nasaka mata hijabin. Yi yai kamar beji abinda Inna ta fad'a ba. Kome ya tuna oho. Se gashi yazo ya  dagani sama ta yadda fiskata  zata  kalli  Inna. Saka min hajabin tayi, yasan Inna  baza ta  iya d'auka taba saboda haka ya ajiye ni a 'kasa amma be sakeni duka ba. Yace "Inna muje ko,'ko'karin fara jana yakeyi, Inna tai saurin daka mai tsawa tace" wai Garba lafiyan 'kalau kuwa?"

Be ce mata komi ba yasa'ba ni a kan kafad'ar sa, Saboda yayi min mugun ta  yazuro kaina 'kasa sosai. jini na se dawo min kai yakeyi, a haka muka isa bakin motar, a gidan baya ya ajeni sannan yashiga gurin zaman direba. Inna  ma  baya tashigo tana mita. domin Allah ya mata mita koda yiki yawanci tsofaffi sunada wannan mitar, kaina nadora kan cinyarta ina matso kwalla bawani bab-ban asbiti ya kaini ba illah asbitin dake cikin 'kauyen mu asbitin shi kadai ne asbiti. kuma babu wasu kwararrun ma aikata acikin sa.

   

idan kunji dad'in labarin ku aikomin da

Comment
       Shear
           Vote

NI DA YAYA SADEEQ
                  
love story 2021 typing free book_

Story & Writer by

Siddiqahtul khair Y Faru
            (S beauty ✍️)
             
                 03
_________Asbitin gaba d'ayan sa a lala ce yake saboda ginin jar 'kasa ne wani 'bangaren ma duk ya rushe, d'a kunan  da ake kwantar da marasa lafiya guda 4 ne kawai, Sai office 1 da ma aikatan asbitin suke zama a cikin sa, gabaki d'aya asbitin gado biyu ne kawai a cikin sa,

a bakin asbitin yah sadeeq yayi faking, Asbitin bashida kofar shiga ko ta ina shiga a ke saboda ba a ke waye yake ba, ya d'auki kusan 10 seconds a cikin motar, kafin ya kashe ya fito,
Saida yafara bud'ewa Inna  murfin 'motar ta fito, san-nan yazo ya bud'e bangaren da nike yad'an zuro jikinsa ciki ya mi'ko hannu ya janyo ni, Inna na fad'in "kabita a hankali ba tada cikak-kiyar lafiya".
'Dauka ta yayi irin d'aukar da a kewa jari-rai cikin Asbitin ya nufa dani,

Inna na biye  dashi a baya,

Da yike yah sadeeq sanan-ne-ne a gari bama iyaka kauyen mu kad'ai ba harda burni. Saboda babban d'an sanda ne

wata nurse ce ta  han gomu da sauri ta 'karaso inda muke, cikin rawar jiki tace "yallabai cikin wancen d'akin zaka kaita zatafi hutawa babu mutane da yawa a cikin sa". Tafad'a haka tana nuna mai d'akin da yatsan ta manu-niya, "alright" shine abinda yah sadeeq kawai ya fad'a.

'Dakin da a kace yah sadeeq ya kaini shine d'akin da ake ji dashi a cikin asbitin saboda a kwai siminti da gado guda d'aya tak a cikin sa, mun tarar da mara lafiya a kan gadon  kwance, saboda yah sadeeq ya d'ora ni aka sauke mara lafiyar gunin ban tausayi gashi masu jinyar ta basa kusa,

"yalla'bai d'ora ta a kan gadon". A cewar nurse d'in data sa aka sauke mara lafiyar

Yah sadeeq beyi ma-maki ba saboda ya saba kawo ni asbitin kuma irin haka ne take  faruwa.

'Dora ni yayi akan godon, yana d'orani ya fice daga d'akin,

Nurse d'in ma tabi bayan shi tare da wa'inda suka cic-ci-'bi marar lafiyar da aka sauke a kan gado,

be jima ba saiga shi ya shigo tare da  wata nurse, hannun  ta rike da wani d'an karamin faran tin silba, kan wani teburi na katako ta ijiye tiran silban, sannan ta matso kusa dani, ta d'ora hannun ta a kan wuya na, "a kwai zafi a jikin ta yallabai, zazza'bi ne ya kamata". Nurse d'in tafad'a tana duban shi, amma ko tanka mata beyi ba sai yayi kamar ba dashi take magana ba,

"meke damun ki?". Nurse ta tambaye ni,

nace "duka jikina ciwo yake min, amma kirji na yafimin ciwo".

