take mgana ne yasa Dole ma ayadda da ita sannan tace ga su hanne ma yaji ta bakinsu su hanne kuma basu taba kwaye ma Amina baya ba, sai su karantamai yadda Amina tace Daga karshe sai abun ya koma kan Sakina yayi mata Fadan itace babbar banza tana Biyema yara sun rainata sannan kada ta kara Hanasu shiga kitchen ta bar su dafa abunda suke so itama ta Dafa nata baya son Fitina.
Tunda ga ranar ko Takai ma Korafin Amina ta mata kaza bai Sauraranta Anty ma Zaginta take yi tace ta Daina Danunta tunda ita Sakarya ce zata Zauna yara kanana su gagareta
Alhalin basu san yadda yaran nan suka Sakata gaba bane barin ma Amina in ta fito falo ta gansu ta rika waka kenan tana cema mata agwagwa in ta yi mgana ta maidata mahaukaciya sannan ba Tsayawa ma take yi ba,ballatana ta Daketa ta huce.
Su hanne wajen kwanansu goma Daga su Har Aminar basa zuwa makaranta da Hajiya tayi mgana ne Mallam yace ta rabu dasu Idi ya rika zuwa yana Daukosu yana kawo su makarantar Daganan,saboda dukkansu yara ne sannan nan gaba kadan In Aminar ta bar garin ina zasu ganta..?
Sannan kuma suma watarana gidan auransu zasu watarana sai dai labari..da Haka ta kyalesu suka zauna achan sai dai Idi ke zuwa yana Daukosu da an tashi kuma ya maida su.
Cin Duniyarsu da Tsinke suke yi ko ajikinsu Sakina ta koma zaman Daki bata Fitowa saboda su in tana son Tsira da Mutumcinta Ranar kwatsam sai ga Aliya matar Aliyu sun zo kawo Amarya wata Diyar kanwar mamanta ne shine tazo gidan ta iske Sakina cikin Daki Amina ta gagareta bata iya ma Fitowa sanda Sakina ke Fadamata tana kuka Sai taga Laifin Sakinar da ta Zauna yarinya karama ta gagareta.
Taja Sakinar suka fito su Amina na Falo sunyi Daidai ga Filets nan da Kofuna da gorinan lemuka da suka gama dasu nan basu Dauke ba suna Hira Ita a Dole sai ta kwatan ma Sakina yancinta..
Haka ta Dinga surfama Amina Zagi tana kiranta kwaila kazama mara Tarbiya su hanne sukayi Tsuru Tsuru Amina ranta ya baci ta mike ta rama Zaginta da Aliya ke yi ita kuma tace Zata Daki Amina ai ko sun ga Hauka Amina ta Tsaya kikam idanuwanta sun juye ba baki sai Fari tace in Aliya ta isa ta tabata tagani Sakina ke jan Aliya tana ta bari kada ta tabata ta ja mata bala"in wajen su Hajiya.
Ita kan Aliyan ta Tsorata bata Taba Aminar ba suka koma Daki tana Borin kunya Amina kuwa ba wani Abunda ya Sameta Zafin ranta ne ya taso mata Taso ta tabata ne Daga Sakinar har Aliyan sai sun raina kansu Wlh sai kuma Allah yaso su su Hanne na tabata Hakuri ta balla musu harara tace sun cika Tsoro ba wanda ya isa ya Takura musu acikin gidan nan.
Aliya taso kwana ne ammh ganin yanayin Amina yasa taki kwana ta koma gidan Amarya ta kwana ko Washegari Datace zata dawo bata Dawo ba ko da Sakina ta Kirata tace mata gata a Hanya zata koma gida ammh Tana zuga Sakina kan Wlh in Amina ta kara mata rashin kunya ta kamata ta mata Dukan tsiya Sakina jinta kawai take ina ita ina taba wannan yar gold din ai sai Hajiya ta saka Umar ya Saketa.
Allah ne ya taimaketa suka koma makaranta Hajiya tace su Dawo gida idi yazo ya Dauketa sai ta Samu Sauki Bata ma haduwa da Aminar sai ta bar gidan take Fitowa sannan Daga ranar jumma"a sai Lahadi take dawowa tana ganin Lokacin Dawowarta yayi zata shige Daki karfi da yaji Bala'in Amina da jindalinta ya Saka Sakina ta kasa Sakewa agidanta.
Gashi Danmallam ya Daina Sauraranta indai kan Amina ne yace yana wata kasar ta daina tadamai da Hankali baya so in bazata kama girmanta ba bazai iya Hana Amina ta mata Rashin kunya ba abu goma da Ashirim ga rashin miji ga Fadan Anty Amarya Data Kirata sai tace laifinta ne sannan ga Amina ta Sakota gaba..!
