mesu a nata fira da sallama na shiga,

Da ido kowa ke bina, "wai Siddi'ka ina ki ka jene haka, gurun muta ne biyar suka kawo 'ka ranki,  Aisha ke basu hakuri da d'an kud'i". Inna ce ke wannan maganar

cikin
in-ina nace "Inna daman naje....".

"Daman me" tace min

Nace "waye yakawo 'karata ban sani ba". ta'be baki nayi nace "wai haka momy ankawo Kara ta".

Momy tace "Hajiyan 'karya zata yi miki, wai Siddi'ka yaushe zaki girma ne kiyi hankali, kina girma kina 'Kara rashin wayau,  Allah ya shir yaki".

"Ameen" nace "ina abinci na?".

"yana kitchen umar" yace "nima banci abincin ba" nace "sai kin zo" to yayi d'auko mana muci me aka girka na bukata,

Yace "fatan doya ne Momy ta girka".

Nace "maza d'auko mana". munaci ina bashi labarin inda naje da kalar tsoka nar da nayi, sai cizon yatsa yake yi  yana fad'in wai meyi sa baki min magana ba, sanda zaki tafi, wallahi da dani za'ayi, da yanzu ba labari kike bani ba saidai ni na bada,

Nace "yo kaya'kuri bansan ai zaka ba na d'auka kai ma irin Khadija ne me tsoran tsiya". wa'ni Umar yafad'a yana nuna kansa Allah ya kyauta ina namiji intsaya tsoro sai kace mace".



Comment
         Shear
             Vote                    
love story 2021 typing free book_

Story & Writer by
Siddiqahtul khair Y Faru
            (S beauty ✍️)                

NI DA YAYA SADEEQ

Page 05

_________Bayan gama cin a bincin mu da Umar na mi'ke ina hamma alamar bacci nike ji,

Khadija ce ta kalle ni tace "ba dai bacci za kiyi ba". Nabata amasa da "eh kwanciya zanyi".

"Dawuri haka" ta tambaye ni

Da "eh". Na bata amsa

"yo in banda abinki khadija ai Allah kad'ai yasan inda Siddi'ka taje bayan fitar ta gida kinga ko dole ta kwanta da wuri". duk Inna ce ke wannan maganar, ta'be baki na nayi nace "Momy zan kwanta saida safe".

Wayarta ta kunna ta kalli a gogo 'karfe goma saura na dare, kallon Khadija Momy tayi tace "kitashi kibita dare yayi goma saura". Umar ma tashi yayi ze bimu amma Momy tace "bata yarda ba tare da ita zai kwana saboda ita batasan kwana ita kad'ai".

A kwai d'akin da idan sunzo suke sauka acikin sa, duk wani abun bu'kata Daddy ya zuba a ciki

saida safe muka 'kara yimu su Khadija ta rigani yin gaba, daka baya na bi bayan ta,

Jinayi kamar na taka 'kafar mutum dayike lungun d'akin a kwai duhu 'kauyen dande babu wuta, janna-reto muke kunnawa zuwa 'karfe goman dare a kashe, to yau yaya sadeeq be kunna ba,

ban tab-batar da 'kafar mutum bace a gurin nataka hakan yasa na 'kara d'ora kafata a kai na murza, 'yar 'kara naji anyi alamun mutum ne, koda na waiga inda nike tsammanin zan sami Khadija wayam babu ita ba alamar ta, zaro ido na nayi da kyau gabana ne yafad'i saka makon ba'kin mugun da nagani, yana wannan Murmushin nashi na mugunta,

A d'an tsorace nace "la yaya". Ban 'karasa maganar ba ta ma'kale,

Saka makon bige min baki da yayi, ya sha'ke min wuya,ya had'ani da jikin bango

Yana fad'in me hali be fasa halin sa gwara na kasheki kowa ya huta,

Da iya 'karfin sa yasha 'kemin wuyan ina son inyi ihun neman d'auki amma na kasa, cikin ikon Allah saiga Momy da Umar, sunzo wucewa hannun ta d'auke da hasken fitilar wayar ta, tana haskawa, mai zata gani wani 'kara ta saki saida wayar ta yafad'i a 'kasa

