Zaka iya kuma cin karo da kowanne a garesu a kowanne irin lokaci koda babu wani ƙwaƙwƙwaran laifin da kai musu. Mawaddat kada ki kalleni a matsayin yayar miji, kalleni a matsayin yar uwarki mace da tasan zafinki da sanin ma'anar kalar raɗaɗin da kike ciki. Minene ke faruwa tsakaninki da shi?. Karki damu ki faɗa min, zan koya miki dabarun da zaki cimmasa, dan nasan Hydar nada zuciya, kafiya, da taurin kai akan abinda yake ra'ayinsa.”
“Aunty ni ban san mina masa ba. Na tambayesa amma yaƙi faɗa. Har roƙonsa nayi bai saurareni ba. Ni gaskiya ina son na wuce gida bazan iya ba....”
A bazata batare da sun san yana a bayansu ba suka ji saukar muryarsa a kansu, “Ai dama bazaki san mi kikamin ɗin ba, gida kuma ga hanya nan a buɗe tunda dama shine burinki tun ba yanzu ba!!”.
A zafafe itama Lulun ta ɗago zatai magana aunty Bilkisu ta jinjina mata kai tare da jimƙe hannunta cikin nata alamar kar tace komai. Shirun tayi sai dai ta fashe da kuka. Tsaki yayi da juyawa zai koma dan dama kofin da ya sha shayi ya fito maidawa kitchen, da sauri aunty Bilkisu ta dakatar da shi da faɗin, “Hydar dawo ka zauna”.
“Aunty ni mizan zauna na mata, kina jin fa abinda take cewa. Dan taga na ƙyaleta bance komai ba har tanada bakin faɗama mutane zata wuce gida. To zuciya take tunanin ta fini ko mi?...”
“Hydar Please cool dawn mana. Nace ka zauna. Idan kuma Ammah kuke son na kira muku nikam sai na kirata. Maybe ita kufi jin maganarta”.
Ransa a ɓace ya dawo ya zauna. Sai faman sauke huci yake. Yayinda ita kuma Lulu take kuka. Sai da aunty Bilkisu ta basu mintina kamar uku zuciyoyinsu suka ɗan risina kafin tai gyaran murya kaɗan tana fuskantar Smart. “Aliyu mike faruwa? Kasan dai Mawaddat amana ce a hannunka, sannan ni shaida ce tanada haƙuri da ƙoƙarin ganin ta ƙyautata maka a matsayinka na mijinta da kiyaye duk wani ɓacin ranka. Shin miya kawo wannan fitinar a tsakaninku haka babu daɗi? Kuna ganin kunmin adalci abu ya faru kuna irin wannan tashin hankalin ina a tsakkiyarku. Wane laifi ta maka? Miya faru kake fushi da ita? Tunda ita ta tabbatar min bata san abinda tai maka ba...”
“Ai bazata sani ba tunda ta ɗaukeni wawa da bai san ciwon kansa ba....”
Cikin kuka Lulu da ke kallonsa ta ce, “Toni ya kake so nayi maka ne Aliyu. Na tambayeka kace ban maka komai ba. Amma kana fushi da ni. Ko magana baka son kayi dani, idan ka gaji da zamanmu ne ka sallaman na wuce tunda ai ba dole bane. Ni dama bance inayi ba balle kaji su bini da tsatstsaga....”
“Oh nine kazar kenan? Ai ba sai kin faɗa ba dama nasan ba ƙaunata kike ba. Dan baki da yanda zakiyi da ni ne kawai kike zaune. Sai dai ban san ƙiyayyar da kike min ɗin takai girman haka ba, har ki guji haihuwa da ni. Na farkon dama ALLAH ne yayi maganinki ya samar da shi a lokacin da bakiyi zato ko tsammani ba, shine yanzu kika bi hanyar takaita ni. To sai ki sake ɗaura ɗammara dan wannan batai dai-dai da ke b.....”
“Ya ALLAH Aliyu...”
Aunty Bilkisu ta katseshi cikin tashin hankali. Dole yay shiru shima yana hucin. Yayinda Lulu ke kukanta ita dai. Shiru falon yayi kusan mintuna biyu sai ajiyar zuciyoyinsu sannan aunty Bilkisu ta sake dubansa. A nutse ta ce, “Kai waya gaya maka bata son haihuwa da kai Hydar? Banji daɗi wannan furucin naka ba sam gaskiya”.
