Acikin abinda baifi minti arba'in ba miliyoyin mutane sun kalla”.
Karo na farko jikin Alh. Sulaiman ya shiga kakkarwa ta haƙiƙa. Bai gama dai-daita da wannan bala'in ba wani kiran ya shigo masa. Mai kula da ɓoyayyen Companyn sa ne na magunguna. Ruɗanin da yake ciki ya sashi ɗagawa batare da ya farga ba. Bai gama dai-daita wayar a kunnensa ba furucin Babban mai haɗa magunguna ɗin Companyn nasa ya daki kunnensa.
“Mun shiga uku Alhaji jami'an tsaro ne zagaye da dajin nan da Companyn nan. Gasu nan sun gama shiryawa da bindigu suna bamu umarnin mu miƙa kammu ta sauƙi kosu cinnama Company ɗin wuta. Yaya akayi haka Alhaji? Taya suka san da wannan wajen duk taka tsantsan ɗin da mukeyi na tsawon shekaru. Shike nan na mutu Alhaji kofa aure banyi ba balle na bar mai mun addu'a” ya ɓarke da wani irin kuka da ya nema fasa kwanyar Alhaji Sulaiman da gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa. Ƙitt ya yanke kiran tare da tada mota a haukace. Wani kiran yaga yana shigowa, baida buƙatar duba wanene ma balle ya ɗaga. Kai tsaye gidansa ya nufa cikin wani irin mahaukacin gudu. Kaɗan ya rage ya take maigadinsa da ya gigita da horn. Baiyi parking na kirki ba ya fita cikin gudu-gudu daya firgita ma'aikatan gidan. Dan babu abinda babbar rigarsa keyi sai tashi sama bulummm-blummm-blummm. Yana gab da shiga falonsa ya nema yin wani uban tuntuɓe sai gashi ƙasa wanwar. Fuskarsa ta wani irin dunguruwa da ƙasa. Duk da azabar datake ratsa masa lips da goshe da kan hanci bai damu ba ya miƙe cikin ƙarfin hali. Sai ga jini na ɗiga yararara. Falon ya afka a ɗari uku da sittin, yana ajiye ƙafarsa ciki wayar da abokan huɗɗarsa ne kawai a ciki ta cigaba da ruri. Kamar zai fasa ihu ya ɗaga....
“Alhaji Sulaiman kayi takanka. Aiki ya buɗe wlhy yanzu haka an kame su Olu.....”
Wani irin kuka Alh. Sulaiman ya ɓarke da shi kawai tare da yakice babbar rigarsa da hular ya watsar. Sai kuma ya kwasa a guje zuwa cikin bedroom ɗinsa. (Gaskiya ka zare😂🤣😂🤣😂🤣😂🤣) Passport ɗin sa ya ɗakko, da gudu ya sake fitowa yana kai waya kunnensa. Malami yake kira yana ɗagawa ya ce masa ya siya musu ticket yanzun nan ta online nama kowacce ƙasane. Jirgin da zai tashi yanzu-yanzu dai yake buƙata. Yayi maza kuma su haɗu a airport.
Hankalin ma'aikatan gidan nashi ya tashi ganin gaba ɗaya kamar ya zare. A take sukai kiran Hajiya Turai suka sanar mata gida da babu lafiya. Dan sun gagara gane kan Alhaji gashi nan ya shigo a haukace, ya kuma fito ya shiga mota da alama sake fita zaiyi”. Kafin sukai ƙarshen wayar ma shi ya fice a gidan a haukace......
