na sha wahala fiye da tunanin mai tunani, shekarata kusan huɗu a can, babu kalar azabar da ban gani ba, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, a gaban ido na ake kwakwalewa yara ido, a yanke wa mata nono da gaban su, baba da kuke ganin nan, shekaran sa zai kai talatin a Daular Mutuwa, su Mustapha kuma a gabana aka kawo su, ba zan iya misalta muku wahalar rayuwa da na sha ba, don ya wuce misali, sannan har yau da nake yi muku magana ban sake jin ɗuriyar wani da na sani ba, ban sani ba mamana tana raye ko ta mutu, duka ban sani ba!" Ta kai karshen maganar tare da kara sautin kukan da take.

Duk falon ba wanda bai yi wa Ayla kuka ba, musamman Rimsha ta fi kowa kuka a cikinsu, sai jan hanci Iya take.

Haɗuwa suka yi, suna hawaye suna rarrashin Ayla, da kyar suka samu ta yi shiru, hakuri iya ta ba ta tare da yi musu alkawarin baban Kausar na dawowa za ta karɓa musu kuɗi a wajensa, ta je da kanta ta sanya su a mota su koma wajen iyayensu, sosai suka ji daɗi tare da zuba mata ruwan godiya.

After some minutes👌

Falon ya yi shiru, miƙewa Iya ta yi ta nufi kitchen, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta tana faɗin, "Ina son in koyi girki Iya." Miƙe kafafu Kausar ta yi ta gyara ta kwanta saman sofa tana faɗin, "Ba sai ki koya ba, ni me ruwana, abin da na sani dai shi ne a girka a ba ni na ci kawai na sani, ni ce ƴar auta a gidan nan, kuma ni kaɗai ce mace dole ba zan yi aikin komai ba, sai dai su boda Wasiu." Ita dai Ayla shiru ta yi tana son koyon girki ita ma, amma ba yau ba, don yau ta tuna da rayuwarta ta baya, duk jikinta a mace ba za ta iya ko motsa jikinta sosai ba.

Ita kam Rismha zagewa ta yi Iya na nuna mata yadda ake girki tana koya, don tun asalinta da ma tana da sha'awar koyon girki, shi yasa ko lokacin da suke gida tare da daddy tana yawan shiga kitchen wajen masu aiki ta tsaya tana ganin yadda suke aiki, saɓanin Jehan da ko hanyar kitchen ba ta bi bare ma ta shiga, ko abu take buƙata a Kitchen sai dai ta sanya masu aiki su ɗauko mata.

Kwanciya ita ma Ayla ta yi saman sofa ta rintse ido tana jin kanta na sara mata a hankali saboda kukan da ta sha, da haka har barci ya ɗauke ta. Ita kuma Kausar ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya daga kwance, ta kafe TV da idon tana kallo,
Rimsha na Kitchen abinta tana koyon aiki tare da Iya.

Ni kuma na tattara kaya na, na wuce Kd don na je na ga wani hali Aunty take ciki?

💞💞KADUNA💞💞

Cike da tsananin tashin hankali Aafia ta figi mota zuwa asibiti, gudu take shararawa a kan titin nan kamar ba gobe, ga shi kuma dare ne, don lokaci karfe takwas da rabi za ta yi

Allah ya tsare, Allah ya kai su asibiti lafiya ba tare da wata matsala ba, tana shiga kuma ta yi sa'a likitoci suka karɓi Aunty hannu bibbiyu, suka shiga da ita A&E (Accident and Emergency) ke nan, sai kai komo Aafia take a bakin kofar, tana ta faman share zufar wahala da ke ta karyo mata ta gefe da gefen kunnenta, sai haki take kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, gabaɗaya ta rasa sukuninta, ta yi da-na-sani har ta gaji.

