na kuma shafawa, abin babu karya ba kuma yaudara tun kafin na kai ga idar da sallar naji zuciya ta wasai tamkar ban taba sanin wani abu wai shi damuwa ba, farin ciki da walwala suka cika rai na tamkar wadda akayi wa bushara da kujerar hajji.

Agogo na kalla wanda ya nuna karfe biyu da rabi na dare na tashi na cire hijab din da na sa na rataye shi tare da maida daurin dan kwali na na nufi gado na na kwanta hannu na rike da calbi ina ja cikin kirari wa madaukakin sarki, cikin rahmar Allah se gashi na samu salamammen bacci me cike da jin dadi kamar kar na farka dan se da nayi da gaske na iya tashi asuba ba kamar ragowar ranaku da ake kiran farko a kunne na ba saboda damuwar da kan hanani bacci, lallai Allah buwayi ne garara misali haka kuma duk wanda ya bar Allah tabbas yayi hannun riga da nutsuwar fili har ma da ta boye.

Ba fa wai na manta da abinda Salees ya min bane, ba kuma na manta da kara ta da ya kai wadda zamu je yau bane kawai dai damuwar hakan Allah ya cire min daga rai na.

Ban yi gigin yin breakfast ba dan ban manta layin d ya shata min ba na cewar in har ban kwana dakin sa ba to bani da girki gaba daya, ma'ana har dafa abinci, a can baya da yasa dokar na damu amma a yau se naji ni hakan ma yayi min dan gashi na samu damar bajewa a gado ina baccin safe kasancewar asabar babu aiki.

Se after 10 na tashi nayi wanka da shower gels dina da ragowar turarukan wanka masu kamshi da gyaran fata wanda a kullum yanayin yadda nake kula da jikina yake bawa wanda suka san ainihin shekaru na mamaki, dan da yawa mutane basa yarda na kai shekaru na, so da yawa se kiga ana bani shekara Ashirin da biyar da shida koma da hudu, nidai in irin haka ta faru sai dai nayi dariya kawai, amma fa bana mamaki dan ko ke kika kalle ni ba zaki ce nayi talatin har da biyu ba wanda sune shekaru na na gaskiya da gaskiya .

Doguwar riga na sa kirar Morocco, kafin kace me na zama wata bakar balarabiya saboda yadda rigar ta min ainihin kyau ta bi dirarren jiki na ta zauna Kamar yar asalin ƙasar, kai har ma nafi dan su ba su da cikakken diri irin nawa.

Karamin fridge dina na bude tare da zubawa kayan snacks din ciki ido sannan a hankali na debi samosa uku tare da drink na maida murfin na rufe, a tsanake naci abina na kora lemo na kara da ruwa me dan sanyi, take naji ciki na y dauka masha Allah na koma  tare da zama kan doguwar cushion din dakin ina bibiyar chats din kawaye na cikin group din mu me suna *UWAR GIDA*.

Knocking din da aka min yasa na dan saurara daga karanta wani post da nake yi kana na tashi na tafi na bude bayan na kuma jin wani, Sahal ne me bin Ilham, tsakanin su shekara daya ne dan yanzu sha biyu yake yayinda ita take sha uku

"Daddy yace ki fito".

Yace tare da barin wajen da sauri, jinjina kai nayi tare da komawa daki ina fadin

"Wata matsalar ta dawo" a raina dan zan iya cewa Sahal har yafi Ilham dan shi kan kamar uwar sa ta bashi zuciyar ta ne, bakin hali a cikin yaron abin se addu'a shiyasa tun farko ban sake masa ba bare ya raina ni ko da dai b wai girmama ni yake ba duk tsare gida na, tun hutu ya tafi gidan iyayen Mariya kuma ko da aka koma makaranta be dawo ba ta can yake tafiya se yau da aka dawo dashi.

Sai da na koma gaban madubi na sake gyara zaman mayafi na na kara turare kadan me sanyin kanshin da baya tashi sannan na dau waya ta da karamar purse dina na fita, basa falon hakan yasa na fita compound bayan na rufe kofar falon.

A tsaye na hango Salees jikin motar sa wadda ina fitowa ya bude ya shiga, takawa na shiga yi zuwa wajen su sedai kafin na karasa ya ja motar sa yana yi wa maigadi horn ya bude gate tsayawa nayi kallon ikon Allah se kuma na bar shi as tun d ta kusa dani zai wuce maybe ze tsaya in shiga,

"Motar ya cika, ki biyo bayan mu a naki tun da kina dashi".

