Na sauko kasa na tarar da duka 'yan gidan kowa yana nan harda Aunty Bilkisu da yaranta guda biyu Samahir da Shakran, Khadija da Umar ga Momy sai Jiddah da ke ta faman danna waya ko me take danna wa? oho ahankali na 'karasa sau kowa daka kan benan gurin Momy naje na rungume ta nace "Momy ya gajiyar hanya". Ina mai hawa kan cinyar ta na zauma
Tace "Siddi'ka rigima ni ban san yaushe zaki girma ba saboda wani abun idan kika yi ko Umar auta ba zaiyi ba".
Momy nidai naji saboda bazan ta'ba girma da hawa cinya ba".
"Sarkin san jiki" Aunty Bilkisu ce tafadi hakan
"La Aunty Balki bari inzo mu gaisa".
"Wai bana hana ki cemin Balki ba suna na bil'kees". Ta fad'a tana gyara sunan mu ka kwashe mata da dariya
Dai dai nan Ummi ta sauko muka dasa firan da ita Samaheer ce kan cinya ta ina yi mata wasa tana 'kyal-'kyala daria
Suwaiba mai aikin gidan ce ta shigo tace "Hajiya na kam mala yana kan dinning".
"to" Momy tace sannan ta kallo mu
"Oya kutashi muje muci abinci dan nasan kowa anan yana jin yunwa".
Kamar jira muke duk muka mi'ke muka nufi dinning kowa ya zauna muna ci muna d'an ta'ba fira taliya ce sai faten dankin turawa da yaji hanta sai farfesun naman kaza mai yaji, babu laifi Suwaiba ta iya girki dan idan Daddy baya nan ita take yin duk wani abu da za aci ko a sha, sa'banin idan yana gida Momy ke girka wa tace mu zo mu taya ta
bayan mun gama cin abinci muka dawo falo muka 'kara dasa sabuwar fira har aka kira sallar isha'i duk da Jiddih tunda na sauko magana bai had'ani da ita ba saboda ita ta nada jin kai ga san nuna ita wata ce ni kuwa ba zan d'auki iskanci ba dama ba shiri nike da ita ba saboda abu kad'an ke had'a mu mu fara dambe kowa bai san raini
NI DA YAYA SADEEQ
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Chapter 11
____Bayan mun idar da Sallar isha'i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho,
_yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani_
_Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya sai mijin_ _yace "almajiri kawo kwanon ka". Sai amarya ta leko ta amsa, ta zuba masa abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tam bayesa meye dalilin kukan nasa "ko abincin ne ba zai isheshi ba?". Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace "to maye kake ma kuka?". Budar bakin Almajiri sai yace "shi ba komai ya sashi wannan kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawa wan mata kafin lokacin su yai_
" Idan ke/kaine ya zaki/ka yi", haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka muhawara suna shirme
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwan ce a kan gadon farook yana cikin Instagram sai kallon hotuna yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yarinya, acikin zuciyar sa yace "daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata 'karamar yarinya ba domin zata iya kaiwa 25 years old da haihuwa". Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*
"Wow" ya fada afili Suna mai dadi *Zuby* haka yaita maimaita wa bata da wani kyau a fuska kuma bawani haske gareta ba amma dagani ta 'kara daman da yake sa hasken fata, 'kirjin ta cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
*Abuja*
Ba muyi wata dinner ba kasan cewar bamu dade da cin abincin ba shayi Momy tasa Suwaiba ta hado mana yaji ni'inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu larabawa 😂
Bayan mun gama kowa ya watse amma nikam sarkin tsoro d'akin Ummi nayi tana 'ko'karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min "sisi yadai". "Anan zan kwana" na fad'a yayin da nike shigowa ciki, ta maida kofar ta rufe
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsaka nina da Jiddah babu jituwa zan iya cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri,
Yau kimanin kwana bakwai kenan da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har sun koma makaranta
Muna falo nida Momy a zaune sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo tana kokarin hada abincin rana kafin su Khadija su dawo,
"dauko min waya ta a bedroom dina" cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi
Bayan na dawo nace "Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing". "Kawo mugani waye ya kirani" ta amsa tana shafa screen d'in wayar sannan ta kara a kunne
"Wa Alaikumussalam". shi ne abinda naji Momy tace kafin tace "lafiya lau".
Ta kara da cewa "wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato kasan dai yanzu ba kamar da bane kanada nauyi a kanka amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka".
Cikin fushi Momy tace "bazan sau rare ka ba Sadeeq baka da abinda zaka fada min na yadda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai".
