Meemah kiji tsoron Allah ni kuwa me nayi da zaki fada in ba kalin sharri ba".

Dariya Meemah tayi ganin yadda Addan tata ta firgita

"Ki bari kawai na fadawa Dada da Adda Haanah kin sha ruwan sanyi immediately after you wake up".

Rau rau da ido Meerah tayi tana kallon Haanah wadda itama ke kallon ta jin abinda tayi bayan likita ya hana ta kuma ta sani

"Why, meyasa kike yin haka Ameerah?".

Sharrr hawaye suka zubo mata dan suna bala'in tsoron baban su dan duk yadda yake wasa dasu yake son su baya hana ya hukunta mutum in yayi ba daidai ba

"Am sorry Dada Allah ba zan kuma ba".

Shiru yayi mata hakan yasa ta kara volume din kukan ta tana bashi hakuri

"Will you pls keep shut, ko baki ga tuki yake ba?".

Kamar an yi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan ta bayan Haanah ta mata magana, ba wanda ya kuma magana se Meemah dake wasan ta ita kadai har suka kai gida, kowa ya dauki bag din sa suka yi falo.

A tsakiyar falon ya tsaya ya zuba wa Meerah ido cikin hukuntata dasu wanda duk yayi musu irin haka suke gwammace wa yayi fada ko ma duka akan wannan silent punishment din.

"Ciki na ne naji yana zafi Dada shine nasha amma ba zan kuma ba, am so sorry pls Dada".

Kallon Haanah yayi se ta langwabar masa da kai alamun itama tana bashi hakuri, dauke kai yayi ya kalli me kawo gulmar Hajiya Meemah, wai dan gulma itama yarinyar nan se ta karyar da kai gefe wai itama hakurin take bashi, wannan dabi'a tasu na matukar burge shi tare da faranta masa rai.

Gashi dai basu yi laifi ba Ameerah ce kadai tayi, amma yanzu da zai nemi hukuntata se duk hankalin su ya tashi ba kuma zasu koma daidai ba har se ya hakura kamar dai yanzu.

Girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom din sa leaving them behind Wanda Haanah ta fahimci ya hakura ne dan haka ta ce

"Se ki tashi ai babar marasa jin magana,ban da wulakanci so nawa kike so in nanata miki ki daina shan ruwan sanyi da safe after kin fi kowa samun you're not fine Amma shine bakya ji, to go ahead and kill yourself se mu zauna mu uku, kinga se mu dinga lissafin ke da Maamah bakwa tare da mu".

Yadda muryar ta ta shiga rawa bayan ta kai karshen zancen ze tabbatar maka tana cike da kewa da alhinin wadda ta kira ga Maamah a ran ta, fashewa da kuka Meemah tayi tana kiran Maamah, ita wallahi Maamahn ta yasa hankalin su tashi.
Shaf Haanah ta manta da cewa tan wajen ya sa ta ambaci sunan Maamahn ashe rabon ta jawo musu jidali ne .

Fitowar Dada da sauri daga dakin yazo ya dauki Meemah tare da ɗorawa a kafada ya shiga aikin lallashin ta, wannan yanayin ya karyawa Haanah zuciya ta shiga hawaye da shessheka abinda yasa itama Meerah fashewa da kuka.

Gaba daya se ya rude ya rasa ya ze yi, waye ze lallasa ma ya rasa se kawai ya juya ya zuba musu idanun sa da suka kada sukai jajir, hada idon da suka yi da Haanah da yadda taga jan da idon sa yayi yasa ta san lallai sun tayar masa da hankali, hakan yasa tayi saurin dakatar da kukan ta ta shiga lallashin Meerah har tayi shiru, jakunkunan su ta dauka ta kai bedroom ta dawo taja hannun Meerahn zuwa bathroom din da ta haɗa mata ruwan wanka, se da ta shiga wankan ita kuma ta fito mata da kayan sawa sannan ta fita.

Kan kujera ta tadda shi zaune ya dafe kan sa ga Meemah a kan shi tana birgima da kuka, da gudu ta karasa tana kokarin daukar ta wanda se lokacin ya bude ido ya girgiza mata kai a hankali sannan ya dago Meemah daga jikin sa

"Shhhhhh, is okay pretty".

A hankali ta fara reducing volume din kukan ta har ta daina gaba daya se ajiyar zuciya da take yi a kai a kai

"What's the problem pretty nah?".

"Dada Maamah".

Ta fada a shagwabe da muryan kuka, seda ya hade abin da ya tsaya masa a makoshi sannan ya iya daurewa ya kakaro wani busasshen murmushi yayi mata yana riko yan mitsi mitsin fingers din ta

"Maamah tayi tafiya na fada Miki sweery".

