wahala ta gama sha ta sanadin Alhaji da ƴaƴan sa amma wai a daina ce musu tambadaddu, ita ta rasa wace irin zuciya Allah yayi wa Falmata amma komai ya kusa zuwa karshe dan ita ba zata zuba ido ba, dole ta dauki mataki ko dq da ba da sanin Falmata bane.

Yin wannan tunanin yasa ta saki ranta ta shiga kwantar wa da yar uwar ta hankali kana ta tashi ta gyaggyara mata daku na inda masu aiki basa shiga mata, se daf da magriba ta yi shirin tafiya bayan ta jaddada wa Falmata cewan ko yaya taji wani ciwo ta kira ta haka kuma ta tambayi Alhaji suje su ga yan uwan su.

Da toh Hajiya Falmata ta amsa mata kana suka yi sallama Farida ta wuce.

Bedroom din ta ta koma ta yi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror dan yin shirin ta sedai se ta bige da kallon kanta cikin madubin.

Gaba daya tayi baki ta rame kamar ba ita ba, farar fatar ta me sheki duk ta yi duhu, kyakkyawar fuskar nan duk ta mokade saboda rama, baka ganin komai a fuskar se dogo siririn yancin ta da ya kara tsayi se kuma kodaddun idanun ta da kallo daya zaka musu ka hango rashin lafiya, damuwa, rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali cikin su.

Hannu tasa ta shafo wuyan ta inda kasusuwa suka bayyana kan su a wajen, ta dade ta na shafa wajen cikin tunanin tana hawaye batare da ta san tana yi ba, tsayin lokaci kafin ta farga ta share fuskan ta kana ta karasa gaban bed da ta aje kayan da zata sa ta dauka ta maida wardrobe, a yadda tayi wannan ramar sam ba zata sa kayan mu na al'ada ba dan ba kadan ba zasu bayyana ramar ta kasancewar duk an dinka su ne lokacin da take falmatan ta ba yanzu da se sunan kawai ba.

Doguwar riga ta sa kirar Oman kana ta aje dankwalin a gefe ta shiga gyara kan ta wanda shima se d aya samu tangarda saboda halin da take ciki, seda ta tufke jelan sannan ta daura dankwalin kan ta, ba karamin kyau tayi ba duk da kuwa fuskar ta babu komai face kwalli da ta sawa idan ta dan ya rage kodewar da yayi.

Kai daga yadda ta daura dankwalin abayar zaka san lallai a da an zuba gayu an kuma kafa dauruka ba kadan ba, ita kan ta murmushi tayi da ta kalli kanta sannan ta kwashi wayoyin ta ta fita falo.

Tare da harira suka zauna dan duk cikin masu aikin ta tan matukar kaunar harira haka kuma ba matsayin me aiki take kallon ta ba, kallon yar uwa kuma karamar kanwa take mata dan ta girmewa hariran nesa ba kusa ba, hirar su suke yi suna kallo sama sama abinda yasa zuciyar Falmata dan samun nutsuwa daga tunane tunane.

Yadda hankalin su ya dauku yasa har basu ji sallaman Alhajin ba balle shigowar sa seda yayi gyaran murya, da sauri harira ta tashi tayi waje ta kofar baya bayan ta gaida shi, kusa da Hajiya Falmata ya karasa ya zauna inda ita kuma ta tashi zuwa kitchen domin kawo masa ruwa.

Kan karamin tray ta dauro bottle water da juice na kwali me dan sanyi kana ta hado da glass cups ta kawo gaban sa ta aje kana ta zuba ruwan ta mika masa ya karba ta kuma shiga zuba juice din.

Seda ya karewa juice din kallo kafin yayi bismilla da karfi sannan yasha, ita dai tana kule dashi sedai bata bashi wani muhimmanci ba har ya shanye lemon ya aje.

"Wanka zaka fara yi ko abinci zan kawo?".

Da sauri kamar wanda tace zata kawowa mugun abu ya shiga kada kai

"A'a, a'a ai ba zan ci abincin nan ba, na riga naci abinci a waje cikina a cike yake".

Dan tsai tayi tana kare masa kallo kafin kuma ta girgiza kai tana dan murmushin da kan kallo zaka san ba na jin dadi bane

"To shikenan, wankan fa?".

"Yanzu zan je can part di na nayi, dama dai nace ba wata damuwa ko?"

Seda ta dan hadiye miyau kan ta bashi amsa

"Maganin da na bawa Adam ne dai har yanzu be kawo ba".

