su suna kukan yadda Allah ya inganta Rayuwar Amina ne da kuma kukan Rashin Uwa garesu ita kuma Amina Wani Daci ne acikin ranta in ta Dago tana ganin Mamanmu a gabanta.
Mamanmu kwata kwata kamar kunnuwanta sun Dode haka taji Hajiya na lura da ita tayi Mirmishi acikin Ranta kafin ta karisa gabanta ta Dafa Kafadarta kamar wacce Shooking ya taba haka ta Zabura sai kuma taga Hajiya Daga ganin yadda tayi Firgai Firgai sai ta baka mamaki Hajiya tace"Balaraba ki karisa mana ki gaisa da yar naki..Sannan ga kayan Lefenta nan nace baza"a bude ba sai kin zo ke da sauran yan"uwanta..!
Mamanmu sai taji kamar Bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana Hajiya taja Hannunta har gaban Amina sannan ta Saketa Mamanmu kafafunta ne suka kasa Daukanta ganin wani irin kallo da Amina ke Binta dashi da shigargun Idanuwanta kawai sai ta Zube agaban Amina ta saka kuka sai kallo ya koma kanta Kuka take yi sosai tana rike da Hannun Amina Fadi take yi"Amina yanzu Ciki kike dashi bansani ba..?
Nice fa Mamanki Amina duk duniya ko kowa baisan Halin da kike Ciki ba Ni bai kamata na Sani ba..?
Tafada Cikin Karaji da nuna yadda abun ya Dameta Goggo Husai ce tayi mgana tana Fadin"Ke Balaraba to wa ya sani..!?
Kina ji ai ko Sa"idu bai sani ba..!
Mamanmu sai ta rumgume Amina ta na kuka Fadi take"Amina waya yi miki Ciki..?
Cikin waye ajikin ki..?
Mganar ta fito ne kamar ma bata san Sadda ta fito ba sai kallo ya koma kanta Cikin mamakin kalamanta Haj.Nasara ce ta kalleta tana Fadin"Ke kam Balaraba da wata mgana kike yi Amina ai kinsan tana da miji..Cikin jikinta kuma ai Jikan mallam da Hajiya ne..!
Mamanmu sai ta Dago gabadaya ta Rude idanuwanta ta fara wurgawa Cikin Falon karaf suka hada ido da Anty Amarya Dake tsaye gefenta Sakina ce da Sadiya sai Aliya sai wasu Dangin su Daga Dutse.
Kallon kallon sukayi ma juna,kallon da basu taba yima juna ba Mamanmu ta kara tsurewa cikin wani yanayi ta kauda kanta kafin ta kalli Haj Nasara tana Fadin"Ba...Ba sun rabu ba. ?
Sai kowa ya Zaro ido yana kallonta Mamanmu sai ta rude ta fara inda inda Tana fadin"A"a na dauka da Hajiya ta Dauketa anan ne..Auren ne ya lalace..!
Sai kuma ta kara saka kuka tana Fadin"Amina kece kika koma Haka..?
Allah Sarkin kyauta da kari..!
Sai kuma ta kara rike Amina wacce in ta riketa kamar wani abun kyama ya Tabata yadda ta Tsani mutuwarta haka ta Tsani ganin Mamanmu shiyasa sai binta da kallon mamaki take yi kamar yadda Hajiya ke gefe tana yi Lokaci Daya tana Sakin mirmishi.
Kafin wani yayi mgana su Hanne sun shigo da Ihu suna fadin ina Aminar take..?
Amina na jin muryan su Hanne ta Bangaje mamanmu ta mike Cikin Fara"a da Tsantsan murna bakinta kamar zai Tsage tace"Gani nan Hanne..Hamida..!
Sai kuma Hawaye Hanne ne kan gaba sai Hamida sai su ya Abida dasu Sa"adatu idon su ya rufe ko Mutanen Falon basu tsaya kallo ba ballatana Cikin jikin Amina suna ganinta Hanne ce ta fara Buga Tsalle ta fada mata Sai Hamida da Zafira wacce dazu tazo Suna murnan ganinta.