Fuska ta ta kalla da kyau sai taga shatun hannu tace "kamar dukan ki akayi ko, domin shaidar hannu ya bay-yana a kan kuncin ki rad'a rad'a".

Na bud'e baki zanyi  magana kenan yah sadeeq ya wurga min hara ra,

Ya kalli nurse d'in yace "ke maye aikin ki?".

"Duba mara lafiya". Ta fad'a bakin ta na rawa,

saida ya d'aure fuskar sa babu alamun wasa a tat-tare dashi yace "to kiyi aikin ki wannan be shafeki ba kiyi abinda yadace".

Cikin in-ina tace "to ranka  shidad'e na tambaya ne saboda nasan irin maganin daya dace na bata, amma kaya 'kuri naga kamar ranka ya 'baci".

Be kuma bi ta kanta ba yafi ce  daka cikin d'akin, tasha fama dani sosai kamin na bari tasoka min allurar da zata samin abin 'karin ruwa, shima saboda naga yah sadeeq ya dawo d'akin ne.

Banfi minti 25 da samin karin ruwan ba, baccin wahala ya d'auke ni,koda na farka bayan wasu awanni da bazu wuce 2 ba

Naga momy zaune a kan wata farar kujera, da alama daka gida aka zo da kujerar mamakin ganin ta ne ya kamani, na mi'ke zaune na jingi na da filo a baya na, kallon ta nikeyi ina muts-tsuka idanu na, ban gama mama ki ba saida naga  Khadija, tashigo d'akin hannun ta d'auke da kular abinci, da kwano, Umar, na biye da ita a baya,

tashi Momi tayi tamatso da kujerar ta kusa da gado na ta zauna  tana kama hannu-na "sannu kinji Allah ze saka miki ya jikin naki". Momy ta tambayeni muryan ta d'auke da damuwa

mada din na bata amsa sai nace "wai momy yaushe kuka zo kuma waya fad'a muku banida lafiya?, Inna dai bata da waya yah sadeeq kuwa nasan ko mutuwa nayi baze kiraku ya fad'a muku  ba".

Momy tace "Babu wanda ya fad'a mana, daka kaduna muke hutun makarantar su Khadija ya 'Kare zamu koma Abuja, shine muka biyo tanan, can gida muka fara zuwa bamu sami kowa  a ciki ba,kun bar ko ina abud'e, hakan ne yasa naji a jiki na ba lafiya ba,  shine nakira yayanku sadeeq awaya.

shine ya shaidamin "bakida lafiya ne ya kawo ki asibiti".

Nace "mai wani asbiti?".

"Asbitin Dande". yabani amsa  daga haka muka yi sallama na kashe wayar.

Sanda mukazo  hajiya Inna ke bani labarin abinda yafaru tana kuka, gaskiya sadeeq bai kyauta ba,

Momy tace "Na kira sa a waya nayi  masa kaca-kaca, kuma nakira Daddyn ku a waya, na fad'a masa, ya ce "muzau na anan Danden  nanda kwana 2 zaizo".

Ina 'Ka'ka lo hawaye  nacire hajabin jikina, nace "Momy kalla kigani fa wallahi babu abinda nayi  masa yayi min wannan dukan kuma". Yace "kad'an yayi min".

Salati Momy keyi tana tafa han-naye "yanzu sadeeq ne yayi miki haka?". Momy ta fad'a tana ri'ke ha'bar ta,

  gyad'a kaina nayi alamar eh,

tace "kiyi ha'kuri Daddyn ku ze zo nan da kwana biyu insha Allah,zai d'auki mummunan mataki yanda koda kud'i a kace sadeeq ya dake ki baze dake kiba".

Khadija da tunda ta shigo ta aje kular hannun ta, ta sami gefan gado na ta zauna, sai alokacin tace min " sannu Siddi'ka yajikin naki  da sauki dai ko?".

"Babu laifi dai zance amma wallahi na daku gurin wancen ba'kin mugun". nace mata,

"ina ke miki ciwo yanxu to?". Khadija ta kuma tambaya na,

Nace "Babu sai d'an abinda baza'a rasa ba".

