Sai da sukai mai isarsu ya jiyo yana kallonta. Ganin yanda ta zuba musu ido ya ɗan ɗage gira da faɗin, “Kallon fa Madam”.
            “To ba dole na kalleku ba naga kun zare. Wai nikam dama kana dariya har haka? Amma da kaita tsuke fuska kamar wanda akaima saƙon mutuwa!”.
     Kansa kawai ya shafa yana murmushi baice mata komai ba. Itama sai ta share ta cigaba da shan Apple ɗin ta. Lokacin-lokaci tana saka masa a baki shi da AA da ke saman jikinsa yana wasa da ƙasumbarsa.......✍️

_🚴Ya kamata mu taya Ummah da Addu'a 🥱🥱🥱_



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣


.......Haka suka cigaba da kasancewa cikin farin ciki da nishaɗi a wannan yini. Sai zuwa wani lokaci yayi kiran Ammah kasancewar su a Nigeria ba daren bane. Sun gaisa sai yake jinta kamar cikin damuwa. Cikin kulawa ya shiga jera mata tambaya. Sai cewa tai babu komai ya haɗata da Mawaddat. Kafin ya bama Lulun ne take tambayarsa babu dai wata damuwa kowa?. Ya ce Alhmdllh yanzu haka ma gasu nan AA ya ishesa da ɓarna. Murmushi Ammah tayi har yana iya jiyo sautinsa. Ta ce, “Ai wannan baban nawa yana ji da ƙarfi da lafiya ne, nima ɗakina ya huta da ɓarnarsa ai yanzu, ga shi nan duk yamun fashe-fashe kala da iri. Dan Babana ne kawai yasa bance a biyani ba”.
      Cikin dariya Smart ya ce, “Ai ba'a shiga tsakaninku da Baban naki kam Ammah. Sai dai nayi mamakin yanda yay girma haka, ashe hoto na rage min girman nasa.”
         “Ai duk kai ya kwaso Hydar. Babu wani abu naka da yaron nan ya bari. Yanzu dai Alhmdllh komai ya zama labari, sai ku sake dagewa da addu'oi dan ita matsalar rayuwa da jarabawa basa ƙarewa. Idan wannan ta wuce watace kuma zata iya kutso kai a kowane irin lokaci. Abinda dai kawai ake buƙata shine bawa ya tsarkake zuciyarsa kada ya nufi kowa da sharri, domin shi ɗan aike ne duk inda ka aikashi sai ya je ya dawo ya tabbatar maka yaje. A zauna da mutane lafiya dan ALLAH, kar a zalunci wani koda da ganganci ne, idan kaima mutum kuskure ka bashi haƙuri ka kuma nema afuwa, sannan ka gyara wannan kuskuren. Ga matarka nan dai ta dawo gareka, sai aji tsoron ALLAH ka sauke hakkokinta da ALLAH ya ɗaura maka, karka zalunceta saboda kana amsa suna Namiji shugaba ita tana mace kai rauni, karka ce akoda yaushe dole kaine a sama da ita, shi aure ƙauna da haƙuri da kawaici ke jagorantarsa yay ƙarko. Sannan shi babba shi aka sani da shanye komai daga na kasa da shi, idan laifi tai maka kayi nazari da bincike kafin yanke hukunci, karka yarda ka yanke hukunci cikin fushi, karka yarda kace zaka zagi iyayyenta a bisa kuskurenta, kada ka aibantata ko hantararta dan kawai ta maka abinda bashi kake so ba. Nasiha da jawowa a jiki shike saka zuciyar waninka maka biyayya komai taurinta, a duk lokacin da ka kasance mai adalci da tattalin rayuwar mace da ƙyautata ma da yin haƙuri da ita ba sai kace ta kiyayeka ba, ita da kanta zata dinga jin shakkar maka laifi ma, bakuma zata taba samun nutsuwa ba idan ta ganka cikin damuwa. A duk kuma sanda tai kuskure ka tsawata mata zata fahimceka fiye da yanda kake buƙata. Ka yabama matarka a duk sanda tai abu mai ƙyau, ko kwalliya ta maka kwarzantata ka nuna mata duk duniya babu ƙyaƙyƙyawa a wajenka sama da ita, idan girki ta maka nuna mata tafi kowa iyawa, babu kuma wani abinci dake maka da ɗi sama da nata. Idan tana magana da kai ka bata hankalinka da ɗaukar kowane furucinta da muhimmanci koda kai a wajenka bamai muhimmanci bane. Ina mai tabbatar maka Aliyu matarka saita maidaka tamkar sarki, zaka zama ɗan lelenta, zaka zama amininta, zaka zama mata ɗan uwa, zaka zamar mata jarumi, zataji babu wanda take so ta birge a duniya sama da kai. Komai iyawar waninka za taga taka itace a sama da kowa. ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka. ALLAH ya kiyaye gaba”
     “Amin ya rabbi Ammah, in sha ALLAHU zaki sameni mai biyayya akan shawaranki da umarninki. Nagode sosai, ALLAH ya ƙara muku lafiya da tsohon rai mai albarka. Ga Mawaddat ɗin dan naga ta ƙagara kamar ta kwace wayar”.  Dariya Ammah tayi, yayinda shi kuma yake mannama Lulu wayar a kunne yana dungure mata kai. Alamar zan rama tai masa tana faɗin, “Ammah na” cikin zumuɗi. Cike da farin ciki itama Ammah da ga can ta amsa mata da “Na'am Mawaddat ɗina. Kun sauka lafiya ko?”.
      “Lafiya lau Ammah ina yini?”.
   Da kulawa Ammah ta amsa mata da tambayarta AA. Tai murmushi kawai batace komai ba dan sosai take jin nauyin Ammah akan al'amarin AA ɗin. Ta rasa miyasa hakan. Saboda ita kaɗai take iyama wannan karan. Garama Mommy itama akan ɗan ɗaga mata ƙafa wasu lokutan. Hira sukayi da Ammah sosai, itama tai mata nasiha tamkar yanda taima Smart, dan tana jinta babu bambanci da ƴaƴanta ne, sosai Lulu taji daɗin shawarwarin Ammah, harda ƴar ƙwallarta. Sun cigaba da hira har takai kunnen Lulu ya jiyo ihu da hayaniya. A tsorace take cema Ammah suwa ke ihu haka?. Rasama mi Ammah zatace mata tayi, shima Smart jin an ambaci ihu ya amshi wayar yasa a hansfree. Cikin ƙarfin hali Ammah ta ce, “Babu komai yara ne ke wasa”.
     Haka kawai Smart yaji bai gamsu ba. Amma sai baice komai ba har sukai sallama. A yanayin damuwa Lulu ta ce, “ALLAH kamar Ammah na cikin damuwa”.
        Kai Smart ya jin jina mata. “Tabbas akwai abinda take ɓoyewa. Kuma tunda kikaga taƙi faɗa mana bamai daɗi bane. Ina zuwa bari na kira Aunty Bilkisu”.
     Wayar ta miƙa masa, yana kira kuwa aka ɗaga. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaya jikin ta. Ta amsa masa cewar da sauƙi. Sai dai jiya mai gidanta yayi maganar cewar wai zai kaita Egypt, “Amma ina zargin dan Abba yay masa maganar cewar kace zanzo wajenka naga likita ne. Dan tunda matarsa ta dawo na kasa gane kansa a gidan nan Aliyu. Ni wlhy zaman nan yama isheni. Hatta yaran nan baya shiga harkarsu, jiya dan Sadiq yay faɗa da yarinyar wajenta bakaga dukan da babban yaronta yay masa ba, wai nayi magana shine yake faɗin banda haƙuri akan yara da kawaici.”
      Sosai ran Smart ya ɓaci, amma sai ya shanye cikin danne zuciyarsa ya shiga bata haƙuri da lallashinta akan karta damu. A yanzu haka ma yana nan yana mata shirin tahowar cikin satin nan Ahmad zai zo ya kaita tayi visa, shi kuma mijin nata ta share batunsa kawai. Yaran kuma ta kaisu wajen Ammah daga can a dinga kaisu makaranta. Taji daɗin shawararsa sosai. Da ga haka take tambayarsa ina Mawaddat. Shekaranjiya abinda ke faruwa a gidan nasu yasata ɗan taƙarƙarawa taje shine Ammah kece mata ai sun komo wajensa. Har take tsogumin basuje musu sallama ba shine Ammah tace ai tafiyar ta shamattace akai babu wanda ya sani..
