Hawaye afili ta Furta"Komai yazo karshe..!
Hamida ta kalleta Cikin wani yanayi tana Fadin"Me..ya ke faruwa..?
Sai Amina ta kasa ce mata komai Tsausayi suke bata yau zasu yi kwanan bakinciki in suka gano wacece ainihin mamansu.
Anty Amarya ta yarfar da Mamanmu nan Tsakiyar Falon Hajiya Goggo Husai ta mike tana Fadin"Ke marliya meye haka kuke yi kamar wasu yara..?
Anty Amarya ta Cire Dankwalinta Taci Damara tana Zaran ido ta nuna mamanmu Dake kifta ido ta rasa mafita Tace"Wannan zaku tambaya Abunda ya faru..Domin tasan komai..Nima shi nake tambayanta yanzu..Dayyaba ni zaki munafunta..?
Ni zaki yaudara ki Ha"inceni..?
Wlh na yi Rantsuwan
ko kaffara bazan yi ba kinsan inda Amina take da Halin Datake Ciki gani kikayi Burinki ya Cika Kin KASHE YAYA..sannan kin Samu Sa"idu yadda kike Fata shine yasa kika juyamin baya..?
To wlh kin yi Kuskure Ni Madina Fitilar Sharri ce ko ba kalanzir sai na kai Safe yadda ta bare dani da Uban kowa sai ta bare yau..!
Tafada Cikin karaji da Ihu kamar wata Mahaukaciya Daidai Lokacin da su Mallam sukayi sallama suka shigo Falon bayan sa kaf Zaratan ya"yansa ne kama Daga ya Danmallam Nazir ,Nasir,Nazeem,Jafar Uzairu,Shamsu Akilu da zubairu, Da Aba Aliyu abokin ya danmallam atare suka bayyana acikin Falon sai kuma waje ya Dau shuru kallo ya koma wajensu mallam.
Hajiya na ganinsu ta murmusa kafin tace"Yauwa ku kariso..Yau abun dake Boye ne zai fito Fili..anyi walkiya za"a ga kowa sannan an Dade ana ruwa kasa na Shanyewa...!
Kai Tsaye ta maida kallonta kan Anty Amarya da ko ganin su mallam bata Damu ba Burinta kawai gayyar ta watse Cikin wata murya tace"Marliya naj kin Fadi wata mgana da sunan HADIZA..?
me kike so ki fada ne..?
Anty Amarya ta kalli Mamanmu wacce ta ke kallonta Cikin Zaro Ido Jikinta na rawa ta tuma gaban Madina ta rike kafarta tana fadin"Madina don girma Allah ki rufamin asiri..Wlh na Rantse da wanda raina ke hannunsa bansan komai kan cikin Amina ba..!
Anty Amarya ta saka kafa ta Ture Mamanmu ta fadi Gefe Cikin Taruwan Hawaye tace"Wlh baki isa ba Balaraba..Ai ke kwalba ce uwar Sharri..Qur"ani kadai zaki Fadamin na yarda Dake..!
Yadda Kasuwar ta bare dani ban ci Riba ba kema yau sai ta bare dake Dayyaba..!
Tafada Lokaci Daya ta maida kallonta kan su Hajiya tana fadin"Hajiya..Mallam Sa"idu ina ya"yan Yaya su Jadwa..?
Tafada tana Binsu da kallo Cikin son suji me take son Fada suka tsura mata ido Ta juya tana kallon Mamanmu dake kuka tana rokonta kada ta Fada ta juya mata baya ta kalli Idon Aba tace"Kunga wannan matar ba Matar kwarai bace..Shekarun data kwashe tana Zaune daku duk na Cutarwarce..Muguwa ce Azzaluma ni Duk Mugunta na ban taba Kisa ba..Ammh Kunga wannan..?
To Tayi kisan kai ta kashe rai Har Lahira..!

Aba Cikin rawan baki dana murya yace"Wa...ta Kashe..?
Kafin ta samu bakin mgana Daga bayansu sukaji wata murya Cikin Kuna tace

"YAYA TA KASHE ABA..!

