fasa yin abin kari ba sanin nike da girki, sharp sharp na hada breakfast tare da zubewa kan table kana na ɗora na Ilham da zata tafi dashi school sannan na koma ɗaki dan shirya wa zuwa wajen aiki, a hanzarce nake komai dan na makara saboda rashin samun bacci da wuri sanadin ɓacin ran Salees da mariya.
Sai da na tabbatar da zaman gyalen jiki na sannan na fesa turare kasa ƙasa wanda ba'a jin ƙamshin sa se an matse min waje sosai sannan na fito, kan table na tadda su zaune cikin farin ciki suna hira abin su, da ka gan su kaga wasu ma'aurata da rayuwa kewa dadi sabanin ni da rayuwar aure na ke cike da bakin ciki, ɓacin rai tare da takaicin da namiji iri iri.
Kau da damuwa ta nayi na shanye ta cikin ciki na na karasa tare da jan kujera na zauna
"Good morning zuma na, fatan ka tashi cikin koshin lafiya".
Na faɗa ina kissing lips din sa kana goshin sa sannan na juya ga mariya
"Barka da safiya maman Ilham, fatan kun tashi lafiya".
Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min har da yar dariyar ta
"Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka".
"Alhamdulillah kam".
"Ehm nace dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in ba wanda ya taɓa yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni kaina da Umma ke faɗa min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu, amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa".
Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan Ina zama na zubawa Salees, ban ɗago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa.
Wahalallen murmushi na kakaro na ɗorawa fuska ta na ɗago ina duban ta
"Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu".
Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son ƴaƴan sa tare da kulawa da duk abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir.
Tissue nasa na goge baki na ina miƙewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye da skul bag ɗin ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan.
Allah ya sani ina matuƙar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya taɓa faruwa.
"Good morning Daddy, good morning Mommy".
Ilham ta gaida iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake daidaita zaman mayafi na tare da ɗaukan handbag dina na kalli Salees
"Ni na tafi se na dawo".
"No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba".
Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na
"Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki".
"To Daddy".
Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take yin spoon na uku a abincin.
"Eat fast pls Baby, am already late".
Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga dama ba, nikam tuni raina ya ɓaci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta kafin ta gama shininnikin ta.
"Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama ba".
Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba
"Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many more, me kike nufi ne?".
Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na juyo Ina tausar Kai na
"Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara".
"Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar".
Ɗan jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara
"Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me ƙarfi, ko rannan ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan bata saba da hidimar yara ba".
Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya
"Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba".
Se kawai fuuu yayi sama,
"Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki faɗa haka, wallahi bana jin dadi".
Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na buɗe baki nasan ba me daɗi zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da ɓacin ran da ta jagoranci zama silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na
"Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in faɗawa uba na ya kai ni, atoh tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane".
Wal haka na ware idanuna na sauke kan fuskar yarinyar me cike da kuruciya hadi da yarin ta da a lokacin take shekara na sha uku, fuskar nan irin ta mahaifin ta a yamutse ta turo baki gaba cike da tsiwa yayinda madaidaitan idanun ta ke wulkitawa da hararar da take min.
Cike da wani kudiri a raina na mike tare da fita daga falon ina dan karkada mukullin mota na har na karasa tare da budewa, farar mota ce me kyau tasha wanki tana ta ƙyalli, da addu'a na bude mazauni na na shiga tare da rufewa kana nayi unlocking sabida ta shiga dan ina hango ta biye da bayana, murmushi nayi jin shigar ta bayan motar wato ta mai da ni driver Kamar yadda ta saba in tafiya ta haɗa mu tun da ta fara wayo.
Sai da muka hau titi sosai bayan na bawa me gadi ihsanin da na saba na cigaba da tuki na cike da nutsuwa, ba wata tafiye me nisa muka yi ba dan bamu gama fita daga unguwar ba na tsayar da mota tare da bude murfin na fita, door ɗin da Ilham ke zaune na bude tare da finciko ta a fusace har seda ta tsorata, na bude gaba na sakata bayan na watsa mata wani shegen kallo me cike da gargadi hakan yasa bata yi yunkurin komawa bayan ba har na shiga mazauni na.
