ɗaya. Sai da ta shagala a abinda take yi yaje ya ɗakko wayarsa, koda ya duba ya ga tayi sallar sai ya sake samun nutsuwa..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣4️⃣
.........Haka abubuwa suka cigaba da tafiya a gidan Smart da ɓangaren kwallonsa. Dan matuƙa ya dage da training da kuma kiyaye cin abubuwa tare da miƙama UBANGIJI al'amuransa, harda azumin kwana uku yayi da sadaka. Maganar shaƙuwa ko hirar arziƙi kam tsakaninsa da Lulu babu. Babu mai shiga sabgar wani ta ɓangaren lalama, garama shi wani lokacin yakan ɗan tsokaleta ita kuma tai masifa. Idan lokacin salla yayi kuma ko baya gidan zai tura mata text message akan tayi dan ALLAH, tai ma mahaifiyarta kuma addu'a. Sosai yake karya lagonta da hakan shiyyasa a yanzu kam Alhamdullah da wahala kaga lokacin sallar ma ya shige bata tashi tayi ba, daya turo saƙon ko batai niyya ba zata tashi taje tayi. Idan kuma yana gidan zai mata magana nan ma tayi. Girki ma dai kullum da rigima ake yinsa na safe dana rana idan har yana gidan, idan kuma ya fita na safen kawai akeyi ita dama ba damuwa tai da abincin ba, da dare kuma shi dama ba damuwa yay da cin abinci ba balle yanzu da yake sake ƙoƙarin daidaita jikinsa. Kayan shaye-shaye dai duk da ya toshe ko'ina da samunsu hakan baisa zuciyarsa ta samu nutsuwa ba, a duk motsinta kaffa-kaffa yake yi, ita kuma duk da ta daure kwana biyu a cikar kwana na biyar sai da yanayinta ya canja saboda matuƙa take buƙatar su, ta rage kulashi suyi faɗa, ta zama shiru-shiru, wani lokacin ma yakan shigo gidan ko ɗakinta ya ganta zaune a lungu ta takure kanta cikin damuwa koma tana kuka, sosai take bashi tausayi, dan haka a duk sanda ya ganta a yanayin sai ya zauna yayta mata nasiha ne cikin tausasawa, yana kuma ƙoƙarin bata ruwan addu'oin da malam ya basa a ɓoye batare da ta sani ba, magani ma na nan zuwa da malam ɗin yace zai haɗa mata inasha ALLAH akan shaye-shayen dai. A ɓangaren karatu da suka fara duk da dai suna ɗan kai ruwa rana wasu lokutan kafin ayi, Alhamdullah ya fahimci tana ganewa, dan a ɗan tsukun kwanakin a ɓangaren salla abubuwa da yawa Lulu ta gyara, tana kuma ƙoƙarin riƙe addu'oi. Nacin fita aiki kuma bata daina ba, shi kuma bai kulata ba. Washe garin da suka cika kwana biyar ranar asabar Aunty Bilkisu da Hawwah da Maryam da Asma'u sukazo gidan, ranar yana gida bai fita ba, dan dama fitar tasa dai ba ko yaushe bace ba, ba kuma ta wuce zuwa gidansu, stadium training, sai ɗan kaikawo akan case ɗintan nan na yarinyar nan da yake mata bincike tunda su Uncle Yousuf sun shigar da ƙara court da mahaifiyar yarinyar da kuma taimakon ƴan sanda. Duk sanda ya fita kuma baya yarda ya daɗe idan yayi tunanin ya barta ita kaɗai dan a ɗan zaman sun nan ya fahimci bata son kaɗaici, sai kuma sauran kai kawon da suke da su Coach akan batunsa na abubuwan da suka saura dole da kansa zaiyi. Tarba suka samu ta muntunawa ga Lulu irin wadda su kansu basuyi zato ba, sai suka ji ƙaunar matar ɗan uwan nasu ta ƙara mamayesu. Fargabar da suke ta wataran zai iya aure matarsa ta rabasu da shi ta fita fit a zuciyarsu. Yana ɗaki