Ana cikin Haka Sadiya Diyar Anty Amarya ta Haihu bakwaini yarinyar tazo ba rai anan Dutse su Sakina ana ji sune gaba gaba ita da Hj.Nasara da Hajiya Babba suka tafi suka Duba Sadiya Dake asibiti domin ance ta Zubar da jini sosai achan suka Rabota Tunda Danmallan ya barta ita ta zauna da Sadiyan har aka sallamota Daga asibiti duk da ga yan"uwa ammh Anty Amarya tafi yarda Sakina ta Zauna da Sadiyan.
Bayan sun Dawo gida ne Sakina ta Fara Zazzaabi har da su karin ruwa koda akaje asibiti akayi Test aka gano Tana da Shigar ciki kimanin wata Uku da kwanaki Ashe koda Danmallam ya Tafi ya jefa kwallinsa araga a maran Sakina basu sani ba.
Murnan wajen Anty Amarya da Sakina ba"a mgana kamar an basu aljannah Hajiya da mallam ma Tare da shi kanshi gogan Danmallam Domin yana matukar son yaga kwansa a Duniya,Sannan da kansa ya Sanar da Sarood ta tayasa murna Har dai yanzu shuru ne ba wani cigaba ammh basu sare ba suna cigaba da shan mgani shi dai har yanzu ne bai yarda da Shawaran Aliyu na ya kira mallam ba yana tunanin al"amarin nasu ba Sihiri bane.

Mamanmu dataji itama tayi murna sannan tasan yanzu tunda Cikin Sakina ya samu sai Madina ta barta taci Gumin Wahalarta ta Daina Damunta.
Su ba Fatan cikin ya zauna suke yi ba kansu yayi girma suna ta Feleke Anty Amarya taso Sakina ta Dawo gabanta ta raini cikin mallam ya hana Saboda za"a bar Amina ita kadai Gidanta ta koma ammh sai Ta tafi da Sa"adatu tana kula da ita ana zuwa Daukansu Ita da Amina da ko mgana basa ma juna Amina taji zencen cikin Sakina ko ajikinta tunda ko"ina Zencen cikin ya Zaga.
Haj uwani na gefe tana kallonsu aranta Dariya take musu domin tasan wannan karon ma ba zai zauna ba Haka kuwa akayi yana da wata Hudu watarana da Daddare Sakina ta tashi Cikin Jini Hankalin Sa"adatu ya tashi ta Kira Anty Amarya koda ta zo ita da Idi Direba suka tafi asibiti sai wankin Ciki akayi ma Sakina cikin jikinta ya Sake fita karo na Hudu.
Abunda Haj.Uwani bata sani ba in na Sakina ya sake zubewa daman chan Allah bai yi Rayayye bane ammh wanda Allah zai rayasa yana nan har ya fara zama gudan jini batare da kowa ya Farga ba Hatta kuwa da wacce Cikin ke jikinta.








*Janafty**TFZB2011*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*


Bayan Sati daya da dawowar su Hajiya Daga maiduguri Ranar wata lahadi da misalin karfe goma na Safe sai ga Aliyu a falonta Danmallam ya aikosa tun daga Dutse har gumel wajen Amina.
Hajiya mamaki ya cikata Lokacin da Ta fito falo suka gaisa da Aliyu yake sanar da ita yazo neman Amina ne mamaki bai bar Fuskar Hajiya Babba ba ta kalli Aliyu Dake zube saman Cafet din falon nata kansa a kasa cikin ladadinsa kamar abokin nasa
Sai da ta gyara zama kafin tace"Amina..?
Cikin sigar mamaki kansa na kasa yace"Eh Hajiya..Yace nazo ne na kawo mata waya yana so zasu yi mgana..
Hajiya tayi wani kayattacen mirmishin su irin na manya kafin tace"To ban da abun Danmallan don wannan sai ya Tadoka tunda ga Dutse har Gumel..haka ake yi..?
Ai da ya kirani sai na basa Aminar suyi mgana sannan ni nace zan kirasa nayi mai bayanin yadda mukayi da mallam kan wayar da jafar ya kawomin sai na manta zuwana Bikin nan sannan da na dawo ma ban zauna ba Sabga tayi yawa..!
Aliyu kansa a kasa bai ce komai ba shima so yake ya gama da Hajiyar ya fita ya Tsitsiye Shehi yaji Dalilin sa na neman yarinyar daya gama Cema kwaila kazama.
