muka gudo, kinga fa yini zatayi amma mu banda mu. ALLAH muna son muma mu yini tare da ita shine mukai shiri tare da Adda Maryam idan akai salla muyima Malam Jabeer ƙaryar zamu rakaki asibiti”.

Hawwah dake dariya tace, “ALLAH ya shiryeku Ammahn kukai ma sharrin ciwo kenan?”.

“A'a wlhy mu bamuce kowa ba, kawai dai munce zamu rakata asibiti”.

“Kuma ya yarda? Bayan nasan Malam Jabeer da shegen bin ƙwanƙwanto”.

Dariya Asma'u tai tana kallon Maryam, ita kuma ta harareta alamar dai akwai wata a ƙasa. “Munafukai mi kuke ɓoyewa?”. Cewar Hawwah tana kallonsu cikin waro ido. Alamar zip Asma'u taima bakinta da faɗin “Ba ruwana ba'a bakina ba”. Lulu da ke murmushi ta ce, “Haba Auta bamu musha mana”.

“Aunty ba faɗar bane matsalar, sai kun gudu gidajenku ta jibgan a ɗaki ko Ammah bazata bari ta sani ba”. Ranƙwashi kuwa Maryam takai mata. Da gudu tabar wajen tana dariya. “Sonta yake ya kasa gaya mata, gashi kuma ya tsaya kallon ruwa kwaɗo yay masa ƙafa. Dan ga wani tauraro mai babban haske ya faso kai da ƙarfinsa”. Binta Maryan tayi suka shige ɗaki da gudu. Kai kawai Ammah ta girgiza da faɗin, “ALLAH ya shiryeku”. Yayinda Hawwah da ke dariya ta ce, “A gama ɓoye-ɓoyen intai wari maji ai”. Lulu dai murmushi takeyi dan komansu burgeta yake yi. Bakomai ya jawo hakan ba kuwa sai yanayin rayuwar data tashi a ciki ita da nata ƴan uwan. Bayan su Maryam sun cire Uniform suma falon suka dawo aka ɗora hira, anan sukaci abincin da aunty Amarya ta gama, bayan sallar la'asar Maryam tai zaman yima Lulu kitso. Dan nakan Hawwah ta gani ya burgeta ta tambaya duk da ba son kitso take ba. Jin Maryam ce tayi sai tace itama aimata ko kaɗan. Shine sukai zamanyi suna cigaba da hira harda Ammah. Nasreen da suka dawo daga makaranta tana zaune a cinyar Lulu suna shan chocolate dan itama shazumamun ce kamar Lulun. Sallamar Smart ta sakasu tsagaita dariyar da sukeyi dan Asma'u ce ke kwaikwayon Muryar malaminsu Jabeer dake son Maryam wai idan ya ganta har ƙara maƙewa yake yi. Akan Lulu ya fara sauke idanunsa kafin yabi sauran da kallo, ya ƙarasa takowa cikin falon yana kaiwa zaune da faɗin, “Miyay muku daɗi haka kuke kwasar dariya har tsakar gida kun cikama mutane kunne? Ammah duk sun zagayeki sun dameki”.

Cikin murmushi ta ce, “A'a basu damen ba Hydar, ai ko kurama da ƴaƴanta take wasa a jeji. Sai yanzu muke ganin ka”.

“Wllhy ki bari dai Ammah. Da ga wani waje mai nisa muke fa, kin san Ahmad da shegen kutse-kutse can wani ƙauye ya samo gona zai gyara yay gidan gona a wajen shine fa mukaje dubawa”.

“Kai masha ALLAH, ai haka mukeso mu kuyita shiga irin hakan dan nan gaba kaɗan kune manyan goben.”

Murmushi yay cikin jinjina kansa. Kafin ya maida hankali ga ƙannensa da ke gaishesa. Idon Ammah ya sa Lulu faɗin, “Sannu da dawowa”. Sai da ya maimaita kalmomin guda uku a zuciyarsa yana mai ɗan kafeta da kallo, sai kuma ya janye shima cikin basarwa ya ce, “Yauwa ya gidan”.