Tana gama fadar haka ta kashe wayar
Jim kad'an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na gane yaya Mubarak ne d'an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne da zama amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi kana tace
"bani ruwa mana mara sanyi nasha". "To" nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta kammala wayan
NI DA YAYA SADEEQ
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Chapter 12
____Washe gari da misalin 'karfe 11am na rana a lokacin Su Khadija suna makaranta, Momy ma ta fita ma'kota gidan wata 'kawarta Hajiya Nafisa, amma tace ba zata dad'e ba, zaune nike ni kad'ai a falo kan kujera ina kallon TV
Ya Sadeeq ne ya shigo bakin sa d'auke da sallama koda yaga ni ce zaune a falon sai ya gimtse bai 'karasa sallamar ba ya d'aure fuska kamar bai ta'ba dariya ba, ni ma nayi kamar ban ganshi ba, tsawa ya daka min "dan ubanki baki iya gaisuwa bane ko nan d'in gidan uban ki ne? Ko da yike shima ubanki' tarbiyar bata ishe sa ba bare kuma kema ya baki".
Inajin zafin gorin da Sadeeq yake mini har cikin raina a lokuta da dama
ya cigaba da cewa "idan ba mummunar 'kaddara ba mai zanyi dake kucaka ki kalle ki, ki kalle ni, kin tafka babban kuskure da kika yarda Daddy ya hada auren nan zan shayar dake madarar azaba gida na zai zame miki tamkar kabari ke koda suna na ki kaji an ambata sai gaban ki yayi mummunan fad'uwa saboda bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, ki fara tunanin yadda zaki rubuta littafi mai suna *NIDA YAYA SADEEQ* saboda irin zaman da zakiyi a cikin gida na ya ciki ki rubuta".
Duka wannan maganar da Sadeeq yayi kaina a 'katsa wasu hawaye masu zafi suna gan garo mini, narasa mai nayi wa Sadeeq da har ya tsane ni haka? Ban ta' ba tunanin tsanar da yake ce wa yayi mini ta kai har haka ba,
Ban tanka masa ba illa mi'kewa da nayi na nufi hanyar sama na fara taka steps kenan ya da katar dani ta hanyar fadin "na tsane ki Siddi'ka na tsane ki, kuma bazan taba sonki ba a duk sanda ki kaji nace ina sonki to kada ki ta'ba yadda dani saboda yaudarar ki zanyi ba gaskiya bane". 😭
Hawaye masu 'kuna suka cigaba da gangaro min a haka na 'karasa haura steps din, Suwaiba da ke faman dafa abinci a kitchen taji duk abinda ya faru tsakani na da Sadeeq
'Dakina na shiga na fad'a kan gado, hawaye mai zafi yana zuba daga ido na, ni da kaina ina jin tausayin kaina saboda a sani na da yaya Sadeeq bai ta'ba cewa zaiyi baiyi ba duk abinda yace zaiyi to sai ya aikata sa
A cikin kukan na d'aga hannaye na sama na ce "ya Allah ka bayyana mahaifiya ta a duk inda take a fadin duniyar nan, ya Allah kasa tana a raye saboda inaso na rayuwa tare da ita, ya Allah kada kabama wani bawan ka sa'ar cutar da ita".
Mama. Na fad'a haka yayin da na d'aga kaina sama ina kalla, "bansan maye dalilin ki na cewa ko bayan babu ranki a daura wa 'yarki aure da Sadeeq ba, nayi alkawarin ni Siddi'ka zan zauna da Sadeeq koda kuwa hakan na nufin zai zama ajali na ha'k'kin ki ne nayi miki biyayya a sanda kike a raye da kuma abinda kika bani umarnin sa koda bayan ranki, Mama ta ina sonki". Na 'kare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya
Allah sarki Siddi'ka ni kaina ta bani tausayi ban san sanda na saki waya ta tafad'i a kasa ba saboda ido na ya cika da hawayen 😭 tausayin halin da take ciki da 'kyar na samu na daidai ta kaina na d'auki waya ta na fita daga d'akin naja kofar na rufe
Momy ce zaune ita da Sadeeq a falon 'kasa, sai zazzaga masifa takeyi "Sadeeq kabi duniya a hankali ko ta d'aga ka zata aje ka, Wallahi Sadeeq ina guje maka ranar da zakayi ladama amma kuma ladamar zata kasan ce da ita gwamma babu saboda ka makaro, ka kasa d'aukar kaddarar ka a yadda tazo maka".