Hajiya tacigaba da Fadin"Tashi ka tafi abunka Aliyu Amina bata nan suna Hadda Yau ma inaga da wuri zasu dawo Saboda hutu zasu yi sun fara Jarabawar tun awanchan satin ne In ya kiraka ka Fadamai ya kirani muyi mgana..!
Aliyu kansa na kasa ya mike yana Fadin"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma mungode..!
Ta amsa da Ameen da Fatan ya gaida iyalansa daganan ya fice zuwa shashen maallam yamai sallama suka Hade da Anty Amarya ya gaisheta cikin Ladabi ta amsa tana kallonsa cikin mamakin ganinsa da Safe haka sai dai bata Tsawaita mamakinta ba Sanin Aliyun yana zuwa gaida Hajiya da mallam Lokaci bayan Lokaci koda Danmallam din baya kasar
Shashen mallam ya koma yamai sallama zai koma domin nan ya fara shiga suka gaisa bai dai zauna bane ganinsa suna mgana da Aba yace bari ya shiga ciki ya gaida Hajiya Mallam bai kawo ma kansa shima wani abu ya kawo Aliyu ba sanin Yadda yake Darajasu Dalilin kawai suna iyayen Abokinsa Umar.
Sallama sukayi yana ta sakamai albarka da Fatan Allah ya kaisa gida Lafiya kiran Danmallam bai shigomai ba sai da ya bar Gumel ya dau hanyar Dutse Gefen titi ya samu yayi fakin sannan ya Daga kiran nasa Daga chan bangaran Danmallan yayi mai sallama kamar yadda kowa yasan shi da zarar ya Dauki waya da sallama itace Farko a bakinsa
Aliyu bai wani amsa sallamarsa ba yace"Shehi wai miye sirrin ne..?
Umar yace"Sirrin na mene..?
Aliyu yace"To gani nayi ka bi ka Rude kan karamar yarinya sa"ar yarka ta Fari kuma kwaila..kuma kazama ka tadani Tundaga Dutse zuwa gumel haka Hajiya ma ta Dinga mamakin wannan aikin naka..!
Umar ya Dafe kansa dagachan bangaran kafin yace"meyasa ka bari kuka Hadu da Hajiya..?
Aliyu yace"Dole kuwa mu hadu don Daga Falon mallam shashenta naje neman Amina ta tabbatar min da batanan suna makarantar Hadda..!
Umar yace"Kash..Da tace haka sai kayi Tahowarka ba sai ka fadamata Dalilin zuwanka ba..!
Aliyu yayi wata Dariya kafin yace"Ai aikin gama ya riga ya gamu Shehi tuni na Rattafamata komai tace in munyi mgana Dakai na sanar maka ka kirata zaku yi mgana .!
Umar yayi shuru kafin yace"Kai dai baka da biyan Bukata duk ka bata komai ni fa kunyarta nake ji shiyasa ban kirata ba ita da mallam..!
Aliyu yace"Oho zakace haka mana Tunda na gama Biya ma Bukata akwai ai watarana ba agama ba..!
Umar yace"Naji bakomai dai nagode zan kirata yanzu..!
Aliyu yace"Ni fa baka Fadamin sirrin ba..!
Umar yace"Wani sirrin kenan..?
Aliyu na Dariya yace"Sirrin abunda ya susuta ka kan Aminatu mana..!
Umar ya saki karamin Tsaki kafin yace"bansani ba..!
Aliyu ya saka Dariya kafin yace"To to..Nagano Sirrin ma..Shiyasa jiya daka kirani bakace min wannan kazamar yarinyar ba kai Tsaye ka kira sunanta Tabbas yanzu ta tashi Daga kazama kwaila ta koma Sweet Amina..Ko Honey ce..?
Umar ya tsaki again kafin yace"Kai fa Dan iska ne..!
Daga haka ya Datse kiran Aliyu yabi wayarsa da kallo yana Dariya sosai in ya Tuna sanda aka aurama Umar Amina yana ta fada yar cikinsa ne ina zai kaita sai gashi kaji sa shuru ya shiga komar yara ya kasa sukuni.
Duk da yayi matukar mamakin yadda Komai ya faru Tsakanin Amina da Shehi sai dai bai Tsananta ba Sanin Tsakanin miji da mata sai Allah ammh Shehi ya bani a wajensa ya Dinga Tsokanarsa kenan.
Yana Mirmishin ya Tada motarsa ya bi hanya yana kara Dariyan Abokin nasa yana kuma Fatan yasa Amina ta mai mugun kamun da sai ya raina kansa.!