       “Wani abu ya faru a gidan ne?”.
   “Ammah bata faɗa maka bane? Ai mugun abin waccan azzalumar matar data muku ne ya koma kanta. Dan yanzu bakaga yanda ta koma wata irin mummunar halitta ba wlhy Hydar. Kowa fa bai iya zuwa inda take yanzu gidan nan cika yake da ƴan kallo harda ƴan jarida. Ai Umma taga ƙarshenta”.
          “Ni duk kin sake dilmiyar dani wlhy Aunty. Please kimin dalla-dalla miya faru da Ummahn?”.
      Tsaff aunty Bilkisu ta zayyane masa labarin abinda ya faru tun jiya da Lulu ta taho. Sosai suka girgiza da jin wai Ummah ce ta musu asirin nan, kuma yanzu haka ma kowa ita yake zargi akan abinda ya dinga faruwa da shi lokacin da yake faɗuwa idan ya shiga filin ball. Komai bai iya cewa ba sai ALLAH ya ƙyauta ganin yanda Lulu duk ta ruɗe harda su kuka. Dole yay sallama da aunty Bilkisu ya rungume matarsa a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jazur. Ganin yanda Lulun ta tsorata ya sashi ɗan sakin jikinsa shi. Fuskarta dake cikin tafukan hannunsa ya ɗago suna kallon juna. Ya ɗan ɗaga mata gira cike da tsokana. Sai kawai ta sake fashe masa da kuka. Dariya yayi a karo na farko. “Wai anya kuwa keda AA kunada maraba kuwa?. Shagwaɓanki yayi yawa. Yanzu minene abin kuka anan?. Ko kina jin haushin an rabaki da mijinki ne harna wata kusan goma bakiji ɗuminsa ba. To yanzu ba gaki tare da ni ba barci sai inda kika zaɓi kwanciya a jikina”.
         Hararsa tai tana ture masa hannu. Shi kuma ya cigaba da dariyarsa yana kai mata kiss a fuskar. Bai barta ba sai da ya ga ta saki jikinta har tana dariya. Cikin sakin ajiyar zuciya a jajjere ta ce, “ALLAH naji tsiro ne Aliyu. Ni dama matar nan haka kawai bana sonta. Ashe muguwa ce. Kenan fa tana cikin wani ƙungiyan secret ne?”.
        “Secret kuma?”.
   “Eh mana tunda gashi tana iya turama mutane Dodo”.
    Fuskarsa da murmushi ya ce, “Ba wani ƙungiya. Kin san a ƙasar hausa mata sun ɗauki kishi wani babban al'amari. Wasun ku zasu iya aikata komai saboda wannan kishin nasu. Bansan dalilin Ummah na aikata min hakan ba, dan ni taimawa ai. Amma nasan koma minene yana da alaƙa da kishi. Na jima da fahimtar ta tsani Ammah da mu kammu. Dan lokacin da akace na aureki baki ji yanda ta tada hankalinta wai na auri ƴar gidan masu kuɗi. Hakama aurarrakin su Hawwah”.
        Cikin mamaki Lulu ta ce, “Oh dan gidanmu da kuɗi ka auran shine matsala kuma?”.
     “Su haka suke gani. A tunaninsu ƴar masu kuɗi sai ɗan mai kuɗi. Idan ma za'ai irin wannan auren bisa ƙaddara ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka yafi ƙayatarwa suke gani. Amma idan ƴar mai kuɗi ta auri talaka kamar zai zama ƙarƙashin mulkin mallakarta ne. Koda yake mafi yawa hakan ce ke faruwa shiyyasa tunanin duk mutanenmu yake a iri ɗaya.”
