ci, shiyasa Akila ta iskota bata kammala cin abincin ba.

Murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ce "Sannunki da zuwa" ɗago kai Rimsha ta yi tana kallonta, lokacin guda ta sakar mata cool murmushi har sai da hakwaranta suka bayyana, a ruɗe Akila ta ce "Wow dimple, open teeth, dogon hanci, karamin baki, kyakkyawar gashin gerar, sleeping eyes da nake mutuwar so, kyau iya kyau duk sun haɗu waje guda, ya ilahi ya lillihi ka bani yarinya mai kama da wannan baiwar taka, kyau iya kyau". Dariya abinma ya bawa Rismha, zuba mata ido Akila ta yi tana kallon yadda take dariyar abin ba'a magana gwanin birgewa.

"Gaskiya kina da kyau sosai" Akila ta sake faɗa tana karisowa wajen da take zaune, saman mirror chair, miƙewa Rimsha ta yi dan ta bata wajen zama tana faɗin "Kece Akila ko?" Da sauri Akila ta gyaɗa mata kai ala'mar sannan ta ce "Yaya Imran ya baki Labarina ko?" "E ya bani labarinki ai ya ce mini ke ce bugun Zuciyar su gaba ɗaya gidan" kara faɗaɗa murmushinta Akila ta yi sannan ta karɓi plate ɗin abincin ta ce "Mu koma tsakiyar ɗakin saman carpet muci abincin a tare" to Rimsha ta amsa mata da shi, sannan suka koma saman carpet ɗin suka fara cin abincin a tare da spoon ɗaya, wannan ta ci ta bawa wannan kamar sun jima a tare haka suka yi sabon lokaci guda.

A ɓangaren Aafia kuwa, tun da ta suma a wajen bata farka ba sai washe gari da safe da Umaisha ta zo ta tashe ta, lokacin already ta mance komai kuma lokacin da dodannin suka ɓace ta farfaɗo daga sumar sai dai kuma barci ya ɗauke ta shiyasa bata tashi ba. Wanka ta je ta yi ta shirya zuwa school, bata zo da motar ta ba kuma Akil baya nan hakan yasa ta hau abin hawa zuwa school ko breakfast bata tsaya ta yi ba domin burinta kawai su haɗu da Rufee.

Karfe 8 daidai ta shiga cikin school, kai tsaye wajen da suka saba zama ta nufa, ai kuwa a nan ta isko Rufee tana zaune ta dukar da kanta kasa. Kusa da ita ta je ta zauna tana faɗin "Good morning Rufee, where is Anisa?" Ɗago kai ta yi bakinta a kunbure saboda dukan da Akil ya yi mata jiya, ganin bakin nata a kunbure yasa Aafia ta fara bata hakuri domin ta san menene sila. B komai Rufee ta ce mata sannan ta ɗaura da cewa "Aafia ina son ki rakani wani wajen idan ba damuwa" to Aafia ta amsa mata da shi sannan suka miƙe a tare suka nufi motar Rufee ɗin.

Rufeen ta ja su suka bar school ɗin. "Ina zamu je Rufee?" Aafia ta tambaya tana ƙoƙarin sanya wayarta a silent. "Wani waje zaki raka ni, ke dai ki zuba ido ba zamu jima ba" "A'a Rufee bana son yin nisa da school dan kin ga yaya Akil ya ce zai yi bincike kuma ga yaya Irfar yana gari, ina tsoron su zo school ba su same ni ba" ta yi maganar cikin raunanniyar murya.

"Kai A'afia kin cika tsoro wlh, to ba wani jimawa za mu yi ba, minti 40 ya yi zamu dawo" Allah ya dawo da mu lafiya shine abin da Aafia ta faɗa kawai, daga nan bata sake yin magana ba.

Sun yi tafiya mai nisa ya yin da suka sauƙa daga kan titi suka keta ta cikin daji, Aafia ta fara tsorata domin bata taɓa wuce school, shopping, kasuwa, sai kuma gidan su Imran, iya in da take zuwa kenan, amma yau ga shi har cikin daji suka shiga, hakuri ta yi ta jure ta zuba ido tana kallon yadda Rufee ke keta cikin dajin da motarta.