"Alhamdu lillah" momy tace

yayin da  Umar yace "aunty Siddi'ka yajikin naki?".

"Dasuki" itace amsar dana basa,

ina mi'ka mai hannu alamar yazo kusa dani, ai kuwa ba musu yakama han-nun nawa, zaunar dashi a d'ayan gefen gadon nayi  suka sani a tsakiya,

dayi ke lokacin da nike bacci ruwan da ake 'kara min ya 'kare nurse d'in tazo ta cire min.

zubamin abincin Khadija tayi, tana fad'in "sister Siddi'ka daure dan Allah kici wannan babu yawa". Tamiya ce fara da mai da yaji

nace "na'koshi"

da 'kyar Momy ta lal-la-'bani naci abin cin d'an kad'an, na ture kwanan

nace "nifa na  'koshi Umar zo kacinye sauran".

Sai alokacin na lura babu Inna, "ina Inna wai?". na tambaya ina kallon Khadija,

takoma gida nasaka driver ya kaita nace "zan zauna dake har sanda zasu sallame mu". A cewar Momy

"to Momy muko ma gida mana na warke". Nafada ina sauka daka kan gadon kamani khadija tai tana fad'in "wannan wani irin ciwo ne Siddi'ka?,🤔
Koda yike kedaman haka kike bakyason asbiti".

"haba khadija ai kwata kwata natsani asbiti wallahi inba dole ba me mutum zaiyi" nabata amsa da haka

Nace "momy kira driver d'in Allah da gaske nike na warke".

Momy tace "bari a fara kiran likita idan tace zamu iya tafiya gida sai subaki  sallama".

dariya ce taka mani sosai nike 'kyal-'kya-tawa,

"Lafiyan ki kuwa Siddi'ka".Momy ta tamba yeni,

nace "wallahi momy kece ki ka bani dariya, baki karewa asibitin kallo bane halan to wannan asbitin da ki ke gani ba a sallamar mutum,
idan aka kawo mutum yaji  sau'ki ka wai tafiya zeyi. Idan kaga dama ne ma sai kace musu zaka tafi, basa saida magani wasu magunan kirki, kuma basa   wani rubuta maka koda zaka siya wani gurin idan su basu da shi, idan ma sun rubata to abu 2 ne kawai fanadol sai farasitamol".🤣na'kara sa fad'a  ina 'kara 'kyal-'kyala dariya

Na cigaba da cewa "nifa momy wallahi a gani na duk basu san aikin su ba, gwara gwara ma Aliya wannan tad'an I ya aikin, itace ma tasamin ruwa, idan fa aka kawo mutum bata nan sunan shi sorry ba'kara min ja-gwal-gwalo mutum ze sha ba".

sosai khadija ke dariya tace "ai ni ban zata ma asbiti bane domin sam baya kama da asbiti".

"'kwarai ma kuwa". Nabata amsa

Nace "kefa da a ka kawo ni wata a ka sauke a kan gadon a ka d'ora ni, nason don sunga yah sadeeq ne duk sanda ya kawo ni gado suke bani".

cikin mamaki momy tace "wata fa ki ka ce aka sauke".

"eh mana Momy" nabata amsa

"to ina suka kaita?". Momy tayi tambayar,

Nace "wallahi Momy ban sani ba lokacin ina fama da kaina".

cikin hanzari momy ta fara lalu bar jakarta tana fad'in "da gaskiyar ki Siddi'ka bari na kira driver yazo ya kaimu gida kamin kema a sauke mana ke, tunda sadeeq d'in ya tafi".

Ina dariya nace "hhhhmmmmmmm Momy da zamu shekara anan babu wanda ze sauke ni".

"saboda me? Yaya ko?". Khadija ta tamba yeni tana kallon idona

  Nace " eh, nifa mutane har mamaki suke bani yadda naga suna tsoran yah sadeeq kamar wani mala'ika".

Momy tace "nidai duk da haka gwara mu koma gida, ko wani asbitin na kudi a canza miki ban yarda da wannan ba za a iya bawa mutum maganin da bashi yadace ba".

Nace "momy nifa na  warke babu wani asbitin da zan sake koma wa".

'Dau kar wayar ta tayi ta latsa nombar  Idi driver, bugu d'aya ya d'auki kiran
kamar tana gabansa cikin ladabi yace "Hajiya na kawo Inna tun d'azun".