A can gida kuma, Abbi da daddy su ma suna can cikin bedroom nasu, ransu na musu barazanar fita daga jikkunansu, sai fafutuka wajen neman ceton rayukan nasu suke, lokacin guda suka zazzage suka yi wata uwar rama kamar wadanda suka jima cikin ciwo, da ma shi Daddy Jelly akwai shi da dara-daran ido kamar na Jellynsa, ramar da suka yi ya sanya idanun nasa kara fitowa sosai abin gwanin ban tausayi.

A takaice dai daddy da Abbi zaune suka kwana, sun daina iya tafiya da kafafunsu, karfinsu duk ya kare, tun suna iya shiga bandaki da kafarsu, har suka dawo shiga da rarrafe, daga karshen a kasa wajen bakin gadajensu suka zube kan gwiwowinsu, suka kwantar da kansu a jikin gadon barcin wahala ya ɗauke su, ba su san abin da ke faruwa a cikin gida ba.

Ita ma Aafia kusan a tsaye ta kwana, don ba su ba ta damar ganin Aunty ba, ita kuma ba ta dawo gida ba, a kujerar da ke bakin kofar wajen ta zauna, idan ta jima ta jima sai ta tashi ta fara zarya a wajen tana tunanin ya su Abbi suke? Idan ta gaji da zaryar sai ta koma ta zauna, haka har dare ya tsala, a zaune saman kujerar wajen barcin wahala ya ɗauke ta.

A ɓangaren Umaisha kuma, kuka take sosai lokacin da Akil ya fita, bai kula ta ba yana jiyo kukan nata, amma yayi buris saboda ta raina shi sai wani cika yake yana batsewa, fuuu ya fice kamar wata guguwa.

Ya je ya shiga motarsa da niyyar ya tafi, sai kuma ya kasa kunna motar, a zahirin gaskiya har cikin dodon kunnensa, yake jiyo sautin kukan nata, ya kasa kunna motar tasa, har cikin ransa yake jin zafin kukan da take, sai dai kuma idan ya tuna cewa ta raina shi, sai ya ji ba zai iya komawa ya rarrashe ta ba, kuma ya kasa tafiya, don yana ji a jikinsa ba zai iya tafiya ya bar ta tana kukan nan ba, zuciyarsa ba zacta juri hakan ba. Shiru ya yi ya kasa gaba ya kasa baya, ya jingina kansa da jikin kofar motar yana tunanin ya zai yi?

Daga karshe dai ya yanke shawarar komawa don ya kasa tafiya, buɗe motar ya yi ya fito ya koma cikin gida.

Yadda ya bar ta tana zaune tana kuka, haka ya dawo ya same ta, kusa da ita ya zauna tare da ɗan rungumo ta a jikinsa yana faɗin "Is okey!" Kankame sa ta yi ta ci gaba da kukanta, hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta, "Ya isa haka kukan nan kin ji?" Shigewa cikin kirjinsa da kyau ta yi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya, ta daina kukan nata, shiru suka yi yana ɗan shafa bayanta a hankali, ya jingina kansa da jikin kayin gadon yana sauke numfashin a hankali, yana jin matukar son ta na kara ratsawa har cikin kwakwalwar kansa.

A ɓangaren Jelly kuwa, sosai Nawid ya ke tunanin yadda zai yi da ita, don a zahirin gaskiya ba zai iya auren Jelly ba, kwata-kwata babu son ta ko kaɗan a ran shi, Jehan yake so, ita kaɗai, bai taɓa jin son wata mace a ransa ba sai Jehan, yana ji a jikinsa cewa, ba zai iya rayuwa da ko wace mace ba bayan ita, har ƴar rama ya yi saboda tunanin mafita.

Gefen shi kuma Abbo tunanin yadda zai ɓullo wa lamarin Jelly yake, don a gaskiya ba zai iya haƙura da ita ba, yana bala'i son ta bai san ya zai yi da rayuwarsa ba.

Kamar kullun suna zaune saman table ɗin cin abinci, suna cin abinci dare, Nawid, Ummi, Jelly da kuma Abbo, Ummi sai faman cin abincinta take cikin kwanciyar hankali, tana farin ciki Nawid nata ɗa ɗaya tilo zai yi aure, kuma zai auri yarinyar da take bala'i so bayan shi, wato baby.

