ya shiga cikinta, bayan ya shiga ne sojan ya zuba mashi maltina cup, cikin girmamawa ya miƙa mashi, girgiza kai ya yi alamar baya buƙata, sojan bai ji komai ba, domin idan da sabo sun saba ba zaka taɓa gane me yake so ba.

Da gudun gaske suka tashi motoncin suka fice daga gidan, kai tsaye white house suka wuce, kamar dai ko yaushe duk wata abin hawa dake a kan hanyar sauka take ta basu hanya su wuce.

Lokacin da suka isa white house, gidan a cike yake tab da jami'an doka sojoji manya-manyan yan siyasa da duk wasu masu faɗa a ji a kasar, gaba ɗaya ko ina ka waiga sojoji da yan sanda ne cike makil a gidan, tun da jerin gwanon motocinsa suka shigo gidan, gaba ɗaya sojojin dake a cikin gidan suka fara kamewa suna sara mashi, wani sojan kam ma, saboda kamewa sai ka rantse da Allah baya numfashin. Lion duniya

Kamar dai kullum kun san mai hali baya fasa halinsa, to haka ne, Lion dai bai kula kowa ba, ko kallon in da suke ma bai yi ba, ya sanya face mask a fuskarsa ya fito, kai tsaye fadar shigaban kasa ya wuce, sojojin sa kuma suka dakata daga bakin kofa.

Yana shiga cikin fadar ya wuce Roosevelt Room, nan ya isko kowa ya haɗu ana jiransa, da gani ran kowa dake cikin wajen a ɓace yake, domin Lion ya ajiye su suna ta jira, ga Tga nan tun ɗazun ya iso wajen, amma shi sai yanzu, kuma haka za su hakura ba yadda suka iya da ahi.

Daga gefe kuma ga yan jaridun white house, wato yan jaridu masu fitar da abin da ke faruwa daga fadar shugaban kasar, manya-manyan mutane suna zazzaune saman tsadaddun kujerun dake a cikin ɗakin, wayan nan kujeru sun haɗu matika gaya, kuɗin wayan nan kujeru ba zai faɗu ba saboda tsadarsu, ta ko'ina Kamshi ke tashi a cikin fadar, amma Lion na shigowa kamshin perfume na jikinsa ya rinjayi gaba ɗaya kamshin da yake a wajen, sai room ɗin ya gauraye da irin kamshin perfume nasa, wani daddaɗar sanyin Ac ne ke a cikin ɗakin, wadda sanyin yana gudu daidai misali ba na wuce ka ida ba, ko wannan su akwai kayan sha masu bala'in sanyi a gabansu ga kuma kyawawan glasses cups a gabansu kusa da abin shan.

Shigowar Lion yasa gaba ɗayan su suka ɗago suka kalle shi, dayawa daga cikinsu kallo ɗaya suka yi mashi suka kawar da kansu suna ɗan satar kallonsa. Bai bi ta kan kowa ba, saman kyakkyawar kuma tsadaden kujerar kusa da His Excellency ya je ya zauna, shiru suka ɗan yi kafin His Excellency ya buɗe masu taro da fara magana.

Kasa Lion ya yi da kansa dan bai ma san akan me zasu yi maganar ba, lokacin da aka kawo mashi takardan bai duba ba, yana wani aikin, sai dai Tga ya sanar mashi cewa karfe 10 za'a yi zaman, iya abin da ya sani kenan, kuma dama bai nemi sanin akan me za su yi taron ba, domin ba ɗaukar maganar su yake yi ba, abin da ya zo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa kawai yake aikatawa.

Kowa ya fara magana yana faɗan arbarkacin bakinsa akan kuɗin da za'a fitar dan kera manya-manyan makamai wadda karfinsu zai iya tashin state guda, ko uppan bai ce da su ba, kowa sai magana yake yi, shi hasalima ciwon kai suke sanya mashi wannan surutu da suke yi, ji yake yi tamkar ya bar wajen amma bai yi hakan ba, saboda akwai abin da yake son fahimtar a tattare da su.