Inna da khadija rige-rigen fitowa suka yi saboda ihun Momy da suka ji,

Umar tuni ya das-kare a gurin, jikake tas tas 'karan marin da Momy ta wanke yaya sadeeq

Amma duk da haka ya'ki sakina don haka ta 'kara mai wani saida tayi mai mari biyar amma ko gezau, beyi ba dayike yah sadeeq namijin duniya ne, "to idan baza saketa ba sadeeq zan cireka cikin 'ya'ya na". Momy ta fad'i haka fiskar ta babu alamun wasa

jin wannan lafazin na Momy yasa Sadeeq yayi jifa dani ida nuwan sa jajur kamar Wanda yasha wani abun, huci yake yi sosai

Kasa nafadi shirim jikina babu 'kwari ina fitar da numfashin wahala Inna da Khadija takaici ya hanasu magana, hawaye ne ke gan-gan garowa a cikin Idanuwan Momy, ta kasa magana han-nuna ta kama muka wuce d'aki na, su Inna na biye da mu abaya

Kan gado ta d'orani, na kwanta yaraf kamar gawa, ruwan fridge me sanyi khadija ta d'ibo min ta d'aga kaina ta bani nasha ina maida numfashi,

Babu Wanda yatam bayi me ya had'amu, duk kuwa da cewa zuciyoyin su cije take da tamba yoyi, daga haka kowa ya tafi ma kwancin sa,

a raina sa'ka yadda zan wula'kan ta yaya sadeeq nikeyi, domin wallahi bashi yake ci wani mugun tsanar sa naji ya 'kara da d'uwa a zuciya ta,

da wannan tunanin bacci 'barawo ya sace ni

Kiran sallar asuban fari a kunne na akayi, banida nauyin bacci, tashi nayi na zauna gaba d'aya jikina ciwo yake min amma wuya na yafi min ciwo,

Tashi nayi tsaye ina mi'ka ko salati banyi ba, ba kuma dan ban iyaba saidan tsabar shagala, da wasa da yayi min yawa,

tsakar gida nafito babu kowa d'an Murmushi nayi saboda zanyi abinda zanyi babu wanda zai ganni a irin wannan lokacin ya Sadeeq ke fitowa yayi alwala, kamar yadda Ladiyo ta tsara min haka nayi, a binda kuwa Ladiyo tace min a kunne shine "na zuba masa karara aruwan alwalar sa, da na wanka, nayi na'am da wannan shawarar da tabani, saboda nasan tanan ne kawai zan iya ramawa,

sad'a-d'awa nayi 'bangaren sa inda yake ajiye butar sa na nufa, "Alhamdu lillah". na fad'a yayin da na hangi butar sa, a jiye a gurin, da hanzari na 'karasa gurin

d'aga rigata nayi na war-ware siketin jikina, na ciro 'kullun ledar karara da nasaka Ladiyo ta sato min na Umman ta da take saidawa

Murmushin mugunta nayi, yayin da na d'aga burar naji ta cije da ruwa, bud'e murfin butar nayi, na zuba sannan nasaka hannu na na kar kad'a ruwan

Yaya Sadeeq baya barin sai zaiyi anfani da abu yanema yana tanadar sa ne tun kamin lokacin amfanin sa yazo saboda bayason bata lokaci

A jiyar zuciya nayi nabaro lungun, a hankali nike tafiya kamar mara gaskiya, Inna na hango idon ta akaina 'kyar da buta a gaban ta, da alamar alwala ta gama, Murmushi nayi na'kara sa gaban ta nace "Inna kin fito kenan?".

"eh na fito, daga ina ki ke?".ta tamba yeni

"daka waje le'kawa nayi, alwala na fito sai yanayin garin ya bani sha'awa shine na le'ka waje" na fad'a mata haka kamar da gaske

"Amma mai yatada ki daga barci" Inna ta tamba yeni a karo na biyu,

wallahi Inna baccin ne ya'ki zuwa min sai naji an kira sallah shine nace "bari nayi sallar sai na kwanta".

Tace "to ya jikin naki?" nace Inna da d'an sau'ki amma na kasa bacci, dana rufe ido sai na dunga ganin kamar zai zo ya sha'keni". Saboda yace "saiya kasheni".

