'kwal-lara 'kara kenan Khadija tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana 'kyal-'kyala dariya

Tace "nad'auka ked'in jaruma ce a she ba haka bane kamar ba kece shekaran jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan tsoran?".

"Kedalla malama sakeni nayi ihun neman agaji".Nace mata

Tana dariya tace "tsokanar ki fa nikeyi".

Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya,

koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen d'in na zauna, a cikin tukun yar naci, inaci ina santi saboda tayi mini dad'i kuma nayi mata irin  dahuwar da nikeso

Bayan na gama ci ne, na bud'e baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu lillah
Na mi'ke tsaye nayi  mi'ka

D'aki na na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan gadon nima na hau kusa da ita na kwanta ina jina wani iri kamar wani abu zai faru dani

Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma na'ki sai ma 'kara gyara kwan ciya ta da nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu'ar tashi daga bacci, na sauka a kan gadon, brush d'ina na d'auka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta d'auke da  murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, "au ashe kin tashi daman ke nazo tasa wallahi". Ta fad'a tana matsowa kusa da ni

"eh na tashi" nace mata "wai yanaga kina ta murmushi ne?".

Tace "ba dole ba Daddy fa yazo" shi yace "na taso ki saboda ya tambaye ni kina ina". Nace kina bacci".

"amma wannan karon yazo dawuri gaskiya" nafad"a ina ajiye makilin d'in hannu na

Tace "Eh". naji yana cewa Inna "da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi shiyasa yayi sammakon zuwa".

Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa "to bari nayi sallah" nace tare muka futo  ta nufi d'akin hajiya Inna

Ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa na zuba a bokitin wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na d'aura al'wala

Tawul na d'auro ajiki na, amma irin 'katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko d'an kwali haka na fito daga cikin bayin

Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, had'a ido mukayi, saida ya 'kare min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya fad'a afili, kana ya wuce ya shiga cikin falon

Saida ya wuce sannan nima na wuce d'aki na, wata doguwar rigar atamfa na ciro mai launin blue da ruwan hoda, baseline na sha a jiki na sannan na saka atamfar, na d'auki hijabi na nasaka na gabatar da sallar asuba

Bayan na idar na  nufi falon hajiya, ina jin gabana yana fad'uwa, narasa mai yisa amma tun jiya da Umar yace "Daddy zai zo" gaba na ke fad'uwa amman yanzu bugun zuciyar tawa yafi tsanan ta

Daure wa nayi, na shiga cikin falon baki na d'auke da  sallama, nasa mesu su duka harda yaya sadeeq d'in, suna karyawa, Daddy da Inna da yaya Sadeeq suna cin d'an wake,  Khadija Momy Umar. Kuma  waina suke ci

Daddy ne ya dube ni yace "wa'alaikum'ssalamu d'iya ta shigo ga wuri ki zauna, ya nuna min tsakanin sa da na yaya Sadeeq, na 'karasa  na zauna a tsakanin nasu

Sannan nace "ina kwana Daddy".

"Lafiya lau". Yace min "na same ku lafiya?".

"lafiya lau Daddy, ya hanya?". nace

"Al'hamdu lillah ". yace min, yana mi'ko min cokali yace "bimismilah
me sunan manya".

Ina lura da yanayin yah Sadeeq ya canza tun sanda na zauna, ya wani d'aure fiska sai mutsu mutsu yake yi, ina saka cokali na cikin kwanan yana cire nasa yami'ke tsaye, Daddy ne yakalle sa, yace masa "ya-ya ana cin abinci ka tashi". na 'koshi ne Daddy".

"dawo ka zauna sai mun cinye da kai".

Badan ran Sadeeq  yaso ba, haka ya dawo ya zauna ya maida cokalin sa, ina lura da yadda yake cin d'an waken kamar yana cin magani.

