zaune ƙalau da yar uwa ta kina min irin wannan kalaman?, Gaskiya bana so".
Mariya ta fada da murya me kaman tana dariya ne ko kuwa, nidai ban tsaya ba na shige kitchen din na Kai jingine jikin Island da sauri ina sauke numfashi a jere a jere kamar wadda tayi tseren gudu, makogaro na ya bushe kamar wadda ta shekara bata sha ruwa ba, da kyar na iya lakato wani yawu me daci na haɗiye ina lumshe ido, a kuma lokacin ruwan hawaye ya fara zarya kan kunci na, halin da na shiga a lokacin ba me bayyanuwa bane.
Sanin suna falon yasa na daure zuciya ta na lallashi kaina na hada fruit salad maimakon noodles da na shigo da niyyar yi, juice na ɗauka me sanyi tare da bowl dina na fita cike da fatan kar wata ta kwata faɗa min irin maganganun nan dan a yadda nake ji zan iya biye musu muyi duk wadda ta kama.
"Auntyn yara angode fa".
Yatsu biyu na daga mata batare da nace komai ba na shige ɗaki, da kyar da sidin goshi na sha salad din nan dan wani daci naji yana min a baki.
Kuskure baki nayi bayan na gama na ture plates din gefe tare da ɗaukan waya ta ina dubawa wai ko zanga missed call din Salees, sedai ga mamaki na ko text babu balle kira, murmushin takaici nayi tare da kiran shi ni, ta dade tana ringing be dauka ba har ta katse na sake kira shima be ɗauka ba, seda na masa miss call biyar sannan ya turo min short text
"Busy".
That's all he said, Ina gani na aje wayar jiki a sanyaye, saboda gudun tunanin da ka iya rufe ni na janyo tablet dina na hada mata keyboard na shiga ayyuka a ciki, duk wanda ya ganni kallo ɗaya ze min yasan ina aikin ne kawai amma ba dan jin dadi ba.
Dake Allah Alhakeem ne se gashi tashi ɗaya ya aiko min da sanadin farin ciki madaukaki, ba komai bane face karin matsayi da ake shirin yi a ma'aikatar mu, cikin rahamar Ubangiji kuma har da suna na cikin wanda za'a yi reviewing Wanda muna sa rai in mun tsallake review shikenan promotion ya tabbata.
Ban yi farin cikin ni kaɗai ba na kira Ummi na na faɗa mata tare da fatan a taya mu da addu'a ta amsa, yayata Salima na kira itama na sanar da ita, ba tun yau ba na fahimci kunya da nauyi na ta take ji ba sedai ni a raina wani irin girman ta nake gani domin tai min abinda ba kowa ze iya ko kwatanta wa ba.
Ta taya ni murna tare da fatan dacewa, tana neman kashe wayar na tare ta da sauri
"Ina yaro na?, Shiru baya neman mommy?".
"Ba haka bane ba maman Haidar, kin san baban makarantar wuni ya kai shi saboda yaki maida hankali a waccan".
"Ayya, dan Allah yaya a kula min da shi sosai, kar a bar min shi da yunwa da damuwa".
Daga cikin wayar na jiyo faffaɗan murmushin da tayi tare da amsa min mukai sallama na kashe wayar sabon zafi na sake hudowa daga kirji na sedai tuni na dakatar dashi saboda bana san abinda ze dinga tuno min da baya, duk da present din ma ba dadi ne dashi ba amma bayan nan akwai ciwo me matukar raɗaɗi.
Seda na tabbatar ƙawayen Mariya sun tafi dan gidan yayi shiru ba hayaniyar su kana na dau bowl din da nayi amfani dashi na fita zuwa kitchen.
Zama nayi a kujera tare da kunna Tv na shiga kallon wata drama da ake yi a mbc Bollywood, cike da zallar nishadi na kalli abina har aka gama na tashi zuwa daki dan It's evening, akwai bukatar in kwance kai na dan sati na biyu yake ciki.
Seda nayi Asr sannan na fara tsifar a falo ina yi ina sauraren wani hirar classmates dina a group da sukai ta hanyar voicenote, a lokacin ne kuma baby ta shigo dan se five ake tashin su, da karfin gwiwar ta ta shigo murya a sama tana ihun kiran sunan uwar ta ita kuma tana saukowa daga sama tana amsawa sedai tashi ɗaya taji dif yarinyar tayi shiru.
