sannan na sanya aka doramai shakkar Sakina da Duk abunda zatamai bazai taba gani ba ballatana ya Dauki mataki akanta Shiyasa sai tayi ta yin abubuwa bai Taba Daga ,kai ya Dubeta ba Sannan wannan aikin mai girma ne Tunda shima yana da Tsari ajikinsa Dakyar aka samu nasara akansa..!
A wannan gabar ne muka Hada hannu da Balaraba wacce ainihin sunanta ne Dayyaba..Ni kuma marliya nake ammh ana Kirana da Madina sai muka juya sunayemmu Domin kada Bacin rana a fahimci in da muka Dosa..!
Ni na kai Balaraba wajen malamin Dake min aiki anan Dutse Bukatarta ta Farko shine ayima Jafar mugun asirin da zai Fandare ya zama gagararree ya bi Duniya ya lalace kada yaji mganar yaya ballatana ta Sa"idu ya Zama YA FITA ZAKKA Acikin Dangi wanda Daga karshe Sa"idu zai gaji ya tsine mai kada dai ya amfana da Haihuwarsa har Abada..!
Sai akaji goggo Husai ta saka Salati Tana kuka tana Fadin"Innalillahi..Ammh wlh Balaraba kin cika bakar muguwa azzaluma..!
Sai kawai ta koma ta zauna tana Fadin"Allah yayi gaskiya..Zai Tsare bawansa a duk inda yake..!
Jafar kuwa ko Dagowa bai yi ta kasan Inda yake zaune Hawaye ne ke Digar masa Danmallan kuma Hannayensa Jimke Cikin na Amina tun labarin Anty Amarya na Sanadin Auransu da Sakina yake ta Hailala acikin ransa..!
Mamanmu kuka take yi kamar ranta zai fita ita da Anty Amarya da suka san yau komai yazo karshe..!
Ba wanda yace musu kala su kansu ya"yansu zuwa Lokacin sun Fahimci komai ban da tashin kukan au bakajin komai afalon..!
Mamanmu na Toshe kukanta ta Cigaba da fadin"Sai dai an samu matsala..Aikin sai ya kuskure maimakon Jafar sai ya Sauka kan AMINA tun Yaya nada Tsohon Cikinta alokacin..!.
Sai kallo ya koma kan Amina wacce ta kifa fuskarta kan hannun ya Danmaallan tana ta kuka,mamanmu na kallon Amina ta gyada kai tana fadin"Tabbas abun bai sauka kan kowa ba sai kan Amina..Mallam din da kansa ya fadamana haka ni da Madina da muka koma da Korafin aiki bai ci ba..Ya sanar damu aiki yaci Sai dai ba akan Jafar ba,akan Abunda ke Cikin Yaya..!
Alokacin gani muke kamar wasa sai da Yaya ta Haifi Amina sannan muka gasgasta kowa yasan tun Haihuwan Amina ta fita zakka cikin ya"yan gidan da kowa ma,sai kuma nayi amfani da kissa na,na rika jan Amina ajiki ina nuna nafi kowa sonta tunda kowa baya kaunarta Saboda Rashin kunyarta da Kuma Yadda ta addabi kowa ban so Amina ta tsaya haka ba naso ne ta Lalace tabi Duniya ta Zama Karuwa sai dai ina burina bai Cika ba Allah ya Tsare Amina duk Rashin kunyarta bata mu"amala da maza ba Sannan Tarbiyan gidan su data gidam Baba Mallam ta Zauna mata Daram Sannan Allah ya Tsareta da Fadawa wannan Halakar..!