An samu bambance bambancen ra'ayoyi dan gane da fitar da wannan kuɗin, wasu sun ce yes a fitar wa su kuma sun ce a'a kada za'a fitar yana da kyau a karawa yan kasa abun yi ne, ma'ana marasa aikin yi domin a ragewa kasa talauci, tun da suna da makamai sosai kawai a buɗe masana'antu companys da dama a ɗebi ma'aikata talakawa da ba su da abin yi domin kasar su ta sake tsabtatuwa daga cutar talauci, shi dai Tga ya tsaya akan gara a sayo kayan haɗa makamai domin sun fi mashi talakawan nan mahimmanci, shi kuma His Excellency hankalinsa ya fi rajaa akan gara a buɗe masana'antu saboda ba shi da burin da ya wuce kasarsa ta cigaba da zama super pawer ta duniya, ya fi son ya ga ya fi kowacce kasa komai.

Ganin sun dame shi da surutune yasa ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya nufi waje, bai kai ga fita ba His Excellency ya ce ina zai je ba su gama zama ba, shiru ya yi bai yi magana ba har sai da ya kai kofar fita sannan kasa kasa ya ce "Uncle please idan kasan irin wannan zama za ku yi kada ka sake kirana". Cikin sauri His Excellency ya ce "To yanzu dai gaya mani naka shawarar mu ji". A takaice ya ce a gina masana'antu, sannan ya wuce ya nufi waje abinsa, gaba ɗaya wajen tsit suka yi, domin sun san koda sun yi magana ma abanza ne tun da Lion ya ce masana'antu za'a gina tofa abin da za'a yi kenan, a ɓangaren His Excellency kuwa tuni ya yanke hukuncin abin da Lion ya faɗa shi za'a yi har ya fara shirye-shiryen rubutawa majalisa takarda dan a samu a saki kuɗaɗen da wuri a fara gabatar da aiki domin kawar wa da kasa talauci.

*Allah sarki manyan kasashen kenan kullun burinsu ta ya za'ayi kasar su ta ci gaba, burinsu a kullun kasarsu ta kasance ta farko a duniya wadda zata mulki ko wace kasa kuma ta juya su yadda take so, kuma sun san cewa kasarsu ba zata taɓa ci gaba ba, har sai sun raba yan kasa da talauci da mutuwar zuciya, da hanya ɗaya kawai zasu iya yin hakan, shine su rinƙa gina masana'antu suna bawa yan kasa talakawa aiki ana sarrafa abubuwa daga masana'antun ana fitarwa kasashen duniya ana sayarwa, su ci riba kuma sun raba matasansu da zaman banza zaman kashe zuciya, ya Allah ka sanya shuwagabannin muma su farka irin haka, Allah kasa su zama irin haka, ba wai bukatarmu a ɗauki kuɗi a bamu ba, a'a a gina mana abun da zamu rinƙa zuwa muna aiki a ciki muna samun halak ɗin mu ko ya yake, ya dai kasance kullun zamu je mu yi aikin mu samu, amma idan kuɗi za'a bamu kwana biyu kuɗin sun ƙare an koma gidan jiya😭 wani kuɗin ma idan aka baka abin ko karamar buƙatarka ba zai biya maka ba, please aikin yi muke so ba kuɗin da bai taka kara ya karya ba🥺😭🙏*

Lion yana fita gida ya koma ya yi wanka ya kwanta yana tunanin yadda tafiyarsa zata kaya, sai karfe 2 ya ci abinci Bawan Allah nan.

A ɓangaren su Musharraf kuwa, Michael na toilet yana wanka shi kuma ya fara haɗa tea ɗin sa don ya sha, domin bashi da wani abincin da ya wuci tea, bawan Allah, yana tsoron cin abincin gidan tun da ba musulmai bane kada ya je ya ci abin da Allah ya haramta mashi ci, hakan yasa ya kikaye kansa daga tea sai fruits kawai yake laptawa cikinsa.