Kyakkyawan mari me kyau nayi wa bakin ta da ya gama zuba min rashin kunya ta yadda seda ta sa ihu tana rike bakin ga ba halin guduwa na rufe motar, kunnen ta na kama na riƙe da kyau ta yadda na san gargadi na ze shige ta na fiddo kyawawan ido na waje na haske ta dasu ina zare su
"Duk sanda kika kuma yi min rashin kunya, kallon banza ko harara se na ci uban ki tun da baki da kirki, kina zuwa school kina haduwa da marasa tarbiyyan yara kina koya ko?".
Da sauri ta girgiza kai jikin ta na rawa dan yadda na mata ba ƙaramin tsorata tayi ba ga bakin ta dake zafi dan har lips din sun fashe
"Ni ba sa'ar ki bace balle ki kawo min iskanci, duk rashin mutuncin da ke kan ki se na sauke miki shi dan duk kika kuma min ɗaya daga abin da na faɗa se na kulle ki a daki na zane ki ciki da bai ko kuwa in wullo ki daga sama ki fado ki mutu kowa ya huta, zaki kara?".
Yanzu ma da sauri ta girgiza kai na kuwa sake haɗe rai tare da zare mata ido
"Baki da bakin magana ne kike min knodding?".
Yadda nayi maganan a tsawace yasa bakin ta na rawa ta furta
"A'a...a'a...ba zan kuma ba...".
A firgice, haka na mata warning me kyau kafin na sake ta bayan nasa ta gyara kan ta na tashi mota muka cigaba da tafiya ina bin karatun Alkur'ani da nasa suratul Noor cikin raina kuwa cike fal da tunanin yadda zamu kaya da boss dina wajen aiki saboda nayi makara fiye da ka'ida a tsukin.
Har cikin school premises din na kai ta tare da kara mata kudin break ta karba tare da barin wajen da sauri, na bi bayan ta da kallo ina tariyo tsoro na da na hango cikin idan ta sannan na fita, se kuma tunanin yadda zamu kwashe da Salees in ta faɗa masa ya fado min, dogon tsaki na ja ina jin na shiryawa duk ma me ze faru, abu ɗaya na sani ba zan dau raini daga uwar ya in Kuma na dau yarinyar ba, yar da da na sami haihuwa da tuni ina da sama da ita sosai, kai baze sabu ba wannan karon nima na shiryawa duk abinda Salees ya taka.
Da wannan tunanin na karasa wajen aiki na inda nake aiki da ma'aikatar haraji wato revenue nake kuma da office na bakwai mafi girma a wajen, sai da na kai uzurin rashin lafiya wa me gidana kan na koma office ɗina Ina istigfar na karyar da Salees yasa nayi.
Aikina nayi cikin nutsuwa duk da sa'i da lokaci wasu abubuwan na daga rayuwa ta kan fado min cikin rai sai dai bana bari ya zauna balle ya hana ni aiki na ke ture shi gefe.
Waya ta ce ta dauki soft ringtone me daɗi wanda na sawa duk family na, ina dubawa na ga Ummi na ce, take naji wani sanyi ya shiga sauka cikin raina na dau call din cike da farin cikin jin muryar mahaifiya ta
"Ummii naa"
"Dijeehh naaah".
Itama ta amsa min cike da so da kauna ta wanda suka fallasa kan su sanadin rashin haihuwa da Allah ya jarrabe ni dashi
"I miss You Ummi naa, hope kina lafiya ba abinda ke damar min mamana".
"Alhamdulillah, Allah ya kara muku lafiya ke da Abba na, matsala kam babu Ummi sai dai duk da haka muna bukatar addu'ar ku".
"Wannan kam a kullum ba'a fashi Khadijah, kullum addu'a ta da fatana shine Allah ya azurta ki da rabo me albarka, Allah ya kare min ku ya tsare ku daga dukkan wani sharri ya albarkace ku ya kuma hada min kan ku".
"Amin Ummi na, Allah ya saka da alkhairi ya kara girma tare da nisan kwana me albarka".
"Amin, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina faɗa miki be manta dake ba ba kuma baya son ki bane ya jarrabe ki, ki rike addu'a ki tsarkake zuciyar ki ki kuma zauna da abokiyar zaman ki Lafiya, dan Allah Khadijah kar ki bari sheɗan ya zuga ki a kan ƴaƴan ta ko ita, in da kara da mutuntaka ya'yan mijin ki naki ne, ki gyara musu ina suka kuskure amma ban da cutar wa dan Allah".