Tace "yayi kyau muma kazo ka d'auke mu ta sami sau'ki mara lafiyar".

Yace "to Hajiya".
sannan takatse kiran

Ba a fi 15 minutes ba saiga Idi driver yazo

dayake d'azun har dashi aka zo yasan asbitin har d'akin da aka kwantar dani ya shigo,

ya kwashi  tarka cen da khadija tazo dasu yayi gaba,

Sannan mumu muka fito, da Aliya muka ci karo A bakin fita asbitin tana Murmushi tace "mara lafi sauki yasamu kenan".

Nace "eh". Tace "to bazaku sai magani bane?".

"muna da irinsu dayawa agida" nace mata

"to shekenan Allah ya'kara sau'ki" ta fad'a yayin da takai duban ta ga Momy tace "Hajiya ya me jiki?".

Momy tace "da sau'ki". Daga haka muka mata sallama muka futo cikin asbitin, muka shiga cikin mota Idi driver ya hau titi

umar ne ke bamu labarin ban dariya a mota sai 'kyal-'kyala dariya muke yi kamar wasu za-rarru Momy dai saidai tayi  Murmushi idan taji ya fad'i abin dariya,

yanxu ma wani labarin bafullatani yake bamu

  Yace " wai wani ba fullata ni ne, ya siyo lemu, shine aka samai lemun aleda, sai yasa ka lemun a bayan keken shi koda ya fara tafiya a kan  kwalta, sai ledar lemun ta 'bule,  lemu d'aya yafad'i a kan kwalta, koda ba fullata ni yaga abinda ke faruwa lemun sa ya fad'i kan kwalta, amma se gudu yake yi, sai ya sauka a kan keken yatsa ya d'auko sauran lemun da suka rage a cikin ledar, ya watsar kan titi", yace "a kin banza a she ku kuna ma tafiya kuka bani wahala,  to muhad'u a gida". 🤣

Comment
      Shear
           Vote


    NI DA YAYA SADEEQ
                     

love story 2021 typing free book_

Story & Writer by
Siddiqahtul khair Y Faru
            (S beauty ✍️)
                
         Page 04

بسم الله الرحمن الرحيم
        
________Sosai muke dariya Khadija harda rike ciki, ni kuwa ba a magana don har tsalle nikeyi, a haka muka iso gida cikin farin ciki da nishad'i na manta da wani yah sadeeq saboda ganin su khadija

"Inna Inna". Na shiga ina 'kwala mata kira buta ce a han-nun ta da alamar ban d'aki zata, mama ki ne ya bay-yana 'kara ra a kan fiskar Inna,

rungume ta nayi ina fad'in ya dai tsohu wa ko baki murna da gani na bane, "ja ira". Inna tace tana jan dogon hanci na "banyi murna daganin kiba zaki ce nida nafi kowa san kisa mu lafiya, mamaki ni keyi saboda sanda naba roki baki san wake a kanki ba".

dariya nayi nace  "yo Inna ikon Allah ai ya wuce gaban komi".

"haka ne Siddi'ka ya jikin" Inna tace min Nace "jiki yayi sauki wallahi".

Inna tace "haka akeso wancen mugun kuma Allah ze saka miki kinji".

"To". Nace yayin da nike nufar cikin falo, ina shiga na zauna a kan kujera ina maida numfashi, kamar wacce tayi gudu saboda al'ada tace,

can sega khadija tashi go

"ke haka ake tarban baki?". tace min

"ina ba'kin suke?". na tambaye ta

"gamu" tanu na kanta, duka nakai mata sannan nace "to ki godewa Allah domin na kar-rama ku".

"A hakan". Khadija
tace min "eh". Nace mata

"bakida kirki Siddi'ka". khadija tafad'a tana zama kan kuje rar danike kai, nace "danayi me?".

Tace "bakisan me kikai ba ko"

nace "eh man". "shike nan ya wuce tunda kin manta".Ta fad'a tana share zancen,

ta'be baki nai nace "kinsan wani abu khadija?".

"A a". tace min na d'ora da cewa "wallahi yaya sadeeq bedaki banza ba zan rama bashi yaci, domin ni ba kanwar lasa bace".