“Gaskiyar kenan ai aunty, inda tana son haihuwa dani bazataje tai planing babu sanina ba. Da haka zamuyita tafiya ni ina tunanin akwai matsala ita kuma tana cutar dani. Da yake bani da hakkinta sai gashi ALLAH ya sanar dani ta hanyar likitar da taje ta dubata. Ni na taɓa cemata bana son yarane? Gidanmu mu kusan talatin aka haifa, yanda na tashi na gammu nima haka nake fatan tara zuri'a. Amma shine zata zaluntan....”
“Niba azzaluma bace, kuma nima bance bana son haihuwar ba ai...”
“Ƙarya kike yi wlhy, idan ba zalunci ba mi kikayi? Da lafiyata da ƙuruciyata ki cutar dani ta hanyar katangeni da ganin jini na. Ke wlhy kika sake maidamin magana zan fasa bakinki ne har sai haƙoranki sun zuba. Bana son raini ki shiga hankalinki kar kiga ina ƙyaleki ki ɗaukeni wani banza can!!....”
A hargitse Lulu take dubansa. Zatayi magana Aunty Bilkisu ta hanata. Shiko sai huci yake yi dan ya gama kaiwa wuya. Abinda Lulu bata sani ba Smart ya tsani yana magana ana maida masa. Musamman idan shi akaima laifin yana sake harzuƙa ne. Duk yaran gidansu sun san wannan halin nasa, shiyyasa suke kiyaye wa. In ko kai kuskuren dagewa akan dole sai ka masa bayanin da zaka fidda kanka zai iya maka dukan hauka ne ya bar uwarka da jiyya. Wannan itace babbar matsalarsa, idan yay ƙololuwar fushi baya iya controlling temper ɗinsa sam. Shiyyasa yake da ƙoƙarin kauda kansa akan abubuwa. Ganin yanda ya fusata ya saka aunty Bilkisu cewa suje su kwanta da safe sa ƙarasa. Shi ya fara tashi fuuu ya wuce, dan haka ta hana Lulu tashi. Nasiha ta fara mata da sanar mata halinsa na son rashin maida murtani ko bama kai kariya. Dan shi idan akai masa laifi ko bayani wani lokacin baya buƙatar ai masa. Gara ka masa banza idan ya gama hawa da saukar zai huce da kansa ya dawo ya binciki gaskiya in ma hukuncinne ya maka. Ta nuna mata kuskurenta tare da bata shawarar taje ta cire abinda ta saka ɗin. Haihuwa ai komai na ALLAH ne. Ayi fatan kawai ALLAH ya bada masu albarka. Lulu taji daɗin nasiha da shawarar aunty Bilkisun, dan haka ta ɗan ji zuciyarta ta rage mata nauyi.
Koda ta shigo ɗakin kwance ta samesa. Batai magana ba ta shiga toilet tayi wanka ta gyara jikinta. Kamar yanda sukeyi a tsakanin nan kwanciyar kai da ƙafa haka ta kwanta yau ma. Ta lulluɓa da bargon data ɗakko. Duk abinda take yana jinta, amma ko motsawa baiyi ba. Sai can cikin dare sosai ya tashi yayo alwala ya zo ya kama salloli. Sai da ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa da karatun Alkur'ani sannan ya tsagaita. Ganin asubahi ta gabato ya haƙura bai kwanta ba har sai da yay sallar asubahi. Alerm ne ya tada Lulu, dama haka yake mata tunda suka samu saɓanin. Kafin ta fito bayi ya haye gadon yay kwanciyarsa...