"Se fa kina yi wa yaran nan uzuri, yana da harkoki da yawa ne, yanzu haka ya ma tafi can kudu kan kayayyakin mu da ze shigo dasu, amma kiyi min texting sunan maganin se na taho dashi".

"Ko kawai ka bawa Bala ya siyo min?".

Ta fada sanin in dai shi ze siyo maganin to kuwa har ta mutu be kawo ba.

"Shikenan zan bashi kudin ya siyo kawai, shikenan ko?".

"Maganar aikin nan alha......".

Tun kafin ta karasa ya katse ta yana mikewa tsaye daga zaman da yayi

"Ai tuni muka gama magana akan wannan, na fada Miki babu kudi a hannu na yanzu amma watan gaba insha Allah se ayi aikin ko a nan asibitin Shehu ne dan gaskiya fita wata ƙasa ze ci miliyoyin kudade kuma kin ga yadda yanzu harkokin suke se a hankali".

Tun d aya fara maganar take kallon shi har ya kai karshe

"Allah ya kara budi, gobe ina so inje gida".

"Gida kuma, wane gidan kenan?".

Ya fada yana bata rai kamar wadda tace masa zata je gidan karuwai ".

"Gidan marayu mana, muna da wani gidan da yafi nan ne?".

"Ba zaki je ba".

Ya fada yana kade babbar rigar sa ya nufi fita waje

"A'a Usman ka bar ni kawai dan wallahi goben nan se naje".

Ta fada da rawar murya, shima Alhaji tsayawa yayi kana ya juyo cike da mamakin yau Falmata ke ja da hukuncin sa, anya be fara kure hakurin baiwar Allahn nan ba kuwa.

"Shikenan kije Allah ya tsare, ki gaida su".

Bata amsa masa ba ta zauna tana kallon tv sedai hawaye ke zuba a idanun ta, yana fita itama ta tashi zuwa daki da sauri, kan gadon ta ta fada tana kuka me shiga jiki, wani kuka me tafe da sheshshekar dake fitowa daga can karkashin zuciya, a hankali nunfashin ta ya fara seizing kadan kadan kafin kuma tari ya turnike ta , da sauri ta tashi daga kwancen da take tare d da finciko tissue dake aje kan mirror din ta tasa a bakin ta zuwa hancin ta dan ta ana abinda ze faru gaba.

Seda tarin ya tsaya mata da kyar sannan ta zare tissuen dake kan hancin ta ta aje haka ma na bakin ta, gaba dayan su sun ɓaci da jini, wani irin bakin jini me kauri, ganin bata firgita ba yasa nasan ta dade yana ganin hakan kenan.

Wata tissuen ta sa ta goge bakin ta sosai kana sa ruwa ta kuskure bakin, ta dauko wani ma ta goge hancin, take fuskan ta yayi tas kamar ba ita ta shiga yanayin ba.

Kora tissues din tayi cikin closet ta karawa toilet din spray sannan ga fito, bedside drawer ta bude ta ciro wani tablet guda biyu manya ta sa a baki tare da korawa da ruwa, Wani ta dauko different from the first shima ta sha biyu sannan ta cire doguwar rigan jikin ta tasa na bacci yayi light off tare da kwanciya bayan tayi addu'a.

Kashegari da wuri ta shirya, tayi matukar kyau cikin Abayan da tasa kirar Dubai, sosai ramar ta ta buya se wadda ba'a rasa gani ba, sallama tayi da su harira sannan ta fita cikin motar ta wadda bata wata me kyau bace can amma kuma ba wai ba ta da kyau bane.

A compound din gidan Hajiya Farida tayi parking ta fito tana sakin murmushi, Farida ce kawai kawar ta ita ce kuma kadai yar uwar ta haka kuma aminiyar ta, gurbin da Farida ta cike mata ba kadan bane haka kuma halaccin ta gare ta me yawa ne duk da dai ita ce ta fara yiwa Faridan amma ba kowa ke iya rama alkhairi ba.

Da sallama ya shiga falon, ihu Hassana ta saki tare da tashi ta nufo ta a guje, duk kai kai kai din da Hajiya Farida keyi be sa ta fasa ba se da ta fada jikin falmatan har da wani dan tsalle kafin ta kankame ta, ita ma sa hannu tayi ta sake riƙe ta a jikin ta suna dariya Farida kuwa ta soma fada

"Ke dai wallahi ban san yaushe zaki yi hankali ba Hassana, ban da rashin mutunci kayar min da ita zaki yi da zaki dane min ita haka bayan kin san ba wani lafiya ne ya ishe ta ba salan ki cuce ni, to Allah ki ka kuma se ran ki ya baci, bana son shashanci, yarinya ga uwar nauyi kaman buhun shinkafa kawai ki nemi illata min yar uwa".