Wani irin rauni ne ya lulluɓe ni kamar yadda ya kasance yana faruwa duk Ummi take min nasiha
"Insha da Ummi na, ina iya kokari na ki cigaba da taya ni da addu'a, ina autan ki ne ban ji shi ba kwana biyu?".
"Allah ya shige mana gaba, auta yana can ya fita neman maganar da ya saba, ai ni dai wannan da se Allah ya shirya min amma jin magana kam ba'a cewa komai".
Da haka muka bar waccan maganar muka koma hirar mu har lokacin da muka yi sallama na aje wayar ina sauke numfashi.......................!
Ouummey 📚✍🏻.
Ouummey 03 {4/29/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 003
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
Hankali a kwance na tashi aiki tare da tattaro kaya na na fito, tsayawa nayi ina gaisawa da abokiyar aiki na me suna A'isha
"Yau ba zaki jira oga ba kenan?".
"Ai bana tunanin oga ya shigo yau dan a gida na bar shi".
Na bata amsa, akan Salees take magana dan wajen aikin mu daya da shi sai dai ya fi ni matsayi da office uku, mataki na uku yake a ma'aikatar ni ina na bakwai
"Eh na manta fa, kin san zasu je meeting a main branch so yau zasu tafi".
Da yake na amsa mata dan na manta da batun haka kuma da zan fito be min sallama ze tafi ba, da haka muka rabu na wuce wajen mota na na shiga tare da barin ma'aikatar.
Sannu a hankali nake driving zuciya ta cike da tunanika barkatai, wato dai yanzu ban da sauran matsayi a wajen Salees, da ni da banza kwance kusan ɗaya muke, to in ba haka ba ai ya cancanta ya min sallamar ze tafi ko.
Wai a duk cikin yanayin da nake sai da wani bangare na zuciya ta ya dinga tursasani yiwa Salees uzuri, ban ja ba na yi masa ta hanyar yin tunanin maybe dan yasan na san zancen ne tun a office.
Seda na tsaya a mall nayi siyayyan kaya shafa na da suka yi kasa tare kuma da undies dina da naga kaman sun ɗan yi sanyi, ban fito ba se da na siyowa baby wato Ilham wata gown me kyau da ta burge ni Amir kuma wani takalmi me kyau, wannan sabo na ne bana yin siyayya ban musu tsaraba ba har Salees, Mariya ce dai ban taɓa ɗorawa kaina yin wannan karyar ba dan ba zan iya ba, shima Salees ɗin daga baya aje wa nayi ganin ba sannu bare na gode.
Sai da na adana motar inda ya kamata sannan na kwashi ledoji na zuwa main falon mu, da sallama a baki na na shiga , yuuuu haka Mariya da ƙawayen ta suka zuba min ido kamar sun ga wata sabuwar halitta lamarin da yasa naji na tsargu dan kafin na shigo kaya kaya haka nake jin surutun su.
Kadaran kadahan na musu sannu da gida na wuce daki na ina tafe ina jin kaifin idanun su da suka min rakiya da shi, zube ledojin nayi kan bed tare da zama ina aje numfashi, seda na huta sannan na cire kaya tare da shiga toilet na yi wanka.
Jakar shopping ɗin su Amir na ɗauka na fita bayan na shirya cikin atamfa ta purple color ɗinkin riga da skirt da suka zauna a jikina suka kuma kama ni wanda yawancin dinkuna na duka haka suke, duk tsadar kaya bana bakin cikin kacaccala shi wajen yin dinkin da nasan zasu zauna a jikina in birge me gida.
"Sannun ku fa, maman Ilham ga wannan nasu Amir ne".
Na faɗa ina aje mata ledar a gaban ta kana na juya zuwa kitchen dan yin girki
"Oh mace har mace amma bata da wani amfani, to meye amfanin juya da bata haihuwa?".
Kalaman daya daga cikin su da na jiyo dan dama a yadda ta daga sauti take magana ta faɗa ne dan naji
"Haba ke kuwa Asmah, bana san neman magana, ya muna
Showing 3001 words to 6000 words out of 43434 words

Sai da tayi yar dariya sannan ta amsa min
"Ina lafiya Khadijah, ina fatan kema haka kuma babu wani matsala ko?".

____________________________________________________________________________
_Free Chapter Three_

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2 Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15