Duk soyayyar da nike nuna ma Amina na karya ne bayan Sihirin Dake tare da ita nima na bada tawa gudummuwar wajen kara Lalata Rayuwarta,Ban taba mata Fadan tayi ba Daidai ba,Duk da alokacin in na Fadamata zataji Domin na Fahimci Duk Duniywa bayan ni da su Hajiya Amina bata yarda da kowa ba sannan tana kaunata Fiye da yaya data kawota Duniya da hakan nayi amfani na Gurbata rayuwar Amina ban taba bari ta ma kanta wani abu ba bana so watarana hakam ya amfaneta sai na Zabi na Sangartata kada ta iya komai ta tashi ahaka ta kuma rayu ahakan na Tabbata watan watarana sai haksn ya Zama illah agareta.
Saboda irin Kaunar da nike nuna mata ba wanda ya taba Fahimta ta Komai sai dai in saka Hamida Amina kuma na Dauketa wata Shashasha ce da bazata iya moran rayuwarta ba Sannan na kara nesantata da Mahaifiyarta yar da har Yaya ta koma ga Allah Amina ko da na Minti Daya bata taba rabarta ba. !
Amina ta Dago jajayen idanuwanta tana kallon Mamanmu kallon Tsana da wani Bakimciki haka Hamida itama da su Zulfa suke kallonta Cikin kyama da wani Takaici Aba dai bai Dago kansa ba har alokacin..!
Mamanmu bata Damu da kallon da suke Binta dashi ba ta cigaba da Fadin"Duk abunda kuka ga Amina nayi ba yin kanta bane..Tana da Sihiri ajikinta sannan da Shafar aljanu su suke sakata ya wan tsorata da kuma Mugayen mafarkai sannan duk abunda ya Faru da Amina kan Aminu na sani ammh ban taba Hanata ba..Ban kuma nuna mata na sani ba da Gangan nake ijiye wayata in da Zata gani saboda ta Dauka alokacin Naso ne Aminu ya lalata Amina Ya yi mata Cikin da zai yi Sanadiyar tsarwata zuciyar Sa"idu da yaya Tunda na Fahimci har ahakan Kaunar da suke ma Amina na Dabam ce ta fita zakka ko acikin ya"yansu ita din mafi
soyuwarsu ce..!
Wannan Karon har Hajiya sai da ta Saki Salati Amina taji kamar dan Ciikinta ya juya ta fara Kokarin tashi Daga jikin Dannallam kawai sai ya kamata ya Rumgumetw zuciyarsa na Bugawa Fat Fat ammh bai Daina kiran sunan Allah ba kada ya rasa natsuwarsa Amina ta nitse Cikin kirjinsa ta wani Fashe da wani marayan kuka Mamammu ta Cutar da ita Cutarwa da bazata taba iya yafe mata ba..!
Mamanmu kanta na kasa tacigaba da Fadin"Sai dai Burina bai cika ba..Allah ya tsare Amina Daga tarkona..Acikin wannan tsukin mallam ya Shammacemu ya Daura mata aure da Danmallam auran daya sa na Harzuka Madina ta harzuka itama,Auran da shine Silar Sanadin mutuwar YaYA..!

"KARYA KIKE YI..Hadiza bata mutu ba..Ke kika KASHETA Balarabaa..!

kawai sai jin kakkusan muryan Aba sukaji ta karade Falom Cikin wani amo mai karfi da ba"a taba jinsa yayi irinsa ba..!
Sai kallo ya koma kansa ayadda Idanuwansa suka kada suka yi Jajir kamar gauta sai ya baka Tsoro ya mike jikinsa na karkarwa yana nuna Mamanmu da yatsa yana Fadin"ke kika kasheta..Kika rabata da Duniya Batare da ta miki komai ba. ?
Meyasa kikayi haka..?
Meyasa kika kashe ran da bata taba Sauya matsayin ki aranta ba .?
Balaraba Bazaki taba gamawa da duniya Lafiya ba..!
Kawai sai kuka jikinsa ya fara rawa yana neman Faduwa Jafar ya mike da gudu shi da Nasir suka taroshi ya Fada Jikinsu yana kuka jikinsa na rawa yana karkarwa yake fadin"Ita ta rabani da Hadiza..Ya Allah ka wulakantata..!.
