ganin abin yafi karfi na yasa na fito daga dakin naja musu kofa, ina yi musu adduar Allah ya shirya su dan wannan dabiar bata mutanen kwarai bace wace irin musifa ce wannan da mace take neman yar uwar ta mace yayin da shima namiji yake neman dan uwan sa namiji, shiyasa annoba bazata rabu damu ba saboda aduk lokacin da akasumu saukar annoba to sabon Allah ne yai yawa akasa, kuma duk masu wannan dabiar a wuta zasu dauwama.
wa'iya zu billah.
* * * * * * * *
Yunwar da ta fara kwakular ciki nane ta tashe ni daga nannauyen baccin daya dauke ni na manta a mota nike saboda haka nai mika gami da yin juyi, ai kuwa cikin rashin sa'a na fada sakon mota inda ake saka kafafu, ihu na fara ina kiran sunan yaya da duk ya bi ya gaji sai mita yake wai Farooq baya gudu ". Shi kuma Farooq na cewa" in ba sama kake so na tashi ba ai wannan gudun ya isa ".
Ihu na ne ya katse musu firar su da sauri yaya ya juyo da kansa cikin motar yana fadin "subhanallah garin yaya haka ta faru maza tashi". Ya karasa maganar yana zuro da hannayen sa da kyar na iya temaka masa ya daga ni, bayan na gyara zama na akan kujera nace "yaya wai har yanzu bamu kai ba ni na gaji yunwa nike ji". Na karasa maganar cikin sigar shagwaba, nuna min Farooq yai yace "duk laifin shi ne kwata kwata baya sauri tafiya yake kamar wanda yake tsoran taka kwalta".
Nace "to ni yaya yunwa nike ji"
Yace "to bari mu karasa can gurin ina kyauta ta zaton karamar kasuwa ce sai muje baza'a rasa abin tabawa ba". Ya fad'a yana nuna min wani guri da nike hangan mutane
"To" Nace yayin da na hada kaina da gwuiwa ta
Ba mufi minti 7 ba muka karasa bakin gurin, kasuwa ce yar karama mata da maza sai zurga zurga sukeyi, yara da manya Farooq yace "banda abinka Sadeeq me zamu samu anan da zamu ci?".
Yace "mu fita ahaka ba zamu gane ba kuma can ma kamar masallaci ne mayi sallar azahar gashi ma kamar ana kiran la'asar duka sai mu sauke nauyi,
Yah Sadeeq yace" ki zauna a mota bari mu fita mugani ko zamu samu abinci".
Ban bashi amsa ba suka fita harda rufe motar
Basu wani jima ba sai ga Yah Farooq ya dawo da kwano a hannun shi da kwarya, bayan ya bude motar ya miko min na amsa, shi kuma ya juya
Koda na bude kwanon danbu ne na gani yaji gyada da zogale yayin da ita kuma kwaryar fura ce acikin ta me rai da lafiya
Ba tare da nayi bismillah ba na shiga cin danbun, duk da yawan danbun saida na kusan yin rabin shi saboda ina mutukar son danbu a rayuwa ta, bayan na koshi kuma na dauki kwaryar fura itama na fara sha saida naji na cika cikina dam, har inaneman gurin numfashi sannan na hakura ba don bakina ya koshi ba sai don cikina da ya koshi
Gyatsa nike so nayi kozan dan ji dadin ciki na amma taki zuwa saboda haka nai ta bude baki ina Jan iska
Can saiga su yaya nan sun dawo hannun Yah Sadeeq dauke da gorar ruwa bayan sun zauna yace "kin rage dan bun?".
Nace "eh".
"yauwa miko wa Farooq danni bazan ci ba furar zan sha ai itama kin rage?"
"eh nace yayin da na miko mai kwanon danbun dana furar
A mota suka ci bayan sun gama suka je suka mayar da kwanon da kwaryar
Daka bisani muka kuma daukar hanya
" Nace yaya amma dai mun kusa zuwa ko?"
