da
burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki
ce". Nurse ta kawo wani dan kwano na silba
Ummi ta wanke baki da taimakon Abba. Likitan
ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata
magani. Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin
wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura
tayi yawa. Kai shi fa wannan Yaya Abban bai
masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko
gaida shi yayi d kyar yake amsawa. Shi fa tun
ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da
Abba ba ya ji ya tsane shi. Umma ta ce, "Abba
an kira Isha'i. Sahabi kaje kai ma ka huta yaran
nan tun tuni ya ke nan". Abba ya kalle shi, "Ya
kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan
ya dan rusuna "Sannu Ummi". Ta ce, "Yauwa"
"Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da
safe. Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a
kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin
wani abu yanzun ba". Umma ta ce, "Abba". Ya
kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari.
Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma
sai da safe". Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar
taka". Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba
halinka ba ne kada in kuma gani". Ya ce "To
Umma". 23. Su Alhaji sun yanke shawarar daga
auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu
masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata.
Gidan su Sahabi sun ji haushi musamman
Innarshi, sun kashe dan abinda suka tattala don
bikin amma gashi an daga, su kam da an daura
auren in ta murmure sai a yi bikin. Sahabi ya
shigo gidan ranshi a 6ace, ya kalli Mahaifiyarshi,
"Inna wai sun ki a dauram?" Ta ce, "Sun ki, dama
ai gaddamar dan yau ce. Ban da shegiyar
gaddama ga 'ya can da a ka baka a daura ka
gaddame, to yanzun ina ranar abin da aka mana?
Gida duk dangi sun cika amma wai a daga biki,
mu kuma karamin karfi ne da mu, bare mu ce nan
da sati biyu zamu sake kashe kudi". Sahabi ya
tuna abinda Abba ya masa a asibiti, shi ne dalilin
da bai sake zuwa asibitin ba, yaja tsaki. "Kin san
Allah Inna ni kaina sai yanzun nake jin haushin
kaina da na ki amincewa da Badariyya. Mu zuba
musu idanu in za su sake kawo mana cikas sai
kawai in koma gurin Badariyya." Inna ta ce, "In
da tun jiya kamin zancan nan da tuni yau ba a
fasa daura auranka ba an ma da Badariyya". Ya
ce, "Kiyi hakuri Inna mu ga nufin su". * 42... An
sha shagalin bikin Fati kuma an kaita gidanta.
Ummi jiki Alhamdulillah, Abba kullum in zai je aiki
sai ya biya. Haka nan in ya dawo gida wanka
kawai zai yi ya tafi, wataran sai goma ko sha
daya. Abokanshi suna ta zuba duba Ummi, ita
kanta da lokacin zuwanshi ya karato ta dinga
kallon agogo ke nan tana kallon kofa. A zaman
asibitin nan Umma ta gama karantar su tsaf.,
matukar son juna suke yi, sai dai taji takaicin da
sai yanzun sonsu ga juna ya bayyana. Lokacin da
ya kasance an riga an bada Ummi ga wani sai
dai ta ci gaba da addu'a Allah yayi za6i na
alkairi. Bashir yayi murna da fasa auran Ummi,
dama a fasa gaba daya. Yana fitowa dakinshi ya
ji Ummarsu tana cewa, "Kin san Allah Tasalla,
uwar yaron nan da zai auri Ummi zata ga bakin
ciki, don mallake mata da za su yi. Tana ji tana
gani sai yanda suka yi da shi. Kuma ba yanda
zata yi sai Allah ya isa". Tasalla ta ce "Ban da
halin mutanan yanzun ba da sai na fada mata ba.
Kin san makotanmu ne ta baya, gashi su ba karfi
ba. Sahabin ne fa ke rike da gidan, kin san shine
Babban a gidan". Sahura ta ce, "Don Allah Tasalla
ki taimaka ki fada musu, don ko in har aka yi
auran nan in suna cin abinci sau uku ne a rana,
to za su koma dau daya". Tasalla ta ce "Ai ko
zanje". Tana fita Bashir ya dawo kusa da
Ummarsu ya ce, "Umma dama da kanki ki ka je,
saboda za su fi yarda tunda sun ga ke kina da
danganta da gidan". Ta ce, "To in Babanku ya ji
fa?" Ya ce "Umma ai in kin fada musu ai kwa6ar
su za ki yi, sannan kada kije a kan lokaci, kije ana
gobe daurin auren". Ta ce, "Saboda me?" Ya ce,
"Saboda su Alhaji Babban suji haushin rashin
fada musu da wuri". Ta ce, "Haka za a yi, kuma
in an fasa Malamai zan shiga don a hanata auran
ma kwata-kwata". Ya ce, "Kada kije wurin
Malamai yanzun tukun". Ta ce. "Ai dama sai an
natsa". * Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau
matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne,
tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta
zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya
nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi
matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin
mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya
ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri
zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi
wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko
garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can
Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta
mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa
ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke
Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya
ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?"
Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai
kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je
gaisheta." Ya ja tsaki tare da cewa, ballahaza
wadda bata san mutuncin mijin auranta ba". Ya
yakice labulen ya wuce yana jiyo ta tana cewa,
"Ba dai za ni ba ko me za ka ce". Ranshi a 6ace
ya isa asibitin, Ummi na zaune kan gado ta kosa
Abbanta yazo, ko karyawa ta kasa yi, yana
sallama suka hada ido. Nan ta ke ya ji ya manta
da duk wani bakin ciki da ya taho da shi, ya isa
bakin gadon fuskarshi dauke da murmushi. Itama
murmushin take yi, ya ce. "Ummi ya ya jikin?" Ta
ce "da sauki". Ya Abba kayi kyau sai ka ce
Manajan Banki". Umma ta saka dariya, shi ma ya
yi 'yar dariya, "To ko bankin zan koma?" Ta ce,
"A'a kafi kyau da dan jaridanka Ya Abba, balle in
kana turancinn nan a labarai". Ya lakuci
kumatunta "Ko kwanwata?" Ya juya ya gaida
Umma, Umma ta ce "Ka zo katafi gurin aikinka
fa". Ya ce, "Umma sai sha daya yau zanje gurin
aiki". Ta ce, "Ni na ma kosa a sallame mu". Abba
ya ce "Ai kila a sallame ku yau. Likitan ya shigo
ne?" Suka ce "A'a. Suna cikin karyawa Likita ya
shigo ya same su, ya kuma kafa mata dokokin
daina tunani, daina shiga duk wani abu da zai sa
ta cikin damuwa. Rage shan gishiri tare da
samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma
su dinga nisantar 6acin
Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 6
ZURFIN CIKI book 3 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:31
Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya
kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin
ranta. 26. 43... ABBA Ya kwaso su ya maida su
gida, cikin satin Ummi ta murmure. Sahabi na
zuwa sai dai da sun gaisa yake tafiya.
Mahaifiyyarshi ma tazo, amma Bishira da Sahura
ko le'ke, Bashir ma yana ta sintirin zuwa. Ganin
haka Alhaji ya ci gaba da shirin biki, mutan kauye
dai dama an ce kada su dawo, Ummi dai bata
maida hankali ga komai ba. Ta ce ma Umma zata
je gidan Fati, Umma ta ce To sai ki je gurin
Sahura ta kwatanta miki. Abba ya same su suna
zancen, don haka ya ce ta shirya zai kaita ya
ajiyeta in ya tashi aiki sai yaje ya daukota. Yanda
ta samu Fati da Angonta ana ta ji da juna abin
ya tsokanota, sai dai ta kasa ganin dacewar
soyayyar da Sahabi. Da mijin Fati ya fita Ummi ta
ce, "Oh, Fati cikin kwana takwas dubi yanda ki ka
yi kyau". Fati ta ce, "Amma ban rame ba?" Ummi
ta ce "Eh to, kin dan rairaye". Fati ta ce, "Kai ai
dole, gaskiya ina koduwa, wallahi ba ya barina in
huta". Ummi ta ce, "Da me?" Fati ta ce, "Dallacan
ki gane mana". Ummi ta ce, "Wai da me? Allah
ban gane ba". Fati ta ce, "Ai ke sokuwa ce, gurin
kwanciya mana. Ummarmu ta samu ta dirka min
kayan sha na mata, gashi nan nazo ina ta shan
wuya". Ummi ta zaro ido, "Da wahala ne?" Fati ta
ce, "Tab, ai kin kusa kema za ki ji". Tsoro ya cika
Ummi. Ta ce, "Zan ce ma Umma ni dai kada ta
bani wannan kayan matan". Fati ta yi ta dariya
tare da cewa, "Ke yanzun sai ki iya wa Ummanku
wannan zance?" Ummi ta ce, "Sosai ma". Fati ta
ce, "Ko ba ki sha ba yarinya sai kin sha zafi, ana
kawo ni ko dan kwana daya bai raga min ba".
Ummi dai ido ya raina fata. Koda Abba ya zo
daukarta duk ta damu. ** ** 44..... Tasalla ta
samu uwar Sahabi ta fada mata cewa, in dole ne
sai danta ya auri Ummi, to ta amso mishi karya
tambaya. Don kuwa wata rana sai ta taso ta
ganshi ko da a hanya ne ta rasa samun hakan.