Sai kuka gabadaya sai kowa yaji ya kara Raunana.
Jadwa da Jaleela suka ruga wajen Abba suka rikesa suna kuka sai ga Jamila itama da Jawahir,har da Jawaad na wurin yana kuka duk da ba Duka yake Fahimta ba ya Fahimci kan Rasuwar Yaya ce.
Ganin haka yasa Amina ta kalli ya Dannallan cikin rauninta tace"Ina so naje wajen Aba!.
Bai musa ba ya Saketa Lokaci Daya ya mike ya taimaka mata ta mike ya karisa da ita gaban yan"uwanta dukkansu suka Dago suna kallonta Aba yana Kuka Kukansa na Fitowa yace"Ki yafemin Amina..ki yafemin..!
Kawai sai Amina ta zube kan kafafun Aba ta wani saki kuka,kukan da kowa yaji sai da jikinsa ya kara yin sanyi Su Jamila suka Fada kan Aba suma suna kuka mai tsuma zuciya Danmallam na gefe yana jin kukan Amina har Cikin Ransa da Ruhinsa ammh ba yarda ya iya Bai isa ya hanata kuka ba..!
Su Zulfa suna ganin su ya Jawaheer wajen Aba ammh kunya da Bakimciki sun saka sun kasa karisawa garesa suna Zaune sai sharban kuka suke kada Hamida ma taji Labari..
Anty Amarya ta runtse ido sai ga Hawaye lokaci Daya Tana Fadin"Tun Lokacin da naji labarin wannan auran Hankalina ya tashi..Saboda bai kamata wata tazo ta sha gaban Sakina ba..Duk da duk kokarina Burina bai Cika ba,Sakina ta samu Ciki sau hudu tana barinsa..Auran Amina ya razanani ni da Sakina razanan da bamu yi shi Lokacin auransa da Sarood ba Saboda ita na saka mallam ya maidata Hoto..An yi ma Umar Sihirin da bazai iya Zama namiji awajenta ba..Awajen Sakina ne kadai zai amsa sunansa Namiji..!
Danmallam ya kalleta Tsam kafin ya juya ya kalli Mallam shima shi yake kallo.
Danmallam kansa ya maida kasa bayan sun Hada ido da Aliyu da mamakin abunda ke faruwa yasa ko motsi ya kasa Anty Amarya ta Cigaba da Fadin"Yadda Mallam ya shammacemu ne yafi batamin rai..Sannan ina Tunanin da Sanin Sa"idu komai ya faru..shiyasa na yi alkawarin shima sai ya Kurbi kwatancin bakimcikin daya kunsamin na Kira Dayyaba muka yi mgana..Nace mata ya kamata Yaya TA,MUTU..ita kuma tace Tabbas ya Dace ta Mutum..Ko domin ta Rama Bakin cikin da Sa"idu ya Dade yana kunsamata aranar na Kira mallam na Fadamai komai,Adaran kuma ya Turo ma yaya Hayakin Daya Turketa ya Sarke mata Numfashi...Numfashin Da yayi Sanadiyar mutuwarta..!
Anty Amarya ta karishe Fada Cikin gunjin kuka ita da Mamanmu gabadaya Falon aka Dauki Salati sai kuka Mamata na Sharan hawaye tana Fadin"Wannan wani irin mugunta ne..?
Gaskiya Balaraaba bazaki gama da Duniya Lafiya ba sai kin lalace..!
Hajiya kanta sai da ta Durkusa kan gwiwiyonta cikin rauni tace"Wani irin Rudin Duniya yake diban ku da har kukayi Tunanin Kashe ran da bata muku komai ba..?
Kai Haabunallahi wa"inamal wakeel..!
Hajiya take fada sai ga Hawaye ganin yadda Hajiya ke kuka ga Aba nayi da su Amina sai kusan kowa ma ya fashe da kukan banda Mallam da Mazan dake da sauran kwarin zuciya.