Inna na salati tace"yanzu Garban ne yace saiya kashe ki!?". Eh Inna shi fa ai ba 'karamin mugu bane". Na 'kara maganar ina yin hanyar ban d'aki,

Na bar Inna da mamaki

Bandaki nashiga nayo fitsari, na fito nazau na a kan kujera, nafara alwala kenan saiga Yaya Sadeeq nan, nayi kamar ban ganshi ba, na cigaba da yin Alwala ta, ta gaba na yazo ya wuce, bayan shi nabi da kallo ina Murmushi, a cikin zuciya ta nace "zaka bawa yan garin ku labari, zaka san kayi da 'yar halak".

bandaki yashiga yajima aciki, can saiga sa ya fito, a lokacin nagama Alwala ta amma ban tashi a gurin ba,

Tashi nayi na koma d'an nesa da inda ya tsugun na

Alwala yafara yi ganin ya manta beyi kus kuran baki ba naji sanyi a raina, d'aki na koma na tsaya a bakin hundo, ina kallon sa,

yana wanke fuska ne naga ya mike kamar wanda aka tsungula gabansa yakama yana murzawa🤣 bansan sanda daria ya kwace minba can kuma yafara kifta ido se yanzu yake tunani tabbas yaji ruwan wani iri lokacin dayeke shakar hanci, abinda yasa baiyi wani tunani ba yaga butar sa ce shi kad'ai babu wanda yake amfani da ita, sosai yake murza idonsa ati shawa na biyo baya haka yaita fama 💃 d'aya hannun rike da gaban sa yana murzawa 🤣

Dariya nike ina tsalle abin nema yasa mu sosai Yah Sadeeq yazama karamin mahau kaci gashi har an shiga masallaci amma shi ko alwalar be samu ya gama ba

Sosai abin ke damun sa musamman gabansa yafi sosa gurin, a haka Momy tafito ta same sa, watsi tayi dashi kamar bata ganshi ba, jin motsin da yayi ne yasa ya d'an bude idon sa, saboda yaga waye, wata a zaba ce ta 'kara shigar masa ido har saida ya saki 'yar 'kara, tsaki Momy taja tagama abinda za tayi nan tabar sa tanai masa kallon mahaukaci, 🤣

Khadija Khadija yah Sadeeq ne ke 'kwala mata kira, barci take yi, ganin yana kiran ta nayi saurin zuwa bakin gadon ina dukan ta,da magagin bacci a idon ta "lafiya?". Tace min 'yar dariya nayi nace "yah Sadeeq ke kiran ki". tashi tayi zaune tana zaro ido kamar ba me magagin bacci ba "yana ina?". tace min "tsakar gida". na bata amsa

Nace "amma fa kiyi a hankali don naga kamar yasamu ta'bin hankali"

jin yana 'kwala mata kira dakarfi yasa ta fad'uwar gaba babu shiri ta sakko daga kan godon, tayo waje, yadda taga yaya sadeeq d'in a tsakar gida ba 'kara mar kunya yabata ba, gani Yaya tafad'a sanda ta 'karasa gansa,

"d'auko bokiti a d'aki na ki zuba min ruwan wanka, ki kai min ban d'aki". Sadeeq ya fad'i haka.

Da "to" tabi shi kamar yadda ya umar ceta haka tayi, a binda khadija bata sani ba ina la'be lungun bayi tana aje ruwan nazuba mai karara nai fitowa ta, tsaye na ganta gurin tana cemai "yaya na kai maka ruwan".

"Kama hannu na to" yace mata, hannun na sa takama har bayi ta kaisa, sannan tafito

Idanun sa a rufe suke har yanzu cire jalla biyar jikin sa yayi, sannan ya laluba yaji babu sosan wanka, kiran sunan Khadija yafa rayi nikuwa daman ina kusa da bayin, khadija kuwa tayi alwala ta tafi d'aki sallah, "kawo min sabulu". Yace

daman Yah sadeeq bai wanka da so so ko kadan sai sabulu kawai, Murmushi nayi naje na dauko mai sabulu wanda na badeshi da zallan tarugun dana ga Inna ta daka sa ta shanya asama jiya,

hhhmmmm nace "ai wallahi tunda ka ta'bani sai kayi da 'ya, taka kujera nayi naje fa mai sabuln cikin bayi

Komawa gefe nayi na zauna inajin raina fes banida wata damuwa,

har gari yafara wayewa babu sadeeq babu labarin shi nikuma na'ki tashi domin ko sallah ma banyi ba

Ya sadeeq kuwa yazama abin tausayi cikin bayi yarasa wannan wani irin bala'i ne, shida yayi wanka domin yasa mu sau'ki amma sai a kasin haka, susar jikinsa yake iya 'karfin sa duk da idan yasosa yanajin wani mugun rad'ad'i a jinkin sa, amma bashi da wani zabin da yawuce susar,

har 7 am be fito ba Inna ce zata shiga bayin na kalle ta nace "Inna fa da mutum".

