ce kuma kawata, wallahi ba zan taba yin abinda zan cutar dake d sani na ba, ki bani dama mu nuna wa Hauwa ita karamar kwaruwa ce, ita yanzu ta soma bariki lokacin da mu kuma muka riga muka maida ita gida".

Shiru Falmata tayi kafin ta saki ajiyar zuciya a hankali

"Ba tsoron Hauwa nake ba Farida, saidai ina tsoron Ubangiji na, ban haifa ba, ban ji dadi ba a gidan aure na sannan kuma na lalata kiyama ta Falmata?, Anya in nayi hakan ban cuci kaina ba?".

Da sauri Farida ta shiga girgiza kai,

"Ba zaki lalata kiyamar ki ba, ramuwar gayya zaki yi wadda tafi gayya zafi, daga lokacin da kika rama zaki ji sanyi a ranki daga nan kuma se mu tuba, amma ai kafin nan itama taji ko da rabin yadda kika ji ne".

"Bazan iya ba Farida, ba zan iya lalata dan kowa ba, ba zan iya sanya mahaifiya kuka ba, ba zan iya fuskantar Ubangiji da laifin shirka ba, na hakura Farida, na barwa Allah shine ze min sakayya kan Alh da Hauwa amma ba zan iya kauce hanya saboda ita ba".

"Banza tursasaki ba Falmata, ban kawo wannan shawarar dan batar dake ba sai dan sama miki salama amma tun da baki yarda ba ba za'a yi komai ba, sai dai kiyi hakuri domin zan janye jiki daga gidan ki dan ba zan iya zuwa ina ganin ki kullum kina ramewa da karewa a tsaye saboda bakin cikin wasu ba bayan kina da yadda zakiyi, zuciya ta ba zata iya hakurin ganin ki cikin matsala ba alhalin kece yar uwa mafi kusanci da ni, kiyi hakuri ba wai na janye gaba daya bane sai dai yawan zuwa zan rage, sai an jima zan kira ki in na koma gida".

Da haka Hajiya Farida ta dauki jakar ta bayan ta yafa gyalen ta ta fara daga falon, babban compound ne da ya lashe motoci kusan sha biyar wanda daga nan zaka san gidan ba karamin girma gare shi ba, gate ta nufa tana tafe kama zatai bindiga saboda haushi da takaicin yar uwar ta, sanyin ta yayi wa, zuciyar ta ta fiye kyau da yawa haka hakurin ta ya wuce ka'ida.

Ta dade da sanin da ita ke rayuwa a gidan matsayin kishiyar Hauwa to wallahi da tuni labari ya dade da suyawa dan ba zata dauki ko rabin rabin abinda yar uwar ta ta dauka ba, da ita ce da tuni ta takawa Hauwa birki dan ai rashin Haihuwa ai ba hauka bane da zata dinga wani iskanci, kai da ita ce da ta nunawa Hauwa itama Shegiya ce dan wallahi yadda take mata iskanci kan haihuwa ita kuma se ta lalata rayuwar yaran ta ga karshen tutiya da tinkaho, abinda take so Falmata ta goya mata baya suyi kenan amma tsarkin zuciyar ta ya hana ta hango me ita take ganowa.

Tana zuwa gidan ta tayi parking tare da shiga falon ta me bala'in kyau, abu na farko da ta fara yi bayan zama shine kiran Falmata taji yaya take, Allah shaida ne tana matukar san Falmata, ta dauke ta yar uwar da suka fito kamar ciki daya ne shiyasa duk abinda ke faruwa a rayuwar falmatan yake matukar damun ta.

Hankalin ta be kwanta ba se da taji lafiyar ta kalau kafin tayi shiru cikin zurfin tunani se kuma ta gyada kai cikin yarda da shawarar da ta yanke.

Tana nan zaune yan matan yaranta biyu suka shigo daga islamiyya, hassana d hussaina.

Har kasa suka gaishe ta tare da mata sannu da zuwa ta amsa kana suka wuce dakin su suka canjo kaya

"Yaya jikin momyn?"

Hassana ta tanbaya a kagauce, sanin yadda hassana ke bala'in son Falmata yasa Farida boye mata halin da take ciki

"Ta sami sauki sai dai zamuje India a sake duba ta, yanzu dai kuje ku dora girki sannan ki kira yayanku kice ina neman sa".

"Da toh". Husaina ta amsa kana suka shiga kitchen yin girki.