Wajen wasu guntayen bishiyoyi masu cikar ganye ta tsaida motar, sannan ta ce Aafia ya jirata tana zuwa, to A'afia ta ce mata amma zuciyarta tsorone a cike a cikin shi fal, kijinta har kerma yake yi, dan bata taɓa zuwa makamancin waje irin wannan ba, ita kuma Rufee fita ta yi daga motar ta kama hanya.

Cikin dajin ta kuma ketawa da kafarta, tun A'afia na iya ganinta, har ta kurewa ganinta. Wajen malaminta ta je, nan ta sanar mashi da cewa tana son ya kwance aikin da ya yi wa Abbi ya mai da shi kan daddyn Jelly, sannan ta bashi hoton Akil ta ce tana son a haukata mata shi, ya shiga duniya kowa ya huta, to bokan nata ya ce sannan ya karɓi hoton ya gaya mata kuɗin da zata biya, buɗe jakarta ta yi ta zube mashi kuɗin sannan ta masa sallama ta dawo wajen A'afia.

"Rufee me kika yi a cikin wannan daji haka?" A'afia ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki ga tsoro kamar zata yi fitsari a wando, shiru Rufee ta yi mata bata tanka ta ba ta kunna mota suka kama hanya.

Suna tsaka da sharara gudu suka ga an tare hanyar da wasu duwatsu, wani irin mahaukacin burki Rufee ta ja, domin basu san da wayan nan duwatsu ba, dan a lokacin da suke zuwa babu su a hanyar, kuma yanzu ma basu lura da su ba har sai da suka iso wajen, saura kaɗan ma su bi ta kai, Allah dai ya tsare suka gani.

Suna taka birki Rufee ta buɗe kofar motar zata fito kenan, wasu mutane suka fito daga cikin dajin hannayensu ruƙe da bindigu, ihu Rufee ta fara kurmawa ita kuma A'afia ta fara salatin annabi kawai. Cikin tsawa ɗaya daga cikin mutanen ya ce su fito daga cikin motar. Gaba ɗaya mutanen sun rufe fuskokinsu da irin rawanin buzayen nan, baka iya ganin fuskokinsu sai dai idanuwansu da hujin hanci da baki.

Ba musu suka fito jikinsu sai kerma yake yi, Rufee kuwa wage baki ta yi tana kurma ihu ko wani zai kawo musu ɗauki, ba imani bare tausayi ɗaya daga cikin bandit ɗin nan ya sanya bindiga ya harbeta a tafin kafarta suna faɗin "Idan baki yi mana shiru ba, sai mun harɓe ki a in da zaki mutu" Wani irin azaba take ji amma haka ta sanya hannu ta toshe bakinta tana hawaye.

Tasasu a gaba suka yi suka shige cikin daji da su, wani irin bakin azaba Rufee take ji, ga shi kuma sun ce sai dai ta taka kafar nata idan ba haka ba su fasata da bindiga, haka ba yadda ta iya ta fara taka kafarta suka bar wajen, suka bar motar a buɗe wayoyinsu da komai yana a ciki.

Cikin wannan azabar suka rinƙa taka kafafunsu a cikin wannan ƙungurmin dajin, banda sunan Allah ba abin da A'afia take kira, ita kuma Rufee kuka kawai take yi, azaba ya yi mata yawa, ga wahalar tafiya ga azabar sun fasa mata kafa ɗaya, sai jini yake zuna kamar me.

Sun yi tafiya mai nisan gaske, har suka wuce wani katon dutse kafin su iso wani waje kamar cam haka wajen yake, an yi ɗakuna da irin manya-manyan tampol ɗin nan.

Gaba ɗaya wajen kewaye yake da manya-manyan maza madaka kanti suna riƙe da bindiga suna tsaitsaye, da alama gadin wajen suke yi.