Ita kuma Jelly tana zaune tana ta yagar cinyar kaza hankalinta kwance, ba ta san me duniya take ciki ba, ba ta san abin da ake shirya mata ba, kun san dai Jelly da masifar kaunar nama, idan tana cin naman nan ba ta ji ba kuma ta gani, gabaɗaya barin duniyar mutane take, ko magana kake mata, ba ta amsawa matukar tana gaban nama. Hmm su Jelly manya.

"Abbon Nawid da ma ina son mu yi magana a kan auren baby da Nawid." Wani irin dum-dum gaban Nawid ya ba da duka, shi kansa Abbo dukan uku-uku jirginsa ya yi, har wani irin duhu ya gani ya gilma masa ta gaban idonsa, lokaci guda ya rasa nutsuwarsa, sai wani ƴan kame-kame ya fara yi kamar wani marar gaskiya

"Abbon Nawid lafiya na ga yanayinka ya canza cikin kankanin lokaci haka?" Cewar Ummi, ta yi maganar cikin kwanciyar hankali, shi ma Nawid ba karamin mamakin ganin Abbonsa ya shiga yanayi marar kyau ya yi ba. Da kyar Abbo ya iya sai ta nutsuwarsa ya ce, "Ina fa lafiya, ai ba lafiya, dole ki ga damuwa a tattare da ni." Zaro ido Ummi ta yi yayin da shi ma Nawid ya bude kunnuwansa yana jiran ya ji me Abbo zai ce? Sai addu'a yake Allah Ya sa Abbo ya ce, wannan haɗin da za a masa shi da jelly, ba ba ya so, bai yarda ba.

Cike da tashin hankali Ummi ta ce "Abbon Nawid ka mini bayani mene ne matsalar?" Ta yi maganar tana kara zaro ido cike da tashin hankali, dogon numfashi Abbo ya ja tare da sauƙewa a hankali kafin ya ce, "Ba na son wannan haɗi na Nawid da wannan yarinya baby?" Wani sanyi Nawid ya ji ya ratsa masa daga tafin kafar sa har izuwa tsakiyar kansa, wani murmushi siririn ne ya bayyana a fuskarsa.

A ɓangaren Ummi kuwa ƙara zaro ido waje ta yi ta ce, "Abbo mene ne ya sa ba ka son haɗin?" A takaice ya ce, "Saboda tsintaciyar mage ce, ba mu san asalinta ba."



_Ni ma na tattare kayana na yi nan wannan dirama ba a nan ba._

Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
[11/11, 8:52 PM] +234 906 579 6460: 💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 15-16🌹🌹


After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma Michael, ya samu sauƙin ciwukan da ya ji a sanadiyar accident ɗin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura ba ta warke ba.

Yau tun safe sosai helicopters ke shawagi a sararin samaniya, daga cikin Washington DC zuwa wajenta, kamar masu duba wani abin. Tun da daddy ya ji shawaginsu ya yi yawa ya san Romeo zai bar kasar ke nan, don da ma in dai ba fitar sirri zai yi ba kafin ya fita kasar sai an tashi helicopters sun yi ta kewaye cikin Washington DC, don tabbatar da tsaro, sai sun duba ko'ina. Idan sun tabbatar normal sannan private jet ɗin Romeo ya ɗaga, amma kafin ya ɗaga sai manya-manyan jiragen sojoji na kota-kwana biyu sun yi gaba, sannan nasa jet ɗin ya bi bayansu, sai wasu jiragen biyu su saka jet ɗinsa a tsakiya sai jirgin yaki ɗaya a bayan jet ɗin, don tabbatar da sun ba wa The General Of The Army kuma jika ga His excellency tsaro mai kyau, don ran Romeo daidai yake da ran zaratan sojoji 100 a cewarsu, don za a tara sojoji 100 ba za su iya aikin da shi kaɗai yake yi ba, kasancewar shi ba komai yake saka wa karfin dantse ba, akwai shi da aiki da kwakwalwa kamar agogo, manyan kasashe na duniya idan abin ya shige musu duhu sai sun nemi taimako daga wajensa, sannan kuma His Excellency yana bala'in kaunar sa fiye da tunanin mai tunani, duk cikin jikokinsa ya fi son lion, daga shi sai Michael yana matukar son su sosai. Ran Romeo babban abu ne mai matukar mahimmanci ba ga iya USA ba, har wajenta. Matukar Romeo zai fita Washington DC to fa sai an bincike ko'ina, har kasar da zai je, kafin ya dira cikin kasar sai helicopters sun tashi a cikin kasar ma, sun duba ko'ina da kyau.