Ranar yini yay barci, dan sai azhar ya tashi. Babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai. Yay wanka ya shirya cikin ƙananan kaya marasa nauyi. Suna falo zaune Iya Tabawa na basu labarin sanda suna ƴammata Lulu na kwasar dariya kamar ba ita tasha kuka jiya ba ya fito, sam ita bata da riƙe abu, shiyyasa idan aka riƙeta take jin zafi. Da gudu AA dake wasa ya nufosa. Cak ya ɗaga yaron sama yana mai sumbatarsa cike da jin ƙaunarsa. A haka ya kai zaune cikin kujera suna dariya shi da AA ɗin da yakema cakulkule. Iya Tabawa ya fara gaisarwa sai aunty Bilkisu. Ya tambayeta yaya jikin tace Alhmdllh sai fatan komawa gida lafiya. Murmushi yay da faɗin, “Ai keda Nigeria sai nan da shekara ɗaya”.
Idanu ta waro sosai da faɗin, “Shi kuma mijin nawa kuyi yaya da shi?”.
Cikin kauda kai da taɓe baki ya ce, “Uhm su miji”.
Kafin aunty Bilkisu ta sake cewa wani abu a fisge Lulu tace masa “Good Afternoon”. Kallonta yayi shima a karo na biyu cikin ɗauke kai yace, “Afternoon” a taƙaice. Daga haka babu wanda ya sake kula ɗan uwansa. Abinci ma sai da aunty Bilkisu ta zungureta ta tashi ta kawo masa. Batai zaton zaici ba, amma sai taga yaci sosai yana bama AA. Bata san yayi matuƙar kewar girkin nata ba ne. Basarwar da yake ɗin ma ta dole ce. Haka ya ƙarasa yinin nan a gida yau ko waje bai leƙa ba har washe gari. Washe garin ma sai zuwa yamma ya fita training center ɗinsu........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣
.......Kwana uku ya ɗan fara hucewa a dalilin murar zazzaɓi da Lulu ke fama da shi. Duk da dai tana nuna ita ƙalau take. Sai da murar tai mata tsanani ne ta haƙura takai zaune. Mata da miji sai ALLAH sai gashi yana tattalinta da matsa mata tasha magani. Harda haɗa mata shayin kayan ƙamshi da kansa. Idan yaga AA zai takura mata ya ɗaukesa ya kaima Iya Tabawa. Ya bata kulawa sosai harta samu sauƙi. Da ga haka aka shirya kamar basu ba aka koma nunama juna soyayya da tattali. Sai aikinsu da suka saka a gaba. Ita aunty Bilkisu ma sai abin ya koma bata dariya. Shiyyasa dai akace duk wanda ya shiga tsakanin mata da miji ya matse. Dan zasu shirya ne su barsa a ciki. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa mura na damun Lulu akai-akai. Ita abin har mamaki yake bata dan bata cika yawan mura ba a da. Sai dai ta danganta yanayin da sanyi da ake yi sosai harda dusar ƙanƙara.
Wasan su Smart na tafiya cike da nasarori da kalubale. Yayinda sunansa keta ƙara cigaba da amsa kuwa saboda yanda yake zura ƙwallaye a raga babu ko ɗar. In dai za'a kirayi sunan wani yaro mai tashe a wannan ƙarnin a harkar ball idan sunansa baizo na ɗaya ba dolene yazo ana biyu. Ballema ALLAH ya bashi farin jinin da akan ambacesan a farko. Sam baya wasa da addininsa. Sannan tsaye yake akan Lulu itama dan har yanzu shine mai ɗora mata karatu datai matuƙar maida hankalinta a kai. Wani lokacin kuma aunty Bilkisu ke ɗora matan.. A gefe kuwa sun matuƙar saka rayuwar Alh. Sulaiman a gaba, dan a yanzu haka ana tsaka da dambarwa ne tsakaninsa da amaryarsa akan Flash. Anyi-anyi ta bada taƙi. Yayi haukan yayi hargagin yayi kurarin duk da tana a gidan nasu tayi kememe. Hajiya Turai dai ce ƴaƴanta suka dawo da ita. Acewarsu sai da Mahaifin nasu ya bar mata gidan badai ita ta bar masa ba. Dan babu kunya suka dinga yaɓa masa magana musamman ma Tajuddeen, Alh. Sulaiman ranar harda hawayen baƙin ciki. Bai taɓa tunanin soyayyar da yakema Tajuddeen zai iya kallon tsabar idonsa ya masa rashin kunya haka ba, al'amarin ya girgiza zuciyarsa kam..