Shi dai Sadeeq jin Momy kawai ya keyi amma baiga wata ranar ladamar da zata zo mai ba kuma ma ladamar ba akan kowa ba sai akan Siddi'ka yaji takaicin kalaman Momy, saboda har cikin ransa ya ke jin kiyayyar Siddi'ka
tace "dama akan maganar makarantar Siddi'ka ne yasa nace kazo tunda kai ba kayi hankalin haka ba kasan dai an koma hutu, so nike ka kaita makarantar su Khadija saboda akwai koyar wa sosai kuma kaga tana da saurin d'aukar abu bazata sha wuya ba".
Yana sosa 'keyar sa yace "Momy gaskiya ni boarding school zan kaita acan katsina nama gama komai yanzu haka ranar lahadi zan kaita".
Momy bataji dad'in abinda Sadeeq ya aikata ba tare da ya nemi shawar ta kona Daddy ba saboda haka tayi mai fad'a sosai kuma tace "bata yadda ya kai Siddi'ka boarding ba".
da yake Sadeeq ya iya dad'in baki kamar d'an siya sa yasan kalaman da zai fad'a ayi saurin yarda dashi, nan take ya siye Momy da da-d'a-d'an kalamai har ta amince masa
A zahiri Sadeeq 'karya ya keyi saboda bai yi mata register ba dama yana da burin yin hakan saboda bai son ya kaita jeka kadawo yasan su Momy zasu takura masa amma boarding sai idan anyi hutu tazo, ko babu komai zai samu sau'kin abun
Bugu da kari yana san ya shigo da batun auren sa da Zuby nan bada jimawa ba, saboda a halin yanzu soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin su sun aminta da junan su har sunyi alkawarin aure duk da basu taba ganin juba ba yau Sadeeq zaije ganin ta saboda itama anan garin Abujan take, saboda hud'uwar da zaiyi da masoyiyar sa ne 'karfin zuwan nasa Abujan domin yana matukar 'kaunar Zuby kuma yana da muradin ganin ta.
Momy ce ta katse shurun da cewa "kuma aji nawa za a sata?".
"Momy yadan ganta da yadda suka gwada ta kinsan yarinyar kwata kwata ba tada 'kwa-'kwalwa yanda kika san dusa haka kanta yake Allah dai yasa ko JS1 ne su d'auke ta".
"Js1 fa kace Sadeeq! Ina laifin 2 idan 3 bai samu ba, to ban lamun ce ba ban yarda ba kayi duk yadda za kayi ta gama prmry
School fa, kai kan ka shaida ne akan makaranta da ta gama, kuma kada na 'kara jin kace bata da 'kwa-'kwalwa zan sa'ba maka".
"Uhm" dai Sadeeq yace wa momy
Daga haka ya mi'ke "Momy ni zan fita a kwai wani aiki da zanyi zuwa anjima zan dawo zan kwana biyu anan kafin na koma ".
_Ya Allah ina rokonka da dukkan kyawawan sunayen ka ka kiyaye duk wani musulmi daka shiga mawuyacin hali kabamu lfy me amfani kasanya mana haquri da juria ya Allah ka kwantar mana da hankulanmu ya Allah kada kabamu ikon butulcemaka koda ka jarabcemu 🙏_
Chapter 13
_____A gaggau ce yayi faking motar sa ya fito ya shiga cikin gidan yayi sa'a babu kowa a falon sai TV da aka bar sa a kunne yana 'kira'ar alQur'ani mai girma, darect sama ya haura bai zarce ko ina ba sai d'akin sa, yana shiga ya aje wayo yinsa ya cire a gogan hannun sa sannan ya fad'a bayi bai wani d'auki lakaci ba ya fito d'aure da towel a 'kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa gaban madubi ya zauna mayuka ne kala kala da tura ruka masu 'kamshi da tsada ya shafa wannan ya mutstsuka wancen saida yabi yagama shafa ko wanne, sannan ya fesa body spray mai sanyin 'kamshi wata dakakkiyar shadda fara ya d'auko wanda aka 'kawata ta da ado da dinkin zamani hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe sannan ya d'auko agogon hannu da safa da ba'kin takalmi mai sheki, a tsana ke ya shirya abin sa tsaf sannan ya d'auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d'in tun kan ya 'karasa saukar yake jin hayaniyar su Momy bai so haka ba, saboda yanzu saita tsare shi da tambayar ina zashi "Momy". Sadeeq ya fad'a alokacin da ya 'kara so cikin falon gaba d'aya yaran gidan sun sha jinin jikin su saboda basu san ya zo ba Siddi'ka kuwa batayi mamakin ganin sa ba, bakin ko waccen su na rawa suka fara gai dasa ya amsa fuska ba yabo babu fallasa "yau she kadawo gidan sadeeq? Kuma ina zaka haka kaci wannan kwalliyar sai kace sabon ango". Yana sosa 'keya yace "wallahi Momy ban jima da shigowa ba bikin wani aboki na zani anyi daurin auren jiya yau ake dinner shine nike ta sauri kada nayi latti".