"Yaushe zata dawo?, Ni dai akai ni wajen ta".

Ta fada tana neman fashewa da wani kukan sedai be bari ba yayi saurin tallafo habar ta

"Look ta kusa dawowa, taje can aljanna ne fa, kin san aljanna akwai dad'i ko shiyasa Maamah bata dawo ba amma zata dawo".

"Da gaske tana paradise Dada?".

"Eh mana princess".

"Yanzu tana can tana cin fruits din aljanna? Su Apple, banana, orange, pineapple, mango, strawberry and...se me ma Adda Haanah?".

Ta fada directing the Question to Haanah, murmushi ta mata trying to karasa calming nata tare da dauke mata hankali

"Eh mana dear, har dasu pawpaw fa, ga kuma su plantain and more".

"Allah yasa zamu shiga aljanna irin na Maamah mu ma muje mu yi ta cin dadin mu".

"Ameen pretty jeki Adda tayi Miki wanka a canja uniform ko".

Tura baki tayi tare da girgiza kai

"No Dada, yau kai zaka yi min, ka manta ka ce min zaka min wankan so biyar in naje school ban yi kuka ba, and kuma ban yin ba ko".

Gyada mata kai yayi yana yake ya mike da ita dauke a jikin sa ya wuce dakin su Haanah na bin su a baya, ita ta haɗa ruwan wankan shi kuma yayi mata, ana yi tana wasan ta tare da bashi labarai kai baka ce yar shekara uku da rabi bace, seda ya shirya ta cikin jeans da riga sannan ya nufi fita se kuwa ta daga murya tana magana irin wai ita tayi masa yadda ze ji ne tun da yayi nisa

"Kar kace wa Maamah ta dawo da Dada, ka bar ta a paradise din ta tayi ta cin dadin ta amma ka fada mata kar ta cinye duka ta rage min".

Wannan karon kam ba yake bane sahihiyar dariya yayi jin wani shirme amma se shima ya dan daga muryar sa kadan ya amsa mata da

"Okay princess bari in je in fada mata".

Da "toh Dada" ta amsa masa tana kwanciya kan dan Karamin gadon ta me kyau shi kuma ya fita,

"Je ki sa a shirya mana table Meerah, lemme take a shower nima".

"Okay Adda ".

Ameerah ta fada itama tana ficewa saura Haanah da Meemah

"Kar ki je ko ina ko da kuwa falo ne har se na fito, and kar ki fara yi min barna if not".

Ta fada tana mata kallon gargadi sosai, cike fa biyayya ta gyada kan ta tana sa bmhannu cikin baki, shigewa bayin haanahytayi daure da towel yana saurin tayi tai wanka kafin Meemah ta bata matsala.

_____

Yana shiga dakin sa ya fada ka bed hannun sa biyu dafe da kan sa da yake jin kamar ze rabe masa biyu, wani irin ciwo kan ke masa na tsananin damuwa da rashin bacci ga kuma yawan tunani dake addabar sa.

Da kyar ya iya mika hannu ya bude drower ya debo maganin da be tsaya duba na mene bane ya afa a baki batare da ruwa ko wani abu ba ya shiga taunewa, dacin da ke ratsa bakin sa be kai wanda zuciyar sa ke masa ba, jiki ba kwari yasa hannun ya sake dafe kan yana rurruntse idanu

"Me yasa Maryam, me ye laifi na, me muka yi miki da zafi da kika zabi yin nesa da mu bayan kin san muna tsananin bukatar ki?, Me yasa kika zabi barin yayan ki da mijin ki cikin wani hali?".

Dan juyi yayi kadan a gadon se kuma ya cigaba

"Na sani laifi na ne ko, shikenan am sorry Maryam, am really sorry but pls do believe that I so much love you Maryam, Ina matukar son ki mairo na, dan Allah ki dawo gare mu ko dan ya'yan mu, kin ga kullum se pretty tayi kukan ki, pls Maryam ".

Kamar kuma wanda ya farka daga bacci se ya bude idanun sa wal wanda suka yi jajir kamar wanda jini ya kwanta

"Astagfirillah, forgive me ya Allah, astagfirillah ".

Se kuma ya sake dafe kai

"Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagees".......

Ouummey 📚✍️.











Ouummey 12 {5/11/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey






                     Ouummey 12
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

               _Free Chapter Twelve_

Haka ya wanzu dafe da kan sa da ke masa matsanancin ciwo cikin wani hali, kirjin sa wani irin bugu yake masa kamr ze faso waje, irin yadda kan sa ke sarawa ji yake kamr ya cire ya yar.