D daddare kuwa se ga dan ta Safwan kamar yazo kamar yadda Hussaina ta fada masa tana kiran sa, bayan sun gama gaisawa da tambayar yaran sa da matar sa ta kawo masa batun da yasa ta kira shi.

Albarka tayi ta sa masa bayan ya amsa wa kudirin ta kana ta sallame shi ya tafi bayan ta bashi tsarabar yaran tace ya kai musu..............

Ouummey 📚✍️.






Ouummey 06 {5/3/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




Ouummey 06
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.


____________________________________________________________________________



_Free Chapter Six _


Tun da akayi wannan case din na janye jiki na daga mutan gidan gaba daya, ba shi Salees din ba ba ya'yan sa ba balle matar sa d dama kissar ta ke kawo ta gare ni, gaba daya na dauke musu wuta, tsakani na dashi gaisuwa, daga ita kuma se maganar d ta zama dole.

Abin dariya wai kuma se hakan ya dame shi, ko da yake amfanin kan sa ne yasa ya damu dan har kwana na daina zuwa dakin sa, wannan kuma ba karar da ya kai ni bace, kudiri na ne hakan tun ranar da yace Amir baze bar daki ba saboda gidan uban sa ne yasa na sawa raina to kuwa ba zan kuma bin shi dakin sa ba, in ya matsu da son kasamcewa dani se ya biyo ni daki na.

Sati biyu muna cikin wannan halin dashi, wata magana kwakkwara bata hada mu in ba wajen aiki ba dan a yadda nake hade rai duk na gan shi yasa yake shakkar yi min magana.

Yau mun tashi daga aiki d wuri saboda matar ogan mu da ta haihu yasa cikin farin ciki ya sallame mu tun kan lokaci yayi, tun da na fito daga ma'aikatar nake tunanin zuwa gida wajen Ummi na sai dai ba ze yiwu in je din ba dan ban tambaye shi ba, haka nake kallon hanyar har na wuce.

Ina yin parking na tattara kaya na na fito tare da rufe motar na shiga falon da sallama, Mariya da kanwar ta na zaune suna hira duk suka juyo gare ni, daga sallamar nan ban kara komai ba na wucewa ta kofa ta ina kokarin ciro mulki dan bude dakin se dai ganin kofar a bude yasa na tsaya cike da mamaki.

Daga ni se Salees ne masu key din kofar, to waye ya bude min dakin?.

Da dan sauri na matsa jikin window tare da daga labulen ina surveying compound din, se kuwa naga motar shi ajiye alamun ya dawo nice ban kula ba da na shigo.

A hankali na saki labulen na karasa dakin na shiga da sallama ina tunanin me ke dalilin da ze kawo Salees daki na balle ma ya bude min kofa bayan bana nan, kan bed na same shi kwance yana pressing phone ya bararraje kamar gadon sa, na dan yi turus ina kallon sa wanda hakan yasa ya dago tare da aje wayar shima ya shiga bina da ido.
Ganin kallon nasa ba na kare bane yasa na wuce shi cikin son basar dashi na aje kayan hannu na na rage mayafin jiki na kana na nemi cushion na zauna Ina bude fridge din gefe na na ciro bottle water me sanyi na bude da bismilla na sha, ina sauke ajiyar zuciya na aje ragowar na sake kishingida ina lumshe ido cike da gajiya, seda na dan huta kafin na tashi na shige toilet na maida kofa na rufe sannan an shiga rage kayan jiki na dan yin wanka.

★★SALEES★★

Tun da ta shigo yake bin ta da kallo cikin son ganin gudun ruwan ta, ya gaji da wannan zaman da ta tsiro tsakanin su, ya gaji da shariyar da take masa, ya gaji da ko in kula din da tayi dashi, ya gaji da komai ma dan yana bukatar kasancewa da ita, yana bukatar jin dumin jikin ya sai dai ya lura in ya biye mata to fa haka zasu cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da shi kan sa be hango zuwan sa ba.

Baki bude ya ke kallon ta ganin yadda ta shigewar ta toilet ta rufe kamar bata lura da zaman sa cikin dakin ba alhalin so biyu suna haɗa ido dashi.

'me Khadijah ke nufi dani' ya ayyana cikin ransa, koma me take nufi yana nan yana jiran ta har ta gama ko me take cikin toilet din dan ba ze dau raini da wulakanci ba, yana zaune ta wuce shi wato ga shara banza mata amfani ko, shiyasa Hajiya Iya ke cewa ta raina shi, a da be yadda ba amma a yanzu tabbas yana hango burbushin hakan.

