koma Nigeria dan muga wani lamari ne ke gudana

💓💓KATSINA STATE 💓💓

Bayan tafiyar Yarima shima Nawid ya wuce ɗakin ɗaya da ya sauka a cikin Hotel ɗin.

Da shigarsa ɗakin bai yi minti 20 ba ya kira Ibraheem a waya a kan ya turo masa Jehan yana da aiki da zai bata, cikin hanzari Ibraheem ya yi maza ya isar mata da saƙon Nawid, da farko ta ce ba zata je ba, amma daga baya da ta tuna cewa Nawid ya mata rana yau, ya ceceta daga hannun yarima, sai ta hakura ta nufi ɗakin nasa.

Jehan mutunce wadda bata manta alkhari komai kankantarsa, in dai ka taɓa mata wlh ba zata taɓa mancewa da kai ba, ko da ka mata sharri daga bayan wannan Alkhari, to zata rinƙa ganin kane da wannan Alkharin, haka zalika bata manta sharrin idan ka mata, komai Alkharin da za ka mata bayan wannan sharri tofa in dai sharrin ka fara yi mata shi zata riƙe.

A bakin kofar ɗakin nasa ta tsaya ta kwankwatsa masa, kamar jiranta yake yi dama, cikin sauri ya buɗe kofar. Fuskar sa ɗauke da kayatatcen murmushi ya ce "Sannu ki" ɗaure fuska sosai ta yi kamar wadda aka aikowa da mutuwa, wani irin faɗuwar gaba Nawid ya ji lokacin da ya ga yadda ta ɗaure fuskar tata.

"An ce kana nema na lafiya?" Shine abin da ta ce masa, wani wahalallen yawu ya haɗiye kafin ya ce "To malama da farko dai sunana Nawid kuma Ni..." Bata bari ya kai karshen maganar ba ta ɗaga masa hannu alamar bata son jin maganar tasa, shiru ya yi ya zuba mata ido.

A yatsene ta ce "An ce kana nema na me kake buƙata, oder me zaka bada?" Ta yi maganar a nitse cikin kwanciyar hankali, da kallo ɗaya zaka mata kasan izza ya samu mazauni a tattare da ita, gata kuma kaifi ɗaya ce, bata magana ta sauya ko me za a yi mata, idan tana magana ɗai ɗai take yin shi, kuma a nitse take, ba ta haɗa ɗaya da ɗaya.

Kakalo murmushin dole ya yi, dan harga Allah bai ji daɗin yadda ta tarbe shi ba, duk da cewa izzarta yasa ya kamu da son ta, amma da ta yi masa shi, bai ji daɗi ba.

"Malama ki bari mana na faɗa miki sunana tukunnan ko?" Kawar da kanta gefe ta yi kafin ta ce "Sunan ka baya cikin jadawalin tsarin aikina, so please ina ganin girmanka, ka kama kanka, just tell me what you want direct kawai dan ina da abin yi" Ta yi maganar tata cikin harshen turanci, dan har yanzu hausa bai zauna a bakin ta ba,

Sosai ya yi mamakin jin yadda take rero turancin nan kamar dan bakin ta a ka yi yaren.

Wow ya furta a ransa, a fili kuma daurewa ya yi ya ce "To shikenan tun da baki bukatar jin sunana bari na gaya miki me yasa na kiraki" kara ɗaure fuska ta yi ba tare da ta yi magana ba, kuma bata kalli in da yake ba.

"A gaskiya malama ba zan ɓoye miki na cuci kai na ba, ke ɗin kyakyawa ce ajin farko, kuma na kamu da matukar kaunar ki da kallo farko" ko aji kin ta, bata yi wani alama da zai nuna cewa ta ji wani abu ko wani mamaki da jin zancen sa ba.

"Malam ba mu sayar da kyau da kuma Kauna a wannan restaurant ɗin nan, daga shinkafa da miyar steew, sai jolof da su tuwon semo, pepper chicken, pizza, burger, shawarma, da dai sauran kananan kayan cima, amma gaba ɗaya cikin jadawalin girke-girken mu babu me ma kace sunan abin cin? Yauwa kyau da kuma Kauna ko? To su dai babu su".