Kadan ya rage su kadata Yakaka da Hajiya har suna Hada Baki wajen fadin"Ku kula fa..Tana da Lalura..!
Sai Sannan sukaji wani abu mai Tauri ya Tokaresu suka Dagota suna Binta Da kallo Daga sama har kasa,cikin mamaki da Budewar Baki Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka kalli Amina Dake sharan kwallah tana kallonsu cikin Annuri fadi take"Nayi kewarku..Nayi kuka nayi kukan kewarku kamar ba gobe..!
Tafada tana dora kanta saman kafadan Hanne Lokaci Daya tana rike hannuwan Hamida Zafira dake gefe Ta leka Amina tana fadin"Amina..?
Amina ta kalleta tana yar Dariya tace"Na"am zafira..Zafira..!.
Tafada Cikin dariya da Hawaye zafira ta jingina da kafadan Amina tana Fadin"Itace.Wlh Amina ce..!
Tafada tana Dariya,Amina ta rikesu kamar ta samu salama bakinta yaki Rufuwa Hanne ta Taba Cikin Amina tana kallon Hamida kafin tace"Hamida Wlh Ciki ne ajikin Amina..!
Taba kiji..!
Hamida itama ta taba Cikin kafin ta kalli Hanne tana fadin"Ciki ne..Amina Zaki Haihu ne..?
Sai Amina ta kasa mgana ta Buge hannunsu tana fadin"Bansani ba..!
Tana hararansu Lokaci Daya kawai sai suka Bushe da Dariya ga hawaye na Binsu suka hada Baki wajen fadin"Wlh Aminene ce..!
Suka koma suka rumgume juna gabadayansu suna Hawaye suna Dariya kowa afalon sai da yaji kamar yayi musu kuka ya Abida ce da ya Zeenatu suka matso kusa ya Abida ta Dafa su Hanne tana Fadin"Dillah ku matsa ai Aminar bataku ce ku kadai ba..Har damu..!
Suka saki Amina suna Dariya Amina ta Daga baki Cikin Murna tace"Ya Abida..!
Tafada Cikin murna kawai sai tace"Na"am Aminene..!
Sai suka rumgume juna suna mai Farinciki haka ma da ya Zeenatu ta Shafa kumatun Amina tana fadin"Allah mai iko Amina ba Fada ba tsiwa..Agaida ya Danmallam..!
Amina ta sunne kai tana Dariya Goggo Husai tace"Ai rabon dake tsakanin su ne yasa auran yazo Cikin gaggawa..Allah ya Rubuta wannan Rabon ajikin Amina yake..!
Mamata mahaifiyar Zafira tace"Kwarai Rabo ai bai bar komai ba..!
Yakaka ta amsa da cewa"Ai yana ma kisa..In aka hanasa bayyana sai ya kashe rai..!
Hajiya na gefe tana ankare da motsin kowa tana dan Mirmishi sai alokacin tayi gyaran murya tana fadin"Ku Dakata da wannan murnan ga lefen Amina nan da kayan Haihuwarta..Sannan akwai gidanta da Mijinta ya siyamata an zuba komai aciki Yana Babura Road zuwa gobe in an watse taron Amare sun mika za"a raka Amina Gidanta nan zata Haihu tayi Jegonta kafin tayi Arba"in Mijinta ya Dauketa su koma inda yake aiki..!
Hajiya Nasara ta zabga Kabbara ita dasu ya Abida,Ya Aisha na Dariya jin Yakaka na fadin"Kwarai Hajiya. kafata kafar Takwarata sai garin ma"aiki..!
Hajiya nasara ce ta fara Bude kayan su ya Jalela na Tayata su hanne na kamkame da Amina suna zaune suma suna kallon abunda ke faruwa Lokaci Bayan Lokaci suma bin Amina da kallon mamaki ita kuma sai ta Hararesu tace"magulmatan Amare kawai..!
In tace haka dadi suke ji Aminar su bata tafi ba ta dawo wannan ranar ta Farinciki ne.