Ammh yau kam Jafar shima kukan yake rerawa Hawaye wani na korar wani.
Anty Amarya bata yi shuru ba ta cigaba da fadin"Mun so auran Amina da Umar ya kare a lalace ne Ganin An Dibi Lokaci basu tare ba sai muka Saki jiki..Sai kuma kwatsam Hajiya ta taso da mganar tarewar Amina Data rugazamin Shirina ni da Dayyaba ba yadda bamu yi ba kada hakan ta Faru ammh ina Bakin Alkalami ya riga ya Bushe Allah ya Rubuta kaddara zama Tsakanin Amina da Umar..Bayan ta tare na saka mallam ya kara mata rashin kunya da Fitsara saboda Umar ya gaji ya sakota sai kuma yazo ya bar garin ta kare abunta kan Sakina..Alokacin hankalina ya karkata kan yadda Umar zai zo ya tafi da ita Madina har kiranye na saka an yi mai ammh ba Nasara hankalina ya kara tashi Lokacin da Sakina ta samu Ciki ta karayin barinsa alokacin ne na gane bayan ni acikin matan mallam ma akwai wata mai Buri irin nawa..Saboda mallaminmu ya tabbatar min da ita ke lalata duk cikin da Sakina take samu..!.
Anty Amarya kawai ake kallo wacce ta Runtse ido ta cigaba da Fadin"Dana Fahimci ko wacece naso nayi fito na fito da ita Sai dai ina sai ta nuna min In an shirye nake ita atafe ta kwana..Daga karshe sai ta nemi ta lalatamin Duka Shirina ta lankwasa komai ya koma kaina..awannan gabar na rasa madafa.sai da naga Umar ya Danu sannan su Hajiya ma haka sai Hankalina ya kwanta..Ban taba kawo ma kaina wani abu zai ya faruwa ba nan gaba ko da Hajiya ta Dauke Amina nayi Tunanin maiduguri ta kaita sannan Daga baya sai mukayi Tunanin ba auran ne sannan Balaraba kuma hankalinta ya karkata kan Sa"idu da ya koma sai abunda tace mai ni kuma ma samu Natsuwa tunda Umar yazo ya tafi da Sakina sannan Sarood bamu da damuwa akanta Sakina tajata ajiki da farko da sai da ta riga ta mata illah taja baya da ita..Sannan Mallam ya tabbatarmin dacewa sai dai ta gaji da zama dashi araba auran sannan ita kanta Aminar banmu taba Zaton wani abu zai shiga Tsakaninta da Umar har ta samu Ciki ba Shiyasa muka bar wannan Gibin bamu Cike ba..Na rantse har ga Allah Sakina bata da Laifi nice idona ya rufe da Cikar burina ammh ita bata san komai ba,sai soyayyar Mijinta da kaunarsa komai ta aikata ni ce Sila..Ni ce silar duk abunda ya faru..Don Allah ku yafemim..!
Sai kuka har da Shasaheka Falon yayi shuru sai tashin koke koke Mallam kansa na kasa yana ta Salati kansa ya Daure acikin gidansa acikin zuru"arsa Shirka ya samu wajen zama bai taba Sani ba..?
Bai sani ba sai da Hajiya da Danmallan suka zo suka same shi da mganganu wadanda ya kasa gasgasta su ya rude ya shiga Dimuwa Sannan alokacin ya kasa gasgasta mganarsu ammh yaji Daga Bakin da bazai mai karya ba Hajiya da Umaru...sannan Amina bazata taba fadin Wani abu kan Balaraba ba indai ba Gaskiya bane..ita kanta Hajiya ta shiga Rudani sanda Danmallan yake sanar da ita abunda Amina ta Fadamai sai dai bata ji ita kadai ba,ta tarasa suka isa gaban mallam ya sanar dasu abunda Amina ta Fadamai alokacin zuciyar Mallam ta raunana matuka tundaga wannan Lokacin baya barci Damuwa da bakincikin irin wannan abunda yake faruwa acikin iyalansa bai kara barinsa ya runtsa Dakyau sannan tun alokacin jikinsa yayi sanyi da bai Taba yi ba.