" eh mun kusa bai fi sauran mu 30 minutes ba mu karasa, ya nuna min wata katan ga da muke ta shigewa yace "nan kinga duk makarantar ce, zaro ido nai nace" kai yaya gari guda haka ".
Yace" eh har tafi haka girma bari muje ki gani".
Haka dai nai ta yiwa Sadeeq surutu yana biye min duk da fuskar sa babu wal-wala amma duk tambayar da nai masa yana bani amsa, a raina nike cewa "nasan yana tsoron nace na fasa ne shiyasa yake amsa min".
* * * * * * * * * * *
Aban garen Zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su tashi sukai suka shiga wanka kamar kullum nan ma saida suka bata lokaci suna tsotse-tsotse kana suka fito fiskokin su dauke da nishadi suka shirya cikin wata doguwar riga me ruwan kwai tana da laushi matuka Lubancy tace "ina zamu yau?"
Zuby tace "gurin shakatawa man, yauwa naga baki hau online ba meyisa".
Lubancy tace "banida data ne, wani abun ya faru ?"
Zuby tace "kwarai ma kuwa ina wannan yarinyar da kika sameni ni da ita jiya?".
Tace "eh na tuna ta".
Zuby tace "ashe yar lekan asiri ce yanzu haka tayi left a kungiya kuma ni fa cemin tai turai ce ta kawo ta ashe karya tai min".
Lubancy tace "nifa shiyasa tun na kalli yarinyar naji batai min ba kwata-kwata kuma yanzu wani matakin aka dauka?".
"Har yanzu dai ba'a samu mafita ba kasancewar wa'innan tsinannun dokokin kungiyar na aiki, ke nifa abun ya fara isa ta gashi yanzu wlh ina cikin damuwa" Zuby ta fada tana sauke ajiyar zuciya
Kusa da ita Lubancy ta matso ta ce "kawa ta me ke damun ki fada mun naji ko zan iya miki magani".
Nan Zuby ta kwashe labarin komai yadda sukai da Abba ta fada mata hankalin Lubancy a mutukar tashe tace "da matsala gaskiya ya zama dole a fada wa yan kungiya saboda su taimaka mana da shawara kinsan a ka'ida ko aure kai baka daina wannan harkar da zaran ka bari kungiya zata tona maka asiri kuma kinga Maheer ba kalan mazan da zasu dauki raini bane".
Gwauran numfashi Zuby ta sauke tace "wallahi kawa ta shiyasa duk na bi na damu amma dai mu dan jinkir ta kafin mukai maganar kungiya idan Abba ya dawo zan roke shi".
Lubancy tace "to Allah yasa a dace".
"Ameen" ta fada yayin da ta mike ta dauki katon hijab din ta gami da fiddo nikabin ta a jaka tace "kawa tashi ki shirya mu tafi".
"To" Lubancy ta fada yayin da itama tai shiga kamar yadda Zubyn tai kana suka fito
Mama mama Zuby tai ta kwala mata kira daga can ciki Mama ta amsa
Zuby tace "kina ina ne Mama?"
tace "ina kitchen"
Shiga kitchen din sukai inda suka tarar da ita tana nuna ma mai aiki wani abun gasa kaza da aka siyo shi sabon yayi.
Fuskar Mama dauke da fara'a tace "sai ina kuma?"
Lubancy tace "wallahi Mama mun gaji da zaman gidan ne shine zamu fita ba jimawa zamuyi ba".
Tace "to adawo lafiya"
"Allah yasa".
* * * * * * * * * * *
Wangala-wangalan get yaya Farooq ya wuce guda biyu, kana yai tafiya marar tsayi a bakin wani guri yai farkin danaga an rubuta staff room, kasan cewar na iya karatu amma ban san ma'anar shi ba,
Shiru yadan ratsa mu kana yaya Sadeeq yace "mu sauka man".
