baza su yafe ba.

Omar yaji komai amma ya toshe kunnensa ya sharesu,dan kawai a zauna lfy, saboda suyi was kawayensu karya su nuna yayansu me kyau ne hadadde na nunawa sa'a zasu nunawa frnds dinsu yayansu dan gayu me kyau ne,wannan dalilin yasa suka kawowa su Mama nasu pass card dinsu,kuma Haj Rahina tana tsoro kar fa bata yashi dukiyar Baffa ba ya saketa akan tambadadde Omar.amma da badan wannan dalilin ba bikinma sai dai su Mama suji anayi.
Amare ba Hutu shi yasa Iklas ta samu sakewa,ba duka ba zagi bare bakar magana,amma da badan haka ba ita kanta tasan da tuni taci wani dukan.
Omar yana zuwa office sosai shi yasa bai cika samun time ba,Iklas kuwa sai schl da kuma gyaran jiki,haka kullum HAJ MERO LALLAUSA me gyaran jiki ta gama tangarar da Iklas wajen koya mata dabarun zaman aure da kula da miji ba kunya.
Iklas har tambayoyi takeyi wai duk dan ta kwacewa Sahar miji.burinta taga Omar bai son kowa,baya kula kowa sai Ita babbar fadar Gomnati take son kafawa a zuciyar Omar.
Omar kuwa son Iklas da kaunarta sun hana masa sakat,kullum cikin kallon pics dinta yake,idan kaga Omar yasa headphone yana jin kida to za kaga yana latsa waya Wanda ba komai yake ba face kallon pics din Iklas yana tuna shirmenta da abin dariarta da sexy body shape dinta,yana jin shauki da nishadi.shi kadai zaka ga yana murmushi kamar Wanda yazo daga zazzau zaria. Lol.

Iklas Gomnati kuwa yanzu akan ta dauki jotter tana rubuta plan gwara tasa kida me dadi tana tunanin gata ga ya Omar suna ta zuba love,watarana in tanajin kidan har hangosu takeyi a wata arniyar mota sun fito ga kida na tashi ana ta kallonsu,ko ta gansu a shegen restaurant sun gama cin abinci yana ta kissing dinta a gaban mutane,saboda tsabar sonta da yakeyi baya iya boyewa a gaban uban kowa.ko ta hangota taci kwalliya ta gama hadewa Omar na ta kallonta da mugun so da sha'awa amma tana masa yanga.
Watarana kuma in tana jin kidan sai ta gansu a gidansu na aure, suna girki,ko tana shiryashi ta masa wanka etc.

Kai watarana kuma da cikin Omar take hangota yana lallabata,shi yasa take kasa tsinana komai sai tunanin Omar,yanzu gani take ma ganin Omar kawai ma yafiye mata Aikin Gomnatinta kai schl dinma gaba daya gani takeyi an cuceta an hanata ganin Omar akan lokaci,gwara ma ta dunga rakashi Office yana kusa da ita.

Ana gobe za a fara shagalin bikinsu Aisha,Gomnati tana dawowa daga schl ko abinci kin ci tayi kamar bikin kanin ubanta ta dauki hanyar fita ita da driver karo sukayi da Omar ya dawo dauke da ledar oasis a hannunsa,
Labewa tayi a bayan labile,jawota yayi gabansa baki da gaskia tunda naga haka kikewa su Mama in kinyi laifi,na ganki da hijab ina zakije,tsadajjen agogon hannunsa ya kalla yanzu kika dawo daga schl fa,
Har zaki kara fita,kuma time din Islamiyyar taki baiyi ba ai,da Sauri tace na dauki Hutu sai an gama biki zan koma.

Kallonta Omar yayi lalai zakici duka,a gida ma sun zaneki inaga kinje musu biki,kiyi zamanki yafiye miki, naga ma ko abinci baki ci ba, na koshi ni lallen biki zanje ayi min da gyaran gashi, hmm duk wannan zumudin da wa zakije?da saleem mana aikin da Mama ta bashi har yayi kudi ya siyi mota fa.
Lallai to ki fada masa kar ya sake yaje bikin kannena bama nemansa.look at u wai kannenka bayan tsine ma sukeyi,rannan ma akanka suka murdemin yatsu,
To amma zakije bikinsu?ae ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar,ya zanyi na hadu da jininsu ai danginane nima.ban gane ba cewar Omar, saurayi nayi dan uwan ummansu fa.
Kaga sun zama dangina,jikin Omar yayi sanyi gani yayi kamar da gaskene zancen Iklas,in kuwa hakane to lallai watan mutuwarsa ya kama.

