ke shiga malamai kawai don su yi
hulda da ni? In ka dade muna hulda shi ne muyi
wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon
shekara daya don yana da hankali". A zuciyar
Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu
ban auri Ummi ba. Sannan ba Allah a ranta bare
taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima". Ya ce,
"Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda
da ke? Sannan daman duniya tasan ki kina
haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina
sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai
sanni ba duk daya. Sudai burinsu kudin". 12......
Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar
ba". Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka
nadama irin wadda waninka ya ta6a yi. In kana
da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka
Ishara". Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba,
domin alamar yana son ji kenan. Da a ce zan fadi
sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin
Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a
TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka
na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta
yaba. Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa
ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba. Sai dai nuna
masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana
kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda
musu zakka ba. Da jin haka sai ya taho, nan
dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da
maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa
masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke
so ba. Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba,
shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi
guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure
ne ya ce zai gudu. Don gidan nan duk masu tsaro
ne har da ma layin gaba daya. Da sauri za a
kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi
kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka
kwana ciki. Domin duk a hannunmu suke, amma
Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya
min shame-shame zai mutu don yunwa. Ba arziki
na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan
karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa
shi a daki. Nasa Malamina ya karasa min shi,
sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan
cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya
kare a nan. To dama iyalanshi suna ta nemanshi
an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu
ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu
a cikin garin nan da ma wajen shi". CIKI book 3 part 3
ZURFIN CIKI book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24
Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare,
Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi
ne ya fara baki abinci a baki. 20..... Watanki
hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu,
Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana.
Lah, goyo? In ji Ummi. Umma ta ce, "Goyo sosai
kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in
naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku
yanzun sai in ta mamaki. Don tun ba ki fita a
tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata
hudu ba, ki ka tantance muryarshi. Haka nan
sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya. Abba
yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da
tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki
Ummi. In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to
sai da wayo da dabara. Ke har an kai lokacin da
kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in
ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki
wakar da yake miki. Ummin Abba da Alhaji,
Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki
dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break
dinsa zai debo miki tsaraba. Umma na bada tarihi
Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin
yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa
lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi
tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka
yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare
kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in
baki nono". Wata sabuwar kauna da so Ummi taji
ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido,
ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya
ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki
ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin
daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce
"Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne,
kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji". Ummi
ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba?
Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama,
suka amsa. Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya
faru da kai? Nan ya warware musu komai, suka
yi ta al'jabi. Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka
mata suka maida aure ba a bakin komai ba?"
Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z
aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka,
don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba
to can gabanta hadu da mai tona ta. Su Alhaji
suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da
jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga
dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda". Abba ya
ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin
aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda
dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai
ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba".
Suka ce Amin. 21... Ranar su Alhaji a tsakar gida
suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take
yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin
da aka bata. Ashe har yanzu Ya Abba na sonta,
Allah ya sa haka har yanzun. Sai kusan sha daya
Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida. Abba ya ji
dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi
suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta
ce, "Ka gaida 'yan gidan". Ya ce "Za su ji, har ya
kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a
kara sace shi fa, duk suka sa dariya". Abba ya
dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur
kuwa? Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba
shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar
galan na fita". Alhaji ya ce, "Na shigo da mai
dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake
cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi
'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a
Allah zai kare ni. Yau kam Ummi ta dade bata ga
daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau.
Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta
fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai
sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin
karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli
matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce,
"Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk
lokacin da na ganka sai gabana ya fadi,
musamman in kazo min da jarida". Yayi 'yar
dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah
Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in
da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan
sako ne. Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da
ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama,
hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan
jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi? Ta
soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har
ta gama. Kafa kurum take karkadawa tana
tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma
duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba. Amma duk
da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga
manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta
kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta
danna kira. 22.... Jim kadan aka daga ta ce,
"Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da
Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba
lau ba, kana ji? Ina yaron da nake baka labari
dan jarida? Ya ce, Naji. Ta ci gaba, Yaron nan
kaga yanda ya yayata ni a duniya? Sai na koya
mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma
ki ka ce sunanshi? Ta ce Idris, ya ce To zan kira
ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai
na gama bincikena duka. Ta ce an gama. Sintiri
tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa
barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin
wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data
duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine. Ta daga da
cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne? Ta
ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai
miki? Ta ce, Hum! Ke dai bari Aminiyata, yanzun
nan na gama karantawa a jarida ban ma san
hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba. Attine
ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku
mana. Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na
kira Teacher ya ce in saurare shi". Attine ta ce,
"Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din
ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba". Hajiya
Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin
maganar tsundum! Don haka dole in yi taka tsan-
tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai
fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta
ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta
bakin Teacher". 23.... Shikam Malamin duk
lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku
saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka.