Danmallam ma ya girgiza da jin wannan al"amarin ballatana mallam..?
Hajiya kuwa duk ta san wani abu sai da labarin Balaraba ya girgizata.
Dukkansu shuru sukayi da mganar Suna jiran wannan ranar da dukkan sirrin Boye zai fito Fili.!
Baba Mallam ya Dago kansa Rawaninsa ya jike da Zufa duk da Sanyin A.C dake cikin Falon Cikin son ya kara Tattabarwa yace"Wacece ita wacce take Lalata Cikin da Sakina ta samu..?
Muna so mu santa sannan mu ganta..Allah ne ya nufemu da Sanin Ainihin Fuskokin wadanda muke Zaune dasu..!
Yafada cikin raunin murya raunin da ko Hajiya bata sam mallam dashi ba.
Anty Amarya zatayi mgana kenan sukaji muryan Hajiya Uwani Daga Bakin kofar Falon na Fadin.

"Gani nan..!

Sai kowa ya juya yana kallonta Baki Sake Nazeem da Uzairu suka kalli juna suna mai Nuna Tsanatsanin mamaki.
Baba mallan yana kallom Haj.Uwani har ta kariso Falon Idanuwanta sum kode saboda kuka ta Zube gaban mallam Tafashe da kuka Lokaci Daya tana Fadin"Nasan ko ban fallasa kaina ba kasan Abunda nake boyewa..!
Don Girman Allah Mallam ka yafemin..Ni ce nayi ma Umar kuruciya shi da Nazir suka kasa zama kusa dakai sannan ni na mai da Nasir mara amfani a wajenka..Ni nake Hana Cikin Sakina Zama mallam duka nice na aikata hakan..!
Ta karishe fada Cikin kuka Baba mallam yayi wani mirmishi Takaici kafin yace"Kema saboda ki same ni dani da Dukiyata ko..?
Haj.Uwani kanta na kasa tace"Mallam kayi hakuri..Idona ya rufe..Burina naga ya"yana ne gaba akomai..Hajiya tasha gabana a wajenka..Sai nayi Tunanin in ya"yanta suka sha gaban ya"yana na gama yawo..Shiyasa na nemi Cikar Burina ido rufe..Ina da wata Bokanya Da muke cema Mama a Niger take ita take min aiki..Sannan ita ta bankadomin sirrukan Marliya da Balaraba,ita ta bani mgani na saka ma Sakina a tea tasha ita da Sarood har da Amina ma na bata..Ammh sai gashi na ganta da Ciki wanda Mama ta tabbatar min da cewa ko sun samu Ciki sai ya zube..!
Ta karishe fada tana gunjin kuka ai Kowa a Falon sai ya kasa motsi ashe abun bai kare ba..?
Hajiya Cikin Zubar Hawaye ta kalli Uwani Tana fadim"Saboda mene..?
Meyasa kika zabi ki kashe rai Uwani..?.kinsan girman Laifinki kuwa a wajen Allah..?
Haj.Uwani na kuka wurjajan tace"Saboda Mama ta fadamin maallam na Matukar son Umar Sannan ya"yansa da zai haifa sune masu soyuwa a wajensa shiyasa na hana matansa su Haihu shi Nazir bai da wani Tasiri ne shiyasa ban Damu dashi ba..Dalilina kenan na daya sa na Tura Nazeem ya rabu da Sa'idu a kan Harkokin dukiyar mallam Burina shine Nazeem da uzairu su zama kan gaba aduka Dukyarka ni kuma na zama nice gaba da Hajiya tunda ya"yana ne akan komai..Wlh sharrin shedan ne ku yafemin don girman Allah sai yau nayi nadama na Fahimci Zakaran da Allah ya nufa da Cara ko ana muzuri ko ana Shaho sai yayi..!