"A dawo lafiya".
Tun a hanyar sa ya kira gimbiyar ya shaida mata ya taho 'kara ta kuma kwatan ta mishi unguwar da misalin 'karfe 8:17 ya isa cikin unguwar daganin ta ma'aika ne a cikin ta saboda gidajen kusan duk iri d'aya ne kamar quarters haka unguwar take
Bayan yayi faking a gefen wani gida, ya d'auko wayar sa da ke ajiye a gefen sa yad'an shafa screen d'in sai ga number tafito da suna Baby a jiki call ya danna sai da ta fara ringing sannan ya kara a kunne
Ringing biyu ta d'auka ajiyar zuciya ya sauke yace "Baby na" daga can 'bangaren cikin shagwaba tace "my heart kazo ne?".
Ce wa yayi "akasi aka samu Baby na bayan na gama waya dake sai ga kira da ga office din mu wai ana son gani na to babu yadda na iya kin san aikin gwaumnati shine na juya a kalar tafiyar hanzu haka ina hanya ban isa ba ha'kuri na kira na baki".
Zuby da ta gama shiryawa, zuwan Sadeeq d'in kawai take jira, batasan sanda kwalla ta fara zubo mata ba cikin shagwa'ba take fad'in "amma my kasan dai bazan ji dad'i ba wallahi har Abbah na sanar masa kuma yana gida inason ka gaisa da shi ga Momy da tun sanda ka shaida min zaka zo na fad'a mata tasa aka shirya maka abin ci yanzu mai kake so na ce musu?". ta kara sa maganar tana fashe wa da kukun shagwa'ba
Tun Sadeeq yana dariya ciki ciki har saida ta fito fili saboda yadda Zuby ke shagwaba gunin ban dariya ga kuma kasala da ya rasa ta maye ta saukar masa duk a lokaci daya
"Haba my wai dariya naba ka?". Niyar fashe wa da wani kukan take yi, yayi saurin cewa "gani a 'kofar gidan ku kisa mai gadi ya bud'emin get ko ba shine mai ba'kin get ba?".
Shuru tayi saboda bata yadda da abinda yace ba
Jin shurun yayi yawa Sadeeq yace "ko in koma ne?".
"Wai da gaske My kana 'kofar gidan mu?".
"Na ta'ba yi miki 'karya ne?".
"A a". Ta bashi amsa
"to kisa abud'e min get".
Ihu ta saka 'kamar 'karamar yarinya ta cilla wayar kan gado
SADEEQ da kallo yabi screen din wayar yana mamakin Zuby d'in wani lokaci idan tayi abu saita koma kamar Baby amma duk da haka tana matu'kar burge sa saboda son ta a kullum 'kara dad'uwa yake yi acikin zuciyar sa
A yanzu haka yanajin idan ba ita bazai iya rayuwa da wata 'ya mace a matsayin matar sa ba
Mai gadi ne ya wangale get d'in Sadeeq ya sulala da motar sa ciki kana ya nemi guri yayi faking
Bai fito daka cikin motar ba wayar sa ta hau 'kara a kasalan ce ya d'auka ya kara a kunne
Daga d'ayan 'ban garen tace "My ga Rahmatu nan yar aki zata kaika falon baki".
"Banga kowa ba ni".
"to baby ka fito daga cikin motar mana zaka gan ta".
Ta fad'a tana 'kara gyara tsayiwar ta a jikin balakona saboda tun sanda Sadeeq ya shigo Zuby ke le'ken sa har kawo yanzu da take waya da shi tsaye take ko motsin kirki bata yi sai Murmushi da take yi zuwa zuwa mai wuyan fassaruwa
Da ya bud'e murfin motar saida ya d'auki 10 seconds sannan ya fito da 'kafar sa
Showing 18001 words to 21000 words out of 51717 words

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
𝑫𝒂 𝒃𝒂𝒛𝒂𝒓 𝒌𝒖 𝒏𝒊𝒌𝒆 𝒓𝒂𝒘𝒂 𝒎𝒐𝒔𝒐𝒚𝒂 𝒏𝒂💃 𝒊 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒚𝒐𝒖 𝒂𝒍𝒍
NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18