Ita kam Iklas a kan Omar tayi magana tunda su Sadiya wai sun zama dangin mijinta, kuma so takeyi kishin Omar yayi tsanani har yace mata shi yake sonta don har yau tana tuna maganar Inusa me wanki yace Omar sonta yake.
Damuwa dankare a zuciyar Omar a fili kuwa snacks da yazo dasu ya dauki daya ya budewa Iklas a tsaye bakin kofa ya dinga bata a baki tana ci aranta tana wlh maganar Inusa me wanki gaskia ce,in ba me Sonka ba wa zai kula da kaci ko baka ci ba,a gaskia zanji dadina a gidan Omar.
Sai lumshe ido takeyi tana lamushe snack,
Shi kuwa Omar yanda take lumshe idon ne ke birgeshi sai kalle mata fuska yakeyi da pink lips dinta,

A haka ya dinga bata har ta koshi ya bata lemo da ruwa a hannunta tare da zaro kudi ya mika mata kiyi me kyau kuma idan naga batayi kyau ba sai sun goge miki ita.
Daria Gomnati tayi ta wuce tana masa bye bye,wajen Mama Omar ya koma shi asan yanda za ayi dashi a aura masa Iklas,Mama tace sai ta yarda kaje wajen Iklas.haushi yaji ya ficewarsa zasu karasa rabawa frnds IV na biki shi da Sultan,

Baffa ma yana gari ya gama kawai ranar Sunday yake jira tazo a daura aure,tuni an masa waya kan ya koma Russia ana nemansa a office aiki yayi yawa.

Baban Sahar har gida ya samu baffa kan Omar ya maida Sahar dakinta tayi nadama zata koma,Baffa yasan karya ne ba wani hali da zata canja Indai Sahar ce,amma idan an gama biki zai shawarci Omar yaji,idan yanaa so ta koma sai a kai masa Iklas itama gidan su zauna gaba daya.

Iklas bata dawo gida ba sai wurin 11 na dare suka dawo da driver, tasha gyaran gashi da lalle.
Ummi tace ke kuwa yar nan kamar kin tafi lallen Shiga Aljanna wannan dadewa,Ummi bafa ni kadai bace wajen,kingani tayi kyau?masha Allah ta Umaru tayi kyau,nasan sai ya bada tukuci daria Iklas ta kyalkyale da ita na jin dadi ta shige wanka.

Saida ta fito daga wanka ta duba wayarta missed calls din Omar ta gani da yawa,ga text birjik yayo mata kan ta dawo gida dare yayi.
Reply tayi so sorry na sata a silent banji kiranka ba,na dawo tuni.Omar yana bacci sai da safe ya gani,Iklas har makarantar boko ta dauki Hutu sai an gama biki.

Gida yayi gida,bangaren su Umma a cika sosai da yan uwa da abokan arziki masu kwana,kawayen amare makil sashensu daban,bangaren su Mama ta gayyato yan uwanta suma na nesa sunzo da yawa zasu kwana,har a gama biki,Iklas hayaniya ta dameta ta gaji dan haka gani su Ummi na hada hadar biki basu San me takeyi ba kusan gaba daya a part din Omar takeyin komai ko yana nan ko baya nan wucewa takeyi ta dinga uzurinta ba ruwanta,akwatin kayan bikinta ta janyesu ta mayar dakinsa,
Iklas tsabar kadifiri har kawayenta hadaddu ta gayyato guda biyu wata yar gayu yar gidan wani kusar Gomnati suna ce mata ANGEL,sai wata yar wanka kyakyawa itama yar wani babban soja ce wato PRINCESS, unguwarsu taje ta fadawa kawarta arniya DAMI DAMZEL itama za aje da ita dan tana aiki a company tana kashe wanka duk cikinsu babu wacce za ace bata hadu ba.kuma iya dinner Iklas ta gayayyacesu suzo.
Ummi ma ta gayyaci mata tsofaffi irinta na tsohuwar unguwarsu mutum uku,Sa'ade,Hasiya da Maman saleem Haj kyauta.

Komai dai share.
Saleem duniya ta samu har sun canja unguwa ya siya musu gida shida mamansa sun koma cikin Abuja city,har yayi motar kansa,
Mamansa ta uzura masa ta gaji da zaman kadaici ya nemo matar aure,shi kuma Iklas ya fada mata yana so,sai tace ya bari idan taje musu biki zata sanarwa Ummi,sai murna yakeyi.
Umma Rahina yaranta ta Tara,kan kar su nunawa yan bangaren su Omar komai,idan ana bikinma su nuna komai daya, ana zaman lfy,kuma suja Iklas a jiki ayi komai dasu,yanda idan sunyi wata kulla kullar jama'a ba Wanda zai yarda cewar su suka aikata,dan tace ana gama biki zata fara harba makami me linzami na bama baman tsiyarta bangaren Mama,zasu sha wutar bala'oinsu.