yana barci hayaniyarsu ta tada shi, bai san kosu waye ba dan haka ya tashi badan barcin ya ishesa ba ya fito, turus yay yana kallonsu, sai bin Lulu daketa faman murmushin yake da kallo, a zuciyarsa kuma yana wani tunani, musamman akan maganar malam da yace tana da ɓoyayyun halaye masu ƙyau, to amma miyasa masu aikin gidansu su take musu duk yanda taso? Kodan su suna a ƙarƙashin ta ne take gani, na biyu ya fahimci bata son kaɗaici sam, dan koshi idan zai fita gidan sai ya ga yanayinta ya canja zuwa damuwa koda bazatace komai ba. Maryam ce ta fara hangosa, cike da jin daɗi ta ce, “Yaya Hydar sannu da fitowa”. Da kai ya amsa mata, yayinda sauran ma duk suka juyo harda Lulu, sai dai kallo ɗaya ta masa ita ta ɗauke nata idon. Falon ya ƙaraso ya zauna, cikin girmamawa ya gaida Aunty Bilkisu, su Hawwah ma suka gaida shi. Daga haka aka ɗan cigaba da hira sai dai basu yarda sunyi wani abinda Lulu zataji a ranta kamar ita barece a cikinsu ba. Wannan abu yayi matuƙar tasiri a zuciyarta, sannan yanda suke girmama juna da shaƙuwarsu da soyayya mai ƙarfi ya matuƙar sata jin kewa da jin inama itama haka take da nata ƴan uwan. Ta kasance cikin farin ciki a wannan yinin, dan ko abinci Maryam da Hawwah ne sukayi basu barta tai komai ba sai Asma'u data gyara gidan, dan wannan shine kema Lulu wahala kuma duk da bata ƙaunar ƙazanta. Ta masa maganar mai aiki yaƙi ce mata komai, shi kuma ba mai aikin ce baiso ba duk da yasan kuɗin biyanta ma a garesa wani abu ne daban, tsoron kar mai aikin ta zame mata ƴar aikar sayo ƙwaya yake shiyyasa yay mata shiru. A lokacin da su Hawwah ke kitchen suna girki Aunty Bilkisu kece masa. “Hydar baka ganin ya kamata kayi haƙuri Hawwah ta koma ɗakinta, mijinta na sonta sannan yana ƙoƙarin sa a kanta, mahaifiyarsa kuma shima tafi ƙarfinsa ne. Tunda su Abba sun bar komai a hannunka ya kamata ayi haƙuri ta koma haka nan ai anja masa kunne, ALLAH tausayi yake ban kullum yana cikin zaryar zuwa gidan nan, ga Nasreen dake damunta kullum ita Abbanta Abbanta, ita kanta Hawwah dauriya kawai takeyi da kuma bazata iya ƙetare maganarka ba, kayi haƙuri ka duba ta koma gidan mijinta kodan halin Umma da bata gajiya da abin faɗa kullum ta ALLAH a gidan nan kan Hawwah, haƙurin shi yafi komai ko ya kikace Mawaddat?”. Ta ƙare maganar tana duban Lulu da ke saurarensu. Jin jina kai Lulu tai da faɗin, “Hakane Aunty, to amma miya kawo matsalar har haka? Sa'id ɗin bashine na gani a wajen bikin nan ba anata kai da kawo da shi?”.
“Shine fa.....” nan ta kwashe komai ta sanarma mata. Sosai Lulu tai mamaki, sai dai kuma hakan baizo mata baƙoba dan sun sha cin karo da irin waɗan nan case ɗin wasu ma sai iyayen mijin sun illata yaran saboda ƙiyayya, wasu ko yaranne fitsararru, sannan kakarsu Dada ita kanta fitinanniyar mace ce da tasan tana ƙuntatama matan kawun nanta matuƙa. Duban Smart tai da faɗin, “To amma shi miyasa bazai zauna yay magana ta fahimta da mahaifiyarsa ba, ko kuma yabar gidan nake ganin hakan zai basu masalaha idan basa ganin juna ai Aunty, ko za'a dinga samun matsalolin ba kamar suna zaune waje ɗaya ba”.
