na fara jin yunwa”.
“Sorry na daina ayi hirar arziƙin. Abinci kam nan kawai ya isheki ƙoshi yau ai”. Ya ƙare maganar da nuna lips ɗinsa.
“Lips ɗinne kuma ya zama abinci?”.
“Sosai kuwa, kona gwada miki”.
“A'a na yafe girmana bai kai can ba”. Ta faɗa tana ƙoƙarin sauka a jikinsa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣
.......Ƙaramar dariya yayi da ɗage gira sama ya ce, “Nima naga alama ƴar ƙanwata babu abinda ta sani sai cin abinci da barci”. Ya ƙare maganar da lakace mata hanci.
Hannunsa ta buge da sake yunƙurin tashi tana faɗin, “ALLAH dai ya shiryaka kai kam”.
Sakin nata yay yana dariya da tashi zaune shima cike da shaƙiyanci.
“Miye na dariyar to”.
“A'a babu komai ƴar ƙararrama, ai ko cikin AA ma a ruwan madara kika sha ni shaida ne.”
“Kaji da shi dai. Fitinanne”.
“Kema zaki zama fitinanniyar”.
“ALLAH ya tasreni wlhy”.
“Sai dai na gaba wannan dai ya faru tunda ga AA a duniya”.
Da sauri ta miƙe cikin ɗage kai tana faɗin, “Oh kama tunamin, yaron nan zai iya tashi ya ce zai sakko wlhy”.
Miƙewar yay shima da cewa, “Yi zamanki ina zuwa, bari na duba shi.” bata Musa masa ba ta koma ta zauna. Sai dai har ya gama haye ɗan steps ɗin hanyar bedroom ɗin nasa tana binsa da kallo, sai da ya shige ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu tana sakin wani ɗan murmushi mai sanyi. Babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da AA kuwa a hannu, sai zillewa yaron yake da ɓata fuska irin na ƙiwa, shi adole bai sanshi ba. Yana ganin Lulu ya wani zabura wajenta yana ɓare baki. Dole ta amshesa dan ya cika mata kunne, yana ganinsa a hannuta sai yay shiru yana kallon Smart da sauke ajiyar zuciya. Zaune Smart ya kai kusa da Lulu cikin damuwa da ɗan murmushi, ya zubama yaron idanu da faɗin, “Kayi fushi da Papa ko Sweet heart? Kayi haƙuri Papa yayi laifi da baizo ya ganka ba tsahon lokaci. Please ka daina min ƙiwa kaji my sweet friend ɗina”. Ya ƙare maganar yana ɗan lakacema yaron hanci. Da sauri AA ya sake lafewa jikin Mamansa ya zata ɗaukar yasa zai sake yi.
Murmushi ya sake saki da girgiza kansa kaɗan. Sai kuma ya dubi Lulu dake saurarensu da kallo kawai. “Yana cin abinci ne?”.
Cikin ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki tana kallon yaron ta ce, “Da ga Kunu sai tea kawai yake sha, sai biscuits haka da ɗan sweets suma wani lokacin ko an bashi bai sha”.
“In dai ya biyo Babansa kam bazai sha ba, dan bana shan zaƙi nikam. Bari na haɗa masa tea ɗin maybe yunwa ce ta tashesa”. Kai kawai ta iya gyaɗa masa. Har ga ALLAH wannan halayyar tashi na saka mata ganin girmansa da kimarsa. A haka idan ka dubesa sai ka ɗaukesa a wani mutum mai jin kai da girman kai, amma sai ka zauna da shi kaga baida damuwa akwai sauƙin kai. Babu jimawa ya dawo da cup ɗin tea, zama yay a gabansu yana fuskantarsu, ya ɗan ɗebi tea ɗin a spoon ya kai bakin AA. A mamakinsu sai sukaga yaron ya ɗan kallesa kamar zai yi kuka sai kuma ya amsa. Dariya suka sanya su duka. Smart ɗin ya ɗan dungure masa kai da faɗin, “Ana son kayana amma ana guduna”. Ita dai Lulu dariya take musu. Tun yana amsa daga cinyarta harya zamo ya rarrafo jikinsa.
“Oh ashe ƙiwar bamai nisa bace Sweetheart”. Smart ɗin ya faɗa yana ɗaukarsa zuwa jikinsa. A haka ya cigaba da bashi tea ɗin suna hira da Lulu duk dai akan yaron ne da yanda yake samun soyayyar ƴan uwanta da nashi. Sosai Smart kejin ɗari a ransa, dan kuwa maganar nan ce dai ta malam bahaushe da kan ce mai ɗa wawa shima ke ɗawainiya da shi....