Tofa, Babbar magana me Jehan ke nufi kenan?🤔

Mutuwar tsaye Nawid ya yi tare da kara zaro idonsa yana kallon ta da kyau.

"A iya sani na ko yan kauye sun san menene so da kuma Kauna, sun san menene kyau, in fact sun san menene aure, amma yarinya santaleliya kamar Jehan gata kalar wayayyu yan gayu, ga iya zuba turanci, amma ta ce ba ta san soyayya ba, anya ba raina min wayo ta yi ba kuwa?" Sai zancen zuci yake.

Zazzakar muryar ta ne ta katse masa zancen zuci nasa da cewa "In kawo maka shinkafa irin ta ɗazun ne? Ko dai na yi tafiya ta?" Kara mamaki ya yi sosai

"Wai shin da gaske Jehan ta ke yi ba ta san menene soyayya ba ne?" Ya sake tambayar kansa da kansa, tambayar kuma da ba shi da amsarta, domin Jehan ita kaɗai keda amsar, kuma bai ga ala'mar fuskar da zai samu damar tambayarta ba.

Ya yi nisa cikin tunani, sai ganinta ya yi ta sa kai zata wuce ta bar wajen, cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya sha gaban ta yana faɗin

"Haba Malama, ya isa haka zolayar mana please" karo na farko da ta ɗaura idon ta cikin na shi, taɓe baki ta yi, alamar mamaki ma ya bata,

"let me pass" shine abin da ta ce masa,

Kin matsa mata ya yi, sai ma kara matsowa kusa da ita da ya yi, ya kara kashe murya kasa kasa, irin salon jan hankalin nan ya ce

"Haba Malama, ni nasan ba halinki bane saboda ba ki yi kalar wulakanta mutane ba, sannan kuma daga ganinki kin san me nake nufi, kuma kin fahimci ina na dosa, wlh ba son wasa na ke miki ba, har ga Allah nake son ki, kuma aurenki zan yi, ba da wasa nazo ba"

tamkar da dutse yake magana haka Jehan ta masa shiru kamar bata a wajen, sai surutu yake zubawa ko uppan bata sake ce mi shi ba, kuma idan baku mance ba Jehan bata da yawan magana bata shiga harkar kowa.

Sun jima tsaye a wajen, bata sake magana ba. Da ta ga ji da jin surutan shi sai ta ce

"Malam ina son wucewa"

mamaki ne ya kama shi kenan yanzu duk wayan nan kalaman soyayya da ya zuba mata bata san su bane ko menene.

A zahirin gaskiya Jehan bata gane kalamansa ba, ta dai san soyayya da kaunar bayan haka duk kalaman da ya mata ba abin da ta fahimta, domin da hausa ya yi su, ita kuma kunsan ba jin hausa sosai take ba,.

Bawan Allah ya zage sai zuba kalamai yake yi ashe duk a banza ya yi su. Kuma sanin soyayya da Jehan ta yi bawai ta san yadda ake yi bane, a'a kawai dai sunan ta sani, dan ita bata kallon finafinai ma bare a ce zata kalli soyayya a wajen, bugu da kari bata da kawaye ko makamancin su, ba wani abin da ta sani game da soyayya bayan sunan shi soyayya.

Ganin Nawid ya yi mutuwar tsaye yana tunani ne yasa ta raɓa gefensa zata wuce, cikin sauri ya riƙo hannunta yana faɗin

"Haba malama kada ki min haka, wlh soyayyarki zata iya yi mini illar ki tausaya min, sosai kika mamaye zuciyata, ta ko ina, har ina ji a jikina ba zan iya rayuwa ba sai da ke, kada ki ce ba zaki karɓeni ba..."

Ji kake tass ta wake masa fuska da wani gigitacen mari ba tare da ya gama kalameta da yake yi ba, a fusace ta kwace hannun ta daga riƙon da ya mata, rai a matukar ɓace ta bar wajen ta bare da ta yi magana ba.

Shiru ya dafe kumatunsa, ya kasa yi mata magana, kuma ya kasa dakatar da ita har ta tafi, ko kaɗan bai ji zafin marin da ta masa ba, sai ma son ta da ya karu masa sosai a zuciyar.