“Kowama haka yake faɗa Mawaddat, to amma maman ce taƙi yarda wai zasu barta a kaɗaici. Shi dai mijinki shi ya kamata yay haƙuri a duba kodan Sa'id ɗin” ta ƙare maganar da kallon Smart.
Shiru kamar bazaice komai ba sai kuma ya ɗan nisa. Cikin ɗage kafaɗa ya ce, “Aunty Bilkisu bawai zaman nata nima namin daɗi bane, sai dai kuma bazan barta ta koma ba haka salin alin, inada shiri nima dan dolene sai mahaifiyar Sa'id ta fahimci kuskurenta ko kuma ya raba musu gidan, inada hikimata na tsaiwa akan hakan dan har mahaifinsa ya dawo sannan”.
Cikin gamsuwa Lulu ta ce, “Hakan da yayi ɗin shine dai-dai, inba hakaba komawar tata haka nan babu wani mataki zai cigaba da bada damar faruwar fiye da haka a tsakaninsu......”
Haka suka cigaba da tattaunawa har su Hawwah suka kammala girki. Wani abu daya saka Lulu farin ciki lokacin da su Aunty Bilkisu sukai zaman cin abincin da suka zuba a tray ɗaya sai ta tsaya kallonsu musamman da Smart ya ɗakko nasa spoon yazo tsakkiyarsu ya zauna yana faɗin “Ni sai a ware ni”. Abune da bata taɓa gani a gidansu ba, itama saita tura baki gaba tace, “Ni baku so naci da ku saboda ba Ammah ta haifoni ba”.
Da sauri aunty Bilkisu ta kamo hanunta ta zaunar kusa da ita kusa da Smart kuma ɗan shine a gefenta, har suna haɗa baki ita da su Hawwah wajen faɗin, “Karkisa Ammah ta dafamu a tukunyarta da jin wannan kalamai”. Murmushi tayi kamar yanda shima Smart ke kallonta ta ƙasan ido yana yi, sai tana mai jinta kamar sabuwar halitta a yau. Lulu da bata damu da abinci ba yau kam saita saki jiki ta ɗan ci. Da son neman magana Smart ya ɗauki naman gabanta, hararsa tayi da tura baki itama ta ɗauki na gabansa batare da tace komai ba, kallonta yay yana ɗan zaro ido ya ce, “Miye kuma na ɗauka min nama Madam?”.
“Nawa daka fara ɗauka naka ne”.
Itama ta faɗa cikin ɗam murguɗa baki kaɗan. Kai kawai ya jinjina alamar zan rama, su dai su Hawwah sai gimtse dariya suke. Can Lulu ta sake ɗaukar naman gaban nasa ta rufe da abinci, sarai ya ganta sai baiyi magana ba sai da ya shammaceta ta ɗakko zata kai baki caraf ya ɗauke sa daga spoon ɗin nata ya lunƙuma baki. “What!” ta faɗa tana kallonsa, miƙewa yay da mata gwalo yabar wajen dan ya ƙoshi daman. Da gudu su Maryam suka tashi suna dariya. Lulu ta dubi Aunty Bilkisu kamar zatayi kuka ta ce, “Aunty kin ganshi ko? Shi baiso a zauna lafiya kullum sai anyi faɗa yake jin daɗi”.
Aunty Bilkisu dake danne dariya da ƙyar ta harari Smart da dafa Lulu da itama ke hararsa ta ce, “Kinga ƙanwata barsa zamu rama. Tsarabar dana kawo takine ke kaɗai nama fasa bashi”. Murmushi tai da sake hararar Smart itama ta masa gwalo da faɗin, “7-6”. Ƙwaɓe fuska ya ɗan yi shima da yin ƙwafa ya ce, “Ki jira game over. Aunty kuma gaskiya ba haka akeyi ba”.
