guda bayan wasu seconds din ya fito da d'ayar Zuby dake la'be a balakona mamaki jan ajin Sadeeq tayi, saboda ko ita da take mace bata da kalan sa.

"Wow" shine abinda Zuby ta fad'a a lokacin da taga Sadeeq ya fito, "gaskiya gayen nan 'karshan had'uwa ne kamar shi yayi kanshi Sadeeq ka riga ka shigo hannu bazan taba bari ka kubuce min ba ban taba jin ina son nayi aure ba sai akan ka zanyi iya bakin kokari na wajen jan hankalin ka kuma zan kiyaye duk abin da zai sa ka gane wace ce Zuby bazan bari wata kawa ta ta sanka yanzu ba ba gaskiya saboda gudun matsala inason asa bikin mu kusa saboda kada yan gulma su yimin cikas". Zuby ce ta fadi haka bayan ta gama 'karewa Sadeeq kallo

gaskiya Sadeeq namiji ne irin mazajen da suke da wahalar samu a wannan zamanin saboda ya had'a duk wani abu da ake san namiji ya mallaka Allah ya bashi yana da tsayi na misali ga kyau da hasken fata ga kudi da ilimi hankali ya iya daukan wanka ya iya soyayya mai daukan hankali duk shigar da yayi sai ta yi masa kyau shiba siriri ba shiba dan lukuti ba gaskiya masha Allah gayan ya hadu ajin karshe ne🥰

Wata matashiyar mace da bazata haura 35 years aduniya ba ta 'kara so gurin sa cikin girmama sa tace "ranka shidade nice Zuby tace na kaika falon baki".

Sadeeq da wani lokaci magana take masa wuya bai amsa mata ba sai nuni da yayi mata alamar babu damuwa ta kaisa, tana gaba yana bin ta a baya har suka isa cikin wani madai-daicin falon da yake d'auke da manyan kujeru masu ruwan orange da baki sai chanis kafet da aka shimfid'a a tsakiyar falon shima ba'ki ne da d'ishi d'ishin orange a jikin sa sai 'katon TV da ya mamaye jikin bangon falon a gefe guda a kwai 'yan 'kana nun tebura zagaye da baba a tsakiyar su gaskiya d'akin ya had'u wani abun ma bazai fad'u ba

bayan Sadeeq ya shiga ya nemi kujera ya zauna a kan 1cter jim kad'an sai ga rahmatu ta shigo hannun ta rike da katon tirai da aka jera kulolin abinci masu kyau da ban sha'awa a kan babban teburin ta jera kulolin sannan ta fita ta kuma dawo wa da wani 'katon turai din mai dauke da fruit da da kunin aya da zobo ta kuma jerawa ta fice
Can sai ga ta ta kuma dawo wa da jok din ruwa a turai da kofuna biyu bayan ta ajiye ta dauki kofi daya ta zuba mai
Ruwan sannan ta saka wani farin abu a ciki kamar 'kankara nan take ruwan ya fara canza color daga fari ya koma ja haka dai yai tayi sannan ta mi'ka masa
Amma sai yaki amsa da taga bashi da niyar amsa sai ta ajiye ta fice acikin ranta take cewa "ko ina Zuby ta samo wannan kyakkyawan saurayin tunda Zuby ke kawo samarin ta bata taba kawo mai kyau da hankali da nutsuwar wannan ba". Abinda ya daure wa rahmatu kai yadda Sadeeq din yayi shigar kamala yana kama da mutanen kirki a fuska to mai yakawo sa gurin Zuby, saboda Hajiyar ta ta san duk wani abu da Zuby ke aikata wa wani lokacin ma ita ke bata karfin gwuiwa sabanin Abban ta da bai san komi ba

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Gaba daya mutanen gidan zaune suke a falon sama amma kowa da abinda yake yi saboda Umar littafi ne a gaban sa yana homework yayin da khadija da Siddeeqah suke fira Momy kuwa laptop ce gaban ta tana danna wa sai Jiddah dake faman danna waya tana cika tana batsewa Ummi kuma Session flm take kalla sun dauki tsawan lokaci a haka