Sakatoto nayi ina bin shi da kallo kafin kuma na kau da mamaki da sauri dan wannan kadan ne daga halin shi, shi in har kuna fada to fa ba zaki kuma jin dadin sa ba, duk yadda ze bata wa mace rai to se yayi so tuna haka se kawai na saki murmushi me kyau na gyada kai na alamun toh na juya zuwa wajen mota ta.

Farin ciki na daya , kamar yadda yace ina da motar, mota kuma ba karama ba domin suna gogayya da tasa a wajen kudi, bangaren tashe kuwa har ma tawa ta zarta tasa, ina tsananin so da kaunar motar domin kuwa Abban mu da hannun sa ya bani kyautar motar lokacin da Mariya ta haifi Amir wata shida da suka wuce.

Cikin tuki na na natsuwa na fitar da motar daga gidan tare da hawa titi na nufi babban gida kamar yadda suke kiran family house din su inda nan ne iyayen Salees suke.

Gefe da tasa motar na aje parka tawa sai dai ban fito ba sai da na gama addu'o'i na na samun rinjaye kan makiyi dan kusan zance makiyan nawa ne mutanen da zan hadu dasu.

Bakin babban falon Hajiya Iya nayi sallama tare da daga labulen na shiga bayan na sabule takalman kafa ta, a duk cikin mutane takwas dake zaune a falon ba'a sami ko daya da ya iya amsa min sallamar da nayi ba wanda hakan ba bakon abu bane a waje na, gefen one sitter na samu na zauna kana na shiga gaida Hajiya da ta nuna kamar bata san da shigowa ta ba tana yi wa Amir dake hannun ta wasa, seda na maimaita gaisuwar sannan ta amsa min a watse.

Daga Lafiya lau din bata kuma cemin komai ba nima kuma naja baki na nayi shiru, sai da ta gama da shalelen ta sannan ta mikawa Hannatu kanwar Salees dake zaune a wajen Amir kana ta fuskanto mu gaba daya.

"Uhm, kace mene?".

Dan muskutawa Salees yayi ya fara rattabo zance kamar me karanta labari

"Hajiya karar khadeejah na kawo miki, ban san meke yawo a ranta ba, ban san wake zuga ta amma gaba daya ta birkice, gaba daya ta canja halaye da dabi'un ta ta kwaso mugayen akidu da ra'ayi ta ɗorawa kan ta.
Babu damar naman Amir tayi wani abu yanzun nan se ta hayyako ta fara fadin maganganu marasa kan gado, kwata kwata bata neman zaman lafiya kamar yadda ita Mariya ke son su rayu cikin salama, a kullum burin ta ta kuntata min ta bata min rai.
Duk ma kuma ba wannan ne babbar damuwar ba, kin ga yaran nan wallahi khadeejah yadda ta tsane su bana jin ko makiyin ta ta tsana haka, daga ni uban su har ita mahaifiyar su bamu san me mukai mata ba da take neman saukewa kan su.
Shekaranjiya iIlham d zazzaɓi ta kwana me zafi saboda yadda ta fasa mata baki ga kuma kunnen ta da ta murde saboda wai tayi mata rashin kunya wanda zan iya rantsewa baby ba zata yi haka ba sedai yarinta, wai kuma daga uwar ta ce ta dinga sassauta hukunci shikenan ta dau fushi da ita da yaran har tana tafiya wajen aiki ta bar baby bata je makaranta ba saboda tana tutiya da tinkahon baban ta ne ya sai mata mota, Hajiya Iya fa abubuwan da zan iya fada miki kenan kuma akwai wasu bayan su sai dai in zan zauna lissafa miki wallahi zamu wuni ba mu gama ba, shiyasa na kawo ta gaban ki ta fadi meye matsalar ta da ni, Mariya ko yayana"..............
Ouummey 📚✍️.








Ouummey 05 {4/30/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey



*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________
        
   
              _Free Chapter Five_

Har ya gama zuba surutun sa ina zaune kamar yadda nake tun farko sedai tsoron Allah ya dade da cika zuciya ta jin wai yau a kaina ne Salees yake rattabo wadannan Laifuka da matsaloli, lallai rayuwa juyi juyi ce wai kwado ya fada ruwan zafi.

"Uhmmm yanzu duk wannan abubuwan ita hamshakiyar ke yi amma ka zauna kana kunsar bakin ciki, lallai sannu khadeejah autar mata".