Akwatuna Bakwai na lefe Biyu na kayam Haihuwa gabadayansu aka Bude su a Tsakar Falon Hajiya su Anty Amarya na inda suke sun kasa motsi ballatana Mamanmu da tunda ta Jabe ta kasa tashi Haj.Uwani na daga Bakin kofa rike da Fashasshiyar wayarta ta kasa gaba ballatana baya.
Hajiya ta kallesu tana Fadin"Amarya..Uwani ku kariso mana..Sakina ku kariso mana..!
Tafada tana kallonsu Daya bayan Daya Har Sa"adatu data koma barayin Uwarta tana kallon ikon Allah kamar kazar da bata da maiko haka suka tako Har wajen kayan suna Tsaye ana ta Daga kayan arziki su Mamata ne gaba gaba da wata abokiyar wasan Aba ana Dagawa su ya Abida na kirga kayan.
Sai da aka Kirga manya atamfofi Talatin da Biyar lesuna Takwas Materil Biyar,Shadda Hudu,Abaya shida,Ya Abida ta Daddage ta Rankwada guda ya Zeenatu na Tayata aka fara Daukan sauran Innes da kayan kwalliiya kayan arziki sai wanda ya gani aka gama aka zo na kayan Haihuwa akwati guda na Amina ne Tsalalan Atamfofi da lesuna kala goma duk an Dinka sai dayan na Kayan yara ne masu kyau da Tsada sai wanda ya gani.
Mamata ta kalli kayan kafin tace"Wadan ga duk kayan na Fitar suna ne Hajiya..?
Ya Aisha ce tace"Duk na sunana Mamata..Na Amina Daya..sauran kuma na Bbys dinta..!
Mamata ta jinjina kai kafin tace"Allahu akbar Diyar Balaraba tayi goshi..!
Goggo Husai ta gyada kai kafin tace"Kaya sun yi kyau masha Allah..Naji Dadi Allah ya sauketa Lafiya..!
Ya Abida ta kara sakin guda Hanne ta mike tana Tayata ita da zafira hamida ce ke Dariya Cikin Daga murya ya Abida ta kara sakin guda Hajiya ta Harareta tana Fadin"Nan gidan bai dace da gud'a ba..kabbara ya kamata kiyi..!
Ya Abida ta kara karkacewa ta saki gu'da ya Aisha ta d'aka mata duka abaya tana Fadin"Mara kunya Hajiya na mgana..!
Ya Jawahir itama ta Daga hanci ta saki nata gudan Ita da ya Zulfa sai Ya Zeenatu itama tayi nata ya Abida ta kara Dorawa suka ruda Falon Hajiya Mamata ma ta Dauka goggo Husai sai Dariya take ita da yakaka Hajiya sai Faman Hararansu take yi ba"a kara Saka Dariya ba sai da Hamida ta karkace tayi nata aka kwashe mata da Dariya Har Amina sai da ta Dara Hanne na Dariya tace"Gaskiya ne Amina TA FITA ZAKKA..wannan zakkan gaskiya ne gashi mun gani..ako"ina itace Zakka komai nata na mussaman ne..!
Ya Abida ta amshe da Fadin"Kwarai Wlh..Aminene badai ta mutum ba sai ta Allah..!
Suka kara karkacewa wannan karon har da su ya Zulaihat suna Sakin guda Hajiya kai kawai ta kada tana Mirmishi,Amina na zaune ita da Hamida suna kallonsu suna Dariya.
Da gayya Hanne da ya Abida suke wannan gudar saboda Sakina domin har Bikin nan da suka hadu bata musu mgana ba tun Lokacin auran Amina da Danmallam bata kara musu mgana ba ko sun hadu sai ta kauda kai..shiyasa suke kallonta suna kara Ruda Falon da gud'a Sakina Gabadaya ta Jike da Zufa,Jikinta ba inda baya rawa kanta ya gama Daukan abubuwan datake ji har wani Dum..Dum yake yi kamar ba nata ba Hakama Anty Amarya gadai tanan ne kawai abubuwan sun tsaya mata Cak ta kasa wani Tunani kamar yadda Mamanmu ke jabe suna jin Abun Al"ajabi tare da Tsamanin Abunda basu yi Tsammani ba..!
