yaya da kuma neman ta ringa tsallake umarnin sa wanda shi kuma baze dauki haka ba.
Be aje ya'yan sa a kusa ba a ran sa, sune abu mafi soyuwa gare shi so baze lamunci yaji ko ya ga tana musu wani abu na rashin kyautawa ya kau da kai ba, haka Mariya, tana iya kokarinta wajen ganin sun zauna lafiya amma Khadijah taki bada dama bayan da farko ita ta nuna ba abinda take nema daga Mariyar face zaman lafiya se gashi ta tankwabe rokon ta da kan ta, amma ban da wannan abubuwan yana son matar sa, Khadijah ce macen da ya fara so haka kuma macen da ya fara kasancewa da ya ke kuma samun gamsuwa wajen ta fiye da kowa, ta ya ya baze so ta ba?.
Yana cikin tunanin yaji ta ingiza shi gefe tare da ficewa daga dakin da sauri, a rikice ya mike ze bi bayan ta se kuma ya tuna da Mariya da kanwar ta dake zaune a falon, dole ya tsaya ya koma dakin ya shiga kai da kawo ransa yayi mummunan ɓaci da abin da tayi masa......................
Not edited ❎
Ouummey 📚✍️.
Ouummey 07 {5/5/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
Ban tsaya a falo ba na wuce garden din mu dake can bayan gidan, ba wani babban waje bane sedai gwargwado yayi kyau, kan elephant grass din wajen na kwanta abina ina sauri numfashi, kalaman Salees na sake dawo min cikin rai na, lallai Salees ma, yanzu shi after all that happened har yana da karfin halin nufin na da bukatar da, ko da yake ba abin mamaki bane.
Amma fa ba karamin juriya da karfin hali nayi ba wajen ture kalaman sa daga raina haka kuma ba karamin kokari nayi ba wajen ganin be yi galaba a kai na ba, dan da gaske zuciya ta ta raunana, so da kaunar sa sun rufe ni.
Ko yanzu ma da nake kwance tunanin rayuwar mu ta baya nake yi, haduwar mu, soyayyar da muka zuba zuwa rayuwar auren mu me cike da farin ciki kafin Mariya ta shigo cikin mu kuma komai ya canja.
Ajiyar zuciya na sauke jin mutum a jiki na da na tabbatar Salees ne, nima dama ban yi zaton ya bar ni haka da wuri ba dan yana cikin maza masu naci kan abinda yake so, sedai na kudire ko yafi antaru taurin kai da naci wallahi baze sami komai daga gare ni ba.
Da sauri na mirgina jin hannun sa ta cikin riga ta, tunkurkur na zauna tare da zuba masa idanu na da mayen son sa suka sa yayi ja lokaci guda ina bata rai matuka, cike da basarwa irin tasa ya nuna kamar be gani ba ya matso tare da son sake shige min sedai tuni nayi baya da sauri Ina turo baki
"Bana son irin abinda kake min wallahi, baka na dawo nan bane, ya kamata ka gane hutawa nake son yi".
Dan tsai yayi yana duba na da mamaki dan zan iya cewa ban taba yi masa gardama ga bukatar sa ba cikin rayuwar da muka yi ya tsawon shekaru goma sha shida, na san dole abin ya dake shi gashi kuma nayi fuska abina tare da komawa na kwanta na bashi baya.
Sosai jikin Salees yayi sanyi sedai he's the type that doesn't give up easily so se ya Kuma matsowa tare da sa hannu ya juyo dani ta karfi, be kuma jira komai ba ya danne ni cikin son se ya hade bakin mu guri daya, aikuwa kamar me haka na shiga fighting din shi na kuma ki bashi duk damar da yake so, ya zata abin wasa ne ya shiga kokarin kashe min jiki sedai ya ga ko kadan ban da niyyar saduda asali ma na kara kai mi ne wajen kokawa dashi dole ya hakura ya daga ni tare da tsura min jajayen idanun sa da ke cike da neman magana ga kuma bacin ran da na tusa masa, yana daga ni na tashi ina gyara riga ta na mike tsaye tare da kakkabe jikina nayi hanyar barin garden din ina karkada masa jiki, ko banza na san shima na bata masa kamar yadda yake bata min.