*_★UK★_*
Tun Smart da ke ganin komai na halin da Alh. Sulaiman ke ciki ta direct camara ɗin su yana dariya har al'amarin ya fara tada masa hankali. Jin da yay Alh. Sulaiman na shirya guduwa ya sashi saurin kiran Uncle Yousuf ya ce suyi report Immigrations office. Dan tabbas suka bari ya tsallake ƙasar yasha kenan. Dan a ƙasashen ƙetare yanada wanda zasu bashi kariya tunda bada kayan aka kamashi a hannu dumu-dumu ba. Cikin sauri Daddy ya aiwatar da hakan kuwa. Lokacin da Alh. Sulaiman da malami ke isowa airport har an fara shelar masu tafiya a jirgin Dubai su shirya. Sunyi farin ciki da samun hakan, dan Malami har ya siya musu ticket ɗin ta hanyar cuwa-cuwa ta hanyar wasu ruɓɓaɓun ma'aikatan da ke da alhakin hakan ta online. Restroom Alh. Sulaiman ya nufa domin canja kaya, yana fitowa har tuntuɓe ya nemayi wajen saurin nufar jirgin da har mutane sun fara shiga. Yana taɓa ƙofar ainahin inda hanyar zuwa wajen jirgin yake aka dakatar da shi duk da ya rufe fuska da facemask da glasses ga p-cap. Cikin masifa yake tambayar ba'asi. Kai tsaye ma'aikacin ya bashi amsa da yanzu-yanzu an tabbatar musu da karɓe lasisin fitarsa wata ƙasa. Sun samu saƙone kuma da ga immigrations office. Jiyay tamkar ya saki zawo a wando. Amma abinka da ɗan cocaine sai ya nema birkice musu har yana ƙoƙarin ture jami'in shi a dole zai wuce. Dai-dai nan aka sauke masa bindiga a saman kai tare da nuna masa handcuffs a kan fuska. A dake aka furta.
“You are under arrest Mr Garko..”
A wani irin hargitse ya juyo kunnensa na bada wani irin sautin tsuuuu!!! Kamar an doka masa guduma a kansa. Ido biyu yay da jami'an tsaro na ƴan sandan farin kaya wato DSS da na ainahin ƴan Sanda, dana immigrations sai na filin jirgin zagaye da shi kusan su hamsin. Kuma kowanne riƙe da bindiga. Gaba ɗaya airport ɗin tayi tsitttt baka ganin komai sai hansken wayoyin mutane dana ƴan jarida. Masu video nayi, masu hoto nayi, masu kallo nayi. Harda masu nunawa live a social media. Sai kawai ya rimtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sun yi bala'in mimmiƙewa ruɗu-ruɗu. Bashi da zaɓin da ya wuce yin surrender kawai. Amma saboda ƙarfin hali da taurin zuciya irin na Tsule sai gashi da fakar ido ya hamɓari na gefensa bindigar hannunsa tai tsalle sama ya tare hannu ya cafe tare da ɗaurata saman kanta. A cikin abinda bai wuce sakan biyu ba hakan ta faru, shi adole sai ya tabbatar musu shi ɗin ƙwararren maharbi ne. Bindigar a saman kansa yana dariyar da tafi kuka ciwo da nunasu da hannu ɗaya ya ce, “Lusarai kawai. Da na miƙa kaina gareku wlhy Gara na kashe kaina. In ce dai shine ƙarshen abinda za'a iya min a duniya ko....”
“Karka aikata haka Mr Garko. Yin hakan kuskure ne ka miƙa kanka ga hukuma salin alin zaifi maka sauƙi”.
Shugaban NDLEA ne dake ƙarasowa yanzu ya faɗa daga inda yake tsaye. Wani banzan kallo Alhaji Sulaiman yay masa. Sai kuma ya kwashe da dariya yana ƙoƙarin ɗan kunamar bindigar. Tauuuuuu!!!! Kakejin sautin ya karaɗe airport ɗin da ya saka mutane fara kwasa a guje cikin ruɗewa da rikicewa.....