Bayan ya zuba duk wani abin da zai bukata a cikin cup, sai ya ɗauki flaks ɗin ruwan tea ɗin, ya buɗe ya fara zubawa a cikin cup ɗin, sai zuba ruwan yake yi, amma cup ɗin taki cika, na cikin flaks ɗin kuma yaki karewa, idan ya cire flaks ɗin daga bakin cup ɗin zai ajiye sai yaga cikin cup ɗin babu komai, alamar ruwan tea ɗin bai zuba a ciki ba kenan, idan kuma ya sake mai da flaks ɗin yana zuba ruwan, tofa sai dai ya yi ta zubawa amma ba zai ga komai a cikin cup ɗin ba, abin ya ɗaure mashi kai, ya kuma tsorata shi sosai, yana tsaka da zubawa sai yaga ruwan tea ɗin ya canza kala daga brown zuwa jawur kamar jini, har wani yaukin jini yake yi, ihu ya kurma tare da sakin flaks ɗin ya yi baya zai faɗi, cikin sauri Michael da ya fito yanzu ɗaure da towel a kugunsa, ya yi maza ya riƙosa yana faɗin


"Uncle ɗin james lafiya kuwa?". Kasa magana Musharraf ya yi sai sunan Allah da yake iya kira a cikin zuciyarsa, amma ya kasa iya furtawa a bakinsa, ganin hakan yasa Michael ya zaunar da shi a saman ɗaya daga cikin chair ɗin table ɗin yana faɗin "Uncle ni bansan meke damunka this two days ba, sai ka rinƙa yi mana ihu yanzu kasa ni fitowa ba shiri" ya kai karshen maganar tare da komawa cikin bedroom nasa domin shiryawa, Allah sarki Musharraf shi ya ga abin da ya gani, a hankali ya ɗaga idanuwansa ya sauke su saman table ɗin, abin mamakin sai yaga komai ya koma yadda yake, duk wasu madara da ya zuba a cikin cup ɗin duk sun koma cikin robarsu, sai lokacin kuma ya samu damar kiran sunan Allah, yana kira kuma ya samu kwarin gwiwa ya tashi ya haɗa tea dinsa ya ɗauka ya nufi cikin bedroom ɗin, yana shiga ya samu Michael naɗe saman bed ya shige cikin bargo.

Da mamaki ya ce "Asif ya na ganka kana kwance? Ba wajen Lion zaka je ba ne?". Can kasa-kasa ya ce "Uncle dan Allah ka kyakeni sai da safe zan je wajen Lion ɗin, now I'm feeling sleeping over" Ya kai karshen maganar tare da janyo barkon ya rufe har kansa, abin ya kara ɗaurewa Musharraf kai, yanzu fa Michael ya fito lafiya Lou baya jin barci, amma daga shigowarsa ɗaki ba'a fi two mins ba wai barci yake ji, anya babu lauje a cikin naɗi kuwa,? Ya yi wa kansa tambayar da bashi da amsarta, ganin ba shi da amsa kuma ya sa ya ce "Asif abinci fa?" Shiru Michael bai amsa ba, da alama ya yi barci ne. Jin haka yasa ya miƙe ya koma saman sofa ya zauna.

Tas ya shanye tea ɗin sa, ya mai da cup ɗin palo, ya dawo shima ya yi wanka tare da shirin barci ya kwanta a bedroom nasa. Asuba ta gari.

Shima dai Lion kamar kullum wanka ya yi ya kwanta ransa fes sai tunainin James nasa yake yi, shima time to time ne dan yanzu tun da ya gano A.E.A bai sa wata damuwa sosai akan ɓatar James ɗin, jima yake yi tamkar ya dawo da James ɗin. Barci mai daɗi suka yi yau, mai cike da annashuwa, ga shi wuraren karfe 1 dare an tapka ruwan sama sosai, sai barcin ta kara armashi.

A NIGERIA KUWA.

Kamar kullum Rimsha na tashi karfe 6 na safe, ta zo ta gyare ko'ina tsab, daga bedroom nata har palo, sanna ta ɗaura masu abinci, yau Akila tana da glass karfe 10 tun karfe 7 ta zo suka fara aikin girki a tare, shima Akil ya bar Umaisha a kan ta zo ta rinƙa koyan girkin, dan ya ji daɗin abincin jiya sosai.