Wai ashe ni da ta tarar cikin falon ne yasa ta ɗauke wuta jikin ta ya shiga rawa, sam ban ma lura ba ni hankali na na kan abinda nake ji seda naji babar na tambayar ta
"Me haka, lafiya na ga jikin ki na rawa?, Me ya faru?".
Da mamaki na daga kai ina kallon su, yarinyar ta maza ta faɗa jikin mamanta tana zare ido, ko da na gane abinda ke faruwa se kawai na dauke kai na cigaba da abinda nake yi ita kuma taja ta daki tana tambayar ta.
Ban san me ta fada wa uwar ba se ganin Mariya nayi a gabana a tsaye kamar wata bishiya
"Wane irin rashin imani ne yasa kika yi wa Ilham wannan marin, kin kuwa ga yadda bakin ta ya kumbura?".
Kamar kar in tanka se kuma na tanƙwasa kai na sanin shi bayani yana da dadi kuma rigima sam ba abar so bace musamman gare ni da ba hali na bace, zama da Mariya ne yasa har ban san yaushe na canja ba.
"Ilham rashin kunya take koyowa Mariya, wai kamar ni zata kalla ta zaga, imagine fa".
"Ban gane zagi ba, kin ga tun kafin raina ya ida ɓaci ki min bayani yadda zan fahimta, Ilham ta zage ki tace miki me ?".
"Kin san dai ko ke baki isa in miki karya ba balle ƙaramar yarinya kamar ta, ce min tayi wai Allah yasa tana da iyayen da suka haife ta tun da ba juya bane su".
"To ai ba karya tayi ba tana da iyaye, shima juyan ai ba sharri tayi ba tunda da juya ne su da basu haife ta ba, shine kawai dan wannan yar maganar zaki nemi lahantata, to wallahi bari uban ta ya dawo dan ba zan yarda ba".
Iya maƙura raina ya kai wajen ɓaci dan haka na mike tsaye nima kamar yada take
"In Kika yarda ma ba sunan ki Mariya ba, haka kuma in Kika fasa fadawa Salees ba ki haifu ba, maza faɗa masa yazo yayi wa khadeeja tuf ta mutu kin ji, shashasha mara tunani, a faɗa miki yarki tayi wannan rashin mutuncin amma ki goyi bayan ta saboda rashin sanin ciwon kai, to ai karki fasa, dan yau dai ba ayi masa haka in zaki gyara ki gyara".
"Naki na gyara, nace naki na gyara ɗin, yar ki ko yawa, aikin banza da zaki zo kina wani kinibibi ai se ki bari se kin haifa se karki goyi bayan naki, ko da yake macen da ta shekara sha shida da aure bata taɓa ko bari ba ta ina zata haihu, wai wanda be san ciwon da bane zece ga yadda za'a masa tarbiyya, mtsww juya kawai mara amfani".
Wannan kalma ta juya itace kalma mafi ciwo a duk cikin kalaman Mariya, sanin babban weakness dina gorin rashin haihuwa ne yasa Mariya daura damarar cewa se ta ga karshe na, gashi ni kuma bana iya daurewa wannan gorin, ko nayi kokarin haka se fuska ta ta bayyana halin da nake ciki, idanuna da suka yi jajir na kalli mariya dasu se kuma na juya na shige ɗaki da sauri ita kuma ta raka bayan da harara.
Cikin son karfafawa kaina gwiwa na dinga tausar kai na dan na gaji da kukan da nake yiwa mariya, na gaji da bata hawayena kan ta, na gaji da komai ma na ta.
Haka na wuni a daki saboda bana san fita balle shaidan ya raya min wani abu na biye mata balle kuma azo ace laifi na ne kamar yadda ake ɗora alhakin komai dake faruwa a kaina, saboda ita ɗin kirsasshiyar mace ce da gane halinta na gaskiya se wanda Allah ya ciyar kamar dai iri na da zama ya haɗa ni kishi da ita na zama victim.
Washegari ban taya jiran wata Ilham ba na tafiya ta aiki, ko da na gama na dawo a nan na tadda me gidan ya dawo dan ina shiga falon idanun mu suka sarƙe cikin na juna, wani kallo me zafi na watsa masa cike da jin haushin sa, tun da mutumin nan ya tafi be kira ni ba balle text, ni nakira shi ya turo min kalmar "busy", daga ita kuma be kuma cewa komai ba haka kuma be neme ni ba, wanda in rayuwa da adalci kamata yayi ko da ace busy din ne in yayi free ya Kira ni yaji ya nake, ya bani haƙurin tafiya batare da ya sanar dani ba tun da ina da hakki amma duk be yi haka ba se dawo wa nayi na tadda shi a dararraje cikin iyalin sa suna hira cikin farin ciki da alamar rayuwa ta gama yi musu daɗi.