Duk wannan Budurin da akeyi Sarood na Falon nan sai kallon kowa take yi tana Bin Baki ita ba wani sanin Amina tayi ba shiyasa bata gane komai ba ammh kuma Kayan data gani ta Zata na su Hanne ne da za"ayi ma aure gobe Ita ba Hausa take ji ba,Shiyasa sai bin Bakin Mutane kawai take achan gefe kamar ma bata afalon.
Haj.Uwani ce ta juya kawai ta Fice Daga Falom Idanuwanta sun kad'a sun yi Jajir Dishi Dishi ma take gani Saboda tashin Hankali.
Tana fita saboda yadda ta Rude yasa bata ko nemi Kebewa ba tana fitowa ta Laluba wayarta Allah yasa gefenta Da saura ana gani haka ta saka lambar Batula saboda yanayin Datake Ciki bama zata tsaya neman Lamba ba.
Batula ta kira gabda zata katse ta Dauka Cikin karaji da wani yanayi Haj.Uwa tace"Mun shiga uku mun Lalace Batula..Hajiya ta gama lalatamin Duka shirina..Hajiya ta Ruguzamin Burina da na Dade ina Tanadinsa..!
Dagachan bangaran Cikin Tashin Hankali tace"Innalillahi Uwani me ya faru..?
Haj Uwani tana Sharan gumin Goshinta tace"Komai ma ya faru Batula..Komai ya Lalace..Amina ce ta Dawo da Cikin Umaru ajikinta Batula..Sannan da kayan lefe dana Haihuwa kamar za'a Bude shago sannan ga Makullin gidan daya Siya mata Batula ni fa bama shi ya Dameni ba Batula Amina Tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe..!
Batula Cikin tashin Hankali tace"Ciki kuma Uwani..?.
Wai Wata Amina..?
Haj.Uwani na faman kokuwa da yanayinta tace"Batula Amina dai da aka Aurama Umar ita ke da Ciki fa..!
Batula tace"garin yaya..!
Ta yaya hakan zai faru alhalin kince kin tabbata ta sha mganin Mama..?
Haj.Uwani ta Runtse ido sai Hawaye Cikin Rawan murya tace"Bansani ba Batula bansani ba..Hajiya ta shammaceni..Shammatan datamin illah har Abada..!
Batula tace"To yanzu menene mafita..!?
Haj.Uwa ta Share Hawayenta Tana Fadin"Bazan karaya ba..Karaya ba na wa bane Batula..Dole ne nayi Nasara Batula ko ta halin kaka ne..Saboda haka ki Tashi sammako gobe ki koma wajen Mama ki fadamata Halin da ake Ciki..Ina so kada Cikin nan ya fito Duniya..Ina so a kashe koma menene acikinta ta haifesa ba rai kada yazo Duniya da ransa..Naji Samun Cikin kuskure ne sannan Hajiya in tasan wata ai bata san wata ba..Zan nuna mata Ni Uwani Kwalbar Sharri ce ko na Fashe ina da Sauran mamora..!
Batula tace"Gobe goben nan zan yi sammako..Wannan Labarin ya Firgitani ammh Hajiyar nar Allah ya Tsine mata albarka..!
Haj.Uwani Cikin Huci tace"Nayi alkwarin sai na Tarwatsa Farincikin su..Sai na Lalata musu wannan jin Dadin na su..!
Daga haka ta Datse kiran tana Sakin Huci kamar zakayan,Ta juyo a Fusace Kawai sai taci karo da Hajiya Tsaye da waya a Hannunta tana kallon Hajiya uwani Cikin wani yanayi.
Haj Uwani gabanta ya fadi ta Zaro Ido Jiki na rawa tana kallon Hajiya wacce ta Daga mata wayar hannunta ta nuna mata Sai ga sunan MALLAM baro baro alaman kira yana tafiya minti Goma sha Biyar alamun tun fara mganarta da Batula..
Jikinta na rawa Gabanta na Faduwa Zufa na keto mata ta ko"ina kawai sai ta Duka kan gwiwoyinta Domin tagama sanin Hajiya tasan wannan Boyayiyar Fuskar nata.