Suna isa wajen ɗaya daga cikin bandit da suka taho da su Rufeen ya ce "Kai Habu ku shigar da wayan nan ciki zuwa anjima idan su garba sun dawo, sai mu haɗa su mu ga yau mutane nawa muka kama" Wadda aka kira da Habun ne ya kariso wajen hannunsa riƙe da bindiga ya sanya irin rawanin buzayen nan shi ma ya rufe kai zuwa fiskarsa, baka iya ganin komai na daga fuskarsa sai ido, jikinsa na sanye da kaki na sojoji, a shekaru ba zai wuci 22 years ba.

Tasa su ya yi agaba zuwa cikin ɗaya daga cikin ɗakunan tampol dake wajen. Rufee dai ya sha azaba iya azaba, ga shi ba halin ta yi wata magana za su harbeta suka ce, ita kuma A'afia tunanin ta ɗaya shine idan su yaya Irfan suka je school ba su same ta ba me zata ce musu, ba ta yi tunanin cewa matsalar da take a ciki yanzu ya ci uban wanda take hangowa ba, a'a ita tunanin hukuncin yaya Irfan take yi, domin ita bata san kidnaping ba, labari kawai take ji, bata san yadda ake yi ba.

Habu na kai su bakin kofar ɗakin ya ce su shiga sannan ya juya ya bar wajen, jikin su a mace suka ja kafafunsu zuwa cikin ɗakin. Mata ne za su kai mata 30 a cikin wannan ɗan ɗakin, gaba ɗaya matan dake a wajen suna ƙoɗe alamar sunci bakar wahala, duk sun yi futu-futu da su, mafiyawancinsu akwai busasshen hawaye a kan fuskarsu alamar sun sha kuka, wasu kuma iyayene da yaransu kanana, wasu yan mata wasu kuma sun manyanta, abin gwanin ban tausayi, duk wata zuciya mai imani idan taga wayan mata sai ta zubar mu su da kwalla, saboda yana yin da ke a kan fuskokinsu ma kawai ya isa ya karyarwa da ɗan adam zuciyarsa, ya sanya shi kuka, ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar kasancewa a waje irin wannan ba.

Babu wadda ta kula su kowacce daga cikin matan nan tana fama da kanta, tsuru-tsuru su A'afia suka tsaya sun kasa gaba sun kasa baya, ga kuma Rufee kafarta na mata ruwan bala'in azaba. Wata wace ce wadda take zaune daga ta bakin kofa ta miƙe kafafu yarta wadda ba zata fi shekara 14 ba ta tada kai da cinyoyinta ita kaɗai ta iya ce da su A'afia su shigo su zauna, ba musu suka je kusa da ita suka zauna a takure, dan dama sun ga ji, A'afia da ta zo zama sai da ta kakkaɓe wajen tas sannan ta zauna, ita kam Rufee zaman yan bori ta yi tare da ciki hannunta daga bakinta ta fara kuka kasa-kasa dan kada su ji.

"Sannunku da zuwa" matar ta sake yi masu magana, Aafia ce ta iya amsa mata ita kam Rufee ba'a magana da kyar ma take iya fidda numfashi.

"Da kin dai na wahalar da kanki kina zubar da hawayen ki a banza ma da ya fi maki, idan baki daina ba hawayen ne za su kare a banza" Cewar matar ta kuma yi maganar tana kallon Rufee.

A'afia ce ta yi karfin halin cewa "To saboda me zata daina kuka? Baki son su ji kukan nata har a sami wani mai tausayi ya tausaya ya taimaka matane?" "Taimako a lallai ke yarinya ce sosai" matar ta bata amsa ta kuma ci-gaba da cewa "Ai tun da ba su ji tausayinku wajen ɗauko ku su kawo ku nan ba, to fa duk abin da za su yi muku ba za su taɓa jin tausayin ku ko kaɗan ba, babu zancen imani a nan wajen, kawai ku yi addu'ar Allah ya kuɓutar da ku, amma a halin da muke a ciki yanzu ma ko an kawo kuɗin fansa suna karɓa sai su ki sakin mutun ya koma gida, mafiyawanci haka suke yi, mu samman idan suna son mace, wlh aurenta suke yi wata zubin suce da yan uwanta yaransu sun kasheta da basa nan wata zubin kuma idan suna son mace taki yarda tofa suna kashetan da gaske kuma su karɓi kuɗin fansa ba yadda aka iya da su, ba mai iya tinkararsu, sun fi karfin kowa ne nake ga a kasar nan, ku dai tun da kuka shigo nan sai ku kama addu'a a cikin zuciyoyin ku domin ko sallah ma basa bari bawa ya yi bare kuma har ya samu damar kai kukan sa ga Ubangiji, amma duk da haka ku dage da addu'a cikin zuciyoyinku dan Allah ya kuɓutar da ku, a yanzu kuɗi baya kuɓutar da mutun daga hannunsu".