Misalin karfe goma 10:00am Daddy zaune a kan kujera Inna na kusa da shi Momy na 2 cter, ni da Khadija na zaune  a 'kasa kusa da Momy, yah Sadeeq kuma na gefen Daddy zaune a 'kasa kanshi a 'kasa yana danna wayar sa

Daddy yayi gyaran murya

Sannan yafara da cewa "da farko ina 'kara jad-dada godiya ta ga Allah ma d'aukakin sarki da yabin damar aiwatar da wannan 'kudirin nawa, tsira da aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta annabin mu Muhammad (S. A. W). Bakomai ne yasa na taraku anan ba, saidan ke Siddi'ka me sunan manya, ya fad'a yana kallo na, ina san yau d'in nan na  ai'watar da 'kudirin mahaifiyar ki akan ki,
Ina fatan zaki yima na biyayya, nasan baki da matsala, saboda mun isa dake ne zamuyi abinda mukesan yi yanzu, ina so kisan bakida Wanda ya fimu a kaf fad'in duniya, bazamu ta'ba cutar da ke ba".

Tun da Daddy ya fara magana gaba na ke fad'uwa, shin wani kalan 'kudiri ne wannan da har Daddy yace 'kudirin mahaifiya ta ne". Banida wannan amsar saboda haka naci gaba da sauraran abinda Daddy zai cigaba da fad'a

Daddy ya cigaba da cewa "naso ace sauran 'yan uwanku suna nanan, amma duk da haka kuma kun isa shaida,  kuma akwai abokai na guda biyu wa'inda tare dasu  zamu tafi lagos, nayi magana dasu, saboda muhimmancin abinda zan tattauna daku zasu biyo tanan".

Kallon Hajiya Inna yayi yace "Hajiya ko  akwai abinda ki ke san fad'a".

Tace "eh ina da abin fad'a". yace "to muna saura ranki".

Tace " 'Karami". Haka Inna ke kiran Daddy karami "ni abinda ke damu na yadda, Garba ya tsani Siddi'ka, kamar ba 'kanwar sa ba, Kaf 'kauyen nan babu wanda bai san da zaman 'kiyar-yar Siddi'ka a gun Garba ba, a gaban kowa nuna wa yake, a gida bai 'kyale ta ba, motsi kad'an tayi ya make ta".

Wani gwaran numfashi Daddy ya sauke, sannan ya fara yiwa Yaya Sadeeq fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sosai Daddy yayi wa yaya Sadeeq fata fata

Sannan ya maida kallan sa I zuwa ga Momy yace "Aisha fa kina da abin da zaki ce".

murmushi tayi irin  na su na manya tace "ai kai da Hajiya kun gama fad'an duk abinda zan fad'a, sai dai a'kara yiwa sadeeq fad'a a kuma ja mai kunne, sai muyi  musa fatan Allah yasa alkairi".

"Ameeen" Inna tace yayin da Daddy yace "alhamdu lillah".

Daddy yace "mai sunan manya matso nan kusa dani kinji". Jikina a sanya ye na matsa kusa na zauna a d'ayan bangaren da ke kallon yaya Sadeeq  sai ban kamin harara yake a sace
nayi kamar bansan yanayi ba

Dafa kaina Daddy yayi yace "Allah yayi miki albarka". "ameen". Nace

Sannan yaci gaba da cewa "𝚂𝚒𝚍𝚍𝚒'𝚔𝚊 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚢𝚊𝚞 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚂𝚊𝚍𝚎𝚎𝚚 𝚣𝚊𝚒 𝚝𝚊𝚜𝚑𝚒 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚣𝚊𝚒 𝚔𝚘𝚖𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒 𝚋𝚞𝚢𝚞, 𝚣𝚊𝚒 𝚍𝚞𝚗𝚐𝚊 𝚊𝚖𝚜𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚖𝚒𝚓𝚒𝚗 𝚔𝚒 𝚍𝚊 𝚔𝚞𝚖𝚊 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒".

duk da ban wani san maye *Aure* ba amma naji sam ba aimin adalci ba

a tare nida yah Sadeeq  muka mi'ke tsaye, duk kannin mu idan mu a waje alamar rashin fahim ta.