Bayan Tafiyar Aliyu Hajiya tayi ta Tunanin me yasa Danmallan ke son mgana da Amina haka da har ya kasa Hakuri..? Bata samu amsar ta ba sai tayi Tunanin kila yana so yaji Lafiyanta ne sannan ya tambayeta ko tana Bukatar wani abu daganan ta watsar da Tunanin ta koma Bedroom dinta tana gyarawa ba Dadewa ta samu kira Daga Danmallam bayan ta Dauka sumgaisa kamar yadda suka Saba sai kuma yayi Shuru yana jin kunyar yayi mata mgana ta san Halinsa Tunda ita ta Haifesa.
Yasa ta gyara Zama tana fadin"Dazu Aliyu abokin ka yazo..akan kai ka aikosa ya kawo ma Amina waya zaku yi mgana ko.?
Dakyar ya iya amsa ma Hajiya gani yake kamar zata Fahimci abunda ya Faru Tsakaninsa da Aminar.
Cikin Dattakonta ta cigaba da fadin"To nace yayi tafiyarsa Sabgoginsa ka taso mutum Tunda ga nisan Duniya Danmallam..! Ai sai ka Kirani muyi mgana ko ba Haka ba.?
Kai tsaye yace mata"Kiyi hakuri Hajiya..
Cikin Ladabinsa bata Damu ba tace"Ni ba laifi kamin ba..gani nayi ka basa wahala..Daman ina ta so na kira ka nayi maka bayanin Dalilin Dayasa ban bana Amina wayar nan ba duk da ni nace ka siya mata mgana mukayi da mallam ya nuna min Rike waya ga Amina yayi sauri sannan Duba da har yanzu akwai kuruciya a tare da ita..hakan zai Dauke Hankalinta har ya Taba karatunta da muke Fata ta Samu,ya nuna min na bari sai zuwa gaba in kazo ka tafi da itan sai ka siya mata wayar Lokacin tana gabanka zaka kula da Motsinta yanzu kuma ya nuna min gaskiya a"a shiyasa kaji Shuru ban bata wayar ba tana nan na ijiyeta..!
Cikin gamsuwa da mganar ta yace"Hakane Hajiya..!
Hajiya tace"To kaji yadda mukayi da mallam da Dalilin dayasa kaji shuru..Sannan yace in kana son jin Lafiyarta ne ka kirani ko mallam din sai in ta na nan sai abata ku gaisa..!
Danmallam yace"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma..!
Hajiya ta amsa da Ameen kafin tace"suna Hadda ammah ina ga bazasu Dade ba in sun Dawo zan kiraka sai na Hadaku..!
Cikin Ladabinsa ya shiga Fadin"Allah yasa agama Lafiya Hajiya Allah ya kara Nisan kwana..!
Ta amsa da Ameen suka rabu bayan ta Tambayi Iyalansa da ayyukansa.
To sun ma gama wayar ba Dadewa wajen azahar sai ga su Aminan sun Dawo suna ta Murna an basu Hutun Sati ukun Dadinsu Daya gobe zasu fara Exam din second Semister a makarantar boko satin daya gabata Gabadaya Revision sukayi.
Amina ke fadin Dama islamiya ma ta bata da Hutu ai da sun ji Dadi.
Ba"a basu Sakamakon su ba sai Sun dawo Hutu sannan.
Anan Shashen Hajiya sukayi sallah Sukaci abinci Hajiya na ciki bata san Amina da Hamida sun koma gida ba Tana zuci zucin ta Kirata sai ta Kira Danmallam din ta Hadasu ko da ta Fito sai Hanne kawai ta gani a Falo ita ke Fada mata Su Amina sun tafi gida kai Tsaye tace Hanne taje ta kira mata Aminar.
Hanne ta mike ta saka Hijabi ta tafi tana zuwa ta iske su acikin Dakinsu har Amina ta kwanta bata ga mamanmu ba tana cikin Dakinta ta kwanta in ji Hamida jawaad ke ta wasa da Karamar kwallo a Tsakar gidan.
Da Farko Amina Dataji Hanne na Tashinta kin tashi tayi sai da tace mata Hajiya ke kiranta sannan ta Mike tana fadin"Kice Wlh Hanne..!
Hanne ta mike tana fadin"Au nace ma Wlh..!?
To ki zauna kin ga tafiyata..!
Amina ta mike tana fadin"Tsayani Hanne mu je..Fatana Allah yasa ba gida zata saka Idi ya kaini ba..!