(Abinda kayi dole ai maka ai dama🚴🚴🚴😂).
*_NIGERIA_*
Watanni kusan huɗu kenan abubuwa na'a rincaɓe musamman a ɓangaren Alh. Sulaiman Garko. Dan anata musu tsinci ɗai-ɗai na masifa ta yanda gaba ɗaya kasuwar tasu ma ta tsaya cak. Ga manyan kayansu da ke gaf da zuwa Najeriya ɗin. Duk yay wani iri da shi duk da har yanzu ma shi bako a fara taɓashi ba. Dan ko'a cikin yaransa kaf babu wanda aka taɓa. Sai aminansa da Hon. Nakowa kawai ya rage sauran duk suna hannun hukuma anyi ram da su. Kullum cikin kiran Daddy yake yana masa barazana. Shiko Daddy na maida shi mahaukaci da naɗe komai a waya tare da kunnashi. A gefe ɗaya ga al'amarin amaryarsa da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Burinsa kawai ya amshi Flash ɗin hannunta koda zai kasheta ne shi babu ruwansa. Tayi-tayi ya saketa kuma yaƙi. A randa yaje har gida ya cima mahaifinta mutunci ta tabbatar masa anzo gaɓar da take jira, dan haka a ranar ta aike ma su Baba Garko da video. Da kanta ta shirya taje har gidan ta danƙama Baba Flash. Har wulaƙanci Dada taimata saboda taje ta gaida amarya da duba yaranta. Ita dai bata tanka mata ba har Dadan tayi ta gama san ranta. Bayan wucewarta ne Dada ta nufi wajen Baba Garko. Ta sameshi da ƴan biyunsa da sukai kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa. Takaici kamar zai tsayar mata da numfashi amma ta danne da ƙyar. Dama bata taɓa ɗaukar yaran ba tunda aka haifesa, dan haka yanzun ma kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta. Ko'a ƙwallar rigar Baba Garko, dan ya jima da fahimtar bakin ciki take da yaran. Sama-sama ya amsa mata gaisuwa ya cigaba dama yaransa wasa kamar ma ya manta da ita. Hakan ya sake Zafafa mata zuciya taji ta tsani yaran fiye da ko yaushe. A cikin tunzura ta ce, “Amma dai Alhaji bai kamata ka fifita rayuwar ƴar wasu akan naka ba. Yanzu yarinyar nan ta gama fetse mana yaro da iskance-iskanceta ta dawo tana mana barikanci. Ni na rasa mi Sulaiman yayi maka haka da zafi ne. Kabi ka tsangwamesa babu laifin tsaye babu na zaune. Idan ma maganar Mawaddat da Tajuddeen ce ya kamata ace ta wuce tunda dai tana gidan mijin da kuke son ganin nata da shi yanzu ai ko”.
Idan ɗakin ya tanka Baba Garko ya motsa, hakan ya sake harzuƙa Dada. Miƙewa tayi a fusace zuwa gabansa ta ɗauke Flash ɗin dake ajiye kusa da shi. Nan ɗin ma bai tanka mata ba harta fice, bai kuma nuna damuwa da ya bita akan flash ɗin ba ya cigaba da yima yaransa wasa. Hajiya Dada kam da masifa ta nufi sashenta. Harta ɗauki waya da nufin kiran Alh. Sulaiman akan yazo ya amsa sai kuma ta ajiye tana faɗin, “Bara dai naga wai ubanmi akema wannan tashin hankalin ne a ciki.” Ta ƙwalama mai aikinta kira. Jiki na rawa ta iso, a gabanta ta zube cike da girmamawa. Umarnin ɗauka mata tab.. a ɗaki ta bata. Babu jimawa ta dawo ɗauke da tab.. ɗin. Ita ta saka mata flash ɗin. Cike da gadara da ƙasaitar mulkin masu akwai Dada ta amsa ana wani gyara zama da busa iska tace mai aikin ta kawo mata lemo. Ita dai mai aiki umarni take bi.