★★SALEES★★
Duk yadda yake tunanin iskancin khadeejah ya wuce wajen, kalli yanzu abin da tayi masa kamar wani kwarto alhalin yana matsayin mijin ta shugaban ta, a yanzu kam dari bisa dari ya yarda raini ne tsagwaron sa tsakanin sa da Khadijah, ta raina shi ne take masa haka, ai da datake ganin girma da kimar sa musu wannan ze iya kirga so nawa ta masa, lallai se ya dau kwakkwaran mataki kan ta, ba dai jikin ta bane take masa wulakanci dan ya bukata?, To ta rike abin ta ta jika tasha dan alkawari ne baze kuma neman ta ba, in kuwa ta kawo kan ta lokacin zata san ita bata iya wulakanci ba dan se ya nuna mata shima tantiri ne kamar ta, yana ji da fiye da duk abinda take ji.
Ya dade zaune a wajen kafin ya iya mikewa ya koma gida, fita ya so yi ko yaji sauƙin bacin ran sa sedai baze iya ba, a yadda marar sa ke damun sa cikin ma da kyar yake taka kafa.
Ganin yadda ya wuce su rai bace fuska hade yasa Mariya tashi ta bi bayan sa da sauri, sedai ko kafin ta kai gare shi tuni ya shige tare da datse kofar, turus ta tsaya tana kallon kofar dan this is unlike him, bugawa ta shiga yi hankali tashe sedai duk iya bugun ta yayi mata banza ko uhm bece ba haka ne bude kofar ba har ta gaji ta juya jiki a mace ta sauka kasa.
Shi kam Salees duk bugun da take yi yana ji kuma yana sane yayi mata banza, abinda bata sani ba dan ita ya rufe kofar dan ya san se ta zo takura masa shi kuma baya bukatar takurar ta dan ba abinda zata iya yi masa, khadeejah ce kawai maganin sa ita kuma ya fahimci hayaki kan ta keyi amma yayi alƙawarin sauke mata duk ma uban dake kan.
Haka ya cigaba da juyi dafe da marar sa se uban gumi yake haɗawa kafin wani wahalallen bacci yayi gaba dashi me cike da mafarkin Khadijah kala kala.
Be tashi ba se after Six, a gurguje yayi wanka ya fita Masallaci jikin sa duk ba kwari, sallar ma ranar cikin wasi wasi yayi ta dan gaba daya hankalin sa na kan Khadijah, tunane tunane kawai yake yi a kan ya, wata zuciyar na fada masa ya sake gwada ta ko zai dace wata kuwa na bashi shawarar fita harkar ta har ta gane kuren ta, be bar masallacin ba se da yayi isha kana ya nufo gidan cike da karbar shawarar zuciyar shi ta sake bata dama.
★★★★
Fadawa nayi kan bed fuska ta cike da murmushi me fadi wanda na manta rabo na da irin shi, wato yau da naga Salees cikin irin yanayin da na kan shiga a dalilin da se naji raina yayi sanyi, sanyi fa sosai dan ba karya naji dadi wallahi.
Juyi nayi tayi ni kadai ina sake shirya yadda zan cigaba da zama da kowa na gidan da halin sa, na daina daukar cin kashin kowa tun da ina hakuri amma ba'a san ina yi ba, da ace duk abinda ke faruwa Salees na bin bayana in Ina da gaskiya da maybe ban sare ba haka, amma babu ruwan sa dani, babu ruwan sa da zan damu ko zuba cutu, shi dai duk abinda aka tsara masa shi yake hawa, duk abinda aka fada masa a kaina se ya yadda, nayi ban yi ba duk ba ze bin cika ba, kamar ba shine a baya yake fada min ba wanda ya kai shi sani na ba, ba wanda ya kai shi sanin hali na, ba wanda ya kai shi sanin abin da zan aikata ko ba zan aikata ba, duk ya manta wannan, duk ya zubar da komai ya watsar da komai, baya kallo na a komai face Khadijah, matar da yake aure wadda bata haihu ba, ba'a ma maganar soyayya, dan yanzu ina tantama in akwai so na a ran sa, dan abinda yake min masoyin gaskiya baze yi shi ba.