Hamida da Hanne suka kalli juna kafin Hanne tace"To in chan din ne fa..? Ai kince gidan mijinki ne..!
Amina na saka Hijabi batayi mgana ba sai da ta gama sakawa sannan ta Dago Tana fadin"Ni yaushe na Fada..?
Allah ya isa na, wuta bal bal in ban Fada ba..!
Hamida na Dariya tace"Daman chan Allah ai ya ishi kowa Amina..!
Harara ta balla musu kafin ta bangaje Hamida ta wuce fuu hamida da Hanne suka.bita da kallo Hanne tace"Kamar an kara mata bala"i wlh bayan auran nan..!
Hamida tace"Kowa ma haka yake fadi..ya danmallam zai yi mganinta bari su koma Madina ki gani nan ta raina achan Ubanwa zata mawa .!
Hanne na Dariya tace aifa Daganan ta bi bayan Amina zuwa gidansu.
Koda Taje Amina da Hajiya na kuryan Daki Hanne na shiga Hajiya Data Kira Danmallam bai Dauka ba ta kalli Hanne ta nuna mata kofa Tana fadin"Jirata afalo..!
Hanne ta Tura baki kafin ta fita Amina ta Fakaici idon Hajiya tayi ma Hanne gwalo ita azatonta wani abun Dadi Hajiya zata bata sai da wayar Hajiya ta shiga kidan larabawa taga Hajiyqn ta Dauka ta mika mata tana Fadin"Karbi Mijinki ke son mgana Dake..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Dakin Harda Rufo mata kofar Bedroom din Amina gabanta ya Fadi tabi wayar da kallo ga sunan Danmallan nan baro baro na kan Layi sai jikinta ya fara rawa aranta tace na shiga uku ni Amina Allah yasa ba wani Abu akace mai nayi ba..
Jikinta a sanyaye ta kara wayar kunne Daidai Lokacin da Sanyayyiyar Muryansa ta Doketa Cikin Sallama da Hausansa daya Cakude da Larabci.
Sai da ya kara maimaita Sallamar sannan ta amsa Bakin da jikinta na rawa Tun kafin ya gama rufe baki Tace"Ina yi..yini..!

Ajiyar zuciyar daya sauke har sai da ta jisa a kunnenta Dayaji muryanta sai yaji Salama da natsuwa Cikin Taushinsa yace"AMINA...!
sai taji kamar yafi kowa iya Fadar sunan nata jin yadda ya kirata ita bazata iya tuna ko yama taba kiran sunanta ba Haka ba, jin tayi shuru yasa ya kara cewa"Amina kina lafiya..?
Cikin Sanyin Jiki tace"Na"am..eh lafiya kalau..!"

"Ya jikin ki..? Ina fatan kin warke babu kuma inda ke miki ciwo..?
Ya fada kai Tsaye domin baya Fatan ace wani abu kuma ya tashi bayan Tafiyarsa kunya ta kama Amina ta Dukar da kanta kamar yana ganinta ta kasa mgana sai gabansa ya Fadi da Sauri yace"Ko da wata matsala ne..?
Da Sauri tace"A"a na warke..!
Afili ta Furta"Alhamdulillah..!
Kafin yace"Naji Dadin haka ina Fata kamar yadda kikamin alkawarin baki gayama kowa ba ko..?
Sai da ta gyadamai kai kafin tace"Eh ban fadama kowa ba..!
Cikin jin Dadi yace"Dakyau naji Dadin Haka..Ya karatu fata kina maida Hankali wajen karatu..?.
Da Sauri tace"Eh yau ma mun yi Hutun Hadda..Gobe ma zamu Fara Jarabawa a boko..!
Kai ya gyada kafin yace"Allah ya bada sa"a..ki rika maida hankali kinji ko..?
Ta gyada kai ya cigaba da Fadin"Sannan ban da wasa ban da Fada ban da gujeguje ke yanzu ba yarinya bace kin tashi Daga su Hamida ke matar aure ce ba Daya kike Dasu ba kina jina ko..?
Nan ma kai ta gyada mai yace"Baki da baki ne..!
Ba nace ki daina min mgana Da kai ba .!
Da Sauri tace"Naji insha Allahu..!
Ajiyar rai ya Sauke kafin yace"Kina Bukatar wani abu..?
Tace bakomai kai Tsaye yace"Ki rika gaida Sakina in kun hadu tana gaba Dake kinji ko..?
Amina ta Tura baki kafin tace"Ni fa in na ganta batamin mgana sai tayi ta Hararana
Showing 39001 words to 42000 words out of 146831 words