Yah Farooq ya fara fitowa sannan sai yaya Sadeeq, bayan ya fito yazo ya bude min kofa yace "fito mun kawo, bayan mun fito office-office mukai ta shigewa har muka isa wani office dan madai-daici, shiga mukai da sallama dauke abakin su yaya, inda muka sami wani malami a zaune da takardu a gaban shi yana ta dubawa, da alamar shine abokin yah Farooq ganin su yaya Sadeeq ya aje abinda yake, yah Sadeeq ya mika masa hannu, yana Murmushi ya amsa, hakama yah Farooq bayan sun gama gaisawa yai musu nuni da su zauna akan wasu kujeru da aka tanade su saboda baki,
Babu abinda nike sai zaz-zare ido ina kara shigewa yaya.take naji bazan iya zama a wannan dokar Dajin ba gaskiya to wai ma in banda abun mutane taya za azo dokar daji ayi gini ace wai makaranta, ni dai gaskiya bazan zauna ba.
Da turan ci malamin yai min magana, ban san me yake nufi ba yaya Sadeeq yace " ya sunan ki yace?"
Nace "Siddeeqah Suleiman".
Yace "suna mai dadi, ku tashi na raka ku ofishin shugabar makarantar".
"to suka ce yayin da suka mike a tare, muka fito ina ta ganin dalibai na wucewa dai-dai haka, wani office din muka kuma shiga ba laifi ofishin babba ne kuma an dan kawata shi wata mata ce muka gani zaune akan kujera fuskar ta dauke da gilashi ba laifi matar ta dan manyan ta fara ce sosai kamar ka taba jini ya fito, dagani hutu ya zauna a jikin ta, tana da kyau dan irin doguwar fuskar nan gare ta tana da manyan idanu da dogan hanci ga dan karamin bakin ta, sanye take cikin kayan alfarma tana dan juya kan kujerar da take zaune, da Sallama muka shiga, fuskar ta dauke da fara'a ta amsa kana ta nuna mana kujeru tace mu zauna, tunda na kalli matar naji ina son ta ban taba haduwa da wanda naji ya kwanta mi arai lokaci daya kamar ta ba,
To aban garan Hajiya Aisha ma haka lamarin yake dan kuwa tana kallon Sadeeq da Siddeeqah taji gaban ta ya fadi, ga kuma kwarjinin da sukai mata har taji son su da kaunar su ya shiga ran ta.
Tana dariya tace "Malam Naseer suwaye wa'innan?".
Yace "ai ranki shi dade sune wa'inda na miki maganar su wannan itace kanwar tasu da akai ma register".
Tace "masha Allah" yan mata ya sunan ki?" Hajiya Aisha tai maganar tana kollon Siddeeqah
"Siddeeqerh" na bata amsa yayin da muka hada ido ta sakar min Murmushi tace "sunan ki babban suna ne kuma nima sunan yarinya ta babba ce".
Nace "Ammi da gaske kema kina da yarinya me suna na?".
Bani da na fadi sunan ba ita kanta Hajiya Aishan yanayin ta ya nuna taji dadin yadda na kira ta shi kuwa yah Sadeeq mamaki ne ya kama shi
Tace "da gaske nike yata amma a halin yanzu bama tare".
Nace "to Ammi tana ina?".
Idon Hajiya Aisha ne ya kawo kwalla ganin haka yasa yah Sadeeq yace "ke Siddeeqah ya isa haka kin cika tambaya".
Jikina a mutukar sanyi nace "Ammi ki yakuri na daina".
Handkerchief ta d'auka ta dan yi sama da glass din ta ta share kwallar data cika mata ido tace "babu komai yata".
Ya Sadeeq ta kalla tace kai ya sunan ka?". Nai sauri nace "Sunan shi Sadeeq yaya na ne kuma dashi Daddy ya daura min aure yace Wai alkawarin kanwar shi ne data...".
"Ke!!!" Yah Sadeeq ya daka min tsawar da saida naji yayan cikina sun kada a tsorace na dago kai na kalle shi inda na hangi tsan tsar bacin ran sa ture ni yai daka kusa dashi ya tashi ya fita fuu kamar zai tashi sama.
