da dariyar sa, shiyasa ita din daban ce cikin yaya ukun da Allah ya azurta shi dasu, ita ce kuma *RIBAR AUREN* Maryam da kullum ya kalla baya dana sani balle nadama yake kuma alfahari da kasancewar ta ikon sa mallakin sa.

"Barka da dare Dada na".

"Barka kadai yaran Dada, hope you all fine?".

"Yes Dada". Suka amsa masa gaba daya ban da Haanah dake ta murmushi tana kallon su, seda ya gama gaisawa da su gaba daya sannan ta durkusa har kasa ta gaida shi, be amsa mata ba seda ya shiga har dakin yasa hannu ya dafa kan ta sannan ya amsa cike da walwala

"Jikin naka yayi sauki ko Dada?".

"Eh babyn Dada, Father baze mutu ya bar babies din sa ba har se ya aurar dasu gaba ki daya insha Allah".

Dariya suka yi su duka ita da Ameerah suna rufe ido at the same time wai kunya, shima dariyan yayi kana ya dauki Miemie a jikin sa ya fita falo suma suka biyo bayan sa, a kan three sitter ya zauna tare da zaunar da Miemie kan laps din sa su kuma suka zauna each by his side.

Cartoon me kau and educational ya kunna musu suka shiga kalla Ameerah da Miemie se hira suke akai, ganin hankalin su ya dauku yasa Rayhanah juyawa a hankali ta fuskanci Dada

"Dadaaaaah".

Ta kira shi cikin low tone dan kar tayi calling attention din su Meerah, ganin yadda ya zuba mata ido yana bata full attention din sa yasa ta karyar da kai gaban ta ba faduwa haka tana ta addu'a a ranta kan Allah yasa ya yarda da abinda zata fada

"Pls Dada kayi aure".

Ta fada tana sunkuyar da kai haka tan jin effect din piercing eyes din sa akan ta, kirjin ta na duka jin yayi shiru ta cigaba da magana da rawar murya

"You're suffering Dada, kullum baka samun bacci, You're always having sleepless nights saboda mu, abubuwan sun maka yawa Dada, kai din namiji ne, ga matsalan office, ga na jama'a ga na namu ga kuma nasu Yaaya, Dada na damu da yawa, tun tasowa na nake ganin ka cikin kunci da damuwa, i want you to live a happy life Dada, fatana da buri na be wuce in dinga hango kwanciyar hankali, jin dadi da farin ciki a idanu da fuskan ka ba, pls dan Allah do me a favor in ga Dada na cikin yanayin da nake fata kafin Allah ya dauki raina kaji Dada".

Tun da ta fara magana babu kalmar da ta doki ran sa kamar irin kafin Allah ya dauki ran ta, abu na zuciya kawai se ya dinga hango har gashi ance ta mutu, ga ta ance itama ta tafi kamar Maryam, se kawai ya shiga girgiza kai yayinda zuciyar sa ta dinga ayyana masa ze iya rasa yar sa mafi soyuwa a ran sa, ze birne rai mafi damuwa dashi

"A'a, a'a, no Haanah, ba inda zaki je, a'a ba zaki mutu ba".

Ganin yadda Dadan ya rikice yasa ta riko hannun sa tare da matsewa cikin nasa

"Calm down Dada, nima ba zan so in mutu in barka ba, I'll not leave you Dada, not now not after, ka kwantar da hankalin ka kaji".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe ido ya kwantar da kai kan makarin kujera se kuma ya bude ya zuba kan fuskar Haanah da ta cigaba da magana

"Zaka yi aure Dada?, Zaka cika min buri na?".

Da sauri ya hade rai

"Kar na kuma jin maganar nan a bakin ki Rayhanah, ko ba yanzu ba, okay?".

A sanyaye idanu cike da kwalla ta gyada masa kai zuciyar ta na karyewa dan ta san ba dan kowa Dadan yaki aure ba se dan su, yana tsoron ya auri wadda zata gallaza musu ko ta nemi raba shi da su