          Baki Lulu ta taɓe kawai. Kamar bazatace komai ba sai kuma can tace, “Ni wannan abin ban ɗaukesa wani abu ba. Kowa bada yanda ALLAH ke son ganinsa ba. Talakawa nawa ne keyin arziki, masu ƙuɗi nawa kuɗinsu ke ƙarewa su koma abin tausayi. ALLAH da Daddy na bani tarihinsu shi da su Mommy da Uncle You har kuka nayi, kaga suma da basu da komai, amma yanzu fa. Kuɗin da duk mutuwa kowa zaiyi ya barsu ma”.
        Kallonta Smart yake cike da jin ƙaunarta, bai taɓa sake tabbatar da tanada hankali ba sai yau. A hankali ya jawota jikinsa ya rungume tare da kai mata kisses tako ina a jikinta. Batai yunƙurin ƙwace jikinta ba kamar yanda ta saba. Sai da taga yana neman sakin layi ne ta shiga turesa, sai dai shi ya riga ya kai inda baya jin kira, dan haka ya ɗakko sabon salon kashe mata jiki har ya ɗauki hanyar cimma burinsa. Sosai ta rikice masa dan a tsorace take da al'amarinsa. Shi kuma ya tabbatar mata da babu gudu babu ja da baya. Duk da yau bata sha wahalar waɗan can matakan ba yanzun ma dai taji a jikinta. Shi kuma yasha raki da langaɓe. Lallashi yay tayi shi dai kam tunda ya samu yanda yake so. Bai kuma wani ja dogon lokaci ba ya sake nuna muradinsa, sai ta sanya masa kuka harda cewa ita Nigeria zata koma bazata iya da shi ba gaskiya. Dariya yayta dannewa, bai kuma ƙyaletan ba sai da ya samu yanda yake so. Aiko yasha baƙar magana a wannan yini, harda cewa sai ta gaya shi da Uncle Yousuf da Ammah. Ya ko miƙo mata waya cikin gyatse ya ce ta kira. Amsa tayi zata kira ɗin kuwa. Yanzu ya sake tabbatar da wautar ɗiyan madara, dan sai fisge wayar yay ya ɓige da cema Uncle Yousuf ya kira ne su gaisa. Dariya Lulu ta koma yimasa harda gwalo, dan ita wasa take masa, yo hauka take tacema Uncle Yousuf ɗin mi ma. Ta kula kallon yarinya Smart yake mata, shiyyasa take zuba masa taɓarar yaran aje a hakan........✍️


_Kiyi son ranki Dan lokacinki ne ta wajen mu🥱😂😂🚴🚴_




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣



.......Smart ya samu zama da Daddy da ya shigo London a ranar da Lulu ke cika kwanaki biyar. A ranar sun buga wasa a cikin London ɗin ne, bayan sun tashi ne sukai zaman tattaunawa su uku harda Uncle Yousuf da ya shigo domin kallon wasan shima. Daddy ya damƙa masa camara, tare da tabbatar masa Sulaiman yana shiri na musamman a kansu. Dan a yanzu haka akwai wata yarinyar baturiya da ya gano an turota ta shiga jikin Smart ɗin. Shiyyasa ma yay azamar kawo masa matarsa kusa da shi saboda gudun kar'a samu akasi. Murmushi Smart yayi da firzar da iska. Kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Daddy in sha ALLAH babu abinda zai faru. Kafin na mallaki iyali nafi ƙarfin kaina ma balle yanzu da na tabbatar da har zuri'a na fara tarawa. In dai al'amarin Sulaiman ne yabar damunka, dan a yanzu haka a tafin hannunmu yake. Abinda nake buƙata a wajenka kawai yanzu bayan wannan camara ɗin shine list ɗin abokan huɗɗarsa. Sannan ka sa su Hassan subar Abuja su koma Kano gabanku. Dan Sulaiman ya fara kai musu hari ta hanyar aboki, a yanzu haka ana gab da jan ra'ayinsu da wani kasuwancin da nake ƙyautata zaton irin shigo-shigon da akai maka ne”.
      Sosai hankalin Uncle Yousuf da Daddy ya tashi, dan sam Daddy hankalinsa bai kai wajenba saboda wani babban business da ya dauki hankalinsa kwana biyun nan. Smart kuma bai sanarma Uncle Yousuf ba dan yakan ɓoye wasu abubuwan gudun tada musu hankali. Muryar Daddy har rawa take wajen faɗin, “Aliyu yaya akai kasan wannan kai da kake anan?”.