Ko da nayi sallama ban lura da sun amsa ko ba su amsa ba nasa kai ciki, kamar in wuce batare da na kula shi ba se kuma zuciya ta tuna min da zaman kishiya a tsakanin mu wato Mariya, haka na daure cikin son nuna babu wata matsala tsakanin mu na tafi gare shi da niyyar yi masa side hug amma se ya goce yana watsa min zazzafar harara lamarin da yasa na ɗan yi turus cike da kunyar yarfa nin da yayi a gaban kishiya
"Daga ina kike?".
"Wajen aiki".
Na bashi amsa a sanyaye idanuna na cika da hawaye
"Me ya hana ki kai baby school?".
Ɗan jim nayi kafin na buɗe baki
"Bata shirya ba ni kuma zan makara".
"A'a Khadijah kiji tsoron Allah gwara ki faɗa masa gaskiya kawai, wallahi dear tun seven na safe baby take a shirye, dalilin ta na kin kai baby kawai dan tayi abu ba daidai ba na yi magana ne. Wai baby ce tayi mata rashin kunya shine ta mari bakin ta da kuncin ta tare da murde mata kunne, to ganin yadda ta dawo da zazzaɓi a jikin ta fuska a kumbure yasa na yi mata magana, daga cewa ta dinga sassauta hukunci shikenan take fushi da mu a gidan nan, ko magana bata kuma yi min ba tun jiya har yau da ta fita shine kuma dalilin barin Ilham, dan Allah ka bata hakuri, Khadijah kiyi haƙuri ni ba da wani abu na faɗa ba".
Irin yadda take tsara labarin abin da be faru ba tare da cakudawa da burbushin gaskiya yasa kawai na zuba mata ido na ma kasa magana, shi kuwa Salees batare da binciken gaskiya ne ko karya bane ya hau kai ya zauna ya dinga surfan bala'i, yi yake kamar bazai daina ba, nikam da na gaji kawai na wuce su na shige ɗaki na kama kuka dan na kasa daurewa.
Wai ashe laifi nayi da na tafi na bar shi a wajen, bawan Allahn nan be yi duba ga halin da nake ciki ba, be min adalcin jin ta baki na ba, be tausaya wa ƙaddara ta ba ya kira Hajiya Iya ya shiga faɗa mata karya da gaskiya.
Kiran wayar Hajiya Iyan ne ya katse min kuka na inda tace tana jira na gobe a gida, da toh kawai na amsa na kashe wayar raina a bace, zuciya ta cike da kunci dan nasan a can ɗin ma ba za'a saurare ni ba, ba za'a bani dama ba, za'a yanke min hukuncin da aka so ne kawai bisa doron son zuciya, nikam ina ganin ƙaddarar rayuwa.............!.
Ouummey 📚✍🏻
Ouummey 04 {4/30/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 004
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
Ragowar ranar nayi ta ne cikin damuwa da tunani, kwata kwata na rasa meke min dadi a duniya, irin yadda kaddara ke kwallo da rayuwa ta abin ba'a cewa komai.
Ko da dare yayi kasa barci nayi, so nake na samu wani mu zanta ko naji sanyi cikin rai na sai dai na rasa wa ya kamata na yi maganar da shi, Ummi na kullum cikin son ganin ta kwantar min da hankali take inda ni kuma nake tabbatar mata lafiya nake a kullum ko da ba hakan bane saboda gudun shigar ta damuwa, yaya ta daya mace wato Salima sai dai bana jin zan iya maganar nan da ita saboda gudun sa ta jin kunya, ragowar yayye na biyu maza ne, duk da suna tausaya min suna kuma so na sai dai bana jin zasu gane halin da nake ciki.
Ban san yadda aka yi hannu na ya danna number Abban mu ba kamar yadda muke kiran mahaifin mu se jin muryar sa nayi yana min sallama, a lokacin dukkan wani rauni da nake ta boye wa da dannewa ya bayyana kan sa ta yadda ban san ya akayi ba se ji nayi na fashe da matsanancin kuka me tada hankalin duk me saurare, shiru Abba yayi be kuma cewa komai ba tun bayan amsa min sallama da yayi, haka ya bar ni nayi kuka na har na gaji murya ta ta dusashe kafin can kasa yayi gyaran muryar da ya shaida min yana bukatar in saurare shi, ban musa ba na katse ragowar kuka na se yar sheshsheka da ajiyar zuciya.