Kiran sallah ya sa na mike tare da shiga toilet na dauro alwala na tada sallah, ina idar wa na yi azkhars dina kana na cire hijab din na fita zuwa kitchen dan yunwa nake ji, noodles na dafa na zauna na ci acan kana na wanke plate din na aje na koma daki, system na jawo na shiga aiki na dan yanzu na sake maida hankali dan bana san abin d zesa suna na ya fita daga cikin masu samun promotion din nan, na saka rai sosai ina kuma fatan Allah ya sa na dace.
Karfe tara na tattara komai na aje na shiga wanka, sleeping dress na saka kana na feshe jiki na da turarukana masu sanyin dadi wanda ko ba zan je dakin Salees ba bana fashin sa su, se da nayi addu'a sannan na kwanta bayan na kulle kofa ta.
Har bacci ya fara dauka ta na ji kamar an bude dakin an shigo, a tsorace na mika hannu na kunna wuta dan switch din na daga saman kai na ne, a boye na sauke ajiyar zuciya ganin Salees sedai a fili se na bata fuska in bin shi da kallon mamaki da kuma gajiya da ganin sa, maida kofan yayi ya rufe tare da takowa ya zauna bakin gado yana kallo na nikuwa na kau da kai gefe ina bata rai.
"Tashi zaune muyi magana".
Kamar ba zan tashi ba se kuma na fara tashin a hankali kamar me ciwon laka wanda ina sane nayi dan na bata masa dan tuni na dade da sanin baya san jira a rayuwar sa, kusan minti biyu kafin na zauna sosai sannan na kai kai gefe.
"Bana san tashin hankali Khadijah, ki fuskance ni mu sami fahimtar juna".
Juyo da kaina nayi na zuba masa ido kamar yadda ya bukata, seda ya dan yi shiru alamun yana tunanin ta ina ze fara kafin ya riko hannaye na, na kalli hannun sannan na maida duba na kan sa
"Bana san irin wannan zaman da muke yi Khadijah, ban taba tsara hakan tsakani na dake ba, in laifi nayi miki ki fada min na baki hakuri a wuce wajen amma bana san gaba da fushi".
Shiru nayi kawai, lallai namiji bai da kunya, wai ni Salees ke tambaya in laifi yayi min saboda yanzu tashi ta kawo shi, duk abinda ke faruwa be ga ni ba, duk abinda yake min ba laifi bane, aikuwa ze ga rainin hankali in dai nice dan nq shirya masa
"Kiyi magana, ki fada min laifi na and we'll sort things out komai ya wuce".
"Baka yi min komai ba zuma na".
Zuba min ido yayi na tsayin mintina kafin ya sake matsowa kusa na har nunfashin sa na sauka kan fuska ta
"No nayi miki, Ina ji a jikina nayi miki laifi, in haka ne meyasa da baki min haka ba se yanzu?, pls ki fada min me nayi miki dan iya tunani na na kasa ganowa".
Murmushi nayi jin wai ya kasa gano laifin sa
"Ka kwantar da hankalin ka pls, baka min komai ba ni hutu kawai nake bukata, pls ko zaka iya komawa wajen Mariya har zuwa wani dan lokaci?".
Izuwa yanzu ina iya hango bacin ran d Salees ke ta kokarin boyewa sedai ko gezau ban ji komai ba a raina akasin da da ban so ko kadan in ga fushi ko damuwa tattare dashi
"To kuwa baze yiwu ba, na biki na lallaba ki, na kwantar da kai na sanyayar da murya duk dan mu zauna lafiya amma kin ki bani hadin kai, zama da nine kika gaji ko kuwa wani salon wulakanci ne?".
Zare hannyeye na nayi daga nasa na koma na kwanta ina bashi amsa
"Babu ko daya cikin biyu kawai dai kamar yadda na fada maka ne ina bukatar hutu, Allah ya bamu alkhairi, pls in zaka fita ka kashe min wutar ka kuma rufe min dakin".