(Umm giyar soyayya ba🤣)

A gaskiya zuciyarsa ma kara yaba mata yake yi ta yi namijin kokarin, hakan kuma ya kara burgeshi, yanzu ya dace ya kara ɗaura ɗamarar neman aurenta, a cewar sa, domin ita ce matar aure, mace mai kare mutumcin kanta wadda ko hannunta bata yarda wani namijin ya taɓa ba.
Sosai Nawid ya sa a ransa dole ya nemi auren Jehan kuma ya zama masa dole ya nemi soyayyarta, ita ta dace da rayuwarsa.

(Tirkashi aikuwa ka haɗa hanya da wahala)

Jiki ba kwari, tunani cike fal a ransa, ya wuce ya koma cikin ɗakinsa. Yana shiga ya tsaya a gaban mirror ɗakin tare da shafo in da ta maresa da hannunsa ya mannawa hannun nasa kiss, har da wani lumshe ido, shi a dole izzar Jehan da kuma kamewarta sun tafi da imaninsa. Shi ga shi ɗan soyayya.

( Soyayya manya.)

Ya ɗan jima tsaye a wajen, kafin ya fara haɗa kayansa dan ya koma Kaduna ya sanar da Ummi abin da ke ransa.

Ita kuma Jehan tana koma, kai tsaye cikin office ɗin Ibraheem ta nufa, yana ganin ta tun daga nesa ya zuba mata ido yana jiran ya ji wani bala'i zata sauƙe masa kuma.

(Ibraheem na cikin gararin da bala'i Jehan🤣 bawan Allah)

"Ibraheem!! Ibraheem!! Ibraheem!! Sau nawa na kira sunan ka?" Shine abin da Jehan ta faɗa lokacin da ta iso wajen, shiru ya zuba mata ido yana kallon ta.

Rai a matukar ɓace ta ce "Na ce ka kiramin ogan ka a waya ya zo nan ina son yin magana da shi"

"Ki yi hakuri zai zo ranar Jumma'a sai ku yi magana" Ibraheem na gama kai karshen maganar ta wuce ta koma bakin aiki ta, tana tunanin idan ogan su ya zo, ya zama mata dole ta faɗa masa, ba ɗakin kato da zata sake zuwa, domin ita ba yar iska ba ce.

Shi dai Ibraheem ido kawai ya bita da shi, dan yanzu shi burinsa ya lallaɓata ta samu ta yi aiki ta biya shi kuɗin sa, shiyasa baya wani biye mata, dan in ta ce ba za ta yi aikin ba, waye zai biya shi kuɗin sa, dan dai yasan gidan su Jehan ba ta in da za'a fitar da dubu ɗari biyar, kuma ko ƙararta ya kai ba ta in da za su iya biyan kuɗin, sai dai ma shi ya sake kashe wa su kuɗaɗen wajen biyan yan sanda da sauransu..

Tofa Jehan yau ake yin ta, ni na haɗa kayana nayi gaba sai mun haɗu da ku a gidan su Aafia gobe idan mai dukka ya kai mu
[11/17, 12:27 PM] +234 906 579 6460: 💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 21-22🌹


Su kuwa ba su kawo cewa Kausar zata musu laɓe ba dan hakan yasa suka saki jiki wajen yin hirar su, a hakan ma kasa kasa suka yi dan kada wani ya jiyosu. Allah sarki bayin Allah Allah dai ya fitar da ku daga cikin wannan ukubar rayuwa.

Bari mu leƙo Daular mutuwa mu dawo.

☠️☠️Ɗaular Mutuwa☠️☠️

Guguwa ne mai karfin gaske ta kewaye ko ina, wani masifaffen duhune ya lulluɓe gidan gaba ɗaya, daga cikin guguwar wasu sautika ne ke tashi kala-kala na muryoyin sheɗanun aljanu daban-daban, masu magana da yaren da ɗan adam baya ji, idan ba kana da karfin imani ba baka iya zama a wajen, gaba ɗaya gidan ansawa yake yana bada wani irin amo mai sautin gaske, gaba ɗaya wayan da ke cikin gidan, kowa ya yi ta kan shi, ma'ana sun shige cikin ɗakunan su.