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣9️⃣
.........Tana gama sakin videon da mintuna kaɗan Abdull na isowa asibitin shi da Asma'u. Da gudu tazo ta rungume Lulu cike da farin cikin ganinta. Basu wani ɓata lokaci ba suka shiga motar da Abdull ɗin ya tuƙo. Kai tsaye gidan da su Ammah ke zaune a yanzu kafin a kammala nasu da saura ƙiris suka nufa. Nan ɗin ma gida ne babba wadatacce da suke zaune babu takura. Duk zumuɗin ganin Ammahn da takeyi sai kuma ta ɓige da jin kunyarta. Ammah dake mata dariya ta rungumeta a jikinta tana mai farin cikin ganinta. Harga ALLAH ita tana jin Lulu a cikin ranta tamkar ƴar da ta haifa bawai suruka ba. Bata bari ta zauna ba sai da sukaje ta gaida Abba. Shima yayi farin cikin ganinta yana ta sanya mata albarka da mata ƙorafin rashin zuwa da AA bayan ya tambayeta jikin Dada. Duk da anan ɗin ma dai ya mata ƙorafin rashin faɗa musu da basuyi ba sai jiya suke sani. Haƙuri ta bama Abban da tabbatar masa suma basu sani ba sai da ga baya. Ta ɗan jima a wajen Abba suna hira sama-sama duk da ita duk a kunyace take kafin suka dawo ɗakin Ammah. Mama tayi ƙarfin halin zuwa mata sannu da zuwa kamar yanda taga aunty Amarya tayi. Bata nuna musu komai ba duk da dai taso taga idon Ummah, amma Asma'u ta sanar mata ai tana gidan yayanta ne sai an gama gini zata koma can da zama, sai dai Abba ya mata saki uku ma. Ko a jikin Lulu, sai ma zama data gyara tana shan kunun gyaɗa datace tana so Ammah da kanta ta dama mata. Dan a kallo ɗaya ta fahimci Lulu na ɗauke da ƙaramin ciki. Murnar kasancewa da su Ammah dan Maryam ma babu jimawa ta dawo daga makaranta ya mantar da ita wani batun Alh. Sulaiman. Sai dai tayi kiran Aunty Naja'atu ta tambayi ko Dada ta farka. Ta sanar mata bata farka ba ance sai bayan la'asar. Dan haka ta sake miƙe ƙafa har sai bayan la'asar ɗinne suka fito harda su Ammah da zasu je duba Dada. Sai a lokacin sukaji halin da garin Kanon ke a ciki. Abdull da Mubarak dake bibiyar komai suka shiga basu labari. Kwaɓarsu Ammah ta shiga ƙoƙarin fara yi wai saboda Lulu, amma sai sukaji lulun na ƴar dariya da faɗin, “Ammah barsu su bamu musha. Indai wannan ne baida maraba da wanda ban haɗa komai da shi ba a duniyar nan, dan inda akwai wanda ya tsanesa to nice farko kuwa.”
Shiru kowa ya kasa cewa komai a motar har suka iso asibitin dan furucin Lulun ya girgiza zukatansu.....
_________★
Ba jama'ar gari ba, hatta jami'an tsaron duk sun ɗauka Alh. Sulaiman ya kashe kansa ne. Hatta Smart da ke kallon komai ta can wani irin rumtse idanu yay da dunƙule hannaye ya kaima iska naushi da faɗin, “Ohhhh Shiittttt!!!!”.
Wahalalliyar ƙarar da Alh. Sulaiman ya sakice ta saka kowa ɗagowa da sauri. Dai-dai Alhaji Sulaiman na kaiwa ƙasa durƙushe akan gwiyawunsa bindigar hannunsa na faɗuwa ƙasa itama ya dafe hannun damarsa dana haggu dai-dai inda ƙwararrren maharbin jami'in ya sakar masa bullet. Kowa kallonsa ya maida akan jami'in, shiko ko'a jikinsa sai ma hura bakin bindigarsa da yay da baki ya turata cikin aljihun wandonsa yana ƙarasowa gaban Tsule. Wani irin fisgar hannuwan nasa duk biyu yay zuwa baya batare daya damu da jinin dake ɓulala a hannun Alh. Sulaiman ɗin da bullet ya ratsa ba balle jin tausayin maɗoɗowar azabar da yake yi ya saka masa handcuffs. Sai a lokacin mutane suka farga da ashe bai kashe kan nasa ba jam'in yay nasarar harbinsa a hannun bindigar ta faɗi.
Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe Alh. Sulaiman. A haka aka taso ƙeyarsa zuwa wajen airport ɗin yayi wujiga-wujiga. Da ƴan uwansa ya fara tozali tsaye reras su huɗu mahaifinsu a tsakkiya cikon na biyar. Kallo ɗaya dayay musu bai sake marmarin ƙarawa ba saboda irin wutar bala'in da ya hanga a fuskokin nasu musamman ma autansu na maza dake wani irin huci kamar kumurcin maciji Uncle Taheer. A karo na farko yaji wasu irin hawaye sun sakko masa masu zafi da ɗaci. Babu zato babu tsammani yaji saukar wani irin gigitaccen mari maisa a gano ƙyallin kabari har saida ya durƙushe ƙasa. Bai gama dawowa a hayyacinsa ba aka sake sauke masa wani. Ba kowa bane da wannan aikin face auta da Uncle Amin. Har sai da sauran ƴan uwansa Uncle Muneer da Uncle Khamil suka rirriƙesu. A hankali Baba Garko ya ƙaraso gabansa hannunsa riƙe da ƙyaƙyƙyawar sandarsa ya zuba masa idanu na wasu sakkani. Sai kuma cikin ƙarfin hali ya saki murmushi mai ciwo. Cike da dattakon nan nasa yasa sandarsa ya ɗago haɓar Alh. Sulaiman da bai gama dawowa daga gigitar marin da yasha hannun ƙannesa na uku dana huɗu ba. Muryarsa da ɗaci sosai yace, “Sulaiman bazan maka baki ba. Sai dai ina baƙin ciki da takaicin saka maka suna mai daraja da kima irin wannan. Sannan ina jin raɗaɗin kasancewar ka jinina. Sai dai bazanma UBANGIJI butulci ba, domin ya bani huɗu gasu nan duk na ƙwarai, tare da biyu mata da basa raye duk da kaine kai sanadin mutuwar Sultana. Sulaiman kai ba mutum bane shaiɗani ne, dabbane tunda har zaka iya haikema ƙanwarka ƴar shekara tara kacal da lafiya bata isa ba. Kaiconka Sulaiman ka tabbatar asararre a wannan duniyar wlhy. Gashi nan kazo a banza zaka koma a wofi dan bana maka fatan shiriya harka koma ga ALLAH. Yau ina kuɗin daka tara ta hanyar haramun ɗin? Ina damar da kake ganin kanada ita ta lafiya da rayuwa da dukiya? Ka lalata dubban al'umma ta hanyar miyagun kwayoyi, kasa iyaye da yawa kuka! Kasa mataye da yawa kuka! Kasa mazaje da yawa kuka! Ina zaka da hakkin waɗan nan bayin ALLAH koda basu furta maka ALLAH ya isa ba. Kaiconka Sulaiman, wlhy bana fatan wani ya yafe maka akan wannan al'amarin koda mutum ɗaya ne. Kaje in dai duniya ce gaka nan a cikin tarkonta, ka gama wahala a cikinta kaje ka fiskanci hukuncin UBANGIJI kuma. Da ga yanzu na haramta maka sake amfani da sunana kona zuri'ata har bada”. Daga haka ya juya yana sharar hawaye. Yaransa dake bin Sulaiman da mummunan kallo suka take masa baya.
Wani irin durƙushewa Alh. Sulaiman yayi a wajen ya ɓarke da kuka. Dan kalaman makaifin nasu sunyi masifar shigarsa shiga mai tsanani da ƙarfi a cikin jini da ɓarko ta yanda baiyi zato ko tsammani ba. Da ƙyar jami'an tsaron suka iya ɗagashi aka jefa a cikin mota....
*_3 DAYS LATER_*
A yanzu kam babu wani latest topic dake yawo a media da gari sama dana Alh. Sulaiman. Hatta maganganun da Baba Garko ya faɗa masa da marin da ƙannensa sukai masa sai yawo suke a social media. Hakama ɓoyayyen Companyn sa na magunguna sai da aka gayyaci ƴan jaridu sannan akai masa filla-filla. Baba Garko da ƴan uwansa sunje har Companyn suma. Sosai hankalinsu ya sake tashi saboda ganin ɗunbin aika-aikar da jinin nasu ya jima yanayi batare da sun farga ba. Harda jarirai a wajen da ake gwada magani a jikinsu kafin a fitar, wasu sukan mutu wasu su kamu da ciwuka al'amarin zattashin hankali dai. Ƴaƴansa kam kuka har suna rasa hawaye. Dan biyu da ga ciki harda saki mazajensu sukai musu.