Sai kallo ya koma inda akaji mganar sai ga Amina ta bayyana a Tsakiyar Falin gaban Anty Amarya da Mamanmu da ke tsuggune cikin Fitar hawaye Duka Biyu.
Gabadaya sai kowa yaji wani sanyin jiki Aba sai da ya Dafa ya Danmallam Dake gefensa saboda jirin Daya kwashesa Anty Amarya kuma Amina take kallo da Mamakin a ina tasan wannan mganar..?
Mamanmu kuma kasa kawai tayi Dakai yauma Tubular sara"i babu Tsima babu Dubara.
Ya jalela da su ya Jadwa suman Tsaye sukayi ya jafar ne ya iya takowa ya iso gaban Amina ganinta da Ciki ba shi ne agabansa ba mganar data Fada ne abun Damuwa..
Cikin Fitan Hayyaci ya kama jijjiga Kafadun Amina yana Fadin"Wata Yayar ne ta kashe..?
UMMANMU..?
Ya fada Cikin Tsawa Idanuwansa Jajir kawai sai Amina ta Fashe da kuka ta Fada Jikin ya jafar tana nuna Mamanmu Cikin wata murya tana Fadin"Itace ta kashe mana Uwa ya Jafar..Itace ta rabamu da Aba..Itace ta rabani da Uwata Shekaru goma da wani abu bansan Dadinta ba..
Itace ta maka asiri domin ka lalace sai abun ya Dawo kaina.
Itace ta hada kai da Anty Amarya ana Zaluntar ya Danmallam itace kuma suka ka Hada kai domin su ga bayan aurena da ya danmallan da alwashin har Abada bazan taba Haihuwa ba..
Ya jafar wlh wannan matar muguwace kuma azzaluma ce ta Dade tana Zaluntarmu bamu sani ba..itace ta kashe mana YaYA DA kunnena naji ta tana Fada..!
Ta karishe fada Numfashinta na Sarkewa,Ya Jafar ya riketa Cikin wani yanayi yanayin da baya fatan ya Bude ido yaga abunda ke faruwa da gaske ne.
Durkushewa Amina tayi kasa Jafar ya Bita ya Tallafeta,ya Danmallam ya kariso ya riketa yana Cire mata Hijabi Saboda ta samu iska tana ganinsa ta Damke hannunta Cikin rawan murya tana Fadin"itace..Ita ta kashe mana YAYA..!
Malam dake tsaye yace"innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..!
Sai kowa afalon ya Dauka Saboda kowa ya rasa abun Fadi.
Mamanmu na wani irin gunjin kuka tace"Kaico na..Bansan akwai wannan ranar ba..Da ban aikata abunda na aikata ba..Don Allah ku yafemin..!
Gabadaya kallonta kawai ake yi Cikin Wani yanayi Aba kuma zaman dirshan yayi a kasan Cafet ya kasa mgana su ya Jadwa kuma suna dai Tsaye da karfin Imani.
Hajiya ce ta kalli mamanmu tana Fadin"Balaraba me Hadiza ta miki kika Kasheta kika raba ta da wannan Duniyar..?
Tafada cikin wani yanayin muryanta kamar zatayi kuka Ranar da
Danmallan yazo mata da wannan mganar bata gasgasta ba har yau tana cikin Tantaman balaraba zata iya Kasje Yaya sai yanzu da komai yake neman bayyana.
Mamanmu tana kuka kanta na kasa ta kasa Dago kanta saboda kunya balle ta kalli Ya"yanta da yayan yaya ga Aba ga kunya mutanen Dake falon Anty Amarya kuma na Tsaye ta shirya komai ayau Sakina ma duk suna gefe banda kuka babu abunda take yi.
Amina kuma Danmallam jikinsa ya Tarairayota ya azata yana ta faman mata fifita da Hijabinta Sakina na kallonsu tana jin kamar ta mutu saboda bakinciki.
Kan Mamanmu na kasa ta fara mgana.

"SOYAYYAR SA"IDU CE SILA..."









*Janafty**TFZB2026*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Gabadaya Ilahirin Falon sai da kallo ya koma kan mamanmu cikin mamakin kalamanta,ita kuma kanta ta kara saddawa kasa hawayenta na diga saman cafet din Daya malale falon Hajiya ta cigaba da fadin'"Tabbas kamar yadda na fada da farko Hakane soyayyar Sa"idu ce ta kaini ga komar Nadama dana ke ciki..!

