wa zaki yaudara da kalaman ki ko da wani fuskar tausayi bayan ke baki tausaya wa kan ki ba, daga yin mafarkin ki kin biyo ta a guje kin daki cikin ta yarinya ta tashi da ciwon ciki da zubar jini, hankali be kwanta ba har seda cikin jikin ta ya zube, cikin yan uku annamimiya kin yi mana asarar rai har uku, wallahi Allah ya isa tsakanin mu dake dan ba zamu taba yafewa ba".
Hajiya Ramatu mahaifiyar Mariya ta fada tana fashewa da kuka yayinda Hajiya Iya ta shiga sharar ido itama su kuma ya'yan su suka rufe su suna basu hakuri da fadin Allah ze saka musu, ni dai tun jin wai Mariya tayi mafarki na se na juya gare ta na zuba mata jajayen ido na ina kallo na tsayin lokaci kafin cikin wata irin murya na tambaye ta
"Na zubar Miki da ciki ta hanyar maita ko Mariya?, Kin yi mafarki na na daki cikin ki gashi kuma ya zube ko?".
Kallo na Mariya take yi kawai bata ce komai ba hakan ya sa na saki wani busasshen murmushi mara kyau balle fasali haka mara ma'ana
"In har na zubar Miki da ciki, in har na taba yin wani abu dan cutar da ke ko ya'yan ki Allah ya saka Miki da gaggawa Mariya".
Na fada da karfi ta yadda kowa ze jini kana na maida duba na kan Hajiya Iya da Hajiya Ramatu
"Kuyi hakuri Hajiya, kuyi hakurin cinye muku cikin Mariya da nayi kuma ku kwantar d hankalin ku domin ba zan kuma saukar da kwadayi na kan ya'yan ku ba".
"Kuma kuyi hakuri". Na fada directing to su Safara'u da ragowar matan da kuma su Rukayya kana kuma na tashi da sauri nayi daki na tare da kullewa da key, irin ciwon da zuciya ta ke yi a lokacin ba me sauki bane, hawaye ya kafe a idanu na, ƙwaƙwalwa ta ta tushe na rasa tunanin da zan yi, daga karshe se na samu kaina da nufar toilet na dauro alwalar da ban san daidai nayi ta ba ko akasin haka, Kur'ani na dauka na shiga karatu a zuci kafin a hankali murya ta ta fara fitowa kadan kadan har ta fito sosai kana kukan ya biyo baya.
Ina jin bugun kofa tare da muryar Salees amma ban ji a raina zan bude kofar ba, ina kuka haka ina karatu ban fasa ba har se da naji mafi girman kason nauyin zuciya ta ya ragu, wani irin bacci ya dinga sanda ta sannan na aje Kur'ani na bingire a wajen.
Ban farka ba se bayan magrib, a lokacin kam alhamdillah bana jin wani bacin rai me girma sedai kalmar maita ta samu wajen zama na musamman a ƙwaƙwalwa ta, seda nayi wanka na canja kaya na ci snacks dina sannan na bude kofar na fito, babu kowa a falon haka kuma gidan yayi shiru alamun duk sun tafi, fridge na bude na dau ruwan da ya fito dani sannan na nufi komawa daki se Salees da ban lura dashi zaune kan kujera ba ya dakatar dani
"Khadeejah".
Juyowa nayi na kalle shi tare da sake masa murmushi ganin yadda duk yayi wani iri, tasowa yayi gare ni tare da riko hannaye na
"Are You fine, ba abinda ke damun ki, ba inda ke Miki ciwo?".
Wani murmushin na sauke jin tambayoyin da yake min wanda shima ya san in nace bana jin kome ya fada karya ne sedai dan na kwantar masa da hankali se na amsa masa
"Ka kwantar da hankalin ka, am perfectly fine and okay".
"Abinda hajiya iya su.....".
Rufe masa baki nayi da hannu na har lokacin murmushi na be bace ba
"Hajiya Iya kamar Ummi na ce, so karka damu da abinda ya faru".
Daga haka nayi gaba leaving him speechless.
Kwanciya nayi kan bed tare da janyo waya ta, ina bukatar shawara a wannan lokacin dan ina jin bazan bar wannan maganar ta tafi haka ba, dole zan dau matakin wannan bata sunan da ake kokarin yi min, kotu zan kai kara, shigar da kara zan yi abin min hakki na, amma kafin nan ina bukatar tattaunawa da wani, ina bukatar wani da ze yi supporting dina ya fada min Yes kin yi daidai Khadijah sedai waye wannan?.