" Koma ku zauna" Daddy ya fad'a, jikin mu babu 'kwari haka muka koma muka zauna, Khadija ma dake zaune mama ki ne yacika ta shiko Umar ko ajikin sa Inna kuwa da momy daman sun san da batun

" 'Kwarai kuwa abinda kukaji nafad'a haka ne ba mafar ki kuke yiba, domin wannan shine burin 'kan wata Aminatu". 'Kwalla ce ta cika idonun sa yayin da ya kasa 'karasa maganar Handkerchief yaciro cikin aljihun sa yana share 'kwallar da ta zubo masa

Da irin murayan Wanda yake son yayi kuka, Daddy ya cigaba da cewa "auren ki da Sadeeq shine burin ta, bamu sani ba ko a raye take ko amace, kimanin shekaru goma sha biyu da wasu yan wattani akai kenan tun tana goyen ki". ya nuna ni "nasan kunsan komai ba sai na 'kara tada muku da zancen ba, saboda bana son na tada mana hankula".

tuni inna tafara shash-she 'kar kuka momy ce keta faman bata ha'kuri

Da 'kyar aka shawo kan Inna tayi shuru

Ba 'karya Dady yayi ba duka family an san labarin 'batar mahaifiya ta amma bamu san yadda al'amarin ya faru ba

Daddy yaci gaba da fad'in "Siddi'ka sai dai kiyi ha'kuri, naje  har gidan ku da 'kyar nasa mu ganin mahaifin ki, na je masa da batun auren ki, yace min shi babu ruwan sa  yama manta dake cikin 'ya 'yan sa  ba tun yauba ai ya fad'a mana ya bar mana ke, idan yanka ki zamu yi, muyi, shi baya da matsala babu ruwan sa". ya 'kara da cewa ai tun ranar da Amina  tabar gidan nan  na manta da duk wani abu daya sha feta yanzu haka abinda yasa bazan sa kar nuka su fidda min kaiba saboda baka sani ba, amma yanzu tunda kasani kada in'kara ganin ka akoafar gidana kai ba kai ba ko Siddi'ka d'iyata ce tazo sai nasa kar nuka suncin ye naman ta d'an ye, saboda haka Get out in my house".

  jiki na babu 'kwari Siddi'ka na fito daka gidan ku

Ban ta'ba jin tsanar mahai fina irin na yauba kuka nike sosai ina tir da halayen sa kowa a d'akin jikin sa yayi sanyi dady ne ke shafa min kai yana bani hakuri

"Siddi'ka ki cigaba da ha'kuri Allah zai miki canji da mafi alkairi, ki cigaba da kai kukan ki gurin Allah saboda shi Allah baya barin zalinci". Kuma kamar yadda nace "yau za a d'aura miki aure da sadeeq idan anyi sallar juma'a babu fashi".

SADEEQ ne zaiyi magana Daddy ya katse sa da fad'in "zan sa'ba maka sadeeq, Ko na tambaye ka ne?".

bazan iya musa wa su Daddy, amma shin maye aure nashi ga uku nake fad'i a zuciya ta, yayin da nike jin bugun zuciya ta yana dad'a 'karuwa


NI DA YAYA SADEEQ
                    
 

بسم الله الرحمن الرحيم
   
          Chapter 09

_______Na shiga uku ni Siddi'ka Yahyah D'an 'kwambo anya su Daddy suna 'kauna ta nasan kaf duniya babu wacce Sadeeq ya tsana kamar ni, amman wai yau ni ce zan zama matarshi

"Kutashi kutafi Allah yayi muku albarka".
Daddy ne ya fad'a haka

Sadeeq yariga ni tashi saboda ni jikina babu kuzari

"ji mana Sadeeq" Daddy yace "ka kira abokanan  ka na kusa a waya ka shaida musu".