Cikin Rawan murya ta hada Hannayenta tana Fadin"Dom Allah Hajiya ki Rufamin asiri sharrin Shedan ne..!
Hajiya tayi mirmishin Takaici kafin ta kada kai tace"Ni ban isa na rufa miki  asiri ba Uwani..Asirinki Daman chan a bankade yake..Duk wanda yace Tukuyar wani bazata tafasa ba to nashi ko Dumi bazatayi ba..Ki Fito ki Fallasa kanki Uwani Domin asirinki ya gama Tonuwa kinga wannan wayar..!.To mallam ne akan layi tun Fara mganarki da kanwarki yaji komai ki jira sakamakon ki Uwani..!
Daga haka ta katse wayarta agaban Haj.Uwani Dake zufa ko"ina na jikinta na rawa ta juya ta koma Shashenta Haj.Uwani na Rarrafe tabi bayanta tana kiran sunanta Hajiya Cikin wani yanayi ko waige bata karayi ba.
Tana shigowa Falon nata ta iske su Abida nata shewa sun tasa Amina gaba da  shakiyanci sannan sauran matan kuma suna ta kara Daga kaya.
Anty Amarya ta kallah Dake Tsaye ta kasa gaba ballatana baya Mamammu kawai take kallo Tana auna yadda Balaraba ta raina mata wayau Saboda rashin ta ido ta gagije ta koma Cikin su Mamata ana ta Daga kaya da ita babu Abunda ya shafeta ko Kaffara bazatayi ba Karya ne balaraba tace batasan Amina nada Ciki ba..?
Ita Zata rufe abai bai..?
Daman ai Tun tuni ta daina Hada hanya da ita saboda taga ta riga ta gama Taimaka mata ta samu Duniya shine zataci Amanarta ta juya mata baya..?
Wlh yadda tayi alkwarin indai nata Burin bai cika ba to gayyar sai ta watse.
Tana cikin wannan Tunanin ne kawai Taji Ihun Sakina da Sauri ta juya sai taga Sakina a kasa tana gunjin kuka su Aliya na riketa da Sauri  Anty Amarya ta kariso da Sauri tana rike Sakina bata so tayi wani abun da Hankalin Mutane zai dawo kansu yasa Cikin Tsawa tace"Miye haka Sakina.?
Aliya da Sadiya ku kama min ita muje Bangarena .!
Tafada tana kokarin wucewa Sakina tayi kukan kura ta Fincike daga rikon su Sadiya ta dira gaban Anty Amarya Duk da yadda Cikinta ke murda mata Ammh ina idonta ne ya Rufe bata ganin kowa sai Hango Amina da Ciki da kuma Uban Dukiyan da Umar ya Laftama Amina.
Anty Amarya ta kauce ma Sakina tana Fadin"Miye haka..?muje bangarena Sakina..!
Tafada tana kama Hannunta ganin yadda Hankalin kowa ya koma kansu Sakina ta Fizge hannunta Tana kallon Anty Amarya da Jajayen idanuwanta Cikin karaji tace"Ba inda zamu. Anan zamu yita ta kare..!
Tafada Sai hawaye Anty Amarya tasan bata Cikin Hayyacinta yasa ta Fizge ta zasu bar Falon ammh sai Sakina ta Kwace hannunta ta Turke Anty Amarya tana Fadin"Kunya kike ji kada mutane su ji yadda kika Dade kina Rainamin wayau Anty..?
Tafada tana sakar mata manyan Idanuwanta, Anty Amarya ta Zaro Ido Tana Fadin"Sakina kina cikin Hayyacinki kuwa..?
Sakina ta Kwashe da wata Dariya kafin tace"Eh tabbas bana cikin Hayyacina..Daman ai na Haukace..kalli kazamar yarinyar nan da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe..Ni kuma kalleni shekara ta nawa ina Wahala ban samu ba..!
Koda yaushe mganar ki kenan na kwantar da Hankali na ni kadai zan zana Mowa a wajen Umar da Danginsa..Hakan ne Mowa..?
Ki kalli abunda ke faruwa a Falon nan kowa ni yake ma kallon kaskasci wannan ne Mowar..?
Ko dai Bora na zama mara amfani..?