Na taso tun ina karamata ban taba ganin wani Namiji daya taba Burgeni kamar Shi ba,Tun tasowata shi kadai ne Namiji kwara Daya daya ke Burgeni Sannan na kamu da sonsa da kananun shekaruna batare dana sani ba,Sa"idu ya shiga raina yayi kane kanen da bazan iya rayuwa ba sai da shi Tun Lokacin suna Gusai kafin barowarsu chan su dawo nan Gumel da Zama saboda Sa"idu yasa ban taba Daga kai na kalli Samarin Dake kara kaina akaina ba ina ganin kamar zai so ni watarana sannan kuma Hankalina da duka Tunani ya karkata akansa shi kadai.
Sai dai me..?sai da girma ya fara kamani Sa"annina suna aure sannan na Fahimci bana gaban Sa"idu bai taba min wani duba ba sai na yan"uwanta duk da kaunar da nike ta Nuna mai a Fakaici in yazo garin yazo Gidanmu Tunda ni ina matsayin Diyar abokin wasan Marigayi Baba Aminu ne,yazo kaida Babani Lokacin Tana Raye bana iya sukuni na Dinga Bare baren jiki kenan a kansa bani da wani Sauran sukuni ammh bai Taba Daga ido ya kalleni ba ballatana yasan Halin da na Dade aciki alokacin har Babani sai da ta Fahimci ina son Sa"idu so kuma bana wasa ba.
Hankalina bai tashi ba sai da naji Zencen auransa ranar sai da nayi karamin Hauka Babani Allah ya jikanta ta Dinga Tausata ta bani Hakuri akan nayi hakuri na Cire Sa"idu a raina na bama wani Cikin Manema na Dama tunda dai Sa"idu bai Juyo gareni ba na Hakura dashi alokacin kamar in make Babani haka naji Sai dai ban nuna mata ba ammh a wannan gabar gaba nake kullawa ga Duk wanda yace na Rabu da Sa'idu ko waye shi kuwa..!
Auran Sa"idu da Hadiza kadan ne ya Rage bai kaini kushe wata ba Saboda Bakinciki da Zafin kishi har sai da na Fara Tunanin na kamu da ciwon zuciya ammh duk da haka ban makara ba sannan ban cire rai ba.
Ana cikin wannan Halin Babani ta amsa kiran Allah ta rasu dani a bakinta da Fatan na yi aurre kada na jirasa ammh ban jita ba Tunda ni kadai ce tare da ita bayan bakwai dinta sai kawu Salisu ya maidani babban gidanmu ina zaune a wajensa..!
Saboda Sa"idu da Soyayyarsa sai da Kaf sa"o"i na suka tafi gidan mazajensu har kannen baya na ma an fara aurar dasu a wanchan Lokacin ana auran wuri ammh ni nafi Shekara ashirin ko Tsayayyen mgana bata akaina Saboda bayan Sa"idu har Abada bana jin zan iya bama wani Namiji Dama.
Kwatsam Naji Labarin Haihuwar yaya da yadda Sa"idu ya dinga rawan jiki akanta da abunda ta Haifa sai Gyambo na ya Dawo sabo naji bazan iya Hakura ba,Da taimakon wata kawata Samira da mukayi Primary tare na Zayyane mata Damuwata tace ta kwana gidan Sauki ita ta Daukeni ta Fara kaini gidan wani malami ko Boka zan ce wanda ke mata aiki akan mijinta acikin garin Tsafe na ZAyyanemai Halin da nike Ciki ya Tambayeni me nake so nace Sa"idu nake so..Ya aureni ko ta Halin kaka ne yana so ko baya so ni ban Damu ba kawai Burina na ganni agidansa a matsayin matarsa..!
Yace an gama ammh zan zube kudi masu yawa na karin aiki ban Damu ba Daman ta Fadamin na Tanadi kudi alokacin wajen Biyan Bukatata komai zan iyayi Zoben Zinaren da na gada wajen Babani na Saida na yi amfani da kudin wajen jawo cikar Burina.
Kamar wasa sai ga karamar mgana ta Zama babba kawu Salisu ya Kira Sa'idu akan yazo yayi auran zumunci Dani alokacin ko gaddama bai yi ba ya Karbi mganar Daganan na Fahimci zama ba nawa bane samira ta Budemin ido da shiga malamai Domin Cimma Burina ban shiga Gidan Sa"idu ba sai da na saka aka kafani sannan aka Saka soyayyata da kaunata a zuciyar kowa banda ta Sa"idu domin bai kaunace ni Fiye da yadda nayi nazo ba,yafi kaunar yaya da Jafar d'anta data Haifa.
Wannan shine Bakinciki na Biyu dana taba Fuskata agidan Sa"idu bayan aurena dashi,Da Farko ina ganin Komai ya kare tunda na auresa ammh Daga baya sai na Fahimci zama bai ganni ba Duk da kuwa Daga Su mallan har ya"yansu suna so na da Girmamani Uwa uba kuma Yaya itama ta Sakarmin komai kamar yadda na nuna Dayan fuskata ta Salihai.