Bayan Momy ta gama abinda ta keyi ne ta dube ni "Siddee'ka". saida naji 'ya 'yan hanjin cikina sun kad'a saboda fargabar abinda zata cemin da hanzari na dago kaina muka hada ido nace "na'am Momy".
"dazun da rana nayi magana da Sadeeq akan maganar makarantar ki". Yace "ya samami ki admission a makarantar kwana har ya gama komai ranar lahadi zai zo ya dauke ki ya kai ki

Ba Siddeeqah kadai ba har su Khadija sai da suka dago kai suka kalli Momyn domin su dad'a tabbatarwa basu ga alamar wasa afuskan ta ba duk da Momyn daman ba mai irin wasa da yarannan bace amma kuma tana jansu a jiki ta yadda duk wani abun da yashige musu duhu suke zuwa neman shawara gurin ta
"Momy makaranta kwana fa ki kace". Siddeeqah ta fada murayan ta a sanyaye

"Eh". Siddeeqah wallahi makaran tar kwana Sadeeq ya nemo miki naso na hana amma sai yace "ya kashe kuda de masu yawan gaske saboda sunan wata a ka cire aka sa naki". Sannan yace "acan sai kin fi dagewa kiyi karatu idan kina gida wasa ba zai barki ba".

"Momy Daddy fa shima ya yarda ko bai sani ba?". Khadija ta tambayi Momy

Sai a lokacin Momy ta tuna ba tayi waya da Daddyn ba dan sanda ta kira sa ta nason suyi maganar yace "mata suna meting idan sun gama zai kira ta".

"A a" Momy tace "zuwa anjima idan ya kira ni za muyi maganar".

"Momy mai yasa yah Sadeeq zai mini haka gaskiya ni Momy ba zani ba gwara in koma 'kyauye gurin Inna ta na hakura da karatun bazan wani yi kuku da ku ba".

"Taso kizo kusa dani 'yata". Jiki na babu laka na tashi na koma kusa da ita na zauna na tsaida idanuwa na akan fuskar ta, hannun ta ta daura a kan kafad'a ta cikin lallashi tace "Siddeeqah ha'kuri zaki yi saboda ilimi gishirin rayuwa ne idan Sadeeq yayi haka ne don ya kunta ta miki to insha Allah aniyarsa ce zata bisa saboda ke gaba ta kai ki
Ki kwan tar da hankalin ki babu abinda zaj same ki sai alkairi".

"Momy kuma wace makarantar?". Ummi tayi tambayar
"Katsina" yace "zai kaita wai akwai kanwar Farooq a can" yace "makaran tar tana da koyar wa sosai kuma suna da kula da dalibai".

Jikin Siddeeqah yayi mutakar sanyi duk da bata taba jin labarin makarantar kwana ba amma dai ba tason tayi nisa da gida ita da take so duk bayan 2 weeks tana zuwa Dande ganin Inna
Gashi yanzu za a kaita wani garin ba garin da take ba

Da kyar Momy ta sha kan ta ta amince ba dan ranta ya so ba sai dan ganin girman Momy da take yi Momy ta cigaba da bata baki da kal momi masu dadi da sanya ya rai har ta amince

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Zuby ce zaune a kan kujerar dake kallon ta sa kura mata ido yayi ko kiftawa ba ya yi

Cikin shagwaba tace "muni na ka ke kallo ko banyi maka ba ko?".

"ko daya ina kallon irin baiwar da Allah yayi miki ne Kin kuwa san wani abu?".

"A a". Tace mai

"Ban taba ganin mace mai kyau irin kiba gaki tun da nike a rayuwa ta ban taba haduwa da wacce na ke so ba har naji ina mura din auren ta sai ke, gaskiya ki kara godewa Allah bai rage ki ta ko ina ba a lokacin da naga kina tafiya sai kikai mini kama da wahainiya hatta muryan ki abar so da kauna ce idan kina magana kamar ana busa sarewa, ga...".