Ba ze yiwu in fadawa Ummi ba balle har hankalin ta ya tashi, yaya Salima kuwa na san in na fada mata kamar na fadawa Ummi ne dan se ta sanar da ita, Abba kuma is not a solution dan hanani ze yi yace in yi hakuri, yayyu na kuwa ba ma zan iya maganar dasu ba dan suma maza ne ba fahimta zasu yi ba.
Na dade rike da waya a hannu kafin na shiga facebook, group din mu na NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS na shiga nayi posting anonymous message, in brief na fadi matsala na tare da neman shawara bayan na canja abubuwa da yawa daga abinda ya faru dan gudun halin mutane na daukan matsalan mutum suyi ta yadawa.
Kafin kace me members suka shiga reacting tare da comments, ban duba ba seda na tara da dan yawa sannan na shiga bi one after the other, sannu a hankali nake karantawa ina analysing bangaren shawarar da tafi yawa, in yi ko kar inyi da dalilin haka, sedai mostly duk suna cewa kar in Kai karar ne saboda ba kowa yayi accusing din ba face uwar miji na, duk kuma so d kaunar da mijina ke min base goyi bayan kai mahaifiyar sa kotu ba hakan kuma ze iya kawo karshen aure na, in bar su da Allah kawai in cigaba da fada masa ze min sakayya da gaggawa.
Wannan itace shawarar da na dauka, se da na gamsu da ita sannan na kashe datan na koma na kwanta ina cigaba da tunani.
Washegari haka na shirya na taci aiki na sedai kukan da nayi juya yasa fuskana duk ya tasa duk da kuwa na dan shafa powder da kohl dan ya boye yanayi na, karfe goma na safe muka shiga meeting din da anan ne za'a fadi list din sunan mutanen da suka yi dace da samun promotion da kuma gurin da aka canja musu na aiki in an canja din.
Suna na ne na biyar a list din, wani irin sassanyan farin ciki da ya sauka a raina a lokacin ba zan iya fada ba sedai be yi nisa ba ya gushe jin an canja min garin aiki an maida ni garin Bakwarni maimakon garin Darma da nake, sanyi jiki na yayi dan a bayyane yake dole haka zan hakura da promotion din in cigaba da zama a nan dan baze yiwu in tafi wani garin aiki ba bayan aure na da mijina na garin Darma ne.
Sunan Salees shine na goma sha biyu dan daga kasa aka fara zuwa sama, shima ya samu promotion me girma haka kuma shima an canja masa gari zuwa Bakwarni lamarin da ya faranta min fiye fa komai dan bana tantama yanzu kam zan je tun da shima dole ya koma can.
Da wannan farin cikin na dawo gida ina tsara yadda zan je in yi wa family na sallama dan sati kadai aka bamu muyi reporting sabon wajen aikin mu, ranar kam a gidan Ummi na na wuni dan saboda guilty din abinda su Hajiya Iya suka yi min Salees ya bar ni na wuni can.
Shawarwari masu yawa Ummi ta bani wanda naji dadin su n al'umma kudire niyyar aikata wa insha Allah, na ziyarci yan uwa da yawa a satin har ranar tafiyar mu yayi.
Ranar asabar da yamma muka yi sallama d jama'a muka dauki hanyar garin Bakwarni ni da Salees da driver, tafiyar awanni goma sha biyu da mintina ya kai mu cikin garin Bakwarni, gidan da Salees ya siya muka sauka dan shi ya zo so daya ya duba yanayin garin tare da siyan gidan da zamu zauna.
Tsananin gajiya be bar ni na yi komai ba a ranar se washegari na gyara ko ina na shirya mana kayan mu, gidan yayi min matuka dan bedroom uku ne se kitchen da toilet a falon, haka kuma each bedroom na da nashi toilet din.
Washegari monday muka yi reporting wajen aikin mu in da Salees ke da matsayi na uku a ma'aikatar ni kuma matsayi na biyar, aiki sosai muka yi dan daidaita alamura ta yadda aiki ze mana sauki, a ka'ida a ranar zamu yi meeting da general head na ma'aikatar gaba daya sedai ya bada uzirin baze samu zuwa ba so a ka daga meeting din zuwa ranar da ya dawo daga tafiyar da yayi.................
*GEN GEN GEN, END OF FREE PAGES YA ZO, DAGA GOBE ZA'A GAMA FREE CHAPTERS AND D SAGA IS YET TO BEGINS.
