Mariya ta shiga maganar playing her own role Wanda ina gani na gane makirci ne
"Haba Sahal wannan wane irin wulkanci ne, ka tashi kaci abincin nan ko se ranka ya ɓaci".
Kawai se yaro ya fashe da kuka tare da shigewa jikin baban sa yana maganganu
"Ka gani ko Daddy, itama Mommy bata sona, i won't eat this food ko zan mutu wallahi, Daddy pls ka maida ni wajen Granny".
Aikuwa kamar wanda ake dannawa remote se salees ya ture Sahal daga jikin sa ya shiga zazzaga masifa
"Wannan wane irin rashin mutunci ne da wulakanci, akan me zaku samin yaro a gaba da tsangwama har yana gwammace wa rayuwar wani wajen kan gidan uban sa, ba tun yau ba na sh fada muku ban hada son da nake ma ya'ya na da kowa ba dan a kan su wallahi zan saba ma kowaye, har kema ki bar ganin kece kika haife shi dan babu ruwa na ke mahaifiyar sa ce hukunta ki zan yi in kika nemi takura min yaro, gargadi na karshe kowaccen ku ta kiyayi taba min yara, ku kiyayi bata musu dan a maimakon yaro ya bar gida sedai ku kubar shi dan nan ne dolen sa gidan mahaifin sa akasin ku, ke khadeejah tashi ki dafa masa sakwarar".
Tun da ya fara magana ban janye daga tagumin da nayi ina bin shi da kallo ba har seda naji last statement din shi
"...ke Khadijah tashi ki dafa masa sakwarar"...
Na sake maimaita kalaman a ƙwaƙwalwa ta dan in tabbatar da eh abinda salees ya fada kenan, bayan na tabbatar din se na dago na zuba masa ido wai dan in gane akan fuskar sa wasa yake yi ko da gaske sedai daga look din fuskan shi babu wani alamu dake nuna wasa, he look so serious ma'ana dai sakwarar yake so in yi wa dan gwal din dan sa
"Is okay boy, kar in Kuma jin kace zaka je wani gidan, you've no home other than this house which is your father's house, and stop crying, your pounded yam is yet to be ready".
Ya fada cikin lallashin dan sa da ya dauka ya dora kan cinya, murmushi sosai Sahal yayi yana kankame baban sa
"Thank you Daddy, I love you so much".
"Thanks so much boy, daddy loves his little ones so dearly".
Se kuma suka saki dariya Salees na mikawa Ilham hannu itama tayi joining din su yamutsa fuskan da Sahal yayi yasa cike da kulawa ya shafa kan sa
"Yunwa ne ko, dan yi hakuri yanzu zaka ci abinda kake so".
Se kuma ya juyo inda nake
"Why are you still seating, pls je ki masa abinda yake so yunwa na damun sa".
Yanzu kam na tabbatar da gaske yake abinda ni kuma ba zan dauka ba kenan, haka kawai saboda san ran sa da na dan sa ya hana mu cin abinci cikin kwanciyar hankali dan ko spoon daya ban yi ba yaron nan ya tashi hankalin mu yanzu kuma ana batun in tashi in masa pounded yam
"Am sorry bazan iya masa pounded yam ba yanzu its too late, gashi ko abinci ban ci ba and ka san dadewan sakwara in nayi sauri in gama in an hour ga kuma abincin dare na jirana".
"So kina nufin ya zauna d yunwa kenan".
Se da na nunfasa kana na dubi sashin da Sahal yake tsaye
"Ba haka nake nufi ba, yau kam yayi hakuri yaci couscous din gobe se in masa sakwarar ko kuma in yi ta as dinner".
Ko kafin salees yayi magana Sahal y riga shi
"Allah ba zan ci couscous ba, akuya ne ni da zanci abu me kaman dusa, ni ba zan ci ba".
"And I'll cook the pounded yam as dinner, now lemme cook indomie for you da sauri'.
"Ni i won't eat sakwara for dinner, ai kin san bana cin abinci me nauyi da dare malamin mu yace mutum yanayin katon ciki".
Confusedly na tsaya ina kallon yaron jin kome nace se ya kushe, ko ta ina na fito se yace ba haka ba, gyaran murya yayi yana kallona strictly yace
"Kawai kiyi masa tun da ya nace, ina ce muna da pounder".
"Ka fa san ya lalace tun kwanaki".
Na fada kaman zan fashe da kuka, se shima yayi shiru na dan lokaci kafin pleadingly yace
"Pls pound it a turmi tun da bashi da yawa, i can't put an eye yaki cin abinci".