Ya ce, Hajiya? Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta
batun yaron nan ki watsar domin yanda naga
al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari
ba. Haka nan allura zata tono garma game da
damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a
gurin maigidanki. Tsaki taja don maigidana
Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda
shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan
kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon
neman kudi. Sam baya biya mini bukatata ba
dole in nema ba? Yarana biyu cal a duniya duk
sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani,
don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min
jinin matsiyaci. Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina
ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin
ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki
yaron yana da kariyar da take kare shi daga
Ubangiji. Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne,
tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba
za su iya tunkararshi ba... Dakata Malam, ta
katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma
muka ci nasara a kanshi? Ya ce kila shi Malamin
kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko
wannan da sauran shan ruwansa. Ta ce, "Kai ne
sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko
kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar
Malam". Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu
wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin
da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja
sannan ta kashe wayar. Har gari ya waye ba ta
daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya
ba. Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun
tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken
ga wasu Malaman. Sai dai guri uku zancan iri
daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri
biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci
sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa
ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun.
Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da
na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana
da makaminsu? Daga karshe ta ce na bar shi
mara rabo". Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun
farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da
shi in nemi wani. Kai jama'a sai kace aikin Allah
menene amfanin zinar ma da har ake shiga
Bokaye dominta? Allah ka tsare mana Imaninmu,
amin. 12 24.... Ummi tana zaune zata wanke 'yan
kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana
faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata
nishadi. Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana
jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na
ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso
dan Yayana. Ta tsoma sikyat dinta da fant da
'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana
maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya.
A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da
sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu
kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi. Ya ce,
"Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan
murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba". Ya ce,
"Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki
ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce
me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa
suka gaisa. Ya dawo kofar Umma yana tabayarta.
Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman
Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta
na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku
ta juri wulakanci. Waccan haihuwar da Zilai
kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan
sunan, amma yau ta koma. Abba ya ce, "Ummata
tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa
ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba
kwarjini". Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi
ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min
farce". Ta hango kayan Ummi na daura ta ce,
"Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki,
ace 'yammata suna saka rigar mama? Kunya ta
cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25.... Abba
ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya
ne? Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar
kujerarta ta zauna. Tir da wannan wayewar taku
ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har
ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta
ba? Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa
goma ba ma ta sa ran mama ba. Abba dariya ta
ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya
kayan ta matse ta aje. Abba ya ce, "Yanzun
Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas
kurum ce fa, bata ma cika ba. Ta ce "Mu lokacin
sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta.
Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa
'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in
huta gorinki. Abba ya matso, "Ummi don Allah in
tambaye ki mana? Ta tsaya da yanke 'kunbar
tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta
bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin?
Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da
hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai
ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce,
Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin
saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi
lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata
sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so
ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji
mai sunan Malam da zancen wofi. Ya ce,
"Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma
dai bari in tafi abina. Ummi ina Azimi yau, zan zo
in yi buda baki anjima. Ta ce, "To." Tsohuwa ta
ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana
la'ke a nan? Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa
lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan
nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani
tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta?
Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba
ne, na 'yan uwantaka ne? Kai ko dai ta fito ta ce
Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa
take ba. Kusan wata daya kenan rabon da ya
samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya
baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma
datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi
ya samu cikakkiyar biyan bukata ba. In ta zo
dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake
maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga
take mishi (Mtsw! Allah rabamu da kazaman
Mata). Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya
matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai
ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya
kare shi da fadawa sharrin zina. 26.... Bai zaginta
ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai
tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi.
Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in
soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan
ruwa. Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma
fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah. Ta
ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa
kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da
ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah.
Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da
yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe
jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata.
Sallamarshi ta jiyo suna gaisawa da su Umma, ta
fito ya bita da kallo, kin yi kyau kanwata, Umma
ta ce yau za ku hoton ne? Ta ce kila, Abba ya ce
shi yasa ki ka yi kwalliya haka? Ba ta ce komai
ba sai dai ranta bai so ma maganar da Umman
tayi ba. Suna hira da Umma ta shirya misi abinci
ta koma kan kujera ta dauki littafi lokaci-lokaci
idanunta suna kan Abba. 13 Suna hira da Umma
ta shirya mishi abinci ta koma kan kujera ta dauki
littafi, lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. Shi
ma haka ya ce wai ni littafin nan da ku ke nacin
karatunshi dame kuke karuwa? Umma ta ce, Ai fa
gara ka tambaye ta, don ban ga abinda ta ba
muhimmanci ba irin wannan littafin. Ummi ta cem
ina karuwa sosai Umma suna koya mana tarbiyya
yyanda zamu tafi da rayuwarmu cikin tsarin
Addini da al'adarmu. Abba ya ce amma basa
koya tsafta da biyayya, Ummi ta ce suna yi sosai
ma, ya ce Umma ni naga jarabar karatu irin na
Bishira amma kullum mugayen halayenta bayyana
suke yi. Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki
kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi
dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce,
"To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na
banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu
lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27.....
Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da
aikin yi? Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi
don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan
ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa
Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don
shiryawa su Alhaji Abinci. Ummi kam sun bar ta
cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura
da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin
yaran nan saura wata nawa? Ta ce, "Wata ko
kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida,
ban ga kana motsi ba? Alhaji bikin nan zai
mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun
kaya?" Ta ce, "Ni da
Showing 21001 words to 24000 words out of 41322 words