KINDLY HURRY UP AND MAKE YOUR PAYMENT BASE MUN FARA A ZO ANA KOMAWA BAYA BA, OUUMMEY IS VERY AND VERY READY TO ENTERTAIN, EDUCATE AND MOTIVATE YOU WITH HER NOVEL RASHIN HAIHUWA, KAR KU BARI A YI TAFIYAR NAN BABU KU DAN WALLAHI YOU'LL MISSED.
INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT 👇
09013101854
Ouummey 📚✍️.
Ouummey 15 {5/15/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 15
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
Zuba mata ido kawai Falmata tayi tana kallo ta rasa me za tace, she's totally speechless da wannan aikin na Farida, ta sani su din sun dade da zamar wa juna yan uwa, sun fi karfin a kira su aminai balle kuma kawaye, matakin alakar su ya koma tamkar blood relatives sedai bata san har haka Farida ke matukar kaunar ta ba se yau.
A hankali ta kuma juya katin hannun ta wanda ba komai bane face passport, kana ta Kuma maida duban ta kan Farida da ita ma take bin falmatan da ido
"Dan Allah maimaita min me kika ce Farida".
"Wani abu na fada na daban ne?, Nace ga shi nan dan ki ya gama yi miki komai da ya kamata na tafiyar ki India, kuma insha Allah jibi jirgin ku ze tashi ke da harira saboda ta kula dake ni kin ga baze yiwu in bar su Hassana su kadai ba ga kuma Business din mu, amma tare zaku je da dan naki ya daidaita komai sannan ya dawo, nima kuma kafin ku dawo din zan zo dan jira nake ayi hutu su tafi gidan yayan nasu, a cikin wannan maganar me ne baki fahimta ba?".
Fashewa Falmata tayi da kuka, kukan farin ciki da kuma takaici at the same time, cikin muryan kukan take magana ma Farida
"Tun da muka taso da ke ban taba jin wai bani da dan uwa ko yar uwa ba a duniya saboda kin cike ko wane gurbi Farida, duk abinda kika san ina so yi kike kafin in furta, kome zan bukata aje wa kike kafin na ambata, ban san dame zan saka Miki ba Farida, ban san me zan Miki ba in biya ki, a kullum roko na Allah ya kara miki budi da daukaka, Allah ya jikan iyayen mu in basa raye, Allah y raya Miki zuri'a yasa masu amfani ne, Allah kuma ya bar ni dake har karshen nunfashi na.
Yanzu dai dubi Alhaji da nake karkashin sa, hakkin neman lafiya ta ke rataye a wuyan sa amma ya nuna lafiyar tawa bata gaban sa, ya tattara ya zuba min ido yaki yin wani hobbasa kan neman lafiya ta bayan babu rashi balle kuntata a tare dashi face zallar son zuciya da rashin adalci, b azan yi masa mummunan fata ba Farida amma tabbas da sannu se hakki na ya kama Alhaji in har ya zalunce ni".
Kwalla Hajiya Farida ta shiga gogewa tana duban Falmata emotionally,
"Ni ya kamata in Miki wannan addu'ar Falmata, ke din macece me kyakkyawar zuciya, ba ni na fara miki alkhairi ba halaccin saka alkhairi da alkhairi kawai nayi, kome Hammad ya zama a yau kin san dalilin ki ne?, Ko wace daukaka Hammad ze samu a rayuwar sa kin san kece jigo, ban da kuma tarin alkhairan ki gare mu tun Alhaji na da rai, Falmata kin so ni tun ina abin ki da gudu wajen jama'a, kin kusance ni yayinda kowa ke gudu na, kin tallafe ni lokacin da na rasa wani mataimaki, shin in ban Saka alkhairi ba me kike so a kira ni, balle kuma ni ina miki kallon yar uwa ce da muka fito daga cikin mahaifa daya, ko kin manta kece.........".
Da sauri Falmata ta sa hannu kan bakin Farida tana girgiza mata kai hakan yasa Farida ta cire hannun daga bakin ta
"In har ba kya san in tuna Miki to ki bar maganar dan in ance za'a ayi tone tone to kuwa kece kika yi sadaukarwar, ni kwatanta wa kawai nake, shi kuma Alhaji kamar yadda kika fada Allah ze Miki sakayya tabbas hakane, a da nayi niyyar in kin tafi can India nikuwa in shiga in fita har se na rama miki abin da aka miki sedai yanzu tsakani na ga Allah na fasa na bar shi da Allahn kamar yadda kika fada, ina kuma fatan ace an yi aikin nan cikin nasara".
"Allah yasa Farida, in har kuwa akayi Nasara ki rubuta ki aje se na rabu da auren Usman domin kuwa bashi da wani amfani gare ni ta kowace fuska".