Abinci Asma'u taje ta kawo masa, sai cewa yay ta maida baya jin yunwa, garama in sunada fura dan yasan dai Ammah bata rabo da ita. Asma'u tace masa akwai, taje ta ɗibo masa a fridge ta kawo masa. Daga haka suka cigaba da hirarsu Lokaci-lokaci yana satar kallon Lulu da akema kitso masu ƙyau. Wajen shida ya kalla agogo da faɗin, “Ku wannan kitson yaushe zaku gama shi har mu wuce? Gashi ina son mu biya ta wani wajen”.

“Ina? Ai ni nan zan kwana yi tafiyarka”. Cewar Lulu da iya gaskiyarta. Murmushi Ammah tayi, yayinda Smart dake mata kallon mamaki ya ce, “Kwana fa? Kin manta gobe Monday zakiyi resuming office?”.

“Ba damuwa jibi naje”.

Murna su Asma'u suka fara yi zata kwana. Ya hararesu duk sai suka nutsu. Ammah dai bata ce komai ba har sai bayan sallar magrib da ya shigo ya sameta a ɗaki, lokacin su suna can ɗakin suna tasu sallar. Zama yay kusa da Ammah, hakan yasata yin addu'a ta rufe Alkur'anin. “Ba dai tafiyarba ko?”.

“Da haka nake so dai ta shirya, da anyi isha'i sai mu wuce dan ina son mu biya ta gaida Kakanta ɗazun Uncle Yousuf ke faɗamin baya jin daɗi ya dawo daga Legos ɗazun, gashi kuma tana batun kwana anan”.

“Karka damu zan mata magana. Amma Aliyu sai nake ganin akwai wani ɓoyayyen al'amari a rayuwar yarinyar nan dake damunta, na fahimci hakanne a ɗan firarmu da ita ta ɗazun. Sannan bata son kaɗaici, dan ta roƙeni na baku Asma'u ta koma can da zama. Danace mata Abbanku bazai yarda ba ina kula da ita sai da idonta ya cika da hawaye. Mizai hana a ɗan samo mata ko tsohuwa haka da zasu zauna tare, sannan kai kuma ka ƙara ƙaimi wajen janta a jiki dan ka fahimci minene damuwarta. Ko yaya ta sanar maka itama zataji nauyin ya ragu mata a zuciya. Ashe mahaifiyarta bata raye kuma?”.

“Ta rasu, tana haihuwarta. Inasha ALLAH zan yi iya ƙoƙarina”.

“ALLAHU akbar. ALLAH ya gafarta mata. Wlhy duk sai yarinyar ta sake bani tausayi. Gata da sauƙin kai da sanin darajar mutane. Sai kuma yanda na fahimta akan aikin nan nata kamar zafinta akan al'amarin fyaɗe nada alaƙa da wani abu daya sosa ranta gaskiya. Ya kamata dai ka zama mai haƙuri da dinga ƙarfafata”.

“Insha ALLAHU Ammah zan yi iya ƙoƙarina. Batun Asma'u kuma haƙuri zakuyi ta koma can ɗin tunda tana son hakan. Kodan ma tafiyar nan dake tunkarowa.”

“To bazance A'a ba, amma ka samu Abbanku da maganar kadai sanshi. In akan tafiyane kuwa bazai yiwu dama a barta ita ɗaya ba. Ko ita da Asma'u kawai dole cikin samarin nan wani ya koma can ya dinga kwana da su”.

“Hakan ma yayi Ammah. Duk yanda kikace haka za'yin”.

Sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha'i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaɓa Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah ɗin shagwaɓa sai Smart ya zama ɗan kallo. Dan mamakin yanda tai bala'in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a ƙanƙanin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin ƙyautukan data raba musu ɗazun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baƙin wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron ƴaƴanta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba'a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo ɗaya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart ɗin suka shigo da tace yaje ita zata je ɗakin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko'ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai ɗakin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daɗi tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haɗa Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daɗin wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep ɗin ɗan anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep ɗin suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke ɗakin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake ɗan murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daɗi mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.

A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep...”

Yanda Dadan ke maganar a zafafe da ɗaga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin ɓata fuska amma ta dakatar da ita........✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣8️⃣


.......Itama dakatar da itan abinda tai niyyar sake faɗan da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai ɓace. “Wai miye haka kuma ban son ƙaranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”

Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama'ar ɗakin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taɓe baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin daɗin jiki Baba ya balbale Dada da faɗa, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki.....

Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buɗe musu suka shiga, gaba ɗaya kayan na'a hannunsa har handbag ɗinta ma. Har ɗaki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daɗin abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata ɗayan nan bazata so a wulaƙantashi ba dan itama dai da taje gidansu ba'a wulaƙantatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.

Shima a can wankan ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya zaɓi shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai taɓa wulaƙantata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa'i da wutri yayi sannan ya fito. Shayi ya haɗa a kofi biyu ya nufi ɗakin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta ƙurama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana haɗiyar busashen yawun daya tokare maƙoshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo ƴar saman rigar data ajiye gefe ta ɗora akan wadda ke jikinta dan ƙarama ce ma da kaɗan ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miƙa mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciya da faɗin, “Thanks.” kansa kawai ya ɗan jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da faɗin, “Kayi haƙuri da abinda Dada tayi, ni ban faɗa mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da faɗa ne sosai”.

Murmushi yay a karo na farko, sai kuma ya ɗan kafeta da idanunsa da suka canja launi kaɗan. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi faɗa kenan?“. Hararsa tayi da ɗan murguɗa baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban ɗauki abinda tai ɗin komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya ɗan tattara mata game da case ɗin yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smart tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiƙe. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai ɗin ba ta ɗago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido ɗaya. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai lumshe idanunsa.

Komawa tai ta zauna da faɗin, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da ɗakko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu daidaiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma ƙasan maƙoshi, tare da faɗa mata dokokinsa akan yanda yake buƙatar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har ƙasa ya sata dubansa cikin tura baki ta ce.

“Hijjab har ƙasa? Ni ce zan saka hijjab har ƙasa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure bane balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a ƙarƙashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunta juna. Ni harka ma ɓatamin rai na”.

Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tashi tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buƙatar abinda zai ɓata mata farin cikin data samu yau a wajen ƴan uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana faɗin (akwai ƙura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitane da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai....

WASHE GARI ta tashi da ɗokin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case ɗin nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban ƙamshi take zubawa dan ta baza turaren nata. Tana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmanta ya shigo ɗakin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har ƙasa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin ƙofar ya jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu kawai. Ƙin ɗagowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta ɗago ɗin ma kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana miƙewa. Da ga sama har ƙasa ya sake ƙare mata kallo. Yayinda ita kuma ta ƙarasa tattare kayanta ta nufo ƙofar kanta tsaye. Kallonsa tai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.

Maimakon amsa mata sai ya ɗan kauda idanun nasa a kanta ka ɗan batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take buƙata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da ɗan kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.

Cikin husky voice ya ce, “Idan baƙyason rasa shari'ar ko makarar go and change your dresses. Na faɗa miki duk abinda bakina ya furta shine nake buƙata kuma bana canjawa da ga ra'ayina akan duk abinda na riga na tsara.”

Cikin ɓacin ran da ya fara yunƙuro mata ta ce, “Aliyu!!...”

Hannu ya ɗaga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buƙata to bana buƙatar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.

Jitai jiri ma na neman kamar ɗibarta. Amma sai
Showing 141001 words to 144000 words out of 294165 words