    Murmushi Smart yay masa, cikin shafa kai ya ce, “Daddy koyarwarka ce ai. A yanzu idanuna a buɗe suke akan duk wani motsin su Sulaiman da tawagarsa. Sannan Usman ya sake zame min cctv camara. Dan yanzu haka yana Nigeria yin wani aiki da ya shafi hakan ma. Sannan Uncle Yousuf shine jagoran tafiyar,..”
     Da sauri Daddy ya dubi Uncle Yousuf. Murmushi yay masa ya kauda kansa shima. Smart yay dariya shima da cigaba da cewa, “Mu yanzu fatanmu Daddy kaje ka kwanta abinka ka huta. Karka damu da duk wani ƙulle-ƙullensu dan biye muke da su. Yanzu haka a daren jiya sunyi zama kanka harma da Abba. Sannan akwai kayansu dake hanyar shiga Nigeria. Kayane masu nauyin gaske da suka haɗa kusan kaso bibbiyu na dukiyarsu domin kawosu, dan mugayen kayan shaye-shayen ne kawai a cikinsu da in har suka samu shigar da su zasu samu maƙudan kuɗaɗe. Target ɗin mu yanzu muna zargin Sulaiman nada Company na sarrafa magunguna a ɓoye, sai dai bamu san a ina Companyn yake ba, shine muke bibiya domin mu tabbatar...”
        Ji Daddy yay kamar ya saki kuka, hannayen Smart da Uncle Yousuf ya kamo a cikin nashi, sai ma ya rasa mizaice da su. Sai ga hawaye kawai na gudu a fuskarsa. Da ga Uncle Yousuf har Smart rikicewa sukayi. A take suka shiga jera masa tambayoyi. Sai ya sakar musu murmushi yana goge ƙwallar tasa da faɗin, “Kunga bafa wani abu bane. ALLAH yay muku albarka. Ban taɓa tunanin zanga irin wannan ranar ba a gareni. Domin na ɓata tsahon shekarun girmana a tunanin yanda zan ɓulloma wannan al'amarin ne. A duk sanda nayi hangen sako su Hussain a ciki sai zuciyata ta ƙi aminta da hakan, saboda su sunada rauni. Sannan har yanzu suna a kan dokin ƙuruciya ne ba komai suke kallo a mai muhimmanci ba. Aliyu kai ɗan halak ne, nagodama ALLAH da yasa ka zamo mijin Mawaddat, na kuma godema ɗan uwana da yay wannan haɗin alkairi. ALLAH yay muku albarka. Ya kare rayuwarku da ta ahalinmu gaba ɗaya. ALLAH ya ƙara ɗaukaka ku, ku zama abin alfahari da babu irinsu a wannan zamanin. ALLAH ya albarkaci rayuwar Aliyu ƙarami da takwarana Isma'il (Ra'is) da Kamaluddeen, yasa suji ƙanku fiye da yanda kuka jiƙanmu”.
        Cikin rauni Smart da Uncle Yousuf ke amsawa da Amin. Smart na ƙara jin ƙaunar surukin nasa na ratsashi. Ga Uncle Yousuf Daddy ya juya. A hankali ya furta, “Nasha gaya maka Yousuf kaine babana a wannan matakin, narasa baba ne kawai a suna, amma ga babana a kusa dani.....”
     Cikin katseshi Uncle Yousuf ya ƙyalƙyale da dariya. Sai kuma ya rungumesa da faɗin, “Oh oh Yaya ni Wlhy kunya kake sakani, ni dai ba sai kace komai ba. Karka manta fa kaine na tashi nakema kallo a matsayin mahaifi kai da aunty Khareema. Kun raineni tun bansan kaina ba. Kun gatantani tun baku san minene daɗin ƴaƴa ba. Wlhy raina fansa ne a wajen kare ku daga duk wani maƙiyi da zaice kune abin harinsa. Ni dai fatana
Showing 249001 words to 252000 words out of 294165 words