Wuni guda haka ya wuni cikin wannan har zuwa karfe biyar da ya iya tashi yana dafe bango saboda jirin dake dibar sa, yana ji ana kiran sallar Asr amma ya kasa tashi har aka idar duk akan kunnen sa.

Anan bedroom din yayi alwala ya gabatar d sallah a zaune saboda jiwar da yake gani, addu'ar da yake so yayi ma kasawa yayi dole ya silale ya kwanta kan praymat din yana runtse ido.

      Oat din ta damawa Miemie kamar yadda suka fi kiran Meemah saboda sunan Maamahn su da taci sannan ta fita zuwa dining dauke da ita a hannun ta ta zaunar da ita kan seat daya itama ta zauna a daya, Ameerah ta zubawa abinci a plate ta tura mata gaban ta hakan yasa ta kalle ta cikin rashin fahimta dan mostly tare suke ci
"Eat your food Ameerah and pls do take care of Miemie bari na gano Dada".

Gyada mata kai Meerah tayi iya kuma ta shiga zuba abinci cikin plate daban, faten dankalin turawa me ruwa ruwa ta zuba masa da ya sha kayan lambu da kuma hanta sosai, cikin nutsuwa ta dora kan madaidaicin tray tare da dora goran ruwa me madaidaicin sanyi se kuma lemon kwali ta dauka ta nufi falon sa.

Kan Centre table din sa ta aje abin kana ta karasa kofar bedroom din sa ta shiga knocking ganin bata gan shi a falon ba, a hankali take knocking din dan har ta takura masa sanin da tayi baya san hayaniya, jin shiru yasa cike da fargaba ta fara tura kofan a hankali har ya bude sosai kana ta shiga bakin ta dauke da sallama.

A gigice ta karasa wajen da yake kwance ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa sedai ya kasa amsa wa, wannan ya kara gigita Haanah ta nemi fita a guje dan neman wanda ze taimaka mata a kai shi asibiti amma dole ta tsaya jin yadda ya riko hannun ta.

"Yanzu zan zo, am coming Dada, zan kira maigadi ya taimaka min mu kai ka asibiti ne, sannu Dada yanzu zan zo".

Da kyar ya motsa bakin sa yayi magana cikin muryar sa dake fita da kyar

"Dauko min drugs dina a drawer Haanah".

A rude ta shiga amsa masa tana mikewa

"Toh Dada, sannu bari na dauko, sannu Dada".

Da tarin magungunan ta dawo gaban sa ta zauna kana ta dauko wanda ze sha kasancewar ta san prescriptions din sa, bottle water din ta bude ta aje kana ta fara kokarin taimaka masa ya tashi zaune, duk da yanayin da yake ciki seda murmushi yayi escaping daga lips din sa, yo Allah ya tuba Haanah ko motsa shi zata iya yine balle ta daga shi.

"Sannu Dada, sannu, open your mouth ka karbi maganin kaji".

A hankali ya bude bakin ta sa masa kwayoyin kana ta sa masa bakin robar ya shiga shan ruwan, seda ya hadiye maganin gaba daya sannan ya janye bakin sa yana sakin numfashi kasa kasa, komawa yayi ze kwanta tayi sautin rike hannun sa tana girgiza masa kai

"A'a Dada, kar ka kwanta maganin ze dame ka, ka dan zauna kadan ya fada maka, lemme bring your food tukuna".

Jingina yayi kamar yadda ta bukata ita kuma tayi saurin fita zuwa inda ta aje abincin sa ta dauko masa, cokali tasa ta debo tare da kai masa baki taba fadin

"Dada haaaaa". A tausashe, girgiza mata kai yayi alamun a'a se kuwa ta kwabe fuska tana neman yin kuka

"Pls Dada ka daure kaci ko ka sami karfi kuma ciwon ya tafi, You know bamu da kowa a duniyan nan da ya kai ka Dada, we loose our Maamah ba zamu so muyi loosing din ka ba, you're all we have, our only strength and source of happiness, pls eat for our sake Dada, for your little ones kaiiii".

A sannu ya bude bakin kamar baya so ko da yake ba kama bane baya so din, ze ci ne dan su kamar yadda ta fada dan mafi girman tashin hankalin sa shine ganin damuwa kan fuskokin ya'yan sa, har can go to any limit dan ya sa su farin ciki ko da kuwa shi baya ciki, a hankali a hankali ya dinga karbar abincin har ya koshi, she's glad ganin yaci da yawa dan farin cikin ta sosai ya bayyana kan pretty face din ta taba ta sakin cute smile

"Ka gani Dada, dama kana jin yunwa, kalli fa ka kusan cinye wa na ji dadi, yanzu zuwa anjima zaka iya kwanciya amma da zaka hakura har kayi isha tun da kaji ana sallan magrib yanzu".