"Amma su ɗin su waye ne a kasar nan har da suke aikata hakan ba mai kama su ayi musu hukunci?" A'afia ta tambaya tana kallon yarinyar dake kwance kan cinyar matar "Ya naga yarinyar nan kamar bata da lafiya?" Ta sake cefawa matar tambaya. Nisawa matar ta yi kafin ta ce "Su ake cewa masu garkuwa da mutane wato kidnapas, yarinya kuma e bata da lafiya, zazzaɓi take yi, amma sun bamu magani ai ta ji sauki".

Shiru A'afia ta ɗan yi tana jujjuya kalaman matar, sun bata magani kenan suna da asibiti ne a nan wajen? Ta tambayi kan ta a cikin zuciyarta, kidnapas dama haka suke? Ta sake tambayar kanta.

Sake ɗagowa ta yi ta kalli matar sanna ta ce.......... Dole na dasa aya a nan na don na so ba sai dan page ɗin ya cika da yawa, mu haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
[11/17, 12:27 PM] +234 906 579 6460: 💖💖TRIPLET'S💖💖


💖After 2days👌💖


(Bari mu fara da restaurant kafin mu yi wani wajen kuma)


Acikin yan kwanaki biyun nan Rimsha ta saba sosai da aikin restaurant ɗin, dama kun san ta da son koyar girki, dan haka sai ta tare wajen girkin hotel ɗin, saɓanin Jehan da ko leƙa wajen bata yi, sai dai idan ta zo ɗaban abinci zata kai wa masu saya.

A yanzu Rimsha fa ta iya abinci sosai, kuma akalla zai kala girki kala 15 ta iya, bata da kiwuyar aiki, haka zalika bata jin nauyin jikinta, sake jiki take yi ta murji aikin ta, idan ta koma gida ta yi wanka ta yi ta barcin ga ji ya, sannan a yan kwana biyun nan kafin ta tafi restaurant ɗin sai ta yi wa maman Sadiq shara da wanke-wanke sannan ta tafi.

Yau ma kamar kullun da sassafe ta tashi ta yi wanke-wanke da shara, sannan ta yi wanka, ta shirya, ta ɗauko wayarta, tun da ta zo sai yau ta ɗauki wayar, kokarin kunnawa ta yi amma ina battery ya kare wayar ta mutu ba charji, turo ɗan bakin nan nata tayi sannan ta yi wa mamam Sadiq sallama ta wuce sauri sauri domin Sadiq yana tsaye a waje yana jiranta.

Tare suka jera zuwa bakin titi, a yanzu saura mata 4k a cikin 20k da Ahmad ya bata, gaba ɗaya ta kashe kuɗin a sayawa maman Sadiq irin su omon wanke-wanke da sabulun wanki da wanka, bata damuwa idan ta zo zata yi abu idan taga babu sai ta ciro kuɗi ta saya, harta tsintsiya ita ta saya musu guda uku, Yusuf mai rakata sayowa, dan shine babban abokinta.