Bata fuska Falmata tayi ganin yadda Hassana tayi rau rau da idanu,

"Gaskiya ni dai Farida kina min abinda bana so, kawai shikenan se ba zata zo ga uwar ta ba saboda bani da lafiya, ko kuwa ke kadai ce me yar uwa da zaki ce haka, dan ma kin samu ana yin yar uwar ta ki, to ni dai kiji ma ya'ya na are above anyone, maza matso ki sake yi min oyoyo sweetheart ".

Ta fada tana sake buɗe mata hannu bayan ta matsa nesa da ita daidai lokacin da Hussaina ta fito daga bedroom suka kuwa kwaso da gudu su duka biyun suka fada kan ta gaba daya suka zube kan kujera suna dariya, ita kam Farida bata kuma bi takan su ba ta cigaba da abinda take yi a kitchen jin yadda Falmata ta gwale ta sedai tana jiyo kyakyacin dariyar su daga nan wadda ta manta rabon da taji dariyar Falmata har haka.

Wani irin tausayin ta ne ya sake kama Farida tuno yadda Falmata ke masifar son yara tun suna kanana se gashi Allah ya jarraba ta da rashin haihuwan kuma ta bata mamaki dan bata taɓa zaton Falmata zata iya karbar wannan kaddarar ba.

Seda ta gama aikin ta sannan ta fito ya same su kamar wasu kawaye

"Oya aje a fito da komai a shirya kan dining bari nayi wanka nima".

Da haka suka tashi zuwa aikin da aka sa su ita kuma ta wuce wanka aikuwa itama Hajiya Falmata ta tashi ta shiga taya su jera abincin, tare suka yi gaba daya sannan suka wuce wanka suma ita kuma ta zauna kallon wata hira da ake yi da wani mawaki a TV.

A shirye suka fito dan tare zasu tafi dukan su zuwa gidan marayu wanda nan ne gidan su Farida da Falmata kasancewar marayun da suka tashi suka budi ido a gidan batare da sanin su waye iyayen su ba, hakan yasa suka riki gidan marayun gida duk kuma wanda ke cikin gidan suka dauke su yan uwa kuma dangi, Hajiya Farida bata taɓa kunyar nuna wa ya'yan ta gidan matsayin nasu gidan iyayen ba, a kullum tana alfahari da gidan dan acewar ta ba'a yi musu rikon wulakanci ba.

Seda suka karya gaba daya har Falmata sannan suka dungu ma zuwa compound suka shiga motar Hajiya Farida leaving behind motar Falmata a gidan.

A motar na hirar su suke yi ita da Farida dake tuki yayinda Hassana da Hussaina ke baya suma suna tasu har suka kai gidan, kayayyakin alkhairin da suka saba bayarwa na kayan abinci duk suka dire haka kuma suka dinga zagaye gidan bangare bangare suna gaisawa da jama'a, da suka tashi tafiya wannan karon Hajiya Farida ce kawai ta bada kudi kamar yadda suka saba dan ita Falmata babu kudi hannun ta.
Haka suka yi sallama da jama'a suka koma gidan Farida suka sauke yan biyu su kuma suka sake fita domin tafiya meeting din kungiyar su wadda Farida ta shiga ne kawai saboda Falmata dan kungiyar purpose din ta babu irin su Farida ciki.

*NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS*

Babbar kungiya ce da ta cika ta tunbatsa da Manyan mata iri iri, kungiya ce da aka kafa ta solely dan matan da basa haihuwa, zaka yi mamaki in ka ga dimbin mutanen dake ƙarƙashin kungiyar domin ta haɗa mata kala kala, manyan masu kudi masu rufin asiri kai har ma d talakawa.

An kafa wannan babbar ne domin kwantar wa d matan da basa haihuwa hankali, samar musu da aikin yi da kuma kwatar musu yancin su a inda ya dace, haka kuma domin taimaka su a gurin da suke buƙatar taimako.

Suna yin meeting din wannan ƙungiya ne annually ma'ana duk shekara, a nan za'a zauna a ji koken juna, me bukatar taimako ayi mata, sababbin members kuma ayi masu rigister tare da councelling kan abubuwan dake jawo rashin haihuwa, in abin me magantuwa ne suna tsayawa kai da fata har se sun ga an ci nasara da izinin Ubangiji batare da duba da ko nawa za'a kashe ba while the treatment...........


Ouummey 📚✍️.