Ya dade zaune kafin ta fito daure da guntun towel din ta da be gama sauka kan kosassun cinyoyin ta ba, jikin ta dauke da abin ruwa shaidar wanka tayi, haka kuma kan ta da ta wanke shima kulle cikin wani karamin pink towel.

★★★

Tun da na fito nake jin tasirin idanun sa a jikina alamun kallo na yake sedai ban nuna na fahimta ba na wuce na zauna kan stool din mirror, a hankali na warware towel din kaina hakan yasa jikakken gashi na ya kwanta kan kafada ta, hand dryer na jona na shiga busar da kan a nutse har na gama kana na shiga shafa mayukan da nake amfani dasu wa gashin, take ya shiga kyalli haka kuma ya sake kwanciya sosai a kafaduna bayan na taje, ribbon me dan tudu kadan na sa na kama shi sannan na kitse jelar na sake ta ta na reto a keyana.

Mai na dauko tare da murzawa a hannu na na shiga bin cinyoyi na dashi bayan na sassauta zaman towel di na, a nutse nake komai kai baka ce na san da zaman wani dan Adam a dakin ba, wani na kuma murzawa na shiga bin kafaduna, kirji zuwa ciki na a tausashe cikin raina ina yabawa taushi da santsin fata ta ko da dai ba banza ba dan kudin da nake kashe wa iya mayuka da shower gel ba kadan bane.

Dagowar da zan yi ba kalli mirror se kawai na ci karo da jajayen idanun Salees a kai na, da mamaki nake kallon yadda ya tsaya bayana daf yana sauke ajiyar zuciya da nishi kamar wanda yayi tsere, dauke kai nayi na fara kokarin mikewa sai dai yadda ya sake matse min waje tare da zuba hannayen sa kan kafada na yasa dole na cigaba da zama.

Lotion dina ya zuba cikin hannun sa da ya dauke kan jikina bayan ya matse min waje ta yadda ba zan motsa ba, bin shi na dinga yi da kallo cikin mamakin me ze yi da man da yake murzawa a tafin hannun sa, na dan fito da ido waje jin ya sauke hannuwan kan bayana ya shiga shafa min cikin wani irin salo da yanayi me tafiyar da mutuwa, ban san sanda na lumshe ido ba sedai ban fasa dakatar dashi ba ta hanyar rike hannun sa kana na bude ido na zube su kan fuskar sa dashi ma ni yake kallo

"Na shafa ai". Na fada ina kubcewa da sauri na nufi wardrobe di na cikin kokarin dauko kaya, hannuwan sa yasa a kugu na ya zagaye ni dashi tare da hade ni da jikin sa yana magana kasa kasa

"Aje dauko kayan nan kizo muyi magana".

"Magana? Ai yanzu ma ita muke yi".

"Maganar na da matukar muhimmancin da nake bukatar nutsuwar ki, muje ki zauna ki saurare ni".

"Ba zan iya zama tsirara ba, ka jira na saka kaya tukuna".

Da alama ya fuskanci yadda nake kokarin hade rai shiyasa ya sake ni ya dan koma gefe, doguwar riga na dauko ta wani yadi me kyau da sulbi na zura, ba kadan ba rigar tayi min kyau haka naji dadin saukewa cikin ta dan bubu ce, hulan da ya hau da rigar na dauko tare da sawa a kaina na kara sa gaban mirror ina sake daidaita mata zama kana na shafa turaren kaya haka na kara da na feshi bayan wanda na shafa wa jikina tun farko.

Waya ta na dauka tare da zama kan cushion na shiga kokarin kunna data sedai ban kai ga haka ba na ji an zare ta, nasan ba kowa bane se Salees, ya zauna kasan ƙafafuwa na tare da zuba hannayen sa kan cinyoyi na

"Dago ki kalle ni Khadijah".

Ban ki ba na dago kaina a hankali tare da sauke duba na kan fuskar sa, ya langwabe kai tare da karyar dashi gefe kamar wani Maraya, idanun sa sun yi jajir, in ba gizo idanu na ke min ba se n aga har ya dan fada dan kwarmin idanun sa sun nuna rama, take naji zuciya ta ta karye, tausayi hade da son miji na suka rufe ni

"Khadijah bani da Lafiya".