"Am sorry Salees, Mariya tayi masa ko kuwa kuje restaurant dan wallahi ba zan iya yin sakwara yanzu ba".
And this my reply shine dalilin da yasa Salees ke ta min fuskan shanu yau kwana biyu kenan, dan kamar yadda na fada ba zan yi ba ban yin ba, ban san yaya suka yi ba, Mariyar ce tayi ko kuwa siya suka fita suka yi...................
*TWO PAGES TO GO💃💃💃, SAURA PAGES BIYU FREE CHAPTERS SU KARE, KINDLY MAKE YOUR PAYMENT FOR IT'S PAID BOOK*
*INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT* 👇
*09013101854*
Ouummey 📚✍️.
Ouummey 14 {5/14/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 14
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
Daga aiki na taso a matukar gajiye, jiki na gaba daya ciwo yake min dan kwana biyu ina overworking kaina saboda gujewa tunanika ga kuma promotion din da ya matso sosai, yanzu haka gobe za'a sanar da sunayen wanda suka yi nasarar samun wannan cigaban, dukan mu ma'aikatan da muka san an yi nominating sunan mu cikin zulumi muke dan kuwa bama fatan list ya fito babu sunan mu, promotion abun farin ciki da so ne ga duk wani ma'aikaci, yanzu haka ji nake kamar in jawo gobe tayi tayi dan kawai in samu peace of mind.
Mayafi na a hannu na shiga falon dan tun a kofar falo na cire shi saboda wani nauyi dana ji ya min, ba abinda nake bukata a lokacin kamar wanka da bacci ko naji daidai.
Turus nayi ganin Hajiya Iya, kannen Salees Rukayya, Sadiya da kuma auta Hannatu se matar kanin sa Sani me suna Lubabatu, kanwar Mariya me suna Safiya, da yayar ta Safara'u se maman su Hajiya Ramatu.
Ban san me yasa gaba na ya fadi ba ganin wannan taron sedai na daure na karasa falon ina kaiwa tsugunne na shiga gaida Hajiya Iya da bata amsa min ba se kare min kallo da ta shiga yi kafin ta karkata kai tana kankance ido
"Wato yawon tambadewar da kike kenan kika fake da aiki, yanzu mayafin ma a hannu kike yawo dashi".
"A'a a kofar falon nan na cire saboda gajiya". Na bata amsa kai a sunkuye
"Uhmmm kowa dai yayi me kyau kan sa".
Jin tayi shiru bata kuka cewa komai ba yasa na juya ga mahaifiyar Mariya itama na shiga gaida ta amma itama bata amsa min ba dan gara ma Hajiya Iya dan ita ko kallona bata yi ba se kau da kai da tayi tana jan tsaki.
Lamarin ya daure min kai dan kuwa ba haka ta saba min ba, ko da ba haduwa muke yi masu wani frequently ba amma in dai na gaishe ta tana amsa wa ko da dai ba wani da tsayi bane dan iyaka ta da ita 'Lafiya' shine amsar gaisuwa ta d ita koyaushe.
Cikin sanyin gwiwa na dan mike sannan na gaida yayar ta Safara'u, ban tsaya jin zata amsa ko kuwa ba na yiwa sauran magana wanda kannen Salees ne da matar kanin sa se kuma kanwar Mariya
"Sannun ku da gida". Da sauri nayi gaba dan jiki na ba bani wannan taron bana lafiya bane, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, wankan da nake dokin yi duk se naji ba zan iya ba, kawai so nake in San meke faruwa a gidan namu inda na shiga addu'ar Allah yasa ba shida alaka dani dan to be sincere tuni na gama gajiya da wannan tashe tashen hankulan, kwanciyar hankali nake bukata a yanzu.
Kamar wanda aka karanta min se kalaman da kunne na suka jiyo min lokacin da nake bude kofar daki na suka dawo min cikin ƙwaƙwalwa
"Hmmm, lallai mugu bashi da kama, kalli matar nan kamar wata saliha alhalin kungurmar munafuka kuma azzaluma ce, yanzu ban da mun san hali ai da se mu karya ta abinda muka ji da kunnen mu".
Rukayya kanwar Salees me bi masa ta fada in da Safara'u ta cafe
"Ke ni fa a wannan zamanin bana tantama kan duk abinda aka ce mutum yayi dan wallahi wani mutumin in zaki shekara goma dashi ba zaki taba sanin wasu bakin halin nasa ba se Allah ya ciyar dake, to balle kuma wannan matar da tun a baya bakin halin ta ya fito fil, kina zaton zata bar Mariya ne cikin kwanciyar hankali bayan Allah ya bata haihuwar da ita ta rasa?".