Wannan nasifaffen guguwa ya jima yana yi kafin haske ya karaɗe gidan, amma ita guguwar bata dakataba. Gingima-gingiman jiga-jigan matsafane suka fara fitowa ta sassa daban-daban daga cikin gidan, munin halittar su ma kawai ya isa ya sa ɗan Adam suma. Gaba ɗaya matsafa dake gidan sai da suka fito yau, sun jeru layi a cikin part ɗin su Baba da Mustapha, duk girma irin na part ɗin nan sai da suka cika shi tab da yawansu, dan suna da yawa sosai ba wasa ba, munanane gaba ɗayan su, basu da kyan gani ko kaɗan, tsayawa zayyana muku bala'i munin su ma ba zai yi wu ba, domin zai cinyemin ɗan fillin dake gareni, dan haka ku ayyana su a ranku kawai, suna da kattin kai da katon hancin ga idon nan nasu jawur kamar jini, kamar kuma zai faɗo kasa saboda girma.

Sun tsaitsaya kamar wasu gumaka, numfashinsu kamar na saniya, sai dai a cikin su babu duna, baya wajen. Ko ina suka kai shi oho.

Daga ta bayan su wani sauti mai bala'i karfi ya fara fitowa, ji kake dip-dip-dip, ƙasa na amsawa, wannan sauti kuma ba komai bane face sautin takun Queen oga kwata-kwata kenan.

Wannan sauti ya ɗan jima yana yi, alamar daga nesa take kenan, sautin na kara matsowa alamar tana tunkaro wajen.

Lokacin da ta iso wajen, sautin ya kara karfin amon da yake yi ne sosai, gaban su tazo ta tsaya.

Kai-kai-kai, ya subhanallah, Queen mummuna ce ajin farko, tana da tsawo sosai ga kuma ƙiba, da kallo ɗaya zaka mata ka san ƙabilar Ebo ce, gaba ɗaya Daular Mutuwa mallakin kabilar Ebo ne. Queen tana da katon hanci kamar tukunya, ga hancin nata a baje a kumatunta, alamar ta kara girma shi da tsafinta, haka zalika bakinta wargajeje gari guda, sannan tana da manya-manyan hakwara guda biyu ta gaban hakwaranta na sama, wayan nan hakwaran nata guda biyu, suna da tsini kamar kifiya, sannan suna da tsawo wadda ko ta rufe baki su basa shiga cikin bakin nata saboda tsawon su, wayan nan hakwara nata masu kama da na zamisa tsab za su iya tsinke jijiya mafi karfi na jikin ɗan Adam, shiyasa ita bata yanka mutun da wuka wayan nan mayun hakwaran nata take damke makogoron mutun ta ɓalle shi ta tsinke jijiyoyin shike nan mutun ya mutu, sannan daga tsakiyar goshinta akwai wani tsagu wadda yazo mata har gemunta, ya yi kamar ya raba kanta gida biyu, ga kan nata ba'a magana girman shi ba zai faɗu a baki ba.

(Tashin hankali ke Queen naki bala'i ya wuci tunanin mai tunani😳)

Fitowar ta sai da ya sanya gaba ɗaya Daular Mutuwa ya girgiza, gaba ɗaya yan adam dake gidan sai da suka suma, baba da Mustapha ne kawai ba su suma ba, amma sun tsorata ainun suma, saboda munin Queen ba kowa zai iya ganin ta bai sume ba, idon nan nata gula-gula jawur da su kamar jini kamar zasu faɗo kasa, gashin kanta kuwa ba'a magana, idan ka gan shi kai ka ce jijiyoyin bishiyoyi ne, a tsaitsaye suke kamar ba lafiya, ga su da bala'i datti kamar me, tsayawa zayyana muku munin Queen zai cinye mana ɗan sauran filin dake gare mu, ku ayyana muninta a ran ku.

Ko da ta tsaya a gaban su, jijjiga jikinta ta yi da karfi kamar wata giwa, sannan ta waje wannan mummunar wagegen bakin nan nata wadda hayaki ke fitowa daga cikinsa, kamar an hura wuta a cikin nata. Da karfin gaske ta kurma wani mahaukacin ihu wadda bala'i sautin sa sai da ya sanya dakarun nata da kansu suka toshe kunnuwan su, ihun nata kuma ya karawa guguwan dake tashi karfin gudu, haka zalika muryoyin dake fitowa ta cikin guguwar suma sun kara sautin muryoyin nasu.