"Ya isa haka my kada kasa na kasa bacci yau amma ka zuga ni da yawa har ka da naji kaina yayi kato".

Duk kuwa da ba karamin dadin kalaman shi taji ba wani d'a na miji bai taba yaban ta haka duk kuwa da ita mutum ce mai san ana kuran ta ta ana zuga ta shiyasa tace "Sadeeq din na musamman ne".

"Ai kin wuce haka Baby na saboda kedin zara ce".

Cikin zolaya tace "Allah My kafi kyau a fili ka dai na wahalar daukan picture's saboda yana rage maka kyau".

"Bawani nan kodai ban miki bane?".

Zaro ido tayi waje gami da dafa kirji tace "wane mutum inji mutuwa".

"amma kinsan labarin zuciya atambayi fuska ko".

"fadamin nason daman dan sanda akwai ku da karantar yanayin mutum".

Zai yi magana kenan wayarsa ta hau ruri Acp Taneem yagani yana yawo a kan screen d'in cikin girma-ma-wa ya kara a kunne ya gaida ogan na su
Ko mai yace masa daga can ban garen oho, Shi dai Sadeeq din yace "okay angama ranka shidade okay okay ahaka dai suka karasa wayar

Ya a je yana kallon Zuby da ta kura masa ido ko kiftawa batayi

"Ya dai" yace mata yayin da ya hura mata is kar bakin sa, sai a lokacin taga rashin dacewar hakan kunya ta kamata tayi sauri ta sadda kan ta kasa tace "kamar ana neman ka A gurin aki ko ne ko?".

Gira yadaga mata alamar "eh"
"to bari na kira Hajiya ku gaisa sai na kaika gurin dady daga nan saka wuce".

Bata jira amsar sa ba ta wuce bata wani dauki lokaci ba ta dawo tare da wata dattijuwar chocolate din mata ita ba doguwa ba ita ba Gajere ba tsaka tsakiya
Amma kuma kina ganin ta kin ga uwar Zuby saboda ba karamin kama suke ba duk da cewa Zubyn ta shafa mai tayi haske

Cikin mutunci Sadeeq ya russuna ya gaishe ta ta amsa mai cikin kula da jin dadi Sannan sukayi sallama ta wuce

"gaskiya Hajiya nada kirki". Sadeeq yace wa Zuby

"Allah da gaske?".

"Ehman ashe ita kika biyo".

Zuby dan dadi har rufe fuska take yi wai yau ita ake yaba haka 💃

"muje na kaika bangaren Abba ku gai sa".
"Muje to" ya fada yana mike wa tsaye

Ta wata kofar suka bi sai gasu a cikin wani madai-daicin falon da babu tarkace a cikin sa da wani datti jo zaune a kan kujera hannun sa da jarida yana karan tawa fuskar sa sanye da siririn glass bayan sunyi sallama suka karasa ciki a kan kafet Sadeeq ya zauna ha gaida sirikin nasa Abban Zuby yaji dadi sosai da yaga sadeeq ne zai auri tilon gudan jinin sa bayan sun gaisa suka dan taba fira Zuby kuwa bakin ta ya ki rufawa farin cikin ta ya bayyana a fili, basu dade ba Sadeeq ya yi masa sallama

babu laifi Abban Zuby yana da haske fata wata kila agurin sa Zuby ta dauko hasken fatar

Har bakin motar sa Zuby ta rakosa tana yi masa shagwaba kala kala da kyar ya samu ya lallashi ta ta barshi ya tafi