Murya acan cikin ma'ko garo Sadeeq ya cewa Daddy "ba sai sun shaida ba". Yana gama fad'ar haka ya fice

A masal-lacin juma'an dake garin buruku aka d'aura auran *SADEEQ ALIYU MAI GORO* da amaryar sa *SIDDI'KA YAHYAH D'AN KWANBO* d'um bin jama'a sun shaida d'aurin auren duk da kasan cewar babu ango da abokanan sa, Daddy ne yayi wakil cin Siddi'ka, inda d'aya daga cikin abokan Daddy da suka hallar ci taran, mai suna Alhaji Imran yayi wakilcin Sadeeq, auren da aka d'aura abisa sadaki dubu tamanin, lakadan ba ajalan ba, yayin da Alhaji Imran ne ya biya sadakin

A kwai 'yan 'kauyen Dande da dama, dasu ka samu halar tar zuwa masal-lacin, saboda su gabatar da sallar juma'a da yawan su mamaki suke saboda kowa yasan tsamar dake tsaka nin Sadeeq da  Siddy amma wai yau ya zama mijin ta ko da shike daman ance idan zaka yi 'kiyayya kada ka tsanan ta haka ma soyayyar

Da haka taro ya watse koda Daddy ya dawo gida anne mi Sadeeq anra sa kuma an kira wayar sa a kashe

Siddi'ka kuwa tun sanda ta shiga d'aki take raira kuka, rarrashin duniya anyi mata amma ta'ki barin kukan kamar ma dad'a zuga ta suke yi, haka suka gaji da lal-lashin ta suka  zuba mata ido, saida Daddy yafa d'awa su Inna zai shigo dasu Alhaji Imran Sannan yaje ya shigo dasu, a falon Hajiya Inna suka zauna daman su Hajiya Inna sun girka shinkafa da miya Khadija ce keta hidama da ba'kin Daddy Sai da suka ci suka sha sannan Inna tazo suka gaisa

Suka yi mata Allah yasa alkairi anan Daddy yayi mata sallama yace su zasu wuce Abuja da a can jirgin su zai tashi izuwa lagos

"To bari na kira maka Aisha d'in ko". Inna ta fad'a tana 'ko'karin mi'ke wa

cikin sosa kai Daddy  yace "ai na sallame su suma nan bada jimawa ba zasu wuce" mamaki ne yakama Inna saboda ita dai bataga sanda 'karami yayi magana da Aisha ba

Hajiya Dady ya kira sunan ta "da mai sunan manya zasu tafi nayi maganar yar aikin za a nemu miki nanda kwana biyu".

"Wace yar aiki! 'karami duk yaran dake ci'kin Dande basu isa ba har sai an nemi wata, ai ko Ladiyo 'kawar Siddi'ka na yiwa iya-yen ta magana tunda yarinyar ta iya aiki, kuma ta ma girmi Siddi'ka d'in,
Nasan baza ta 'ki ba, sai ta dunga zuwa tana tayani d'an wanke wanke da shara tama dun ga d'ebe min kewar siddy d'in".

Inna ta cigaba da cewa "Idan wata yayi kana yima ta d'an ihsani".

"babu damuwa" Daddy yace yana mai ciro kud'i daga aljihun sa masu tarin yawa, 'yan dubu dubu ya mi'ka mata

" 'Karami kud'in wancen watan ma daka bani suna nan ban taba suba saboda duk abinda nike so akwai a gidan nan da ka bar shi kawai a gurin ka Allah yama albarka".

Hannun ta Daddy ya kamo yasa ka yan bandir d'in 1000 guda biyu "haba hajiya ki karba koda sadaka ne kinayi dasu  idan ki ka ga mai buka ta".

Godiya Inna tai ta kwara rowa 'Karami tanayi mai addu'ar Allah yatsare

"Ina mai sunan manyan take ne Hajiya?". Daddy ya tambaya

"ai tun sanda ka fita ta shiga d'aki tana rusa kuka mun gaji da lal-lashi ne muma".

"Wani d'akin?".

"na can karshe". Ta bashi amsa

Tashi yayi ya cewa abokan sa "minti biyar".

A kan gado ya same ni kwance nayi rufda ciki 

Siddi'ka Daddy ya kira suna na cikin sas-sanyar murya

Inaso kisan duk abinda ha'Kuri bai ba bawa ba a rayuwa rashin sa ma ba zai ba da ba, kuma wannan shine burin mahaifiyar ki tin sanda aka haife ki tace "idan Allah ya raya ki d'an ta Sadeeq shine mijin ki ko bayan baran ta mu cika burin ta, A halin yanzu bamu san awani hali Amina maman ki take ciki ba, zai iya yuyuwa tana nan a raye nesa damu, zai kuma iya yuyuwa Allah ya d'auki ranta, amma muna nan muna addu'a idan har Amina tana a raye Allah ya bayyana mana ita, nayi hakanne a yanzu saboda bani da tabbacin zan 'kara wasu shekarun a raye, nasan ko bayan babu raina na cikawa kanwa ta burin ta za tayi alfahari dani, kiyi mana biyayya amatsayin mu na iyayen ki bazamu taba cutar da ke ba zakiga ribar abun nan gaba".