Fuskar data fara bayyana ta saka ƙirjin Dada bugawa, jikinta ya fara tsumar kewa. Mawaddat ɗinta ce, yarinya mai hankali, mai sonta da ƙaunarta, sai dai ita kullum tana a cikin hantararta ne saboda tana ce mata kaza ba daidai bane kaza ne daidai. Kalaman Mawaddat suka cigaba da jan hankalinta kafin kace mi ta jiƙe sharkaf da zufa. Maimakon hasken ɗakin ta koma ganin duhu. Tun tana iya jin sauti da motsi har komai ya tsaya mata cak sai razanannen ihunta daya karaɗe kunnuwan duk wanda ke a kusa da sashen nata. Rige-rigen shiga masu aikin nata suka shiga yi inda take, sun sameta wanwar a ƙasa kofin lemon da aka ajiye mata ya kife da alama ma a kansa ta faɗa. Duk da hankalinsu ya tashi da ganin a yanda take sai da suka ɗauki tab.. ɗin suka kalla abinda ya razanatan. Yayinda mai tausayin cikinsu ta fita a guje kiran Baba Garko. Ai suma sai suka ƙare da ƙwalla ƙara a dai-dai shigowar Baba Garko da amaryarsa, dan tana tare dashi sanda mai aiki taje kiransa....
An ɗauki Dada babu alamar rai a tattare da ita ga jini na zuwa ta inda gilashin kofi ya jimata ciwo. Shi kansa Baba Garko a kiɗime yake dan bata taɓa kasancewa a irin hakan ba duk wannan rikicin da akeyi. Iyaka dai ta suma da'an zuba mata ruwa ta farfaɗo. Amma yau babu abinda basu gwada mata ba ko motsi. Da tab.. ɗin ya fita a hannunsa, dan yasan koma mi ya sakata a wannan halin bazai kasance ƙaramin ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya isa kunnen ƴaƴanta da jikoki. Kafin wani lokaci asibitin da aka kaita ya cika da Garko family, zuri'ar Uncle Khamil dake Abuja ne kawai babu suma suna tafe sai na auta dake a Saudiyya. Har zuwa washe gari ba'a samu kan Dada ba, dan haka hankalin kowa ke'a tashe. Hatta shi uban gayyar a wannan karon hankalin nasa a tashe yake. Dan koba komai fa yana son matarsa, sannan itace uwar ƴaƴansa. Tun shekarun ƙuruciya suke tare har zuwa tsufa da daɗi babu daɗi tana zaune da shi. Washe gari zuwa sha ɗaya na safe auta ya iso tare da nasa iyalinsa, tamkar shi Dada ke jira ya iso ta farfaɗo, sai dai fa numfashin farko da taja ta fesar da jini ta fesoshi. Wani sabon tashin hankalin kenan, dan likitocin ma sun kasa musu bayani, sai kai-kawo da shigi da fici sukeyi. Duk wanda suka tunkara sai dai ya zame da faɗin yana zuwa. Duk wannan abun da akeyi babu Alh. Sulaiman sai ƴaƴansa da uwar gidan sa. Karan farko da Tajuddeen yaji baƙin cikin halin mahaifin nasa. Shin wai minene na wannan gabar, a ganinsa mahaifiya ai tafi gaban wasa. Dada na a irin wannan yanayin har yace yanada wata hujjar cigaba dayin gaba. Duk wanda yaga Dada a jiya zuwa yau dolene ya tausaya mata. Shi kansa Baba Garko ya ajiye makaman yaƙinsa harda hawaye yake da sambatun ta tashi dan ALLAH kada ta tafi ta barsa. Cikin ɓacin rai Tajuddeen ya dannama ubansa kira. A lokacin yana ɓoyayyen Companyn sa suna tattaunawa da yaransa malami da wasu abokan cinikayyarsa mazauna Legos akan kayansu da suka iso Nigeria a daren jiya. Sai dai sun rasa yanda zasu fidda kayan daga bakin ruwa saboda kamar fa an saka musu ido... Yana ɗaga wayar Tajuddeen ya fashe masa da kuka cikin masifa yake faɗa masa “Yanzu nan Dad har kanada lokacin nishaɗi haka mahaifiyarka kwance ranta a hannun ALLAH tana aman jini likitoci tun daren jiya tsaye a kanta. Anya
Showing 273001 words to 276000 words out of 294165 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92 Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99