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
"Ku tashi kowa yaje ya kwanta dare yayi sai kuma idan Allah ya kaimu gobe" Momy ce ta fadi haka yayin da take kallon 'ya 'yan ta "to" duk suka ce masu tarkace suka dauka Ummar da dakin sa yake a kasa ya shige haka Jidda ma nata a kasa yake itama ta ce "Momy good night" tuni mu uku muka dun guma zamu haura sama amma sai Momy ta kwala min kira "Siddeeqah na manta zo ki dauki abincin yayan ku ki kai masa ban garan sa tunda saman zaku haura gab yake da shigowa

*Ash wash kash*😂
_Na gaji hhhmmmm idan ban ga ruwan comments ba za a dade banyi typing ba_ 😂

*Kada ku manta*
_Comment kyauta ne haka ma share da vote_😂

Taku har kullum _Sbeeuty✍️

NI DA YAYA SADEEQ
                  
بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 14

_____"To". Nace wa Momy na nufi hanyar kitchen bayan na shiga na d'auko kular abinci da zobon da Momy ta hada mai akan wani madai dai cin tirai na d'oro su sanda na fito babu kowa a falon har Momy ta wuce d'akin ta saboda haka nima na haura sama sai da na fara zuwa daki na na sauya kaya na saboda izuwa yanzu nima na fara sabawa da kayan baccin idan ba dasu ba bana jin dadin baccin saboda haka na sauya izuwa wata farar doguwar riga mai kauri ta bacci akwai wata yar baza mai kamar leshi a gaban ta ina sau yawa na nufi bangaren ya Sadeeq da yake dan nesa da mu saboda saikin bi ta wata kofa sannan zai sada ki da bangyaran sa dake dauke da falo da d'akuna 2 sai bayi da kitchen, nayi sa'a saboda kofar shiga a bude take ina murmushi na karasa ciki saida na gama karewa falon kallo sannan naja dogon tsaki ina ta'ba baki na ce "shi ko kunya baya ji daki sai kace na mace". A bude na bar kofar sannan na wuce bedroom din sa da shiga ta naga gado a gyare luf luf dashi ya lailaye zanin gadon sa ji nayi ina sha'awar hawa gadan saboda haka na ajiye kular abincin a kan wani teburi nayi sufa kan gadon😜 ina 'yan tsalle tsalle na ina dariya ni kadai

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tafe yake a kan hanya tunani ne fal a cikin zuciyar sa ya sa'ka wannan ya warware wancen duk da tuki yake yi amma yayi zurfi a cikin tunanin sa ta yadda bai san mai yake yi ba Allah ne ya tsare sa da kuma kasan cewar ba akan babban titi yake ba ringing din wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula fir gigit Sadeeq yayi saida ya dafa kansa "ya Salam ni Sadeeq mai ke damu na haka wani irin tunani ne kuma akan me nike yin sa mtssss" .yaja dogon tsaki ba shida amsar tambar sa saboda haka ya lalubi wayar sa da yaji tana ringing bai wani tsaya ya kalli sunan wanda ke neman sa ba yana dauka ya kara a kunne.
Daga d'ayan bangar akace "wallahi aboki baka da mutunci daka zuwa Abuja ganin Princess sai ka manta damu, munafuki amma da anyi magana kace baka son yarinya ka tsane ta".

"shege akace maka kowa mayen mata ne irin ka ka rasa dawa zaka hada ni sai da yar karamar yarinya wacce ko...".

"haba malam kada kaci ka min baki daga karshe kazo ka fada tarkon karamar yarin ya".

"Wa ni?!". Ya fada yana nuna kan sa da yatsan sa ". Kamar Farooq din yana ganin sa "Allah ya kyauta ai na fada mata duk sanda taji nace ina son ta kada ta taba yadda dani saboda ba da gaske bane".

Farooq baiji dadin yadda abokin sa yayi su'bul da baka ba saboda haka yace "uhm Sadeeq idan Allah ya tashi kama ka bazai maka kadan ba kuma gaskiya bazan ji tausayin ka ba koda zanji sai ka ji jiki, saboda duk abinda ka Shuka shi zaka girba dama na kira ne naji ya kake ya Momy tunda duk kuna lafiya sai da safe".