"Insha Allah ba zan Kuma magana ba Dada, a koyaushe ni me bin umarnin ka ne, komai zan yi kai nake fara tunani kuma wannan ne dalilin da yasa na kawo batun aure dan nasan insha Allah in kayi dace da mace nagari zaka yi farin ciki a rayuwa, zaka sami nutsuwar da ka rasa tun zamanin kuruciya hak kuma zaka sami kwanciyar hankalin da baka taba tunani ba.
Na sani saboda mune kake dodging maganar aure Dada saboda kana tunanin makomar mu in ba'a yi dace da tagari ba, sedai ya kamata akan komai mu zama positive, what if muka yi dace da tagari, kai ma da muma duk zamu sami jin dadi da walwala, and above all hankalin Yaaya ze kwanta, kayi tunani akan Yaaya, itama mahaifiya ce kamar yadda kake mahaifi, yadda kake kaunar mu haka Yaaya ke kaunan ka, yadda kake son ganin mu cikin farin ciki da walwala haka itama Yaaya ke son ganin ka, na sani ka san yanayin da take ji tun da kaima kana jin makamancin sa, shiyasa na kawo maganar da na san zata faranta maka da ita amma ba zan kuma ba insha Allah tun d baka so, am sorry for upsetting you Dada, am sorry pls forgive me".

Gaba daya se yaji Haanah ta daure shi da jijiyoyin jikin sa, se yake ji kamar ta sa wata igiya me karfi ta zazzarge shi dasu, kawo batun Yaaya ya sanyaya gabban jikin sa gaba daya, eh ba karya tayi ba domin duk wanda ya kwana ya tashi a gaban Yaaya yasan babu abinda take fata da burin gani irin yayi aure a yanzu, ta sha zaunar dashi tayi masa nasiha, ko kuma tayi ta bashi labari mai cike da hannun ka mai sanda amma duk se ya nuna baigane ba, yanzu kuwa da ta alakanta abinda mahaifiyar sa take ji da wanda yake ji se ya gane radadin me girma ne, haka kuma akwai ciwo a zuciyar mahaifiyar sa dangane dashi

"Na amince Haanah, amma not now, ban kuma ce a zaba min ba, a bar ni har zuwa lokacin da zan ga wadda ta kwanta min da kaina".

A zabure ta ke kallon Dadan nata ido waje,

"Da gaske Dada?, Da gaske ka yarda zaka yi aure?".

Gyada mata kai tayi babu digon fara'a a fuskar sa, sedai ga mamakin sa hakan be sanyaya jikin Haanah ba balle har ya hana ta fara'a se ma wani karsashi da ya ga ta samu lokaci daya, karo na farko kenan da Rayhanah tayi farin ciki lokacin da shi yake cikin damuwa................

_*3 PAGES TO GO, FREE CHAPTERS A YET TO END*_.

_*KAR KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE KAMAR YADDA TUN FARKO NA FADA HAKA KUMA NAKE ADDING PREFIX DIN _FREE_ A HEADINGS DIN KOWANE PAGE, SO GA MASU BUƘATA SHOULD HURRY UP AND START MAKING THEIR PAYMENTS DAN 15 PAGES NE FREE*_.

ME BUKATA ZE IYA DM TA WNN NUMBER👇
*09013101854*


Ouummey 📚✍️.










Ouummey 13 {5/13/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey






                      Ouummey 13
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

 
          _Free Chapter Thirteen _

Yana lura da yarda Haanah ke walwala da farin ciki har zuwa lokacin da suka yi masa sallama suka tafi daki dan yin bacci, da ido ya raka su har suka shige daki yayinda ya sake gyara zaman sa kan cushion din da yake yana kwantar da kan sa kwakwalwar sa na yin nisa cikin tunani.

Seda ta tabbatar ta Miemie tayi bacci kafin ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta da sauri, curiously ta shiga kiran layin kakar ta without minding dare ya fara nisa dan ita after ten lokacin, seda wayar ya kusa karewa kafin aka daga tare da sallama, a dokan ce Haanah ta amsa wa kakar ta and without sauke numfashi ta ɗora da dalilin kiran

"Albishirin kin Yaaya".

Daga can bangaren dattijuwa ce zaune ina gadon ta me kyau kamar na yaran amare yan gata, ba wani shekaru ne da ita da yawa can ba sedai zata kai sittin da wani abu zuwa close to saba'in, cike da son jikar tata ta amsa mata da

"Goro fari kakal Rayha".

Ta bangaren Rayhanah duk da bata san yadda Yaaya ke bata mata suna amma farin cikin da take ciki yau ya hana ta complaining

"Dada ya yarda ze yi aure Yaaya" ta fada excitedly tana washe baki kamar gonar auduga, unbelievably Yaaya ta zaro ido tana sake manne wayar da kunnen ta

"Kai haba dai, wa ya fada miki wannan tatsuniya?".