"Allah yayi Miki albarka Rayhanah, Allah ya hada kan ku da yan uwan ki ya albarkace ku da mazaje nagari".

"Ameen Dada, Ameen, in kama ka kaje kayi alwalan?".

Dariyar sa me kyau yayi

"Haba dai, Dadan ki is not as weak as you're thinking, zan je da kaina, kema je ki kuyi sallah da yan uwan ki and stay with them nima yanzu zan fito".

Pecking goshin sa tayi tana wide smile
"Okay Father, a fito lafiya".

Ta fice rike da tray din kayan abincin sa, a falo ta tadda su Miemie da Ameerah zaune suna kallon cartoon, kallon ta Meerah tayi tare da daga mata gira alaman yaya yake and she answered cikin yi mata alama da hannu alamun he's fine.

Duk suna yin body language ne saboda Miemie dan tana jin ance Dada sun san zata addabe shi ne ta hana shi sukuni da kiran Maamah da a rana se ta kira yafi cikin calbi.

Rayhanah bata mamakin hakan dan a bayyane yake Miemie Maamah's girl ce akasin su da suke Dada's babies, a rayuwan su basu taba sanin wani abu wai shi kulawar uwa ba hakan yasa tsakanin su da ita kallo ne da gaisuwa, daga nan kuma se su takure waje daya, walwalar su kuwa har se idan Dada na gida.

Zama tayi kan dining ta dan ci abinci a gurguje kana ta tashi zuwa bedroom tana musu magana

"Oya girls, time for magrib prayer".

Tashi duk suka yi zuwa dakin inda one after the other suka yi alwala Ameerah tayi wa Miemie sannan suka saka hijabs din su da Rayhanah ta dauko musu kana suka jeru kan praymat daidai lokacin da Dadan ya leko, ganin su a haka ya juya ya fita zuwa Masallaci suma suka tada nasu sallan.

Suna idarwa suka yi azkhars din su again Rayhanah ta tashi ta dauko musu kur'anan su dake bedside drawer ita da Meerah suka fara karatu inda Meerahn ke biya mata karin da aka yi musu juya zuwa na yau, seda suka gama sannan ta kara mata verses biyar inda ita kuma ta cigaba da maimaita wa Haanah kuma ta koma ga Miemie.

Cikin wayo da dabarar da Allah ya mata ta yi sa Haanah ta biya mata aya dayan da ta kara musu yau a school, tar yarinyar ta kawo karatun ba ko tuntube hakan yasa ta kara mata aya biyu marasa tsayi, shima se da ta ga ta iya sannan ta bar ta.

Hijab ta cire ta karbi nasu ma da suka cire ta ninke tare da maidawa cikin wardrobe kana ta juyo se kuwa idanun ta suka fada cikin na Dadan ta da ke tsaye yana bin ta da kallo cike da soyayya da kauna me tsanani, a ko da yaushe ya kai kan sa kasa da sunan sujjada baya dagowa face yayi godiya ga Allah da ya albarkace shi da samun ya daya tamkar da dubu, yar dake matukar so da kaunar sa hadi da tsananin tausayin sa, yar da ba dan ita ba be san yaya rayuwa zata kasance masa da yaran sa ba alhalin yanzu da ba mahaifiyar su ta gushe.

Rayhanah yarinya daya ce amma a wajen sa tafi yaya dari domin kuwa ta share masa hawaye tun kan ta san kan ta, tun tana karama take da basira da wayo hadi da nutsuwat fahimtar abubuwan da suka girmi hankalin ta, a maimakon abin ya dame ta yasa ta cikin wani hali se ya koya mata tausayin mahaifin ta da halin da yake ciki, wanda ta taso ta girma dashi ya ke kuma karuwa a kowace kwana da wuni, kaunar ta gare shi bata buya a ko ina a kuma ko wane irin yanayi, ita ce rai daya dake gane kowane irin hali yake ciki tun kafin bakin sa ya furta, ta san shi ciki da waje sedai kawai yayi mata ta babba da yaro ya layance mata wasu abubuwan amma ba wai dan bata fahimta ko gane ba.
Tana fifita cin sa kan nata, walwalarsa kan nata, farin cikin sa kan nata haka kuma tana damuwa da damuwar sa tayi dariya
Showing 27001 words to 30000 words out of 43434 words