Na Dade ina Fama da kuncin zuciya da Bakimciki kauna da wannan Tsausayin da bana ganinsa akan kowa sai akan yaya ni kuma sai dai Zaman Tsausayi da yan"uwanta ka ban taba ganin wannan kaunar da nake son gani atare dashi ba Sannan sai na Fahimci Duk wani Buri na Sa"idu yana kan Jafar ne bashi da sukuni in yana gida yana Tare dashi ko da Ranar ni ke da girki sannan duk kokarinsa na yaboye wannan kaunar bata Boyu awajena ba Dalilin Dayasa Idona ya Rufe da Kishi kenan da Bakincikin yaya da ya shiga raina na har Abada.
Hankalina ya kwanta dana Samu Cikina na Farko ina Tunanin Namiji zan Haifa nima Sa"idu yayi rawan jiki akaina da abunda na Haifa sai dai kuma ina hakan bata Faru ba haihuwar ZULFA sai ya koremin wannan Burin nawa sannan kuma sai na Fahimci kamar Sa"idu bai yi murna da wannan Haihuwar ba Duk da yadda ya dinga min Hidima yaya da Hajiya na Tsaye kaina ban taba Gani ba Saboda gani nake yi Itace ta Hanani Samun abunda nake so tun Farko Sannan tasha gabana a zuciyar Sa"idu.
Na yi ta neman Samira domim mu koma wajen mallan sai na samu Labarin mijinta ya tafi da ita Lagos inda yake Neman kudinsa sai hakan ya katsemin hanzarina ban koma wajen maallam da wuri ba har Tafiya ta Cigaba da tafiya alokacin Yaya ta Haifi Jadwa da Jaleela ni kuma ina Goyon zahra kaf alokacin ni nake rainan duka ya"yan da yaya ta Haifa Saboda na kara jawo Hankalin kowa da Tunanin kirkina akansu kuma naci Nasara na zama ban damu da komai ba a Bayanne a boye kuma ba wanda ya kaini Bakinciki.
Hankalina bai kara tashi ba sai da naga na kara Haihuwar Zulaihat ban samu Namiji ba sannan ga Jafar ya girma sai nake ganin yaya ita ke da gida ni kuma ta barni bani da Tsuntsu ballatana ta tarko sai nayi Shirin komawa wajen mallam sai dai nayi Rashin Sa"a an ce ya tashi Daga nan kuma ba wanda yasan inda ya koma Hankalina ya tashi Saboda alokacin na kasa Hakuri so nake ko ta Halin yaya ne na sami mafita na gaji da Kunsan Bakim cikin Sa"idu da yaya.
Hakanan na Dawo gida tunda bansan wani Malamim ba sai dai kafin na Samu mafita zuciyata ta riga ta gama kekyashewa Tsanar yaya da ya"yanta ya gama Cikamin zuciya wannan Bakincikin Tun aurena da Sa"idu yake Cikin Raina bai Taba gushewa ba Sai Ranar da YAYA ta bar gidan Duniya..!
Mamannu ta karishe Fada tana gunjin kuka Mallam ya girgiza kai Cikin Wani yanayi yana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..!
Kafin ya karisa ya samu Daya Daga Cikin kujerun falon Hajiya ya Zauna Rawaninsa duk ya jike da zufa Aba kuma yana Durkushe inda ya Sulale kansa na kasa ba wanda yasan Halin Dayake ciki su Nasir da su Nazir kuma duk kasa suka sulale suka zauna jin wannan labarin mai kama da al"amara.
Su ya Jadwa da su Jaleela suma kafafunsu ne ya kasa Daukansu suka zube nan saman cafet suna Faman kuka kada su Zulfa su ji Labari gabadaya kowa da abunda yake sakawa acikin ransa Amina kuma na Rumgume jikin Danmallam Tana kuka yana faman share mata Hawaye yana Shafa bayanta Jafar kuma kansa ya Dukar kasa Hannunsa Daya Dafe da kan nasa ya kasa yarda da abunda yake ji kuma yake gani
Gabadaya kowa acikin Falon ka kallah sai ka Hango tashin Hankali da al"ajabin wannan abunda dake Faruwa.
Mamanmu ta Dago Jajayen idanuwanta ta Sauke kan Anty Amarya da jikinta ya fara rawa sai alokacin ta Fahimci Komai fa ya kare sai dai babu wani tsumi ballatana Dubara.
Cikin Muryan kuka da Nadama Mamanmu ta Cigaba da Fadin"Ban taba Sanin bayan ni agidan Baba mallam akwai mai irin Halina ba Sai daga baya..Har ga Allah da Farko bansan Haka marliya take ba sai da watarana na jita tana waya da malamin Dake mana aiki kan Hajiya da mallam alokacin nasan itama irina ce..muna neman abu Daya agida Daya sannan alokaci Daya..!
Ban nuna mata na jita ba Sai daga baya,Na koma na nuna mata fuskata na bayyana mata Duka Burina da Fatan zata bani Hadin kai mu cure waje Daya wajen Cikan nmu burin..!
Tafada tana kallon Anty Amarya da kallo ya koma kanta komawa tayi ta Zauna Dabas saman Cafet sai kuka Cikin wani yanayi ta cigaba da fadin"Alokacin da Balaraba ta zo min da wannan bayanin na tsorata Saboda ko ni ban taba Tunanin haka take ba..Ammh data zauna ta warwaremin komai sai na Fahimci Rauninta nima ina Cikin irin haka..Sannan in muka Hada Hannu zamu cika namu Burin atare..!