Seda ta tura baki gaba jin yadda Yaaya ke neman karyata ta bayan ta san karya bay acikin habits din ta sannan ta bata amsa

"To wallahi da gaske nake kuma ba tatsuniya aka bani ba shi da bakin sa muka yi magana dashi kuma ya yarda yace ya amince ze yi aure".

Wani irin kwallan farin ciki ne ya taru a idanun Yaaya da yasa muryan ta ya raunana

"Allah yayi miki albarka Rayhanatu, Allah ya jikan mahaifiyar ku ya sa ta huta, ke kuma Allah baki miji na gari da yaya masu albarka da zasu ji kan ki kamar yadda kike jin kan mahaifin ki".

Da Ameen Ameen Haanah take ta amsa Yaaya har ta gama addu'ar ta ta shiga share hawaye

"Dama na fada miki ki daina raina karfin talakar gani, kina ta wani fada min ba zan iya ba b azan iya ba se gashi ba baki mamaki, kuma ina nan ina jiran alkawarin mu dan ban manta ba kince zaki bar min murjanin ki in dai na sa ya yarda, bye dare yayi se anjima".

Rayhanah ta karashe tana dariya jin muryar Yaaya itama tana darawa, aje wayar tayi tare da kallon bed din Meerah se ta ga tuni ta yi bacci so se itama kawai ta kashe wuta ta kwanta kan gadon ta wanda kowa da nashi a dakin.

Ta can wajen Hajiya Yaaya kuwa tana jin Haanah ta kashe waya itama ta aje taya tare da daga hannu ta shiga godewa Allah idanun ta na zubar da hawayen farin ciki, a cikin kaf rayuwar ta a yanzu dai bata da wani rai da take kauna kamar dan ta mahaifin su Rayhanah, tsananin soyayyar da take masa ne ya jagorance ta wajen aikata son zuciya ko kuskure zata kira abin wanda ya zama Mabudin duk kan wani kunci, damuwa, tashin hankali da rashin walwalar dan nata haka kuma suka zama makullin farin ciki da jin dadin sa, bata fahimci tayi kuskure ba seda lokaci ya riga ya kure ta yadda bata da wani abin yi musamman ma da duk lokacin da ta nemi yin wani hobbasa dan nata ke dakile t ta hanyar nuna mata ai komene tun da ya kasance zabin ta to he can endure it even if it'll cost his whole life ne.

Bata yi kasa a gwiwa ba t shiga toilet ta dauro alwala tare da tada kabbara dan mika godiya ga Allah tare da fatan ya sallada abin a ran dan nata ba se nan gaba ya tubure yace be san zancen ba wanda a yanzu wannan opportunity din kadai take kallo as hanyar gyara kuskuren ta dan haka zata yi iya kokarin ta wajen ganin ta bawa mafi soyuwar dan ta farin ciki.

________

Rayuwa na ta tafiya abubuwa na faruwa masu dadi da akasin ta, a kalla yanzu kusan wata hudu kenan da muke zaune lafiya a gidan mu se yan abinda ba'a rasa ba, duk da zan iya cewa a kwanakin nan yanayin namu ze fi kyau da a kira shi kadaran kadahan dan kuwa dai ba wai muna cikin farin ciki bane, haka kuma ba wai ana tsananin tashin hankali ko rigima bane.

Fushi ne dai yake yi kan wani incident da ya faru shekaran jiya, abin ba wani me zafi bane amma dake a wajen Salees ko me ya shafi ya'yan sa me zafi ne ba ya daukan shi da wasa se kuwa ya daukaka abin har fiye da misali.

A shekaran jiyan ni ke da girki, hakan yasa na shiga kitchen kamar kowane lokaci na shirya launch kasancewar Sunday kowa yana gida, before in fara girkin da se da nabi ka'idar da ya tsara na cewa duk wadda ke da girki zata fara tuntubar yaran sa abinda suke so, in bakin su ya zo daya su biyun shikenan se a yi wanda suke so din gaba daya ko kuma ayi musu su biyu sannan me girki ya dafa abinda yayi niyya daga baya, in kuwa bakin su be yi daya ba to kowa a dafa masu wanda yake so individually, tun lokacin da yasa dokar na fada masa hakan wani karin aiki ne na daban gare mu amma se yace shi haka ya tsara dan in yaran sa ba su ji dadi sun yi walwala a gidan su ba a ina zasu yi?, Dole haka na yarda a wancan lokacin dan maganar shekara hudu baya nake yi wannan.