"To wa ya hana ta haihun ita, aikin banza, Allah ne fa ya san nufin jaki da be bashi kaho ba, wannan da ta haihu ba musan me zata yi ba, a haka ma muna fama da ita, ai ni na godewa Allah da be Kaddara min hada jini da wannan bakar jarabar ba".
Hajiya Iya ta fada tana wani tsuke baki, sauke numfashi nayi bayan na gama tunani na, lallai akwai wani abu, tabbas akwai sharrin da aka kulla min da har yaja min wannan bakaken maganganun sedai ina fata Allah yasa komai ya zo min da sauki ya kuma bani juriya da hakurin dauka.
Da kyar na iya nayi wanka na canja kaya, yunwar da na shigo da ita kuwa tuni ta fece haka ma baccin da nake kuzun nayi shima duk ya yi nasa wajen, jira nake kawai in ji an doko min kira an fara tuhuma ta, dalilin tuhumar ne dai ban sani ba.
Kwankwasa kofar da aka yi yasa na dan zabura kadan kafin na kurawa kofar ido, da kyar na iya mikewa naje na bude, kallo daya za'a min a san a firgice nake.
"In kin ga dama ki fito Hajiya na magana".
Hannatu ta fada min tana wani yatsuna fuska haka at the same time tana harara ta kasa kasa, tsabar kidima ko dankwali na da ya fadi ban tsaya dauka ba na bi bayan ta ina kiran Allah a zuciya ta.
Wannan karon gaba dayan su ne a falon har da Mariya da Salees da kuma wasu mata biyu manya da nake kyautata zaton yan uwan ta ne dan ban san su ba cikin familyn Salees, kowanne ka kala fuskar sa a hade take babu alamun wani abu wai shi fara'a yayinda idanun su ke kara kaina a jiki na kamar zasu dauke ni da ido.
Daga fuskar su zaka hango tsantsan hasssada da kishi ganin irin kirar da Allah ya zuba min, riga da skirt din jikina ya kama ni dam kamar yadda kayana suke dan faranta wa miji na, ban lura a haka na fito ba dankwali ba balle mayafi se da Hajiya Iya dai ta yi magana
"Sannu isasshiya, hamshakiya mandiya, shima dankwalin kina jira yaron naki ya je ya dauko miki ne?".
Gaba dayan su suka kuma watso min na mujiya lamarin da yasa naji na takura matuka, na mike da sauri dan daukowa se ta kuma dakatar dani
"A'a koma ki zauna dan na tabbatar da kina sane kika fito, koma me kike so mu gani mun gani sedai Allah wadaran irin wannan kyan na dan maciji".
Komawa nayi na zauna jiki na kamar an min duka, wai shi dai wanda baya sanka kome kayi se ya kushe, kome kayi baka iya ba, kuskure a wajen sa ganganci ne, Allah ka rabu mu da wahala Ameen.
"Dago ki kalle ni nan Khadijah, ba na tsoran ki bana tsoran fada miki magana dan ba zan zuba ido ki cigaba da cutar min da da matar sa tagari ba uwar ya'yan sa bayan ke ko kara baki aje ba.
Na dade da sanin ke din ba karamar muguwa bace munafuka kuma azzaluma tun lokacin da kika nemi raba ni da dana sedai Allah ya fiki ya tankwabar da mummunan nufin ki, sedai ban san rashin imanin ki har ya kai ace ki karbi maita dan cutar da matar Salisu ko yayan sa ba, kin yi asara, wallahi kin yi asara Khadijah dan kin dade da kwashe kayan ki daga gaban Annabi".
Wani irin dam kunne na yayi, ƙwaƙwalwa ta ta dakata daga aiki, kwata kwata kaina ya toshe, gaba daya na daina ganewa d fahimtar komai da suka cigaba da fada se aikin kallon bakin su d ana cigaba da yi dan tun da Hajiya Iya ta ambaci maita na dago kaina daga sunkuyar dashi da nayi.
Fiye da mintina biyar kafin ƙwaƙwalwa ta gama accessing all she've said, maita, na karbi maita, meaning suna nufin ni din mayya ce, mayya fa, innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
A lokacin wani irin Hajijiya nake ji cikin kaina, kaina ya shiga juyawa kamar wanda ake wujijjigawa, dakin ya shiga juyawa dani kamar zan kife yayinda kalman maita ya shiga yawo a kunne na, lamarin da ya tilasta min saka hannaye na toshe kunnuwa na tare da runtse ido na da sauri haka kuma at the same time Ina girgiza kan tare da furta kalman a'a, a'a da karfi cikin wani irin yanayi me ban tausayi ga masu zuciyar imani.