Mi'kewa Khadija tayi alamar razana tana dafa kirjin ta, "zakiye me". Ta kuma tambaya ta. "ramawa". Nace mata

Tace "ke kuwa ta  yaya". Nace "kedai kitsa ya kiyi kallon ikon Allah".

da ido ta bini da kollo irin bakida hankali yarinya

Nace "kinamin kallon banida han kali ko to zan tab-batar miki da a cikin hay-yaci na nike amma tabbas yaya be daki bulus ba".

"hhhhm". tace tana cire gyalen ta, ta ajiye a han-nun kujera

Umar ne yashigo bakin sa da sweet yana tsotsa, la Umar zo kasam min". Na fad'a ina mi'ka mai hannu na, yace "za kisha ne?".

Nace masa "eh". Yace "nakawo miki naki, bari naje na  d'auko miki yana d'akin Inna".

Nace "to"

"nima katawo min dashi". Kadija tafad'a

beda d'eba saiga shi yakawo mana, nan ya zauna mukai ta shirme daman idan muka had'u a guri babu dama

Ana idar da sallar magriba ina sula lewa nabar gidan 'yar kasuwa nanu fa ina tafe ina gad'a ni kad'ai, a can na iske kawata Ladiyo, kaf kauyen Dande banida kawa sai Ladiyo saboda nafi san a kullum nice shugaba, bana son raini ko kad'an sauran duk nayi fad'a dasu saboda halin mu be zo d'aya ba, itama Ladiyo tana da hakuri ne kuma kome zan mata batayin fushi

Ladiyo nakwala mata kira daka nesa saida nasake kiran ta, ta na waige-waige tajuyo inda nike baki washe ta nufo ni, tafawa mukai alamun munji dad'in ganin juna

"Ai nazaci bazaki futo ba". Ladiyo tace min".

"Saboda me". Nace mata

Tace "saboda abinda yayan ki yace d'azun wallahi na tsorata bazan 'kara zuwa gidan kuba". Wani dogon tsaki naja mastssttt

Nace  "kefa sakarya ce bakida wayau, yo  saiki yarda da maganar sa, shi ba mala'ika ba ba kowa ba, abinda ma yasa baki ganni da wuri ba banida lafiya ne saida aka kaini asbitin bakin gari".

Ladiyo tace "Siddi'ka baki da lafiya fa kika ce" d'aga mata kai nayi alamar eh

"meke damunki nidai banga alamar rashin lafiya atare dake ba". Tace min

"Ke wallahi kuwa". Nace mata "yah sadeeq ne yaimin dukan mutuwa saida akai min 'karin ruwa". Ido tazoro waje tana dafe kirjin ta tace  "dukan mutuwa fa kika ce".

Tsaki nayi nace "dube ta kamar ita a kaima dukan duk ta firgice". Tace "yo  dole na firgi ce, d'azu fa da yana min magana wallahi ba'kara min tsoro naji ba, saboda dana bar gidan ku kafin inkai gidan mu nayi fitsari gurin sau uku, kuma kinsan d'an Sanda ne, mugunta babu wacce be iya ba domin rannan tsallan kwad'o naga yasa wasu yara a layin ku zanzo gurin ki, zuwan da banyi ba kenan".  duk Ladiyo ce tayi wannan bayanin

ta'be baki nayi sannan nace "hhhhmm kinsan be daki banza ba ko domin wallahi bashi yaci abinda ma yasa nafito kenan neman mafita domin yau ba tsoka na zanyi ba".

Tace "ai kuwa naji dad'in ganin ki domin bakiga yadda su Mariya da Harira suke tsokanata ba wai inyi magana suyi min dukan tsiya tunda bakyanan".

"Me kika cemusu". na tambayeta

"babu komi". Tace min

kwafa nayi sannan nace "bari na gama da yah sadeeq sai na juyo kansu".

"Yanzu nidai fad'a min me zanmai na huce". Na kuma tambayar ta

Shiru Ladiyo tayi  a lamun tana nazari can tacemin "a dake dai baze dakun miki ba saidai muyi masa mugun ta dai-dai da dukan daya miki".

"mugun ta kuma?" nace mata

"eh". tacemin "kawo kun- nen ki kiji yadda zamuyi".

A kunne tarad'a mun aikuwa naji dad'in shawar ta domin nasaki raina tunda nasamu mafita, nayi tsokana iya tsokana se gurin tara na koma gida, a d'akin Inna nasa
Showing 3001 words to 6000 words out of 51717 words