Ya fada yana kama hannu na ya kai wuyan sa, tabbas bashi da lafiya dan zazzaɓi ne ma a jikin sa

"Ban san me nayi miki ba kike fushi dani Deejah bayan kin dade da sanin fushin ki ba karamin illa yake yiwa zuciya ta da jiki na ba, kin saka zuciya ta cikin rudu da halin ko in kulan da kike min".

Yayi shiru tare da kallo na, nima kallon sa kawai nake ba ni da alamun yin magana sedai zantukan sa na shiga ta yadda ya kamata dan wani irin sanyi na ji jiki na yayi wanda na san hakan Salees ya karanta yasa ya matso sosai tare da shige min

"A da ba zan iya kwatanta girman soyayya da kaunar da Khadijah ke yi wa Salees ba, soyayyar da tasa take hakuri da duk wanda ke tare dashi dan kawai tayi rayuwa dashi, soyayyar da ta kasa boyuwa har a gaban iyaye da jama'ar da ke kewaye dasu, haka shima Salees yake mutuwar san Khadijah, yake yin komai dan farin cikin ta har wasu ke ganin an mallake shi ne bayan tsantsan kauna ce kawai ke aiki, shin Salees yayi wa khadeejah laifi ne da yasa ta daina ko take kokarin daina son sa alhalin shi a yanzu ne yake kan ganiyar so da kaunar ta?".

Wani irin laushi da rauni zuciya ta tayi a lokacin, kai wallahi maza sun iya dadin baki ta yadda zaki yi abu se bayan kin aikata ki dinga tunanin taya ya kika yi, me ya kai ki, wanda ko gobe se kin kuma yi in baki jajirce kin kai zuciyar ki nesa ba.

Idanunsa da suka cika da hawaye na dago na kalli Salees, soyayyar sa ta cika min rai, na far kokarin bude baki na dan shaida masa ban dena son sa ba, ban bar kaunar sa ba haka kuma zan cigaba da hakuri dan kawai in yi rayuwa dashi, sedai kamar wadda aka dannawa pause haka na tsaya ina kallon sa na kasa fada, ba komai yasa hakan ba face abubuwan da ya dinga aika ta min a kwanakin baya, irin bakin ciki da bacin ran da ya kun sa min, wai har a gabana yake fadawa kishiya y fara gajiya da hali na, meaning ya fara gajiya dani, wanda a da be san da halin nawa bane ya so ni da a yanzu ze ce wai hali na, kawai nice ya gaji dani yake neman wulkantawa shine kuma yanzu ze dauko wasu shanyayyun kadafun sa ya zo yana karanta min karya.

Eh karya mana a yanzu, na san a da Salees ya so ni Kamar yadda ya fada, nima kuma nayi haukan son sa, sedai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu baya min ko da rabin rabin son da yayi min a da, akwai dai abinda yake bukata daga gare ni, akwai abinda yake so nayi masa ko yake nema a waje na shine bari ya yaudare ni da kalmar soyayya.

Murmushi na saki bayan na gama kallon idon sa, se yanzu na gane me ya kawo shi daki na, se yanzu na fahimci soyayyar d yake fada yana min, ni dama nayi mamakin wai Salees ke fada min kalaman soyayya haka abinda in ban mance ba rabon da in ji irin wannan kalaman a bakin shi tun bayan haihuwar Sahal shekara goma sha biyu kenan yanzu.

Be yi tsammani ba be yi tunani be se ji yayi nq ture shi daga gare ni na dauki waya ta nayi waje a hanzarce dan bani da lokacin zama magana dashi, ban shirya hakan ba tukuna dan wallahi alkawari nayi se na rama ko da kashi daya ne cikin kashi darin bacin ran da yasa ni.

★★SALEES★★

Ido ya zuba mata yana sake kankance ido cikin son tabbatar mata eh da gaske yake yanzu ya fara son ta ma, ganin yadda itama take kallon sa yasa zuciyar sa ta shiga tsalle a kirjin sa yana addu'ar Allah yasa ta yadda da abin da ya fada mata dan ya kai makura wajen san kasancewa da ita.

Ba karya ya fada ba har yanzu yana son ta yana kaunar ta, sedai wasu halaye da ta ara ta yafa wanda be san ta dasu ba yasa yake yi mata abinda ya ga dama don ba zata bata masa rai a banza ita tayi farin ciki ba, be san wake koya mata bakin hali ba da yasa har take tsanar masa
Showing 12001 words to 15000 words out of 43434 words