Farooq yace "ranki ya dade ki yaquri haka yake zuciya gare sa".
Hajiya Aisha da ke saka abubuwa bar katai a ranta tace "ba komai, amma abinda ta fada gaskiya ne dan ta tuna min da wani dana shima haka yake kamar wannan?".
Farooq yace "eh gaskiya ne".
Daga haka babu wanda ya kuma furta wata kalmar
Malam Naseer ta duba tace "Malam jeka dasu office din ka kaina ya fara min ciwo ka bata ajin da ya dace da ita"
"To" yace muka fito, yah Sadeeq na hanga acan jikin mota, harara ya wurga min nima na rama harda murguda baki, a zuciya ta nike cewa ba zai taba canzawa ba".
Bayan mun zauna a office din
Malam Naseer yace "
"A jin ki nawa a makarantar da kika baro?"
Nace "Js 1"
"Shekarun ki fa?"
"sha hudu 14" na bashi amsa a takaice
Wata farar takadda ya dauko ya danyi rubuce-rubuce kana ya shiga yin magana da turanci yah Farooq na bashi amsa bayan sun gama ya miko min wata yar takadda yace "zan sa students su zo su tafi dake yanzu hostel din ku, dan yanzu dalibai suna aji ana karatu amma ke bazaki samu damar yin karatu yau ba saboda an kusa tashi ".
" to" nace bayan na amsa takaddar
Bayan mun fito da gudu na isa gurin yah Sadeeq na kan kame shi ina kuka nace "yaya yanzu tafiya zakai ka barni? saboda ba ka kauna ta, kalli fa kaga ni dai na fasa bazan iya rayuwa anan ba".
Rage tsayin sa yai ya tsugunna yace "kowa da haka ya saba kema zaki saba karatu ne kuma ba'a samin sa a sauki saboda haka ki jure sannan banda rashin kunya dan akwai ban banci tsakanin makarantar kwana da ta jeka ka dawo, idan senior tace kiyi kiyi banda kin ji dan idan kika ce zaki rashin kunya wuya zaki ci".
Hawaye ne masu zafi suka cigaba da wanke min fuska na kara rungume shi, yah Farooq yazo yace "sake shi Siddeeqah saki shi haka nan, ki hakuri ba wani jimawa zaki ba zaku tafi hutu".
Ban sake shi ba na cigaba da kuka na "da kyar ya Sadeeq ya dago ni yana cewa" nace ya isa haka ki daina kuka muje na baki number na kuma insha Allah idan na samu lokaci zan zo na duba ki, kuma idan lokacin ziyara yai su Momy zasu zo".
Nace "to yaushe ne ziyarar?".
"an kusa". Ya bani amsa yana Jan hannu na muka nufi gurin mota
Bayan motar ya bude ya fiddo wannan katon akwatin kana ya maida ya rufe
Yace "yauwa wannan shine akwatin ki duk abinda kike so akwai a ciki".
Kanshi ya dan dafa yace "Farooq munyi mantuwa fa"
"ta me?". Farooq ya tambaya
"Uniform din ta mana".
yace "a haba na dauka ka dinka mata ne bari naje in karbo".
Cikin office din da muka baro ya koma bai wani jima ba sai gashi ya dawo da leda a hannun sa
Wasu students ne guda uku suka zo inda muke da turan ci suka gaida su yaya suka ce Sir Nazeer ne yace muzo mu kaita hostel din ta, yah Farooq yace "to gata nan dan Allah amana ku kula mana da ita".
"insha Allah suka ce".
Kana ya Sadeeq ya ciro kudi ya bani nace "bana so yaya wanda Daddy ma ya bani suna gida na baro su".
Yace "ki amsa ki nada bukatar su".
Duk yadda yaso na amsa ki nai ba yadda ya iya wasu kudin ya ciro yabawa yan matan yace "wannan naku ne ku raba wannan kuma nata ne idan tanada bukatar wani abun sai ku bata".