"Waye?" tace min "yah Sadiq ne" na bata amsa,

Inna tace "me yake yi agidan har yanzu da bai fita gurin aiki ba, naga da an idar da sallar asuba yake tafiya".

Nace "to Inna kika sani ko anyi musu canji ne kinsan ana canza su ai".

"haka ne" Inna tace min, d'an matsa wa nayi kusa da ita, sannan nace "Inna amma fa yau yah Sadeeq wallahi kamar mahaukaci, domin tun asuba yake abayin nan, kafin yashiga ya dad'e anan tsakar gida yanayin wasu a bubuwa masu kama da na mahaukata". Zaro ido inna tayi
na d'aga mata gora, nace idan baki wa yarda ba, Ki je tambayi Khadija ko Momy saboda dukan su sun ganshi a cikin yanayin,

♾️♾️♾️♾️♾️
Nagaji da typing atara gobe in Allah ya kaimu domin jin yadda za a kwashe tsakanin Sidda'ka da sadeeq kucigaba da bibiyata nikuma zancigaba da nishadantar daku
♾️♾️♾️♾️♾️
NI DA YAYA SADEEQ
                     

Chapter 06

بسم الله الرحمن الرحيم

_____Jin jina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar d'akin da Momy take, ta 'kwan 'kwasa musu kofa, ta d'an jima a bakin 'kofar, kafin Momy ta bud'e ta fito, "ina kwana hajiya". Momy ta gaisar da hajiya

cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta "ya ba'kun ta?".

"Lafiya lau". Momy ta bata amsa,

"to alhamdu lillah".
A cewar Inna

ta dora da cewa "kiya 'kuri na tashe ki kina tsaka da bacci".

"babu komai Inna" cewar Momy,

Inna ta cigaba da cewa "daman Garba ne wai tun asuba yake ban d'aki". Har yanzu bai fito ba, Siddi'ka tace "yau kamar bashi ba yana tayin wasu abu irin na taba'b-'bu" shine nace "bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya".

Momy tace "Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin magana".

Inna tace "Ha'kuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya kinga da ya idar da  sallar asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru".

"To". Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban 'dakin

Koda su Momy suka 'kara sa bakin bayin sunan shi Inna takira "Garba Garba". kamar babu kowa a ciki, saboda bai amsa ba, saida Momy tace "sadeeq wai lafiyar ka?".

Da wata iriyar  murya yace "wallahi Momy nima ban sani ba".

Tace "au daman kana jin Hajiya na kiran ka kayi shuru, saboda ka raina mutane, ai sai ka fito ka bawa mutane guri, saboda gari ya waye".

Yace "Momy bazan iya fitowa ba".

"saboda me?". Ta tambaya

Momy wlh yau Ban san me ke shirin faruwa dani ba, ko nayi gamo ne tun nafito sallar asuba na had'u da bala'i ko sallar ma banyi ba". 🤣

Salati suka hauyi Inna natafa hannu kace "baka yi sallah ba tom wai me kake yi a cikin bayin ne haka?". Cewar inna

Cikin jin zafin tambayar da Inna tayi mai sadeeq yace "Wai baki ji nace ina cikin bala'i bane, amma kike sake tamba ta".

Momy ce ta daka mai tsawa "rufe min baki anan gurin ko na ci maka mutun ci, kuma kafito kabawa mutane guri suna son shiga bayan gida".

Sadeeq yace "Amma Momy...".

Katse shi tayi da "ko baka ji abinda nace maka bane".