Kuka take kamar ranta zai fita Mallam ya Datse Hakoransa waje Daya Cikin Bakiimciki,Sai ga Hawaye sharr na zubar ma mallam hawayen Tsausayin kansa da Bakincikin yadda iyalansa suka Gurbace suka gurbatamai zuru"a.
Hajiya ce ta share Hawayenta tana Fadin"Allah ki kayi ma Laifi shi zaki roka uwani..Allah ya gani ban Taba Zama Daya daga Cikin ku da wata manufa ba Shiyasa Allah ya nuna muku iyakarku..Kun ga dai ku baku isa kuyi abunda Allah bai yi ba ko..?
Amina tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe ina Mganin da kikace kin bata..?
Sannan ita kanta Saratun Ciki gareta yakai Wata Hudu ni nace kada a fallasa mganar Cikin ina mganin da kikace kin bata itama..?
Sannan ke marliya ina Sihirin da kikayi ma Danmaallam..?
Kin Fahimci in Allah yace kun yafakun bawa bai isa ba. !
Sai kallo ya koma kan Sarood da mamaki Sakina kuma cikin ta taji yana Juya mata saboda Tsabar Tashin Hankali.
Hajiya ta cigaba da Fadin"Daga karshe nagodema Allah da komai naku ya kare a kanku..sannan ina kara Fada muku ni ban Dogara da boka ko mallam ba..Ni Allah na rike shiyasa na Gagarara har yau har gobe..Kuje Allah zai muku sakamakon abunda kuka aikata Hakkin Rayukan da kuka kashe kuka gurbata bazai taba barin ku ba..!.
Hajiya ta fada tana juya baya Lokaci Daya tana sharan Hawaye..
Nazeem na kuka uzairu da shamsu nayi ganin yadda iyayen nasu ke kuka suna neman gafara.
Nazifa har muryanta na Dishewa.
Hajiya Nasara sai kuka take yi tana Fadin"Wlh ban taba sakama kaina Bakinciki ba..Da zuciya Daya har ga Allah nake zaune da kowa..!
Kawai sai ta saka kuka Mamanmu da Anty Amarya da Haj.Uwani Duke suna kuka neman gafaran ya"yansu da Su mallam ammh ba wanda ya kallesu yan gusai kuwa haka suke aibata Mamanmu suna kirarin bazata gama da Duniya Lafiya ba.
Tashi tayi tana kuka tana Rangaji ta isa gaban su Amina ta Duka tana kuka tana Fadin"Don Allah Sa"idu kai da ya"yan Yaya ku yafemin..Sharrin Shedan ne nasan na cutar daku..ammh ku yafemin ku yafemin ko domin Darajan su Hamida..!
Tafada tana kokarin rike Kafafun Aba yayi Saurin janye kafarsa ya juya baya yana Fadin"Bazan taba yafe miki ba Balaraba..Insha Allahu sai kin girbi Abunda kika shuka..!
Sai Hawaye Mamanmu ta Dukar da kanta tana Kuka tana kokarin rike Amina fadi take"Amina nafi cutar dake don Allah ki yafemin..!
Amina bata yi sanya ba ta mike da katon Cikinta ta saka Hannu ta Dago mamanmu Tsaye kowa mamaki ya kamasa Ammh basu gama mamakin ba Amina ta Cire Hannunta ta Zabga ma Mamanmu mari kafin ta taso ta kara mata a Hannun hagu kafin ta kara tasowa ta kara mata

Sai da ta Durkushe kasa,su Hamida sai kuka ba bakin mgana ba kuma wanda ya Hana Amina.
Cikin hucin kuka da Hawaye ta nuna mamanmu tana Fadin"Marin farko na kashe mana uwa da kika yi ne..!
Mari kuma na Biyu na yadda kika Lalata
Showing 114001 words to 117000 words out of 146831 words