“To ni haka zanyi”. Cewar Aunty Bilkisu tana hararsa. Sai kuma ta kalla Lulu, “Kin san wani abu shi fa dama Hydar akwai zura tun yana yaro, idan aka zuba abinci aka bashi sai yace shi bashi yake so ba na Ammah yake so, idan aka bashi sai kuma yace (Ni wannan ina co) ya sake nuna namu, nan ma a bashi sai ya sake nuna wani nanma yace shi wannan yana co, hankalinsa bazai sake kwanciya ba sai yaga kaf abincin an tara masa gabansa zai bar kunnen kowa ya huta kuma fa ba ci zaiba.
“Kai aunty miye na faɗa mata kuma” Smart ya faɗa cikin shagwaɓa. Aiko mi Lulu zatai inba dariya ba. Sai ta kallesa tace “Ni wannan ina co” ta ƙyalƙyale da dariya. Sai da takai ya kwashi filos ya fara jefa mata ta tashi da gudu tana cigaba da faɗa. Dole aunty Bilkisu ta dara itama tana sake jin ƙaunar Lulun a ranta. Waɗan nan abubuwan sun matuƙar ɗauke ma Lulu kewa da sakata a farin ciki a wannan yinin, yayinda gefe ɗaya ta takurama Smart da faɗin ‘Ni wannan ina co’ har bayan tafiyarsu. Shima sai abun ya koma bashi dariya dan ya fahimci ta samu abin yi.........✍️

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣5️⃣
........Washe gari bayan ya dawo motsa jikin safe da yake fita yace ta shirya zasu fita, da mamaki ta dubi agogo da faɗin, “Da sassafen nan? Ko 8 fa batai ba”.
Shima agogon ya kalla sai kuma ya dubeta. “Ina ganin kafin mu kammala shiryawan tara ma zata iyayi, dan inada abune mai muhimmanci shiyyasa nake son mu fita da wuri”.
“Wai ina to zamuje?”.
“Idan mun fita ai zaki gani, ke dai ki shirya”. Ya faɗa yana ficewa, kitchen ya nufa ya sake ɗaukar ruwa ya sha sannan ya nufi bedroom ɗinsa ya cire kayan motsa jikin dake jikinsa ya faɗa wanka. Itama a ɓangaren Lulun wankan ta tashi ta shiga, dan dama dai tana duba karatun da ya ƙara mata ne kafin fitarsa training. Harga ALLAH tana jin daɗi da farin cikin karatun da sukeyi na addini, abinda kuma ke sake zaburar da ita akan hakan watarana akan wani case an gayyaceta hira a gidan wani tv tare da wani lawyer da basa shiri sam saboda duk karon da tai da shi a shari'a sai ta kaisa ƙasa. A cikin hirar kawai ɗan jaridar sai ya sakko wata magana data shafi addini, amma sai ta kasa amsa masa dan bata sani ba, sai shi lawyer ɗin ya amsa da karsashi da son nuna isa har yana mata shaguɓe akan bata da ilimin addini. Abin ya mata ciwo, tun a lokacin kuma tayi ƙudirin fara neman ilimin sai dai bata san tayaya zatai hakan ba, sannan bata da shaƙuwa da wani a ƴan uwanta da zata iya kawo zancen ta yanda za'a fahimceta, na biyu rashin barin abu a rai da take da shi ya sata tattara abin ta ajiye gefe ta cigaba da sabgoginta. To bayan fara karatun nan da Smart ke koya matan sai ta fara fahimtar abubuwa da dama, sannan tana jin wani nutsuwa da jinta daban da dacan duk da bawani nisa sukai ba can sosai, dan ma dai ƙwaƙwalwarta mai saurin ɗaukar abu ta taimaka mata matuƙa. Kamar yanda ya faɗa sun kai kusan ƙarfe taran, dan sanda ya fito bayan ya shirya koda yaga kayan data saka kai tsaye yace mata ta sakesu. Taso masa gardama amma sai yace tayi haƙuri gidansu fa zai kaita ta gaida su Ammah kuma can zata yini sai dare. A take yaga farin cikinta ya bayyana, dan ita dai tunda Asma'u suka bata labarin yanda Ammah ke sonta da bibiyar abinda take yi sai take jin ɗokantuwa da sake ganin Ammah ɗin duk da a waccan zaman na kwana ɗaya da aka kaita gidansu bazata ƙarar da fuskar kowa ba. Kanta tsaye ta ce, “To dan ALLAH zoka tayani zaɓen wanda zasuyi”.