A lokacin da na budi ido se gani na nayi kwance kan gado na Salees tsaye a kaina ya jingina da bango, nauyin da naji kaina yayi ya tilasta min mai da ido na rufe kafin kuma in a blink of an eye na sake budewa lokacin da tiryan tiryan abin da ya faru a falo ya dawo min kaina, a gigice na fara kokarin mikewa wanda hakan ne ya ankarar da Salees cewa na farka, da saurin sa ya matso ze rike ni na goce na nufi kofar da ke rufe wadda ake kan bugawa tare da kiran sunan sa, da sauri ya riko ni na shiga kokarin kwace wa
"Ina zaki je haka a gigice, ki tsaya kar ki je ki fadi".
"No, sake ni, ka sake ni in je in fada musu ni ba mayya bace, ka sake ni in ji me na musu da zafi da zasu hada ni da kalmar maita, dan Allah ka bar ni naje na musu bayani ko zasu fahimta suyi withdrawing wannan mummunar kalmar daga gare ni".
"Naji zan sake ki, but first ki tsaya ki nutsu kar ki jiwa kan ki ciwo".
Duk yadda Salees yaso dakatar dani naki, so nake kawai na fita na fada musu ni ba mayya bace, so nake in ji sun ce Khadijah wasa nake muke miki ke ba mayya bace.
Kubcewa nayi na nufi kofar tare da murza key din da ya sawa kofar na fita, Rukayya, Sadiya da Hannatu duk na tsaye bakin kofar, ashe suke bugu tare da kiran sunan sa suna fada masa Hajiya Iya tace ya fito daga daki na kafin ran shi ya baci.
"Rukayya Sadiya ai kun san ni kun san ni ba mayya bace ko, kema Hannatu kin sani ko?".
Wani matsiyacin tsaki Sadiya taja tare da juyawa ta nufi falon ragowar suka rufa mata baya suma bayan sun yi nasu tsakin Hannatu na kunkuni kasa kasa, a haukace na rufa musu baya ina kuma yi musu magana, ni dai buri na kawai su yarda ni ba mayya bace.
Fisgo ni Salees yayi jikin sa ya rungume, duk yadda nake ture shi ya sake ni ya kiya har seda ba hakura na lafe jikin sa na shiga maida numfashi da karfi da karfi kafin kuma wani maraitaccen kuka yi kwace min, kuka nake yi me suna kuka wanda tun d nake shiga tension a gidan Salees ba na tunanin na taba makamancin sa, Muryar Hajiya Iya ce ta sa Salees janye wa da sauri yana sosa kai
"Sake ta sallamamme, sake ta nace karamin mara mutunci, mara zuciya kawai, kai in da kasan kan ka har ka kuma kallon wannan abar bayan abinda tayi, wuce muje, kema munafuka muje dan yau ko mutuwa zaki yi karewar mutuwa se an yi maganar nan yau".
Hak ta tasa mu gaba har ciki falon, na sake neman waje na zauna haka ma Salees itama ta koma wajen ta ta zauna
"Abinda y faru jiya d dare zuwa yau ya zama na farko na karshe, wallahi tallahi rantsuwar dan musulmi kika Kuma taba min suruka ko jikoki se ran ki ya baci, in zaki yi maitar ki kiyi ta can a waje amma ban da nan dan b zaki ci riba ba".
Seda na saki sheshshekar da ta taso tun daga kasan zuciya ta sannan na dago
"Na rantse da girman ubangijin da ya halicci sammai da kassai Ni ba mayya bace Hajiya, a cikin trend din dangin mu wallahi babu maye balle in gada".
"Yo Allah na tuba maitar da ake siyarwa yanzu kamar alawa a kasuwa, ai ba abin mamaki bane dan babu a dangin ki kuma an same ki da ita, ni dai na fada miki wallahi ba zan lamunta ba dan gwara ki cinye kan ki da ki taba min zuri'a".
"Me nayi muku da zafi hak da zaku jefeni da kalmar maita, me na tare muku da zaku min wannan accusation din, auren Salees gare ni ne laifin da har yaja min wannan zargin ko kuwa tsabar tsana ce?".
Na tambaya hawaye na kafewa a fuska ta yayinda ya koma zuba ta cikin zuciya ta
"Yi man shiru munafuka mara tsoron Allah,
Showing 33001 words to 36000 words out of 43434 words

____________________________________________________________________________
_Free Chapter Fourteen_

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12 Chapter 13Chapter 14Chapter 15