Kamar jiya yauma a tare suka yi girkin, bayan sun kammala, kamar yadda suka saba suka jere a Palo, ko wacce ta wuce ɗakinta dan ta je ta yi wanka.

Bayan sun yi wanka sun shirya ne suka sake dawowa suka haɗu a Palo, Imran ne ya kira Akil a waya ya zo suka haɗu suka yi breakfast a tare, Akila ta tambayi Imran ko dai su rinƙa sakawa Ammi da Abba abinci ne, e ya amsa masu da shi tare da zuba masu ruwan albarka, sai murna suke yi suna amsawa da Amin.

Bayan sun kammala Rimsha ta ce Akil ya kara mata karatu shafi biyu, to ya ce mata sannan ta kara karanto mashi na jiya, sosai ya ji daɗi yadda take son karatu kuma take mai da hankalinta sosai a kan hakan.

Shafi biyu ya kara mata sannan ya miƙe ya fice daga palon yana sa mata albarka, har cikin zuciyarta Umaisha ta ji wani irin bakin ciki, ta ji ba daɗi ganin yadda Akil yake yawan sakawa Rimsha Albarka, abin ya sosa mata zuciya, Akila ta lura da hakan sai addu'a take yi a zuciyarta Allah yasa kada hakan ya jawo masu matsala a tsakanin su.

"Rimsha yau ku kunna kaba ɗaya fridge ɗin gidan nan, anjima za'a shigo da wasu kayan drinks ku shirya komai yadda ya kamata, ku gyara koina, saboda ina da babban bako, Saif zai zo yau". Cewar Imran, to suka amsa mashi da shi sannan ya miƙe yana sanya masu Albarka ya fice daga palon zuwa bedroom nasa, dan ya je ya yi wanka ya shirya zuwa gidan su Irfan.

Su kuma ɗakin Rimsha suka wuce, ita kuma Umaisha ta ki binsu domin ta fara jin tsanar Rimsha a cikin zuciyarta, saboda Akil yana kula ta yana saka mata albarka.

(Toh fah kishi kumallon mata Umaisha manya)

Hira sosai yau Akila da Rimsha suka sha, sai karfe 10 Akila ta wuce school ita kuma Rimsha ta fito palo dan yin aikin da Imran ya ce su yi, wato gyaran gida da kunna su fridges da sauransu.

💖💖A WASHINGTON DC KUWA💖💖

Misalin karfe 8 na safe yana tsaye a gaban mirror ɗakisa, yana duba wasu takardun da suke a wajen, ya yi shirinsa tsab na tafiya, sai tashin kamshi yake yi, ya saki wannan dark black curly hair nan nasa bai ɗaure ba, wannan guntu na gaban yana nan shima, sanye yake da wando jeans mai bala'in kyau Black colar sai high neck t-shirt fari tas, ya yi wa kayan kyau sosai da sosai, kamar kullum fuskarsa sanye da face mask black color kyawawan fararen kafafunsa na sanye da black sos cikin white Boot mai bala'in kyau da tsada, a takaice dai yau wankan Black and white ya yi, tsabar kyau kamar shi ya yi kansa.

Baki ɗauke da excuse Micheal ya shigo cikin ɗakin, ta cikin mirror gabansa ya kare mashi kallo, shima dai Michael ɗin kallonsa yake yi, ganin haka yasa Lion ya juyo suna kallon juna da kyau, ya zubawa Michael wayan nan rikitattun idanun nasa masu rikitar da ƙwaƙwalwar wadda ya kalla, ya rasa natsuwarsa, sosai yake kare mashi kallo kamar mai tuhumar shi, cikin sauri Michael ya kariso Wajen ya rungume shi yana sauƙe nauyayyar ajiyar, hannu bibbiyu Lion yasa ya riƙe shi da kyau yana mai jin matukar kaunar Triplets nasa a cikin ransa. Wani nishaɗi na musamman suke ji dukkansu biyu. Allah sarki jini ba wasa ba, dole ku ji daɗi.