"Allah ya kai mu, nidai fatana a dace in ga kin dawo gare ni lafiya lau, wannan shi ze samar min da kwanciyar hankali da nutsuwa".
"Allah ya yarda, in Kuma bani da rabo...".
Wani irin ƙatuwar harara da Farida ta balla mata yasa bata karasa a binda zata fada ba ta kyalkyale da dariya tana dagewa Faridan gira cikin tsokana lamarin da yasa suka tuna baya su ka kuma sake darawa sosai...
____________
"Yaaya na fadawa Haanah ai kar ace za'a sama min mata a bar ni in zaba da kaina".
Cikin son kwantar masa da hankali ta yadda ze amince wa kudirin ta ta shiga yi masa bayani
"Kar ka damu kan ka Ibrahim, duk abin da za'a bukata a wajen mace Saratu na dashi, halin ta kuwa base na ce maka komai b adan kasan daga gidan d take, fatana kawai amincewar ka dan ba zan maka dole ba".
"Amma yaya bakya tsoron a maimaita yar gidan jiya?".
Da sauri ta shiga girgiza kai
"Insha Allah ba abinda ze faru, bana fatan in maimaita kuskuren da nayi a baya shiyasa ma ban yi maka magana ba se da naji t bakin ita Rahinatun kuma alhamdillah tayi na'am dan yadda take walwala ya shaida min tana farin ciki da lamarin".
Shiru Dada yayi dan daga jin yadda Hajiya Yaaya ta ambaci sunan sa Ibrahim kai tsaye yasan ta kai makura wajen son hadin nan ta yadda komai daze fada ba zata gane ba duk kuwa da tace wai amincewar sa take nema dan haka se ya shafawa kan sa lafiya kawai
"Shikenan Yaaya, Allah ya sa hakan yafi alkhairi".
"Ameen, ko kai fa, insha Allah wannan karon se mun ce gwara da akayi".
Shidai be Kuma cewa komai ba har ta gama maganganun ta ya mata sallama ya fice, sedai fa a fili yake ya amsa mata ne kawai dan ba yadda ze yi dan ya kasa boye hakan a ransa, sanadin bacin da ran sa yayi ranar a gidan ya bar su Haanah suka kwana abinda ba ya iyawa se an kai ruwa rana dashi, jikin Hajiya Yaaya yayi sanyi ganin hakan se dai kuma wani bangaren zuciyar ta na fada mata ta share shi da sannu da kan sa ze dawo yana gode mata.
To abu kamar wasa karamar magana na neman zama babba dan kuwa sati biyu kenan babu Dada babu labarin shi, shi be zo gaishe da Yaaya ba kuma be zo dibar su Meerah ba, a kuma tsukin lokacin har an yi maganar sa da Rahinatu an karbi komai na aure in da saura kwana biyar a daura kasancewar ta bazawara.
Ba wanda ya kuma ganin Dada se ranar daurin aure wanda shima ya je ne dan kar ya kunya ta mahaifiyar sa cikin jama'a, haka yabi dangin amarya Rahinatu da ke ta masa barka da zuwa dan cewa Yaaya tayi wai yayi tafiya.
A ranar amarya ta tare inda Yaaya ta rike su Haanah wai zasu yi mata sati in da a fakaice ta bawa Dada da amaryar sa damar sakewa ne, dan a ganin ta yaran zasu takura su sedai bata san tayi wa amarya bukulu bane dan kuwa Dada tun da aka kai amaryar be kuma komawa gidan ba se bayan sati shima se da Haanah ta kira shi a waya cewar sun koma gida.
___________
Wata daya kenan da kwana biyu da fara aikin mu yau, shirin da muka yi yau na musamman ne dan tsawon lokacin da muke ma'aikatan yau din ne zamu fara ganawa da shugaban mu gaba daya don haka kowa ka gani cikin shiri yake tun bare da muka sami labarin he's a non nonsense Man, he's very strict and concentrated kan aikin sa.
Moroccon gown ce a jikina light purple in color se dark purple veil da nayi using, jaka na da takalmi duk dark purple, a rayuwa ta ina son purple dan lokacin da ina secondary school da miss purple ake nicknaming dina.
Gaban mota na hakim ce Salees ya shiga owner's corner ya tuka mu muka bar gidan zuwa ma'aikata,
Showing 36001 words to 39000 words out of 43434 words

____________________________________________________________________________
_Free Chapter Fifteen _

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13 Chapter 14Chapter 15