Good 2mins ta ɗauka tana kurma wannan balaƴaƴƴen ihun, kafin ta tsagaita, ta sake girgiza jikinta, gaba ɗaya dakarun nata tsugunnawa kasa suka yi a gabanta alamar girmamawa.

Cikin yaren su na matsafa ne ta basu Umarni a kan duk in da su Rimsha suke, su tabbatar sun nemo su cikin kankanin lokaci sun dawo da su sun mata ferfesun su, idan ba haka ba ransu zai yi mummunar ɓaci, domin dole ne su Rimsha su karɓi hukunci saboda sun karya mata record na gidan ta, ba'a shiga a fito da rai, su sun shiga sun fito, abin da ba'a taɓa yi ba wai ɗan adam ya shiga kuma ya fito a raye, ina sai a kan su Rimsha.

Sosai dakarun nata suka rinƙa bata hakuri tare da yi mata alkawarin ko ina su Rimsha suke sai sun dawo da su cikin gidan nan, yanzu za su fita gari, su shiga cikin al'umma, za su saje da su su nemo su. Wucewa kawai Queen ta yi bata sake yin wata magana ba, tana taku kasa na ansawa, haka ta wuce cikin fadarta, dakarun dake tsaron fadarta ne suka rufa mata baya.

Da haka taro ya watse, dakaru goma ne suka shirya suka rikiɗe zuwa siffar kyawawan matasan samari sannan suka wuce izuwa cikin gari, cikin jama'a dan neman su Rimsha.

Su kuma sauran kowa ya koma bakin aikinsa.

A cikin Daular Mutuwa dakaru basa amfani da kaya irin namu na mutane, saboda ba zai shigesu ba, wani irin tamfol suke using mai matikar karfi da tauri kamar fatar shanu, kuma basa ɗinka shi kamar yadda mutane ke yi, no ɗaɗɗaura tampol ɗin kawai suke a jikin su, sannan gaba ɗaya Daular Mutuwa iya maza ne kawai matsafar dake ciki, Queen ita kaɗai ce mace, kuma mai jagorantar su, Asali gidan na kakantane chigozie, shi ya wallafa Daular tun shekaru 40 baya, dukkansu kuma kabilar Ebo ne, sai dai basa magana da yaren Ebo a gidan, da wani yare nasu na matsafa suke amfani, sannan kuma basa da yawan magana, duk gidan duna ne kawai mai magana da mutane, su Barbushi sai dai yanka da shan jini, manya-manyan gidan matsafa daga sassa daban-daban a faɗin kasa da wajen ta suna zuwa wajen Queen domin sayan wasu sassa na jikin ɗan adam domin yin tsafinsu, shiyasa idan suka kasa shan jinin mutum sai su ajiye shi zuwa lokacin da wasu gidan matsafar zasu bukaci wani sassa daga jikinsa, sai su yanka shi su sayar, amma sai dai duk wani gidan tsafi dake son sassar jikin mutun, akwai wani waje na daban da suke haɗuwa dan yin taron, ba a cikin Daular Mutuwa wajen yake ba, yana daga gefe.

Baba da Mustapha bayin Allah, suna zaune shiru a cikin ɗakin, a cikin zuciyoyinsu suna yi wa su Rimsha addu'ar Allah yasa kada Queen ta yi nasarar gane in da suke, Allah yasa sun tsira kenan, shi baba haka kawai yake jin matukar kaunar Rimsha a cikin ransa, baya son ganin ta cikin wahala, gara masa shi ya mutu da wani abin ya same ta.

Allah sarki baba bai san cewa Rimsha jikarsa bace.

(Wayyo duna ko ya suka yi da shi oho, muje dai zuwa mu gani kila gaba mu sani, bari mu leƙo lion mu gani.)


💓💓Washington DC💓💓

Wunin yau zumbur Jay
Showing 66001 words to 69000 words out of 344390 words