Neman kwasheta ganin Iklas manne jikin Omar, ta daflafaleshi,wato ita yake rainawa hankali,ko dakinta baya shiga,
Nan take Sahar ta fara mintsina ido cike da bala'i kamar zata tashi garin,kut billahillazi Baku isa ba,wato ni
Showing 63001 words to 66000 words out of 104017 words