Mallam Dake zaune yana jin abun al"ajabi ya Bude Bakinsa Cikin wani yanayi yace"Ke menene naki Burin..?
Burin daya sa kika fifita Duniyarki Fiye da Lahirarki marliya. ?

Anty Amarya bata iya kallon mallam ba Saboda yadda taji muryansa ba wannan amon ballatana karkashi Abunda ke Faruwa ya Dakushe komai Tana sharan Hawaye ta Cigaba da Fadin"Ni burina shine na Zama Tauraruwa a wajenka..Na zama ni ce agabanka kafin kowa..Sannan Burina na zama na Dara duka matanka a wajenka..Sai dai ina burina bazai taba Cika ba indai Hajiya na Duniyarka na yi barnar kudi akan ka mallam da Hajiya Saboda kawai na Zama Tauraruwa a wajenka sai dai hakan bai Samu ba kowani aiki baya Tasiri akan ku saboda kun rike Allah sannan ko acikin Wani Hali baku daina ambatonsa ba. !
Sannan tun zuwana gidan nan na Fahimci Hajiya ta yi mana Fintikau,Komai naka itace,Daga ita Sai SA"IDU sune kadai suke gabanka da su kake shawara sannan uwa uba Sa"idu ne ke jan Ragamar Duka Dukiyarka nayi iya Bakin kokarina na Raba hakan sai dai ban cimma gashi ba..Sai na Sauya shawara da taku..Na Fahimci in ni bazan zama Tauraruwa ba ta Sanadin Sakina zan iya Cika Burina Har fiye da yadda nake Tunani..!

Tunda ta ambaci Sakina Danmallam ya zura mata ido yana kallonta sakina kuma jin an zo wannan gabar kawai sai ta kara Volume din kukanta ta soka kanta Tsakanin Cinyoyinta tana gunjin kuka ko Aliya Dake gefenta bata da karfim gwiwan lallashinta.
Anty Amarya na jan Hanci da majina ta Cigaba da Fadin"Har ga Allah Lokacin da na Dauko Sakina ta zauna awajena da zuciya Daya ne sai daga baya..Data fara girma na Fahimci Tana matukar Kaunar Umar in ta gansa ta Dinga mai rawan jiki kenan shi kuma alokacin bata gabansa ita da su Jidda da su Nazifa duk Daya ya Daukesu..Ban tabbatar ba sai da na Samu Sakina mukayi mgana ta Nuna min in ba Umar ba bazata iya auran kowa ba Daga Lokacin na hango Cin ma nasarata ta bangaran Sakina..!
Ni na shiga na fita na Karkato da Hankalin Danmallan akan sakina..Duk da alokacin akwai ya"yan malamai manya wadanda suka fita komai da suka so su hada zuru"a da Maallam kwatsam yace Sakina yake so..Nasam ko Hajiya alokacin tayi mamaki Sanin ba wata alamar Soyayya a Tsakaninsu sai dai sanin ita bamai yawan maida kai kan sha"anin Umar bane yasa bata nuna komai ba ko a Fuskarta ba..!
Hajiya ta jinjina kai tabbas ai Biri yaso yayi kama da mutum Rana Tsaka Danmallam yace Sakina yake so ashe Ba yin kansa bane lalle Allah shine Sarki.
Anty Amarya tacigaba da Fadin"Mallam kuma bai nuna komai ba sai ma farinciki zai yi tuwona maina..Tunda yarcda ya rikeni Sakina Tsakani ga Allah haka yake rike da ya"yansa Daya Haifa,ammh duk ban gani ba Zuciyata ta kekashe da cikar Burina..!
Ban yi salama ba sai da aure ya Kullu Tsakanin Umar da Sakina sannan naji Hankalina ya kwanta
Showing 111001 words to 114000 words out of 146831 words