Cikin taku irin na jaruman maza masu jini a jika, ya fito daga ɓangarensa, jikinsa na sanye da blue jeans mai bala'in kyau, sai Round neck T-shirt black color mai ratsin blue, a saman kayan nasa ya ɗora wannan jacket ɗin nasu, wato Puffer Jacket, ita ma black color, kalar rigarsa, kyawawan fararen kafafunsa na sanye da Hermes Birkenstock sandal, hannayensa na sanye cikin hand gloves baka, yayin da fuskarsa ke sanye da face mask baki, ya ɗaure dark black curly hair sa nan a baya, ya bar na gaban goshin kamar kullun. A yau fusatacciyar fuskar nan tasa ta fi ta koyaushe razana mai rai, domin yau fuskar tasa a ɗaure take tamau kamar wani hadari, har wani siraran jijiyo ne suka bayyana masa a goshinsa saboda ɗaure fuska sosai da ya yi, girarsa sun haɗe waje guda, saboda ɗaure fuska da ya yi, da ma gashin girar nasa ya kusa haɗewa saboda yawa, shi yasa da ya ɗaure fuska sai girar tasa ta haɗe, kwarjininsa ya kara bayyana sosai, tamkar wani zakin da ya yi shekara babu abinci, kallo ɗaya za ka masa ka san yau a fusace ya ke ainun.

Yana sako kafarsa ta saman benen zai sauƙo kasa, shi ma Musharraf yana sako tasa kafar zai hauro, bawan Allah bai san da cewa idan lion na saman staircase to ba wanda ya isa ya hau ba, har sai ya sauka, shi bai ma san waye lion ɗin ba, sunansa kawai yake ji.

Ga shi yau ran lion a matukar ɓace yake, don shi kaɗai ma sai wani huci yake, kamar ba lafiya ba, yana tafiya yana wani bubbuɗe kirjinsa, da ma kuma ga kirjin nasa a bubbuɗe.

A daidai tsakiyar staircase ɗin suka yi karo da Musharraf yana ɗan jan kafar sa a hankali yana ɗingisawa.

Wani mahaukacin mari lion ya sauƙe wa Musharraf a fuskarsa, wadda ya sanya shi yanke jiki ya zube kasa sumamme, kasancewar bene ne, hakan yasa ya gangara a sume ya sauka kasa, tsallakawa ta kansa lion ya yi, ya nufi hanyar fita daga cikin falon, don ma yana sauri ne shi yasa ya yi wa Musharraf mari ɗaya ya wuce.

"My lion where are you going?" Cewar daddy da ya fito daga ɗakin magungunansa da yake kasan benen, a hankali lion ya juyo da kallon sa kan daddy. Ganin fusatacciyar fuskarsa ba karamin razana daddy ya yi ba, ya sha jinin jikinsa don ya san halin ɗan nasa, kun san halin daddy da saurin birkicewa nan take ya ruɗe ya fara haɗa wa lion words yana in-ina. "My lion what is going on? What is happening? What is wrong with you?". Sai jero tambaya yake yi yana haɗe words, kuma ya yi maganar cike da tashin hankali.