Daga haka na ja bargo na lullube ƙafafuwa na tare da kulle ido na, tabdi bala'i ni kaina na san na tsokana masifa sedai sanin na shirya mata yasa nayi banza da duk bala'in da Salees ke yi
"Kar ki maida ni wani shashasha mana, bar ganin ina bin ki ina lallaba ki amfada miki tsoranki nake ji, ko kuwa kin fi karfi na ne, to wallahi kyale ki nake yi kawai darajar su Abba, amma ban da haka ke in ance kiyiwa Salees iskanci ba zaki fara ba, wacece ke da za'a dinga bin ki kina wani daukan kai, ban da ma kin kasance butulu duk rufin asirin da nayi kiki baki gani ba, duk suturar da nayi miki amma nine zan zama abin wulakancin ki, to bar ganin ana wani cewa kin raina ni kin mallake ni, wannan duk karya ne dan ba macen da ta isa ta raina ni, ba'a haife ta ba wallahi dan kuwa se ta koma gidan gyatumi tun da babu abinda ya zama dole, kuma wallahi tun muna shaida juna maza ki koma hayyacin ki kafin mu kai ga yin batacciya dan akan haka wallahi komai ze iya faruwa, in nace komai ina nufin komai".
Ya sa kai ya fice tare da banging min door din, duk da cikin fadan nasa akwai kalaman da suka zafafa min amma se ban bari sun yi tasiri a raina ba, mafi aala shine na bata masa rai wanda shine aiming dina kuma na ci riba dan haka se na tashi na maida kofa ta na rufe tare da kashe wuta na koma na kwanta tare da rufe ido bayan nayi addu'a, aikuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba dani.
Washegari tun bakwai saura na fice dan bani ce da girki ba bana kuma bukatar abin karin su, a office na hada tea da heater na dan ina da komai na bukata, na karya a nutse hankali kwance sannan na shiga aiki na raina fes.
Karfe tara daidai na kwaso takardu zuwa cikin hall din da zamu yi meeting din ma'aikata gaba daya, a nan naga Salees sedai kallo daya yamin ya dauke kai ni ma kuma ban kuma kallon sa ba muka shiga abin da ya kawo mu, muna gamawa na koma office dina, karfe biyu nayi na tashi aiki, yau kam ban iya dauke ido daga hanyar gidan mu ba duk da zuciya ta na fada min kar nayi amma wata bangaren na tunzura ni kan naje dan ko na tambayi Salees baze bari ni ba, tun bayan auren Mariya ya dauki wata banzar akidar kulle ya ɗorawa kan sa, har gwara ma ni ina zuwa aiki ita Mariya ba inda take zuwa se ta rufe watanni shida bata fita a gida ba, sauƙin ta yana kai wa iyayen ta ya'yan ita ce dai se sanda ya so sannan ze kai ta da dare, nima haka se dare yake bari na zuwa gida ko ya kai ni, daga baya ne nake takura masa in wuce daga wajen aiki shima ba ko yaushe yake yadda ba.
Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama daidaita parking a compound din gidan mu kana cike da matsanancin kewa nake bin ko ina da ido ganin an sake gyara shi yayi kyau fiye da da, gwanin sha'awa ko ina ya sha sabon paint ga kuma shuke shuke masu daukan hankali, ba karamin kokari su yayan mu ke yi ba akan gidan mu shiyasa kullum cikin sa albarkar Abba da Ummi suke, gidan mu babban gida ne tun a da dan Abban mu na cikin masu kudin unguwar mu, compound din gidan mu babbane dan yana daukar motoci sama da biyar, a takaice dai ze dauki mota bakwai ko takwas batare da takura ba, sassa uku ne a gidan mu, bangaren samari wanda yanzu duk sun yi aure, bangaren Abban mu se part din Ummin mu inda a nan muka rayu ni da yayata salima.
A hankali na bude kofa na fito me gadi ya washe baki yana min sannu da zuwa haka ma sauran ma'aikatan mu, na amsa a mutumce muka gaisa kana na nufi main falo din mu.......................
Ouummey 📚✍️
Ouummey 08 {5/6/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 08
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda
Showing 15001 words to 18000 words out of 43434 words

____________________________________________________________________________
_Free Chapter Seven_

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6 Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15