Karfe 8 daidai ta shiga restaurant ɗin nasu, kai tsaye wajen girki ta nufa, masu shara har sun yi sun goge koina, wajen ya yi fes,

Rismha akwai goshi kamar me, tana shigowa suka fara samun baki, har Ibraheem ya campa abun, kullun cewa yake yi idan Rimsha bata zo ba basu samun ciniki, amma idan ta zo kuma, tana shigowa restaurant ɗin yake fara cika da jama'a, amma fa wa su ba abinci suke zuwa saya ba, kallonta suke zuwa yi sai su ɓige da sayar abinci, idan ta kawo musu abinci sai suyi ta rokarta akan ta basu number wayarta, amma ko kula su bata yi, suna yi mata kallon babba saboda tana da tsawo kuma tana zuba hijabi har kasa, a cikin hijabi sai ka yi mata kallon babba, amma idan ta fito yar firitu zaka ganta.

Bata taɓa kula kowa ba, fuskar nan nata kullun a ɗaure kamar hadari. Sanya wayar ta ta yi a charji kusa da Ibraheem sannan ta fara karɓar oder kowa tana kawo masa abin da yake buƙata, ita da Faiz suke wannan aiki, shi kan shi Faiz ɗin daurewa kawai yake yi yana aiki tare da ita, amma magana ta gaskiya ya gama faɗawa da ita, haka zalika shima Ibraheem ya faɗa da ita sosai daurewa kawai yake yi saboda bata ba shi fuska ba.

Bayan ta kammala kaiwa duk wayan da suka zo a lokacin abincin ne, sai ta koma saman wani kujera da suke zama idan sun kammala aiki, shiru ta yi tana tunanun rayuwa, tunanin ina zata sake ganin su mum ɗin ta kawai take yi, tunanin Ayla ne ya faɗo mata a ranta, cikin sauri ta miƙe ta nufi wajen Ibraheem.

Tana zuwa ta ciro wayarta daga charji ta shiga neman layin Ayla, abin haushi gaba ɗaya wayar number Ahmad ne kawai a ciki, shiru ta yi tana tunanin a ina zata samu number Ayla.

Tana tsaka da tunani wayar tata ta fara ringing, kallon screen ɗin ta yi, Yaya Ahmad shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar.

Picking call ɗin ta yi tare da kara wayar a kunanta. Daga ta cikin wayar ta ji wani nauyayyar ajiyar zuciya da ya sauƙe, muryarsa can kasa-kasa ya ce "Hello Queen of beauty" dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali.

"Yaya Ahmad baka da lafiya ne?" Nisawa ya yi sannan ya ce "Bani da lafiya my princess" zaro dara-daran sleeping eyes nata ta yi tare da marairace murya cike da tausayi ta ce "Allah sarki sannu ka ji? Allah ya baka lafiya, ka ga ma ko sallama ban yi ba bare mu gaisa, saboda yadda na ji muryar ka" "Allah sarki Queen of beauty ai kece silar rashin lafiyar tawa". Zaro idanuwanta waje ta yi, tana ƙokarin yin magana Ibraheem ya ce mata ga baƙi fa sun zo tun minti biyar da suke wuce, kuma sune masu wannan restaurant ɗin, jin haka yasa ta sallami Ahmad a kan anjuma zata kirashi, bata jira amsar shi ba ta katse kiran, sauri sauri ta nufi bakin dan tambayar me suke buƙata.

Sallama ta yi musu, Dr Nawid ne da Imran, Imran ne ya amsa mata sallamar nata shi kuma Dr Nawid cewa ya yi "Ina Jehan? Ki je ki ce ta kawo mana abinci".

Tana kokarin yin magana muryar Imran ya katse ta da cewa "Rimsha Nawazudden right?" Ya yi maganar yana zaro idanuwansa waje.

Dawo da kallonta kan shi ta yi, zaro idanunsa waje ya yi sosai yana kare mata kallo, tabbas ita ce, abin da kawai yake faɗi a zuciyarsa, ita kuma kokarin gane wanene shi ai na kuma ya santa kawai take yi, shi kuma Nawid ya zuba mu su ido yana kallon ikon Allah.

Sake maimaita mata tambayar Imran ya yi "Rimsha Nawazudden ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar E.

A zabure ya miƙe tsaye yana binta da kallo, ganin ya miƙe tsaye ne yasa Nawid ya ce "Imran lafiya? Ai na kasan ta? Wace ce
Showing 138001 words to 141000 words out of 344390 words