An tashi yaune za ayi event har biyu daya 3pm-6pm za a dawo a koma na 9pm-3am ko wanne wajensa daban za ayi, Iklas ce ta wuce Omar a palonsa fiiii zata shige cikin bedroom,jawota yayi baya ina zakije haka,kinfa takurawa room dina, na gaji da wankemin bra da panties naki ke ba matata ba ko kunya bakyaji na gani,

To mene abin kunya a pant da bra amma a t.v settelite ai nagani rannan kana kallon american film da bra da pant jikinta kana kalla me yasa nan banga kaji kunya ba,sai idonka ma da naga ka kara warewa,
Ni ai na saba gani,ke nake nufi,baki ta murguda to Nima bana jin kunya agaban kowa zan iya shanyawa,da masifa Omar yace hey mind ur tongue,kar ki jawo na huce fushina kanki.
Ita Iklas duk haushin Omar takeji yaki cewa yana sonta, ta gaji da jiran sa.

Me zakiyi cikin Room din to, wankan party,no ki bari sai na 9pm zamuje.batayi musu ba tace to Allah kaimu.
Da hannu ya yafitota come come muga lallen da akiyi miki jiya,na mantama ban gani ba,a nutse ta wara masa hannayenta,kalla yayi sosai har na kafa dama gata fara kar, lallen ya gama tafiya da Omar, harda shafa hannun,gashin ma ba a magana, har mamaki yakeji yaushe Iklas tasan wurin gyara a Abuja haka.
Omar bai San aikin Mero Lallausa bane me gyaran jiki.
Zame hannuta Iklas tayi,tabe baki Omar yayi mutum ya biya kudi an hanashi ganin na kudinsa.
Je ki dafa min indomie da kwai,ki hada min coffee. Tafiya tayi cika umarnin Omar,Hips dinta yabi da mayen kallo.

8pm sai shirin dinner party akeyi, su Abdallah shi ke yawo dasu Suleim 8:30 sunyi shirunsu kajifa yara, bangaren Amare mafa nan ake cakarewa.
Iklas zata shiga wanka Omar ya sa key a toilet din wai baza suje da wuri ba,haka ta koma na Mama duk shirye shirye akeyi,ita kuma baza ta shiga toilet din da wasu yan biki suke shiga ba,sauran rooms du Mama tasa musu key.
Dolenta ta jira Omar sai abinda yace.9pm sannan Omar yace tayi wanka,10pm sun gama shiri tuni frnds din Iklas sunje can,sai waya suke mata,Sultan da amaryarsa Yasmin, Raj ma yaje.

Kwaalliyar su Iklas fa


INA TARE DAKU MUTANENA




Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

125-130


By
Asmabaffa




Iklas ce tayi shiri idan ba mugun saninta kayi ba baza ka gane ta ba,wani tsadajjen material tasa na nunawa a gari,Red ne da zanen Arsh color jiki, yayi mugun kyau,duk yafi na amare kyau da tsada,dan Omar ba karamin kudi ya zuba ya siya ba,Riga da skert ne,tasha kyau kamar Ku saceta dan tsayawa ma fadar yanda shape dinta ya fito bata baki ne, Omar yasan size dinta mayene.takalmi me tsini arsh da wata shegiyar pose yar gaske same color da shoe,Omar ya fito daga wanka sai da kyar ya tabbatar wannan Iklas ce,
Iklas fa har gwagwaro itama ta kai aka Nada mata na kece raini,gashin nan ta gyara jelar na reto a tsakiyar baya murtukekiya,ta fito da ita ta tsakiyar goggoro,dama ga jiki yasha gyara ko ina kyalli takeyi,turaruka kuwa sai da Omar ya koreta,zama tayi tana jiransa yana shiryawq tana ta guntse dariarta wai ganin sandar girman Omar a short wando,yana kalonta ta gefen ido,kin San Allah zanyi maganinki ki koma Palo ki jirani kan me zaki sani gaba ki dinga kallona kina daria,baki ta rufe da tafin hannu nayi shuru to.