Furzar da iska mai matikar zafi daga bakinsa lion ya yi, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakinsa ya ce, "Zan je Spain ne dad, I need your prayer." Yana kai karshen maganar bai tsaya ya jira amsar da dad zai ba shi ba ya fice da sauri, don ba abin da zai hana shi dira cikin Spain yau, kuma bai son ganin tashin hankali da dad zai shiga, don ya san ba karamin tashin hankali zai shiga ba, ya san halinsa sarai, musamman ma Michael ba ya nan James ba ya nan, halin da zai shiga ba zai yi kyan gani ba, kuma ba tafiyar sirri zai yi ba ya zama dole daddy ya sani, ko bai faɗa masa ba, dole zai sani ko don jiragen dake shawagi a sama, shi yasa ma bai ɓoye masa ba, ya sanar da shi ga in da zai je kawai.

Yana fita daga falon ya nufi jerin gwanon motocinsa dake jere kamar kullun suna jiran tafiya kawai. Gidan nasu yau ya cika da zaratan sojoji sosai ta ko'ina, saboda sun san da tafiyar tasa, gabaɗaya sun jeru layi kamar wadanda za su tafi fareti, tun daga farkon kofar falon har zuwa, babban gate na gidan, Jibga-jibgan zaratan sojoji ne. Tun da ya fito suke ta faman ɗaga hannu suna sara masa tare da buga kafafunsu ɗaya a kasa.

Ko kallon in da suke bai yi ba, ya wuce ya nufi motoncin nasu, yau saɓanin kullun ne, don an kara yawan motoncin nasu, saboda kowa ya san da tafiyar tasa, don karin tsaro zuwa airport, shi yasa aka karo manya-manyan motocin sojoji masu numfashi.

Motarsa da ya saba shiga nan wannan Baturen ya buɗe masa kofar motar, ya shiga ya zauna. Yana zama Tga ya fito hannunsa riƙe da system da wayar lion, shi ma Tga yau sanye yake cikin kaki. Zuwa ya yi, ya miƙa wa lion system ɗin sannan ya ɗaga hannu ɗaya ya sara masa, karɓar system da wayar kawai lion ya yi ba tare da ya kalli Tga ɗin ba.

Runtse dara-daran idanunsa ya yi, har cikin ransa yake jiyo sautin kukan Brady, don yasa su Tga sun kulle Brady a ɗaki, saboda ba zai tafi da shi ba, kun san Turawa yadda suke da dabbobinsu, lion ya fi jin zafin rabuwa da Brady a kan su Tga, har ga Allah yana jin ciwon kukan da Brady ke yi, shi ma kuma Brady sai haushi yake dakawa da karfi, don Romeo ya ji shi ya dawo ya ɗauke shi, amma ina Romeo na jin shi, sai dai ba zai yiwu ya tafi da shi ba ne kawai.

Zuba masa ido sojan da zai tuka motarsa ya yi wato direbansa na yanzu tun da ya tura Tyrone gadon asibiti, da ma Tyrone shi ne asalin direbnsa, Tga kuma na hannun damarsa, kuma uncle nasa, ɗan autansu daddy. To har yanzu Tyrone na asibiti tun dukan da ya masa a kan watch.

Yau tun daga cikin gida suka saki jiniya mai tashin kai, tamkar fillin daga za su tafi, jiniyar yau ma ta daban suka saki, wadda da ka ji ka san manya-manyan jiga-jigan kasar ne za su fita.

Da gudun gaske motoncin suka tashi, don sun saka alamar danja a gaban motoncinsu, duk da cewa ko ba su saka alamar danja ba ma, babu wani abin hawa da ke hawa titin da suke kai har sai sun wuce, to amma yau da yake za su yi gudun wuce ka'ida sai suka sanya alamar danja don bin doka, kada su zama suna matsayin masu doka kuma suna karya doka da kansu.

Tun kafin su iso bakin gate security sun wangale musu katafaren gate ɗin gidan, a guje suka danna hancin
Showing 36001 words to 39000 words out of 344390 words