"Uwatah".
Yadda ya kira sunan cike da kwantaccen lafazi da sanyin murya yasa naji sabon kuka na neman kufce min, na amsa masa da murya me rawa
"Na'am Abban mu".
"Bani hankalin ki nan ki saurare ni sosai".
A wannan karon itama sheshshekaar dakatar da ita nayi tare da sake shigewa cikin katifar gado na me aminci
"Rayuwar duniya gaba ki dayan ta jarrabawa ce, ita kuwa rayuwar aure yar hakuri ce, uzuri a gurin da babu muhallin sa, kau da kai a abinda yake zahiri ko da an cuta maka, danne bukatar kai saboda ta abokin rayuwar ka, ji ka nuna baka ji ba, ka gani ka nuna baka gani ba haka kuma a taba ka ka nuna baka san an yi ba ta hanyar yafiya.
Base kin ce min komai ba ba kuma se kin fada min halin da kike ciki ba, kukan ki ya bayyana min komai, sai dai ina so in tuna miki da abin d kika manta, ni baban ki ne, dan Adam kuma ajizi, da ni dake Allah muke bautawa gaba ki daya haka kuma wajen sa muke neman taimako, kama ta yayi da damuwa tayi miki yawa ki tashi ki dauro alwala ki fuskanci qibla ki kai kukan ki wajen me duka cikin kaskan da kai, yi masa kirari da kuma tsarkake shi, ina me tabbatar miki da wallahi in kika yi hakan zaki sami saukin kome ke damun ki, damuwar ki zata yaye, ruhin ke ze aminta haka kuma zaki sami nutsuwar zuciya.
Ba kamar ni ba da in kika fada min sai dai in miki kalamai wanda bayan haka ba abinda zan miki in Kuma ba so kike in zama uban kawai me shiga sha'anin rayuwar auren yar sa ba.
Yanzu maza ki tashi kiyi kamar yadda na fada miki kinji, insha Allah nima zan taya ki, a kullum cikin addu'a ta kike uwatah ke da sauran yan uwan ki amma zan kara da izinin Ubangijin mu, ina fatan Allah ya yaye miki kome ke damun ki, ya aminta da ruhin ki ya kawo miki sauki da salama a rayuwar ki, zan kira ki da safe, Allah ya bamu alkhairi".
Kit Abba ya kashe wayar sa da ya gama min wannan bayanin, be saurare ni ba, bance masa komai ba game da halin da nake ciki amma ga mamaki na wallahi se na ji kaso fiye da hamsin cikin kuncin da nake ci ya kau, lallai na gaida iyayen mu, ya Allah kasa iyayen mu su cika da imani ka saka musu da mafificiyar aljanna, Amin.
Batun yanzu ba ina sha'awar rayuwar Abban mu da Ummin mu, so da yawa ina fadar in da ace kowane miji kamar Abban mu yake da ba'a samu gurbacewar rayuwar aure ba, da ba'a sami yawaitar matsalolin aure ba, da ba'a samu yawaitar zawarawa ba haka da mata basu ji tsoron aure ba, in Kuma na dube shi ta fuskar uba se in ga lallai babu ya'yan da suka kai mu yin dacen uba nagari, se in dun ga tausayin wanda Abba be kasance mahaifi gare su ba har in dinga ganin lallai sun yi rashi babba.
Alwala nayi na shimfida tsaftatacciyar pray mat dina dake nan kamar sabuwa saboda samun gyara na sa wadataccen hijab dina na kabbarta sallah, a cikin kowace sujjada kuka nake yi gaban Ubangiji ina rokon sa sauƙin rayuwa, farin cikin rayuwa, haka kuma yayewar bakin ciki tare da cikawa da imani, irin kukan da nayi ba zan ce ga sanda nayi shi ba dan tun da na dora goshi na a kasa naji bani da wani sauran karfi ko kwarin zuciya.
Cikin ikon Allah na yi raka'a goma wato sallama biyar sannan na daga hannu na cigaba da addu'a, ina shafawa na dau Kur'anin da na aje gaban sallaya ta na budo Suratul mu'umin na soma karatu cikin kyautatacciyar kira'a murya can kasa dan gudun takurawa abokan rayuwa ta a gidan, sai da nayi surori uku bayan ta sannan na rufe tare da sake wasu addu'o'in
Showing 6001 words to 9000 words out of 43434 words

Ƙanƙance ido tayi cikin rashin mamaki balle damuwa

____________________________________________________________________________
_Free Chapter Four_

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3 Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15