Ina alkawarin naki..?
Ashe duk karyace bazaki iya komai ba Daga ke har malaminki makaryata ne Babu abunda zaku iya tunda har Amina ta Samu Ciki da Umar baku sani ba..!
Ta karishe Fada Cikin gunjin kuka Lokaci Daya tana jijjiga kafadun Anty Amarya tana Cigaba da Fadin"Kin manta kin Fadamin auran Amina haka zai kare a banza..?
Kin manta kin Fadamin yadda aka Daurasa haka za"a kwance sa..?
Ashe duk karya ce..?
Ashe ni kika raina ma wayau Marliya..?
Ta karishe Fada Cikin Tsawa da Budewar Murya da ya Sandarar da kowa acikin Falon har da su Sadiya da Jidda da suka zaro ido sun kasa Fahimtar me ya faru Hajiya na gefe tana kallonsu tayi mirmishi takaici ta Harde Hannayenta saman kirji Tana kallon abunda ke faruwa.
sakina ta sulale kasa tana kuka Tana Fadin"kin cuceni kin sa na yarda da kowa sama Dake...Ashe karya kike Fadamin..Ashe bazaki iya ba..Bazaki iya ba..!
Tafada tana Saka fuskarta Cikin Tafukan Hannayenta tana wani irin kukan Bakinciki da kishi.
Anty Amarya tana kokarin Daidaita kanta kada su tona ma kansu asiri ta Duka Zata riko Sakina tana Fadin"Sakina Saurare n..!

"Kada ki kara Tabani malama..!

Sakina ta Katseta Cikin karaji da sai da Anty Amarya ta fadi kasa jidda da Sadiya suka karisa suka riketa Jidda Ta kalli Sakina Cikin bacin rai Tana Fadin"Sakina Lafiyan ki kuwa..?
Kada Zafin kishi ya saka ki rasa natsuwarki mana..!
Sakina ta Dago Jajayen idanuwanta Ta balla mata Harara kafin tayi mgana Anty Amarya tayi saurin kwace jikinta cikin nasu Jidda tana Fadin"Yau za"ayi walkiya kowa zai bayyana..Na rantse da Allah ni MADINA bazan karbi Faduwa ni kadai ba..Sai dai mu yi Faduwar Guzuma..!
Tafada Lokaci Daya tana neman Balaraba Dake falon sai kawai ta Tsince ta Sum sum zata fice tun da taga Abunda ke faruwa tsakanin Madina da Sakina ta fara kokarin Barin Falon Cikin Rawan jiki Anty Amarya na Hangenta ta Daka Tsalle ta Rikota tana Fadin"Ina zaki kuma..?
Munafuka..Ai sai ki Tsaya kiga yadda wasan zai kare ko DAYYABA..?
Tafada Cikin tsaananin Tashin Hankali Datake Ciki da Jajayen Idanuwanta.
Mamanmu ta fara kokarin kwace kanta Cikin Borin kunya tana Fadin"wata dayyaban kuma..?
Marliya kada Zafin kishin ganin Amina da Ciki yasa ki fara Hauka mana..
Ko kafin ta rufe Baki Anty Amarya ta Tsinketa da mari mai Lafiya sai da kowa afalon ya Zaro ido Cikin mamaki Mamanmu sai da ta Duke Anty Amarya ta Bita ta Chakumo Wuyan riganta cikin karaji take fadin"Zaki ga Hauka yanzu nan Don Kutumar Ubanki Dayyaba..!
Lokaci Daya ta Jawo ta Tsakiyar Falon kamar kayan wanki ya Zulfa ta tare Anty Amarya tana fadin"Meyasa kika mareta kuma kike janta haka..?
Anty Amarya ta balla mata Harara da Jajayen Idanuwanta tana Fadin"Matsa ki bani wuri..Ai ke Mamanmu kika sani Balaraba baki san Wacece DAYYABA..ba yau zaku san aihinin wacece Fuskar wannan azzaluman matar..!
Sai kowa ya saki Baki Amina na Zaune tayi Dariya jin Dadi sai
Showing 108001 words to 111000 words out of 146831 words