Duk yanda Baba Garko ke ƙoƙarin danne komai ya cigaba da zama ba komai ba hakan ya gagara. Dan kuwa dai sai da takaisa kwanciya a gadon asibiti. Yayinda aka samu ita kuma Dada ta maro. Sai dai bata iya dogon magana sai kuka da jama Sulaiman kalaman ALLAH ya isa da faɗin, “Nayi dana sani ni Hajarah, dama Mawaddat tasha faɗa min Sulaiman na lalata yaran masu aiki kuma nima na sani amma son zuciya da son ƴaƴa ya hanani ɗaukar makaki sai da akaima Sultana fyaɗe. Ashe na rigada na makara tun a wancan lokacin, ashe shine ya wulakanta min mutuncin yarinya ya halaka min ita. Yarinyar da ko cikakkiyar lafiya bata da shi. Kaicona ni Hajara kaicona da irin son zuciyata. Gashi nan takaini ta baroni a gaɓar da bazan iya komai ba na dawo da baya balle na gyara. Wane irin abin kunya ne wannan da tozarci. ALLAH ya tsine maka Sulaiman. ALLAH ya ƙuntata rayuwarka tun daga nan duniya. Wlhy bazan yafe maka ba. Inama ɓarin cikinka nayi ko mutuwa naima gaba ɗaya a lokacin haihuwarka. Dama kin cemin zanyi nadama mara amfani idan ban gyara ba, kin faɗamin banji ba Mawaddat,, ban saurareki ba, da ace na saurareki da banga wannan mummunar ranar ba a rayuwata. Inama na mutu kafin zuwan wannan ranar. ALLAH ya isa Sulaiman.....” ta sake fashewa da kuka. Lallashinta aketayi akan ta daina tsine masa da muguwar addu'ar nan. Amma ina Dada idonta a rufe yake. Babu abinda take hangowa sai Sultana kwance cikin jini, yarinyar da har aka kaita makwancinta jini bai daina fita a jikinta ba. Haka aka sakata a kabarinta likafaninta duk jini.
Lokacin da Lulu dake kwana a wajen Ammah yanzu ta shigo Dada ta riƙota jikinta tana kuka. Itama sai Lulun ta kama kuka. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu da ga jikin Dada saboda aman jinin data fara. Dama Doctor ya sanar musu zuciyarta ta taɓu sosai sai abinda ALLAH yayi kawai. Hankalin kowa ya sake tashi, dan Baba Garko ma hanawa akai a faɗa masa..........✍️

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣0️⃣
........Sai da suka tabbatar ya gama jigata da bullet ɗin da ke jikinsa sannan suka cire masa. Washe gari suka bisa da duka na hauka wanda ya kaisa harda karaya a ƙafa, suma kam yayita babu adadi suna farfaɗo da shi. Duk wanda yaga yanda ake wajiga rayuwar Sulaiman zai tabbatar da al'amarin da biyu ne. Inda ma aka ɓoyesa kawai tashin hankali ne. Dan da ƙyar Daddy da Lulu ta matsawa da son ganin Alh. Sulaiman ɗin sukaje aka barsu suka ganshi, ya samu wannan alfarmar ne kawai saboda taimakon da ya bama jami'an tsaro wajen cafke su Alh. Sulaiman ɗin. Daƙyar Alh. Sulaiman ya iya ɗaga ido ya kalla Daddy da Lulu data juye masa tamkar mahaifiyarta, saboda duka ya taɓa masa ido ɗaya. “Miya kawoka wajena?!”.
Ya faɗa da ƙyar muryarsa na karkarwa. Iska Daddy ya firzar yana mai ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido. Dan ganin yanda akaima Sulaiman ɗin raga-raga a kwana biyu kacal ya ɗaga masa hankali. Da ƙyar ya iya danne rawar lips ɗinsa ya furta, “Nazo ne na tabbatar maka wasan ya ƙare Sulaiman. Dama irin wannan ranar nake guje maka a baya amma ka kasa raurarena da fahimtata sam. Ka ɗauki tsawon shekaru kana tsula tsiyarka amma ka duba cikin abinda bai wuce awanni arba'in da shida ba ka koma tamkar bakai ba. Wannan fa kamun
Showing 279001 words to 282000 words out of 294165 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94 Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99