Duk maganar da Daddy yayi na kasa d'ago kaina, Ko motsin kirki na kasa ina nan a yadda ya shigo yasa meni, jin shirun da nayi ne naji ajiki na ya fita daga d'akin, kaina na d'ago ina 'karewa d'akin kallo Bansan mai nike nazari ba amma inajin kamar raina zai fita

Umar ne yashigo hannun sa d'auke da kular abinci har kan gadon ya hau yace "aunty Siddy please kada kicemin a a don soyayyar da kikewa goggo Amina ki tashi kici abincin nan nasan dai kina mutu'kar santa kuma duk 'yar da aka ce tayi abu dan iya yen ta to indai tana son su za tayi".

Jin Umar ya ambaci mahaifiya ta na tashi zaune saboda babu 'yar da zata'ki mamar ta "mi 'komin kular". Nafad'a murya ta a dashe

Koda na bud'e shinkafa ce da miya har da nama a ciki, cokali nasa na fara cin abincin amma kwata kwata bemin dad'i ba ji nike  kamar ba asaka  magi aciki ba

"Umar wai haka abincin nan yake". Na tambaye sa

"mai yayi" yace min

"naga kan infara ci yana ta zuba 'kam shi yanzu kuma da nike ci wallahi ji nayi kamar inacin magani".

Kallo na yayi muka had'a ido dashi yace aunty siddy inaga bakin ki ne domin kowa ya yaba girkin nan yadda yake da kamshi haka yake da dad'i abaki ma".

"To iya magana". Nafad'a ina tura masa kular abincin

"Kaddai har kin 'koshi". Yace yana kallo na

"na 'koshi mana tashi kasa momin ruwa".

"To" yace ya fice daga d'akin, jim kad'an sai gashi da ruwa a cup

yace "Momy" tace "kiyi wanka yanzu gata nan zuwa".

"To". nace

dama akwai bayi a d'aki na amma tsabar neman rigama yasa bana shiga, kuma da sabo dan munriga munsa ba da bayin tsakar gida tun kafin  a maida mana gidan mu ginin zamani

Yaukam ciki na shiga wanda nike tsokanar ko sunan sa ma bana son inji ankira min

Ban wani dad'e ba na fito daka bayin kaya na tarar abakin gadon da alamar sababbi ne harda bra da fnt

Ina cikin mamaki sajga Khadija ta shigo fes da ita cikin wata tsaleliyar atamfa "cikin zolaya tace min amarsu har yanzu baki shirya ba Koda yake daman shirin amare ance yana da dad'e wa, sai kiyi kishir ya dan ke kad'ai muke jira".

a kwati na na nufa saboda na d'auko kayan da zan saka,

  da mamaki Khadija tace "Siddi'ka baga kayan ki nan ba akan gado". Momy tace "su zaki saka".

Hau shin kowa nake ji cikin masifa nace wa Khadija "naji to sai ki ban guri".

Sai da ta 'kyal-'kyale da dariya sannan tace "amarsu kada in 'bata miki rai naji ance ba'a san a 'bata ma amarya rai, musamman ranar d'aurin auren ta, idan ni baki bud'e min ba zaki bud'e ma yayana".

Khadija tagirme ni da 2 years nasan ba zata rasa sanin aure ba tunda ita abirni take kuma tana zuwa makaran ta, sa 'banin ni da nike yawan gyad'a

Tana fita na rufo 'kofar sai da na shirya tsaf sannan nafito sai 'kam shin turare ke tashi
Da alamar kan a kawo min kayan sai da aka fesamusu
Showing 12001 words to 15000 words out of 51717 words