*_NIGERIA_*
A karo na farko tun bayan sakinsa da dawowarsa ƙasar yau sukai zaman meeting na farko da abokan cin mushen nasa. Wato Alh. Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau. Sai yaronsa Malami da aka dakatar daga waje kafin lokacin tasa shigowar yayi, dan akwai abinda ya ke son su fara tattaunawa da ba dole bane sai malamin yaji duk da kuwa a cikin sirrikansa babu abinda bai sani ba. Wani abu ma daya sani su su Alh. Baitan basu sani ba. Sun ƙara jajanta masa abinda ya faru cikin nuna ɓacin rai da tattara laifin gaba ɗaya akan Daddy da ɗan ka-ce-na-ce akan yanda akai suka san inda Lulu take. Shi dai shiru yay kawai yana saurarensu har suka gama bai ce uffan ba. Sai ma ya ɗakko musu batun kayan da yayo order da lokacin da yake ganin zasu iya shigowa Nigeria. Sun ɗan tattauna sosai akan hakan sannan suka dai sake komawa batun Daddy. Duk wani tsare-tsare a kansa sun yisa ne a wannan ranar harda ita Lulu da Smart suna a cikin plans nasu. Hatta da Abba wannan karon shima ya shigo lissafinsu.....
*_UK_*
.....Tunda suka dawo bedroom ɗin domin kwanciya sai tsoro ya shigi Lulu saboda ganin take-taken Smart ɗin a kanta. Sai dai tana ta ƙoƙarin basarwar cike da ƙarfin jali. Alwala tayo zatayi shafa'i da wutri yace ta jirashi. Jitai kamar zatai kuka, ta ɗan kai dubanta kan AA da ya haɗa da tarkacen kwalaben turarensa. Babu jimawa ya fito shima da alamar alwalar yayo. Kayan jikinsa ya canja zuwa jallabiya, cikin umarni ya jasu jam'in salla raka bibbiyu har sau uku, da ga ƙarshe suka rufe da shafa'i da wutrin. Juyowa yay gareta ya ɗaura hannunsa na dama saman kanta ya karanto addu'a. Zuwa yanzu tana da ɗan iliminta na addini gwargwadon iko, dan haka ta fahimci sallar da sukayi, duk da kuwa ita bawai ankawota bane matsayin amarya, sai dai a wancan lokacin ma ai sunyi irin sallar a randa komai ya shiga tsakaninsu. Sai ko ga shi shi da kansa yana faɗa mata cikin tsokana da murmushi ya ke cewa, “Kin san ke yau a amarya kike, dole ai miki tarba irinta amarya”.
Bata iya cewa da shi komai ba, sai dai tuni taji zuciyarta ta fara gudu a cikin ƙirjinta tuno da wahalar da tasha a waccan ranar da sakamakon abinda ya biyo baya na samuwar cikin AA. Sai ma taji ta gagara tashi a wajen. Ganin ya tashi shi ya koma saman gado waje ɗansa hankalinsa a kwance jiki a sanyaye ta jawo handbag ɗinta ta fiddo Alkur'ani itama ta fara karatu. Ta wutsiyar ido Smart ke kallonta yana jin wani irin farin ciki mara misali har tsigar jikinsa na tashi, sai dai baice komai ba dan a ganinsa lokacin cewar baiyi ba. Ya cigaba da yima AA wasa har yaron ya sake ɓingirewa barci. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da kwashe kayan ya gyara masa kwanciya, dan tunda suka shigo Mamansa tai masa wanka da canja masa kayan barci, sai ƙamshi yake mai daɗi. Kwanciyar yay shirin yi shima abinsa bayan ya shiga bayi ya gama uzirinsa ya fito ya canja kayansa zuwa na barci da feshe jikinsa da turarruka ya haye gadon harda yin addu'ar barci. Hakan ya saka Lulu ɗan jin nutsuwa, ganin har ya ja bargo ya rufama kansa ta saki ajiyar zuciya. Mintuna kusan goma sha huɗu baya ta rufe Alkur'anin ta miƙe itama. A tunaninta Smart yayi barci. Toilet ta shiga ta ƙara gyara jikinta kamar yanda aka koyar da ita salo-salo a wannan fanin duk da ita batayi da manufa ba, dan bata ma fatan a kai ga hakan saboda tsoro yake ji sosai. Ta jima tana kallon kanta a mirror kafin tai ƙundunbalar fitowa. Ta ƙasan ido Smart da yay likimo yake kallonta, gaba ɗaya tsigar jikinsa ta shiga tashi dan rigar barcin da ke jikinta ba wata ta kirki bace, sai dai a gareta ita bawai tasa da wata manufa bane dan dama can tana sakawar a ita kaɗanta. Gadon ta nufa zuciyarta dai na kai-kawo, dan haka data ɗan kai zaune a bakin gadon ta tsurama Smart ɗin ido. Ganin bai ko motsa ba ta sake yarda yayi barci, sai kuma ta dubi a inda ya kwantar da AA, da ga gefensa sai dai ya kakkaresa da filos ta yanda ko juyi yay bazai faɗi ba, shi kuma ya kasance kamar a tsakkiyar gadon ya bar mata ɗayan gefen nashi. Sai da ta ɗan hararesa duk bata san yana kallonta ba sannan ta tura baki tana kaiwa kwance a hankali, tasan idan tace zata ɗakko AA ta maido tsakkiyasu Smart ɗin zai iya farkawa, koma yaron ya farka shi ya sanya mata daru duk da dai yanzu ya bar kukan dare, dan haka ta haƙura akan zuwa da safe dole a nema mafita, tunda dai taga ba ɗaki ɗaya bane a gidan ita zata koma wani ɗakin ta bar masa ɗakinsa, tun ma ɗazun da ace tasan nashi ne bazata yarda ta sauka anan ɗin ba. A hankali ta ɗan ɗaga bargon kaɗan ta yafama jikinta tana wani rumtse ido da cije lips, harda waigawa ta dubi Smart sai taga yana a yanda yake dai ko. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sake saki da lumshe ido ita a dole tasha da ƙyar.