Idanu kawai ya zuba mata sai kuma ya saki murmushi zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama. Baiyi zaton zata nuna ɗokin sake zuwa gidansu ba tunda ta kwana a ciki taga yanda yake. Ya fahimci gane wacece ita kai tsaye abunne mai wahalar gaske, dan idan ya gama haddace nan ya buɗe mata sabon shafi sai yaga nan ɗin ma dai akwai abubuwan ban mamaki a cikinsa fiye dana baya daya baro.
Da kansa ya zaɓa mata kayan kamar yanda ta buƙata. Atamfa mai ƙyau da akaima ɗinkin zani da riga, sai hijjab. Anan ne ta ɓata fuska da ɗauke hijjab ɗin gefe ta ajiye ta ɗauka gyale. Zaiyi magana ta marairaice fuska. Shiru yay baice mata komai ba ganin gyalen nada girma. Sai kuma wajen ɗaura zani ma wata sabuwa. Dan Lulu bata iya ba, da tayi-tayi taga ta kasa saita shiga ƙwala masa kira dan sanda zata saka kayan catai sai dai ya fita, shi kuma baiyi musu ba ya fita ya tsaya a ƙofa. Kiran nasa da tai ya sakashi dawowa. Cikin ɓata fuska ta ce, “A canja wasu gaskiya”.
“Saboda mi”.
“Toni na iya ɗaura zani ne”.
Dariya taso ƙwace masa amma ya danne. Ya ƙarasa shigowa ciki yana faɗin, “Kin yarda na ɗaura miki?”.
Shiru tai kamar mai tunani, sai kuma ta ɗan hararesa da faɗin, “To wlhy ka rufe idonka, dan inka kallan ban yafe ba”.
“Oh hakama zaki ce daga taimako?”.
Baki taɗan murguɗa batace komai ba. Shi kuma sai yay murmushi kawai da ƙarasowa inda taken dan bai son ya biye mata Coach nacan na jiransa. Da taimakonsa ta ɗaura zanin duk da anata masa masifar ya rufe ido kuma karya taɓa mata jiki, duk da yana da abubuwan faɗa baice komai ba shi dai. Ɗaurin ɗan kwali ma bata iya ba. Cikin dafe kai ya ce, “Naga takaina, na auri bahaushiya a zahiri amma bata da banbanci da turawa ni Aliyun Ammah”.
Harara ta zuba masa ta figi handbag ɗin ta da mayafi ta fice. Sai wata leda da bai san ko minene a ciki ba hartayi gaba ta dawo ta ɗauki kayarta. Bayanta yabi yana dariya da faɗin, “8-6 kenan”.
Sai da ta hararesa ta ce, “Kama isa. Wlhy 7-6 na sani”.
“K matsalata da ke rinto, garama ki yarda kinyi game over”.
“Never give up wlhy, mai sama da hundred ne yay wining”.
Ta amsa masa nan ma tana hararsa. Ita ta fara fita, shi kuma ya kashe kayan wutar dan an haɗa musu tv yanzu ya kullo ƙofar ya fito. A jikin motarta ya ganta tsaye, sai ya ɗauke kansa ya nufi gate. “Ina kuma zaka je?”. Ta faɗa tana kafesa da idanun ta. Kansa tsaye ya bata amsa batare da ya juyo ba. “Zan sama mana Napep mana”.
Da mamaki ta ce, “Napep kuma? Ita kuma wannan motar fa? Ni malam bana son ƙauyanci kazo mu wuce danni kam bana hawa Napep. Bamma taɓaba”.
“Sai ki fara da ga yau”.
Ya amsa mata yana yin gaba. Tana nan tsaye mamaki da jinjina girman kansa na cimata zuciya, dan ita abinda ta fassara kawai kenan a
Showing 135001 words to 138000 words out of 294165 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46 Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99