Abinda ya faru shekaran jiya kuwa shine na tambayi Sahal abinda yake so kafin na shiga kitchen se yaron yace me zan dafa, take nace masa jallof couscous se watermelon juice, da farin ciki da komai Sahal yace min shi zai ci meaning base na masa different girki ba, ita kuwa Ilham da na tambaye ta se tace rice and stew zata ci, daga haka na shiga kitchen na hau ayyukana, nan da nan na hada abubuwan da zan yi na jera kan dining sannan na wuce daki na yi wanka tare da canja kaya kana na kwanta na huta ina jiran dawowar mijina daga masallaci

Karfe biyu ya shigo wanda tun da na hango shi ta window na fito falon yana shigowa na masa sannu da zuwa tare da masa jagoranci zuwa dining din Mariya da yara suka biyo bayan mu, seda kowa ya zauna sannan na shiga serving din su daya bayan daya har n gama kafin na zubawa kaina na zauna dan fara ci sedai abin kamar almara se kuwa Sahal ya ture plate din gaban sa a shagwabe yana tura baki nan da nan kuma idanun sa ya tara hawaye, irin yadda baban ya rude yana tambayar sa lafiya se kawai na zuba masa ido ina jiran jin me ze ce, zuciya ta kuwa har da ayyana min may be shi da mahaifiyar sa ne

"Bana son abincin nan Daddy".

Da sauri na zaro ido jin abinda yace fuskar sa a kwabe kamar ba shi ne har da tsalle dan nace jallof din couscous din zan yi ba

"Why didn't you tell your Aunty da zata yi girki?, She would have cooked your heart desire for you".

Salees ya fada trying to rarrashi dan sa yaci abincin

"Daddy I've told her ni pounded yam nake so while Ilham tace rice and stew, but see what she serverd me after serving Ilham her favorite".

Strictly Salees ya dago yana dubana with plain expression a fuskan sa

"Shi meyasa ba'a dafa masa abinda yake so ba after kuma yayi mentioning?".

Seda na hadiye wani yawu ganin yadda yake interrogating dina kamar wata yarinya gaban ya'yan sa da matar sa sannan na iya na bada amsa

"I've asked him me zeci and shima se ya dawo min da tambayan me zan dafa so i replies with jallof couscous, har da tsallen sa yana cewa yana so kafin na tambayi Ilham ta fadi nata, and here's the same boy narrating different story dan ban San yaushe yace pounded yam yake so ba".

Daga yadda yake kallo na na fahimci ba wai zance na ya gamsar dashi bane sedai be yi hukunci directly yadda ya saba ba se ya dubi Ilham

"Wane amsa yayan ki ya bawa auntyn ku da tambaye shi kan abinci?".

Wlh a lokacin I was speechless, kenan salees na nufin be yarda da abinda na fada ba?, Mu sa ma be yarda ba, mu sa a ransa kawai yana ganin karya nayi, in ma hakan ne kenan baze iya rufa min asiri gaban yara ba se ya zubar min da kima, ko so daya shin Salees be kamata yayi tunanin tarbiyyan ya'yan sa ba, gaba daya se naji komai ya fita a raina, shikan sa Salees din naji ya zube min a ido na

"Daddy naji fa sanda yake cewa couscous ze ci fa, Allah be fada mata sakwara yake so ba".

Irin yadda Mariya ke bin Ilham da wani mugun kallo ka dauka kisan kai yar nan tayi bayan gaskiya ne kawai ta fada, shi kuwa Sahal yana jin me Ilham ta fada se kuwa ya ture plate din a matukar fusace da har yasa abincin kai ta zube kana ya tashi yana jan tsaki ya nufi barin dining din, zuba ido nayi kawai in ga hukuncin da salees ze yi ko da dai ba wani sabon abu bane cewa zeyi yaro ne.

To ny utmost surprise se kuwa Salees ya mike a hanzarce har yana neman ture table din ya maza ya riko hannun Sahal dake huci kamar ze daki wani, cikin lallashi da kwantar da murya ya shiga lallaba shi kan yaje yaci abincin

"Wallahi ba zan ci ba Daddy, kawai saboda ba'a sona ita Ilham se aka dafa mata abinda take so ni aka ki, shiyasa ma ni na tsane ta dan bata da kirki, mtsww".

Ya sake jan tsaki, burin salees dan sa yaci abinci kar ya zauna da yunwa so se duk be yi overlooking wannan rashin kunyar da yayi a gaban sa ba, shi dai damuwar sa yaci abinci, ganin yadda uban ya damu se ita ma
Showing 30001 words to 33000 words out of 43434 words