Dariya Smart ke dannewa da ƙyar, sai da ya tabbatar ta gama dabarun nata sannan ya mirgino jikinta a hankali ya rungume ta tsam. A firgice ta juyo jikinta har yana rawa. Sai ya sakar mata murmushi da kashe mata ido ɗaya.
Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Dama idonka biyu?”.
“A'a yanzu na farka” ya bata amsa cikin gimtse dariya.
Kallonsa take cikin rashin yarda da cewar yanzu ya farka wai. Zatayi magana ya ɗora yatsansa saman lips ɗinta da faɗin, “Shiiii!!!”.
Dole ta haɗiye maganar idanunta na kawo ruwan ƙwalla. Juyota yayi da ƙyau suna fuskantar juna, murya ƙasa-ƙasa yake magana yana busa mata iska a fuska. “Amarya mai tsoro da fa ƙyar take sha a hannun ango. Karki zama raguwa mana Nooru Nisa”.
Fuska ta ɗan ƙwaɓe kamar zata sakar masa kuka. Sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Aliyu kaga dai ALLAH ni har yanzu wajen da akai min aikin nan bawai ya gama warkewa bane, sannan ma banda wani isashen lafiyar jik.....”
“Irin wannan sharhi haka Madam. Ni nace zanyi wani abu ne?”. Ya faɗa cikin katseta da kai yatsarsa saman lips ɗinta yana zagayawa. Sai kuma duk taji kunya ta lulluɓeta, irin wannan kama kai har ina. Shima murmushi yayi dan ya fahimci ya rufe bakin maganar, abin faɗar sun maƙale. Idanunta ta maida ta rufe a hankali tana haɗiyar zuciya, daga haka ta fara ƙirƙiroma kanta barcin dole. Jin numfashinsu ya sake kusanta da juna ya sata buɗe ido da sauri, sai dai kafin tayi wani yunƙuri lassafin ya canja, dan Smart ya rantse yau fa a angonsa yake, ya barta ne kawai ta gama kame-kamen nata..........✍️
Hummm🚴🚴🚴🚴

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣
.......Al'amarin Umma kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba. Dan ita kanta tun tana ɗaukar abun matsayin ba komai ba sai gata ta fara hawaye cikin tashin hankali. Dan kuwa dai ƙawarta Hajiya Naqiba tazo, amma tana shiga ɗakin nata itama da gudu ta dawo tana ihu mai firgitarwa da yafi na jama'ar gidan. Hankali tashe Umma ta biyota tana faɗin, “Na shiga Uku ni Yaha, Aminiya kema ɗin abinda suke min zaki min? Wai mina muku ne haka kuke irin wannan firgita da ni? Dan ALLAH ki faɗamin Aminiya kar ki min yanda suke min kema”.
Ina Hajiya Naqiba ba sauraren Umma take ba. Ihu kawai take kwarawa da iya ƙarfinta har maƙwafta da mutanen waje na iya ji, daga ƙarshe ma ta yanke jiki ta faɗi a sume dan Ummah taƙi daina binta. Cikin tashin hankali Umma ta isa gareta ta na jijjigata, a dai-dai nan mutane suka fara shigowa gidan da ga waje hankali a tashe. Ai sai ga maza na dafe huluna suna juyawa a guje. Duk wanda ya shigo yana tozali da Umma rungume da Hajiya Naqiba sai ya afa da gudu ya juya. Ba matan ba ba mazan ba ba yaran ba. Cikin ƙanƙanin lokaci zance ya zagaye anguwa. Masu ƙarfin hali na cigaba da shigowa domin tabbatar wa. Sai dai fa babu fashi duk wanda ya shigo zai juya a gujensa yana ihu da faɗin “Wayyo Dodo!! Wayyo dodo!!.”