Ouummey 10 {5/9/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey





                       Ouummey 10
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

                  _Free Chapter Ten_

Hajiya Falmata da Hajiya Farida sanannu ne a kungiyar saboda irin gudunmawar da suke badawa, ba wai sun fi kowa taimako d kudi bane, a'a irin matsalar da Falmata ke ciki da yadda take da jarumta da juriyar mai da komai ba komai ba yasa ka bata mukami dan na kasa suyi duba izuwa ga rayuwar ta su kuma yi koyi da tawakkali hadi da karfin zuciya irin nata.

Kamar ko da yaushe yau ma cikin nasara aka gama gabatar da meeting din, inda yau taimakon nasu ya karkata ne kan wata mata da ke da matsalar karin mahaifa da ya hana ta haihuwa gashi kuma mijin da iyayen ta ba masu karfi bane hakan yasa jin labarin kungiyar da irin taimakon da ake yi a cikin ta yasa ta kawo kanta haka kuma aka saurare ta duk da bata kasance wata hamshakiyar me kudi ba, ba kuma wata celebrity ba haka kuma ba wata kusar gwamnati ba, motto din kungiyar shine mu'amala da kowa with equality, babu ruwan su da mai kudi ko talaka, abinda suka sani shine they all are one family and have almost similar problem so they'll come together in finding a solution.

Miliyan uku da rabi ake bukata domin aikin dan abin yayi worsting ta yarda har ya fara neman lalata mahaifar hakan yasa ake bukatar aikin urgently, wani abin burgewa shine a wannan zaman da suka yi da kowa be san za'a iya kawo matsala ba se gashi tashi daya har an hada miliyan biyu da rabi, inda wasu suka karbi bank account na kungiya domin sending kudaden wasu kuma suka tura, abinda be isa ba za'a cika a asusun kungiya.

Compound din building din tuni ya cika da kayayyaki, kayan masarufi, kayan amfanin mata kama daga kan sabulai da turarukan wanka, kayan sawa, mayukan gyaran fata da gyaran gashi, takalma, kai abubuwa dai da yawa da mace zata bukata na gyara daga wajen mijin ya, ba mutum daya ne ya kawo ba, kowannen su kan zo da abinda Allah ya hore mishi ne in aka hada se a raba, suna yin hakan ne dan ragewa mata takaicin namiji da wani baze iya bada kudin gyaran jiki ko wani gyaran gashi ba, musamman ma masu irin matsalar su da mata ke kallon basu kudin gyara ko wani abu as a waste of resource.

Kowanne ka kalla fuska cike da farin ciki ana wasa ana dariya suka rabu, Falmata cikin ranta bata ji dadin yadda abun ya zo mata cikin rashin kuɗi ba sai dai taji dadin yadda yar uwar ta kuma aminiyar ta Farida ta rufa mata asiri domin kuwa ashe kayan masarufi ne cike damkan a bayan motar ta bayar da sunan Falmata.

Gida ta mai da ta bayan sun zagaya gari duk saboda tayi lightening mood din Falmata wadda duk abinda Farida ke yi ta na ankare haka kuma zuciyar ta cike take da matukar godiya ga Allah bisa kyautar wannan rai mafi tsananin so, kulawa hadi da tausayi gare ta, bata san me yasa ba se take jin wani matsananciyar kewar Faridan tare da ita duk da gata a gefen ta suna tare.
Har bedroom Farida ta rakata, duk yadda take fada mata ita fa lafiyar ta lau bata bar ta ba se da tayi wanka ta canja kaya gaban ta ta ci abinci sannan ta kwanta kana hankalin Farida ya kwanta har ta iya ta mata sallama ta tafi nata gidan.

Kallon Hassana tayi dake zazzage karamar akwatin yan kunnen ta, wani babban saiti ta dauka me hade da awarwaro, zobe, sarkar kafa da kuma zobe, jujjuya su tayi kana ta dauka ta sa a handbag din ta dake gefen ta kana ta umarce ta ta maida ragowar, cike da dimbin mamaki Hussaina ke kallon ta wanda duk Farida na hankalce amma se ta nuna kamar bata gani ba ta mike tare da nufar bedroom din ta tana umartar Hussaina da ta bi bayan yar uwar ta su kwanta se kuma gobe, haka dole ba dan taso ba Hussaina ta yi dakin su ranta cike fa mamakin me maman ta zata yi da babbar sarkar auren ta, sarkar da iya rayuwar ta zata iya fadar so nawa ta sa ta saboda son da take mata.

Washegari tana tashi Falmata ta fara kira, jin ta garau yasa hankalin Farida kwanciya sannan ta gabatar da
Showing 21001 words to 24000 words out of 43434 words