"To" suka ce yayin da suka shiga Jan akwati na
yah Sadeeq yace ce "to Siddeeq zo ki amsa number kada na manta mota ya shiga ya dauki memo da biro ya rubuta number ya miko min na amsa
yace" sai na dawo duba ki Allah ya bada sa'a".
Ameen yah Farooq yace inda shima ya shiga mota hannu nai ta daga musu har saida naga sun Kule min sannan na daina na kalli wa'innan yan matan guda uku nace "ina zamu yanzu?"
Ba wanda ya tanka min suka cigaba da Jan akwatin da kamar na daina bin su sai dai nace bari naga gudun ruwan su
* * * * * * * *
Sanarwa
Sanarwa
Sanarwa
Follow
Comment
Vote
Dan Allah kada amanta ayi following dina sannan ayi min comment da vote please kuma ku min uzuri akan rashin jina akai kai abubuwa ne suke min yawa amma insha Allah zaku dunga jina
kasancewar bana typing kullum na manta wasu sunaye danasa to za kuga na canza suna insha Allah idan nagama littafin zan gyara🙏
taku har kullum Sbeeuty
NI DA YAYA SADEEQ
•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Not edited
Chapter 29
_____Iska ce mai dadi take ta kadawa tako ina saboda yawan bishiyoyin gurin, dalibai sai zirga zirga sukeyi, can na hangi wasu dalibai su biyu durkushe akan gwuiwoyin su, wata budurwa ce mai Jan dan kwali ke ta zabgar su kamar ta samu bayi da alamar yaran da ake duka magiya suke a kyale su saboda naga sai daga hannu sukeyi alamun ban hakuri, sai da muka matso dab da wa'innan matan naga wata zabgegiyar bulala ce ta darbejiya a hannun mai dukan, take naji na tsane ta raina yai kuna zuciyata na yin radadi, yaran da ake duka duk sunyi laushi idan su ya furfuto waje, adai-dai inda mai dugan taje wa'innan yan matan da aka hadani dasu suka tsaya, ba shiri nima naci burki.
Wannan firifet din tana ganin mu tayo kan mu tana dariya tace "sista Zamra daga ina haka". bata lura dani ba, dan kuwa na dan boye a bayan daya daga cikin wa'inda aka hadani dasu
Wacce aka kira da Zamra tace "wallahi daga staff muke"
Daya daga cikin matan da muke tare tace "ke dai Jamlah kullum kina cikin duty ko gajiya bakyayi wallahi da akwai kanwar ki a makarantar nan sunan ta sorry dan ta gama kadewa".
Wacce aka cewa Jamlah tace "hhhmmmm Saudat kenan ai shiyasa naki bari a kawo Sajida yanzu haka kano aka wullata".
Wacce nike bayan ta ce ta goce sai alokacin Jamlah ta lura dani dago kai nayi muka hada ido take naji gaba na yai mummunan faduwa har saida na sa hannu na dafe kirji na saboda yadda yake buga min.
Ita ma a bangaren Jamlah kusan haka taji faduwar gaban, sai dai bai kai nawa bugawa ba kallon kallo mukayi har saida Wasilah tace "yaya dai Jamlah kin San ta ne?".
Da sauri Jamlah ta dauke idon ta daga gareni tace "a a ban san ta ba naga dai tana kama da Wanda nasani ne".
Zamra tace "koda naji dan new commer ce yanzu haka hostel zamu kai ta".
Murmushi Jamlah tai daya kara fito da kyawun ta tace "yakamata ku han zarta kaita dan kuwa dole muyi mata welcome to......". Bata gama karasawa ba Wasilah tace "wai ke Jamlah wace irin muguwa ce? na lura Sam bakya jin dadi idan baki ci zalin yayan mutane ba to wallahi wannan bazaki dake ta ba
Showing 45001 words to 48000 words out of 51717 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16 Chapter 17Chapter 18