"Kaga Farooq kada ka kashe a kwai maganar da nike so muyi".

"Ina jin ka to"

"yanzu haka fa a hanya nike naje naga gimbiya ta, gaskiya babyn ta hadu tafi kyau a fili nike fad'a maka komai yaji zam-zam hhhmm nasan ba lallai ka yarda ba tunda kaki ko hotan ta ka gani amma tun na ganta na shiga wani yanayi".

"Haba Sadeeq daman wannan ce maganar da kace za muyi?.

"Eh amma da akwai d'ayar nafi zumud'in wannan shiyasa na fara fada maka ita" kuma kasan nace "Momy ce take nema na ashe akan makarantar yarinyar nan ne to shine nike so ka nema mata admission a makarantar da Sadiya take saboda na cewa Momy na gama komai tafiya ta rage".

Shuru Farooq yayi na wasu yan da'ki'ku alamar nazari can ya numfasa yace "haba Sadeeq wai meke damun ka meyisa kake son ka kuntatawa yarinyar mutane wani irin makarantar kwana ana zaune 'kalau don Allah kajanye wannan maganar kaji tausayin ta
Har yanzu fa Siddy yarinya ce karama na tabbatar ma batasan maye aure ba da tasani wallahi da...". Bai karasa maganar ba Sadeeq ya dakatar dashi da cewa "malam don Allah ba shawara na tambaye ka ba
Dan kaga na biyo ta hanyar ka shine zaka tozartani idan baza kaimin ba kawai ka fadamin"

"Allah ya huci zuciyar ka". Farooq ya fada kana yace "aji nawa za a sata?".

"Ko js1 ne asata ba matsala ta bace zan fi son haka saboda na more soyayya ta da Baby na kan tagama karatun"

Farooq nason yace wani abu amma gudun kar yakara laifi yace "babu damuwa zanyi kokari insha Allah ko js2 su kaita".

Daga haka sukayi sallama

Bayan Sadeeq ya gama faking din motar sa ya fito jinsa yake wani iri saboda haka ya haura sama bai kai ga shiga dakin ba yaga kofar abude yayi mamaki bai gama tsinkewa ba sai da ya shiga bedroom din sa ran sa a mugun bace ya karasa kan gadon da niyar fusgo ta amma sai yaji kamar an soka masa kibiya a cikin sa bai san sanda ya zube a kan gadon ba numfashin sa nafita da sauri da sauri Siddeeqah garin juyi ta wurga wa Sadeeq kafa ransa bace ya wur ga mata harara tuna aikin banza yayi tunda bacci take yi ya shiga kwala mata kira "ke ke uban wa ya ce ki shigo nan?"

Siddeeqah da kamar a mafarki taji ana kiran ta a fir gice ta bude idanuwan ta suka sauka akan na Sadeeq dake mata kallon tuhuma fuskar sa a murtuke babu alamar wasa yace "dan uban ki uban wa yace ki shigo min daki?".

Siddeeqah gaba daya ta rike ce bakin ta na rawa take fadin "lah yah...!".

"Yayan uban ki zakiyi bayani wallahi bazaki sauka ba sai na yi ball da ke".

'Kokarin tashi yake amma cikin sa ya kara murde sa nan take ya rike cikin yana kiran sunan Allah a rude Siddeeqah ta 'karasa gurin sa ta kama hannun sa "yaya yaya meke damun ka haka me yasa meka".

A wahalce Sadeeq yace "cikina". Kama hannun ta yayi ya dora a kan cikin sa ji tayi kamar akan shocking ya d'ora mata hannun saboda haka tayi sauri ta janye yaya bari naje na kira Momy saboda ni bansan mai zan maka ba zata sauka kenan Sadeeq ya kama hannun ta idon sa a rufe yake cewa "kar ki tafi ki banni kizo dan Allah kada ki tafi" cikin karfin hali ya janyo
Showing 21001 words to 24000 words out of 51717 words