Harara ya watsa mata yana ta shirinsa tana satar kallon jiki da kira me kyau irin na Omar, Allah ya bashi diri da kyau ga skin dinsa kalarta ta kwashewa Iklas Imani,
Wani rantsatsen yadi me taushi Omar ya sa,shara shara sosai arsh color kalar material din Iklas komai Arsh yasa,dinkin zamani dai dai jikinsa wandonma,Omar uban yan wanka suma taci wani gyara me kyau,tayi luf,turaruka ya fesa sosai,ya fito kwas rike da waya,Iklas ma wayarta fankaceceiya a hannunta,mikewa tayi daram ta isa wajensa yaya Omar kalli fa kayanka shara shara har singlet ana gani,wandonka ma dan an masa landing daga samane amma ai sai adinga hango uhmmm.....uhmm....da ka canja shadda ma ,ke jikinki ko nawa ina ruwanki cewar Omar.kowa ance miki irinki ne me kurawa mazan wasu ido,let's go idan zakije if not na tafi,
Ita Iklas kar a kallar mata kyallin fatar miji,gashi tasan dole Sahar tana can.

Hannunta ya rike suka fito duk gidan Shuru sai yan aiki da suke aikin gyara gida kafin a dawo.
Wata sabuwar mota fil arsh color itama Omar ya bawa driver key a baya suka kame kamar sune amarya da angon,kajifa yan fassion
Har wajen driver ya kaisu,tun daga waje zaka San wajen ya girmi me karamin karfi.
Sahar da frnds dinta an kwafe a kujera tana baza idon ganin Omar,dama su gulma ce ta kawosu da niyar wulakanta Iklas gaban mutane,
Amare da Angwaye ana kujera an fara shagali suna kallon masu rawa da liki,su Kansu Omar suke son gani saboda frnds dinsu su kalli haduwa,najja da sauran kannensu sai iyayi akeyi a fili ana kada hips,kaji kannen Amarya fa.Iklas ce ta masa rada pls ka fita munzo fa idan ka fita ka bude min kofa na fito a Gomnati ta.
Driver ne ya budewa Omar kofa.
Murmushi Omar yayi tare da fita cike da kasaita,omar kuwa zagayawa yayi ya budewa Gomnati itama ta fito,tana fitowa zuruf ta sakalo hannunta Dana Omar ta kara shigewa jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba daya ba space da ko tsinke zai iya shiga.wani kar kar kawai Omar ke ji a cikin jininsa kawai Iklas yake bukata, kara manneta yayi suka tafi domin shiga hole din,

Duk Wanda yayi tozali dasu sai ya saki baki da ido dan kallon kyau irin nasu,ga iya wanka,ga shiga me tsada da ka gani ba sai ance ba,gasu sun birge masoya da gani wannan real love ne,dama Iklas tace bikine daga mota sai hole shi yasa taki daukan gyale,

Sultan da Raj suka fara gani cikin wurin,daria suka dinga yi sun San Iklas sarai, wuyan Sahar da frnds dinta kamar zai tsinke dan kallon su Omar,suma su Najja sai nunawa frnds Omar sukeyi ga yayansu babba,wajen da aka tanadar masa najja ta nuna masa suka zauna,Mama da Ummi suna can baya sunga su Omar har murmushi sukayi,Iklas ba dama cewar Ummi.

Duk Iklas ta kasa sakewa yanda taga yan mata na kallon Omar,kamar tayi kuka,shi kam Omar ta kansa yakeyi ganin Saleem a wajen su Angel kawayen Iklas,
Yayan amare aka kira kan ana so ya chashe a fili dama Iklas ta matsu su shiga fili rawar Igbo zatayi yau tace, ai kuwa kafin Omar ya juyo sai gani yayi Iklas har ta danyi doro kamar zatayi ruku'u tana ta kada hips,tafi da ihu fili ya dauka kafin kace me an rufeta da liki maza da mata,su Kansu su Sadiya ta birgesu rawar,
Maman waleeda ma sai liki takeyi sai da ta karar da yan kudin cefanen da Baban waleeda ya bayar na 1mnths,kinga ta kanki da me zasuyi girki,Jamila sule,Haj jamila duk sai balle bakin jaka sukeyi,Zulaihat da su Juwairiya duk an Hallara a fili,sai Diyar katibi me gyara fili ce tazo ta koresu kasa tukunna.

Omar sannan ya fara likiwa Iklas yan dubu dubu,itama mikewa tayi ta gama rawar ta fara barin kudi musamman Omar ya bata dama,masu DJ sun washe da Naira, Omar ne ya janye Iklas suka koma mazauninsu sai radar masifa yake mata kan tayi rawa,
Angwaye da Amare na fitowa suma sai da su Iklas suka yi ruwan kudi.su Aisha ransu ya fara baci fa anzo gidansu ana satar musu dukiyar Uba ana bawa wata banza,
Sahar takaici ya kamata ganin inda Iklas ke barin kudi Omar ne kuma yake bata,a gabansu ma ta karbi wasu,ita kuwa sahar taga ko time din da take matarsa baya bata haka.

Da kyar ya bar Iklas taje wajensu frnds dinta
Showing 57001 words to 60000 words out of 104017 words