Sake kasa da kai nayi ina jin tune din da Hajiya Iya ke magana dashi kafin ta ja dogon tsaki

"Ke dago nan ki kalle ni bana son munafurci, ana magana kina sunkuyar da kai kamar wata mumina bayan kasurgumar muguwa ce ke, dago nace ki kalle ni".

A sanyaye na dago na zuba ido na cikin na Hajiya Iya

"Yanzu ke dan kin kasance butulu wadda bata san alkhairi ba har ya'yan Salees abin ki ne a wajen ki bayan dimbin halaccin da yayi miki a rayuwa?, Da zaki fidda hannu ki daki yarinya karama irin haka saboda baki san zafi da ciwon haihuwa ba, anyi magana ke ga Sarkin an iya bakin rai kin dauki fushi da su".

Se kuma ta juya kan Salees

"Ai duk kai ne shashasha shi yasa har mace ta raina ka, ban da raini kana kallon ta tana iskanci ka zuba ido baka yi maganin ta ba, ko da yake ai ta gama da kai yanzu ma da sauki tun da kana iya ganin laifin ta".

"Saurare ni nan kiji, in kin gama da Salisu to ni na fi karfin ki, shima kuma gashi nan Allah ya fara karya alkadarin ki ta hanyar matar kwarai da ya samu, na san ba komai ke damun ki ba face bakin ciki da hasssada tare da asararren kishi, ke a rashin tunanin ki se mu bar Salisu ya zauna da ke kadai bayan ba haihuwa kike ba, kullum yayi ta cika miki ciki da abinci kina juye wa a masai babu fus balle as, to ta Allah ba ta ki ba, jinin Salisu ne gasu nan kina gani, karewar bakin ciki ki hadiyi zuciya ki mutu ni da wallahi farin ciki zan yi dan zaman ki gidan dana dan kawai babu yadda zan yi ne amma ba so nake ba.

Batun yara kuma daga yau na shata layi tsakanin ku, ko da wasa kika Kuma kai hannun ki kan jikoki na wallahi a bakin auren ki dan se Salisu ya sake ki ko na tsine masa albarka, uwar su kuma in dan kin ga me hakuri ce kike cuta mata to Allah yana kallon ki kuma baze bar ki ba".

"Kai kuma in zaka dauki mataki akan juyar matar ka ka dauka in kuma zaka cigaba da zama tana raina ka kai ka sani".

Hakuri Salees ya shiga bawa Hajiya Iya ganin har dashi cikin fadan sedai ni tun daga gaishe ta ko tari ban yi ba balle wani ban hakuri, na bata hakuri akan me, me nayi mata, bayan duk cin zarafin da aka min kuma na bada hakuri, tabdi.

Aikuwa rashin bada hakuri na ya sake tunzura Hajiya ta cigaba da bala'i da fade faden maganganu na cin mutunci d zarafi a kaina har muka mike zamu tafi

"Allah ya bamu alkhairi Hajiya".

Na mata sallama batare da na bada hakurin ba, Hannatu tayi tsagal ta zage ni yarinyar da yanzu take shekara sha takwas, fadin shekarun da na bata ma bata baki ne

"Juyar banza da wofi mara amfani kawai, ciki ba komai se kashi, mtsww Allah dai ya raba yayan mu da kayan bakin ciki".

Na jita sarai kuma zagin ya ci min rai dan na tsani raini a rayuwa ta shiyasa duk runtsi bana yarda na wulakanta ko cin mutuncin na gaba da ni.

Ashe shima Salees zagin ya masa zafi dan har na dan yi gaba se ji nayi ya fisgo ni baya kofar dakin hajiyar ya hade rai tamau yana yiwa Hannatu mugun kallo

"Dan ubanki matata sa'ar ki ce?".

Ya tambaye ta a kausashe lamarin da ya matukar daurewa Hajiya Iya kai dan su a ganin su ai yanzu Salees ya daina so na dama suna cewa soyayyar sihiri ce, to tun d yanzu ya karye ai zasu taka ni yadda suke so

"Kar ka kuma zagar min ya in ba haka ba ranka ya ɓaci".

"Amma Hajiya kin san dai hakan ba daidai bane, ban da iskanci karamar yarinya kamar Hannatu ta kalli khadeejah ta zage ta, Hannatu da bata fi kanwa ta kusan shida ba wajen khadeejah, to wallahi tun wuri ki shiga hankalin ki in ba haka ba se na kusa karya ki, mahaukaciya mara hankali kawai".