Umma da ke zubama hajiya Naqiba ruwa tana kuka dan ganin abin da bana lafiya bane ta zabura jin aminiyar tata ta sake fasa gigitacciyar ƙara. Dan tana farfaɗowa taci karo da ita a kanta. Yin ƙurin da zatai domin ceton ranta ƙafa ta gurɗe jikake ɓass kamar an ɓalla katako ba ƙashi ba. Sai ta sake zubewa a ƙasa cikin wata irin wahalalliyar ƙarar azaba ta sake sumeya. Duk da abinda ke faruwa kaf ƴan gidan na maƙale ta windows suna kallo har ƴaƴanta da suka rarrabu. Wasu a ɗakin Ammah wasu na Mama. Ita dama aunty amarya da yaranta ɗakin Ammah suka afka suma. Ammah da al'amarin ya jijjiga ma zuciya na zaune a kujera tana cuɗawa da kwancewa. Dan in har lissafinta yayi dai-dai ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya fa a wannan karon. Tukunyar da suka gani tarwatse a tsakar ɗakin Ummah itace asirin da taima su Aliyu matarsa ke ganinsa da mummunan siffa irin wadda suke ganin Umma da ita a yanzun. Abba ne yay hikimar kiran yaranta na ma'auri da su Salim yace suzo babu lafiya. Dan shikam yama rasa ina zai kama a wannan lamari. A yau dai ya sake tabbatarwa Umma na bin bokayen tsubbu, kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya mai kamanceceniya da juna akan al'amarin Aliyu da matarsa da wanda Umma ke'a ciki yanzu. Yau matar Aliyu ta koma wajen mijinta, hakan na nufin komai ya daidaita tsakaninsu asirin ya dawo inda aka aikashi. Dama ai sharri ɗan aike ne, idan ya isar da saƙonka sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Har zai kira Smart sai kuma ya fasa cikin girgiza kai dan a yanzu ya tabbatar dare ne a UK.
Yaran nata ma koda suka iso duk wanda yay tozali da Umma sai gudun ceton rai. Umma ta fashe da kuka da tun ɗazun take irinsa har muryarta ta dishe. Ga aminiyarta kwance ƙafa sai kumbura take kowa ya kasa zuwa a taimaka mata saboda Umma da ke a wajen. Al'amarin dai sam babu daɗi, Umma na cikin tashin hankali fiye da wanda al'umma ke ciki akan ganinta a mummunar halittar da kowa ke ganinta. Ita kuma lafiya Lau take kallon kanta, dan har ɗaki ta nufa ganin kanta a madubi babu wata damuwa ko tawaya tattare da halittar ta sai fuskarta datai kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka ɗauke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi masifar kumbura damm abin zattashin hankali......
*_UK_*
Wahala iya wahala Lulu tasha a wannan dare hannun Smart. Dan zata iya rantsewa ita kam bata ga banbancin sa da daren farkonsu ba, kodan ta saka ma ranta tsoron al'amarin ne oho. Amma tabbas ko a yarda da ita ko kar a yarda Smart namijin gaske ne da ko'a cikin mazan ma zai iya amsa sunan mazaje ne. Sai dai bata sani ba ko ragwantakarta yasa take masa irin wannan kallon ko kuma dan shi ta sani bata san sirrin sauran mazan ba.
Shi kansa sai da ya koma tausayinta, dan magana ta gaskiya fa bai raga mata ba, wahalarsa ta kusan shera ɗaya da wasu watanni sai da ya fanshe abinsa tsaff. Sai dai kuma shi a karan kansa bashi da zaɓin da ya wuce hakan. Bai sani ba ko tsananin begenta da yake a cikine ya sashi jin yau ɗin babu bambanci da wancan daren da ya kasa goguwa a zuciyarsa, amma ako ina kam zaiyi alfahari da baiwa irin ta matar tasa. Dan a wancan dare shima sabo yake, yau kam ya banbance tsakanin aya da tsakkuwa. Ya kuma zaɓi yimata mai gana ɗaya ne dan cire mata tsoron nan da ya lura yay mata tasiri. (Humm gyaran su iya Tabawa bai faɗi a banza ba kenan🥱🤣🚴).
Langyare iya langyare, raki iya raki yasha shi. Kuka kam muryarta har bata fita. Tun ana bashi haƙuri da roko da magiya har dai aka koma kiransa mugu. Yaƙushi da cizo duk ya samu rabonsa kafin duk wani ƙarfinta na neman ceton kai ya ƙare ta koma zallar hawaye da jiran mala'ikan mutuwa (acewarta🥱😜😂).
Shi ya fara farkawa lokacin da alerm ɗin da ke tadashi sallar asuba
Showing 243001 words to 246000 words out of 294165 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82 Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99