"naji". Ya fad'a a ta 'kaice,

d'an matsa wa suka yi nesa da bayin,

niku wa da tun tuni nike zaman jiran fitowar sa, da naji Momy tace "ya fito". Sai Na 'kara gyara zama na a kan kurer tsakar gida

Saida ya d'auki tsayin minti biyar kafin ya cire sakatar, ya bud'e 'kofar ya fito, babu ko riga a  jikin sa, sai d'an gajeran wando, basu Inna kad'ai ba hatta ni da niyi  zaman jiran fitowar sa, saida na tashi tsaye saboda yadda yayi wani iri, kamar ba yaya sadeeq d'an gayu da 'kwalisa ba

Yayi wani wuji wuji dashi ida nuwan sa sunyi jawur  se muts-tsuka su yake ga jikin sa duk ya karce sa da farce, harda shedan jini, ba 'karamin ciwuka yajiwa jikin sa  saboda susa ba, hatta da fiskar sa bai bari ba akwai alamun karta, duk ya fad'a fuskar nan yayi zuru zuru,

mamaki ne kwance a kan fusko kin su Momy

Momy tace "Wai sadeeq me ke damun ka haka kamar me borin jini?".

"momy nima bansani ba". Ya bata amsa

Yanzu yaji sau 'kin 'kai-'kayin da jikin sa ke yi, sai dai rad'ad'in da fatar jikin sa ke mai,

"to ai saika je ko jallabiya kasa mutafi asbiti". Inji Inna,

"A a Inna ba sai kunje ba don asbitin gari zani kuma da nisa ku zauna a gida". Ya fad'a yana tafiya

ta kusa dani yazo wuce wa, saida muka yi  ido hud'u  dashi  na kwashe da dariya🤣

kallan tsana yayi min, sannan yanu foni dagudu na mi'ke nanu fi bayan Momy ina haki, biyoni yayi shima,  da hannu Momy ta da katar dashi san-nan tace "amma walahi sadeeq kaji kunya kanwar kanwar ka itace abokiyar yinka, ba dole ta raina ka ba,
Wallahi ka bada maza wuce kabani guri, kamin ki'kam a gaba kamar wani soja, Ko wannan iftila'in daka fad'a be isheka ishara karabu da yarinyar mutane ba". Momy ta fad'i haka tana nuna mai hanya da hannu

Badon yaso ba saidan yabi umarnin mahaifiyar sa,

had'a ido muka yi dashi nayi masa gwalo ina 'kara yin dariya ciki ciki😄

Yace "Zan kamaki  yarinya wallahi zakiyi bayani".

Inna tace"Ai gashinan alhakin tane wannan abin da ke faruwa da kai, saboda Allah ba azzalimi ne ba saidai bawa ya zalinci kansa".

"Kwarai ma kuwa".  Momy tace

Jikin sa babu 'kwari  ya wuce mu, tashi nayi nima nakoma d'aki, saboda na gabatar da sallar a subahi, sai a lokacin nayi sallar takwas saura, ina idar wa ko kan sallaya ban sauka ba nahau rawa da juyi, saboda na rama a binda sadeeq yayi min gado na koma saboda yau bazan je 'yar kasuwa yin tsokanar safe ba bacci zan koma

♾️♾️♾️♾️♾️
Abangaren sadeeq kuwa koda yaje asbiti, kulawa ta mu samman suke bashi saboda asbitin su na 'yan sanda yaje har gado aka bashi sannan aka saka mai ledar 'karin ruwa, saboda yana bukatar ruwa ajikin sa

Harda allurar bacci a kamai saboda ya sami hutu

♾️♾️♾️♾️♾️
Koda na farka daka bacci 'karfe sha d'aya saura11:00am naji dadin baccin sosai domin ya ragemin damuwa

Kamar yadda nasaba idan natashi bacci mi'ka nayi  babu ko salati, na sauka daga kan gadon, na d'auki brush d'ina na fito tsakar gida nayi, san-nan nanufi falon hajiya, acan na iske su Khadija suna cin waina da miya,

zama nayi kusa da Momy nace "ina kwana Momy".

"lafiya lau". Tace min "kin tashi lafiya?".

Nace "eh Momy lafiya lau". Saboda ni bana son doguwar gaisuwa

Tace "ba inda ke miki ciwo?".

kai na d'aga mata
"madallah" ta ce masha Allah haka ake so

Inna na kallah naga
Showing 6001 words to 9000 words out of 51717 words