Ya fada yana karasa directing maganar kan Hannatu, nidai ina samu na zame hannu na daga cikin nasa se kawai na yi gaba abina na fice dan wallahi ko kadan shigan min da yayi be burge ni ba.

Na riga su isa gida dan haka na shige daki na kulle tare da yin lamo kan gado na, in ka ganni zaka yi zaton wata marainiya ce d babu uwa kuma babu uba haka babu sauran gata, kulle ido na nayi ina sauke numfashi ina fadawa kai na rayuwa ce haka kuma Allah yaso gani na, jarrabawa tace da ban isa na tsallake ba har na samu na ji sanyi a raina kafin na shiga toilet dan yin wanka.

★★★★★

"Yanzu haka zaki zauna kullum kina kuka akan matsala daya, na baki shawara tuntun tuni Falmata amma kin share, kin gwammace ki yi ta asarar hawayen ki a banza ko, to ai shikenan".

Babbar mace da a kalla zata kai shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar ta fada tana kallon kawar ta dake zaune ta zuba tagumi hawaye na bin fuskar ta kamar an bude famfo.

Ganin bata ce komai ba yasa matar jan tsaki tana duban Falmata

"Bata akan ki kadai abin ya tsaya ba, yanzu haka ina fada miki da zan shigo na hadu da wancan fitsararren dan Adam, wallahi yaron nan akan ido na yayi min tsaki har da tsartar da yau sannan ya shige bangaren su, shin haka zaki zauna ke a raine wanda ya alakantu dake ma ana masa kallon banza shara wofi mara amfani Falmata, shin ba zaki yi komai domin kwato abin da ya kasance naki ba tun farko? Ko kuwa zuba ido zakiyi har se rayuwa a gidan nan ta gagare ki, ki dubi karamin yaro Haisam irin motar da yake hawa ki kuma dubi taki wadda kike jin jiki da ita tuntuni, ya kamata ki farka daga barci da kike yi ki amso what is rightly yours, Ina baki shawara ne matsayin yar uwa aminiya wadda bata san ganin ki cikin komai face farin ciki".
 
"Ban damu da nawa ze kashewa yayansa ba Farida, ban kuma damu da kyautatawar sa gare su ba, damuwa ta yadda kome na bukaci Alh yayi min se ya kawo uzuri, ba kuma ze yi abin nan ba ko da zuwa da shekaru nawa ne, a cewar sa kullum nauyi kara karuwa yake a kan sa saidai yana mantawa cikin nauyin nasa akwai ni, ina da hakki a kan sa wanda a yanzu ya sauke wa kan sa, da ni da babu duk daya ne a wajen sa, se ya shigo ya ishe ni da dadin baki, kin san matsalar da nake fama dashi na ciwon ciki, naje naga likita akan shi sedai ya bukaci naje babban asibiti, to ko da naje sun ce se an min aiki, yanzu halin da ake na fadawa Alh dan ya shirya min tafiya zuwa India ayi min aikin a can amma yace be da kudi se gashi dazun nan a gabana yayi wa yar lelen sa alkawarin sabuwar mota zuwa gobe, ban face ya bini ba, ban kuma ce ya biya min tare da wani da zai kula da ni ba, iya ni kadai nace amma yace babu se gashi be rasa na canja wa yar sa motar hawa ba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun".

Hajiya Falmata ta fada tana sake rushewa da kuka, hatta da Hajiya Farida hawaye take yi na tausayin kawar ta, aminiyar ta kuma yar uwar ta

"Mata sune matsalar mata yan uwan su Falmata, na rantse miki da girman Allah duk abinda Alh yake miki da sanin Hauwa kuma tsarin ta ne, tun asali matar nan bata son ki kin sani ta ya zata so miki kwanciyar hankali, kai hasbunallahu wa niimal wakeel".

"Farida ina ganin zan hakura da auren Alh kawai dan be da wani amfani a waje na, gara kawai in san single nake da ciwon zuciyar da Alh ke kokarin ganin ya kakaba min karfi da yaji".

"Ba zaki bar mata gidan ki ba, ba zaki bar mata mijin ki ba, wallahi ba zaki je ko ina ba, kenan ma kin yi biyu babu, baki ga tsuntsu baki ga tarko inaaa, sam wallahi".

"Gwara in tafi da in zauna Ina kun sar bakin ciki".

"Kece kin cika sanyin rai, tuntuni na kawo miki shawarar yadda zamu yi maganin ta amma kin xayan wasu tunane tunane, ke yar uwa ta
Showing 9001 words to 12000 words out of 43434 words