Sun ɗan jima a haka ba wanda ya ce da ɗan uwansa kala, daga bisani suka raba jikinsu, Michael ya koma bakin gado ya zauna yana faɗin "My Lion please i need money" a cikin natsuwa Lion ya tako zuwa wajen bedside drawer ya sanya hannunsa ya buɗe drawer ya ɗauki sarkar nan da ya ajiye mashi ya miƙa mashi, karɓa Michael ɗin ya yi tare da sanya a wuyarsa ba tare da ya tambaya daga ina ta fito ba.

Sake turo ɗan bakin nan nasa ya yi murya a shagwaɓe ya ce "Lion please money" Shiru kamar kurma haka Lion ya yi mashi, daga karshe ya ɗauki wayarsa da laptop ya nufi waje, cikin sauri Michael ya miƙe zai bi bayansa, bai kai ga fita ba ya ji alert wadda ko bai duba ba yasan kuɗin da ya buƙata ne Lion ya tura mashi, wani daɗi ya ji, cike da murna ya fara ayyana irin business ɗin da zai buɗewa Aryan da kuɗin a cikin zuciyarsa.

Shi kuma Lion kai tsaye palon kasa ya nufa, wani irin taku yake yi wadda duk in ya taka kasa sai dark black curlysa nan ya girgiza, ya watse daga bisani kuma ya sake haɗewa, kai ka ce hura gashin iska ake yi, amma ko ɗaya kawai dai yana yin tafiyar da yake yi ne, da alama yana sauri sosai, babu kowa a palon kasan sai wayan nan jibga-jibgan bodyguards ɗin da suke a wajen dining table, su daddy a lokacin duk suna ɗakin su, basu kai ga fitowa yin breakfast ba tukunnan.

Kai tsaye wata kofa dake ta kusa da Kitchen ya nufa a maimakon kofar fita palon, yana buɗe kofar ta sada shi da wajen dawakansa, ta nan ya ratsa izuwa wani ɓangare daga ta cikin gidan, tafiya kaɗan ya yi ya shiga ta lambun daddy ya fito ta kofar sirri dake a wajen, yana fita gidan Tga da Tyrone suna tsaye da mota a wajen sun gama shirya mashi gaba ɗaya kayan sawarsa dama tun jiya da daddare a cikin bayan motar, yana fitowa ba ɓata lokaci Tyrone ya buɗe mashi gidan gaba na motar ya shiga suka bar wajen, kai tsaye airport su nufa.

Ko da suka je airport ɗin bai fito daga motar ba sai da ya sanya wata dankareriyar long coat mai bala'in kyau da tsada Black colar a jikinsa, coat ɗin ta haɗu sosai, a iya gwuiwa ta tsaya mashi, wani rawani irin nasu na turawa ya ɗauko mai jikin mage ya ɗaura a wuyarsa saboda sanyi da ake yi, cikin wannan natsuwa tasa da class ɗin ya fito, already su Tga sun gama shirya mashi komai, a Airport ɗin ba kowa ne ya iya gane shi ba, kai tsaye cikin jet nasa ya je ya shiga, ba ɓata lokaci suka daga suka lula sararin samani. Sai da su Tga suka ga tashin shi sannan suka shiga mota suka juya zuwa gida, sai tunanin yadda za su kare da Brady Tga ya ke yi, dan karen baya yarda da kowa sai Lion, idan ya ga Lion baya nan ne sai kaga ya ɗan saki jiki da Michael, tunani cike fal ransu suka koma gida.

Nikuma na haɗa kayana zuwa Gida NIGERIA kasarmu da gado.

Misalin karfe 6:40 Imran ya shigo ɗakin Rimsha bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya iskota ita da Akila suna shirin zuwa garden dan su kaiwa Akil haddarsu ya kara masu wani, yau bai dawo gidan da wuri bane shiyasa ba su fara karatu da wuri ba.

"Rimaha ki kawo wa Saif ruwa mai sanyi da maltina, ya yi azumi kuma lokacin shan ruwa ya yi, mai sanyi sosai za ki kawo mashi kin ji? Yana ɗaki na" gyaɗa mashi kai ta yi alamar
Showing 162001 words to 165000 words out of 344390 words