Inna ta tsure ta ce, sai a fasa babu dole, ita
dama tuni abin ya sire mata. Ana gobe daurin
aure gidan su Ummi suna ta shiri Ummi na ta
kuka, wannan karon ba Umma ba har Alhaji da
Tsohuwa sun kule da wannan iskancin da Ummi
ke yi. Alhaji ya ce "Ki sani uwata, wannan karon
ko kin tsokalo ciwon nan naki auren nan dole ne
babu fashi. Idan yaso jinin naki ya tashi ya ta6o
sama ba zan kuma daga auran nan ba". Lokacin
da Alhaji ke wannan fadan Abba yana gidan yana
zaune dakin Umma yayin da Ummi ke gefanshi
tana rusa kuka. Umma ta shigo ya ce "Umma
don Allah ki lallashi Alhaji a dan daga bikin nan
mana". Abba bai ta6a ganin ranar da Umma tayi
mishi irin wannan kallon da ta masa yanzu ba
tun tasowarshi. Sannan bata ta6a daka masa irin
wannan tsawar ba ta ce "Kai! Abba shiga
taitayinka, me yasa yanzun ka canza, ko kai ba
za ka hukunta Ummi ba da irin wannan yaro da
hankalin da take mana? Don gidansu kanta a ka
soma aure? To wannan karon ba za a daga bikin
ba, in yaso ta mutu, ke ko mutuwa ki ka yi
gawarki can gidan mijinki za a je a miki sutura".
Tsohuwa ma daga can tana yo nata fadan tare da
dauko tarihe-tarihen da tana cewa, "Lokacinsu
kaza-kaza". Abba ya sake kallon Ummi,
matsanancin kukan da take yi yana daga mishi
hankali, ya mike tare da kama hannunta, "Zo
muje". Ya bude mazaunin direba ya ce ta shiga,
shi ma ya koma ya shiga motar ya tasheta, tafiya
kawai suke ba tare da ya san in da suka dosa ba.
Kukan Ummi na tsikararshi, sun yi tafiya mai nisa
sannan ya tsaya a hankali cikin wata irin murya,
ya ce "Ummi ki fada min gaskiya kina son
Sahabi?" Ta dago ta dube shi, "Ni bana son shi".
"To me yasa ki ka fito da shi?" cikin dasasshiyar
murya ta ce, "Ba ni da yanda zan yi ne, saboda in
ban za6i Sahabi ba za a bani Bashir". Ya ce, "To
ke yanzun fada min wa ki ke so?" Gabanshi ya
shiga faduwa don tsoron kada kunnenshi ya ji
mishi ta ce wani ba shi ba. Ta kuro shi da ido
tamkar ta ce kai, amma sai take ganin in ta fada
mishi haka dan shirin da suka soma yanzun zai
wargaje, kila ma sai ya hada mata da duka. Wasu
zafafan hawaye suka gangaro kan kumatunta,
daidai lokacin da yake cewa "Ko dan digo ki ka ji
son ko waye a ranki kada ki rufe min". 45... Ta
girgiza kai "Ba na son kowa Ya Abba". Cikin wani
irin yanayi ya dubeta, "Shi kenan, sai ki je ki
hakura da Sahabin a sannun kin so shi". Cikin
kuka ta ce, "Ya Abba Allah ni bana son shi, kai to
ka hada ni da ko waye mana". Ranshi 6ace ya
dubeta cikin tsawa ya ce, "Ki rufa min baki tunda
ba ki ta6a son kowa ba ki zauna da wanda ki ka
za6i zama da shi. In da kina son wani ne to da
sai in cije in tunkari su Alhaji, tunda kuwa babu
sai in ce musu me?" Ya fada mota, ya koma kofar
gidan. Koda ya tsaya tafi minti uku sannan ta
fito, yana kallonta maimakon ya wuce gida sai
kawai ya nufi gidan Maman Iman makociyarsu da
suke shiri da ita. Shima kanshi na kan sitiyarin
motar har ttsawon shudewar wasu dakiku,
sannan ya nufi gida. 27. Misalin karfe tara
Umman Bashir ta rangada sallama a tsakar gidan,
Innar su Sahabi ta amsa tare da fadin "Shigo".
Sahura ta shiga tana tambayar "Ba kowa dai ko?"
Inna ta ce "Shigo mu kadai ne". Bayan sun gaisa
ta ce "Ba ki sanni ba ko?" Inna ta ce, "Eh."
Sahura ta ce, "To ni dai tsakani ga Allah zuwa
nayi in ba ki shawara bisa ga yarinyar da danki
zai aura. Tsakani ga Allah yarinyar ba ta da
mutunci, sannan iyayenta za su mallake miki da,
don ni kaina ya faru da ni". Sahura don makirci ta
soma rishin kuka. "Dana maigidana ya ba su riko,
ina sheda miki wannan zance 'yar uwa yanzun
tsakanina da shi sai ido, sun makkale shi komai
shi yake musu, ni ko da nayi wahalar ciki da
nakuda sai na tashi a banza. To da yake an ce
ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, shi ne nazo in
sanar da ke. Amma in kin ji haushi kiyi hakuri".
Ta yunkura zata mike. 46... Inna ta ce, "Zauna
'yar uwa, na gode. Nima fa tuni auran nan ya fice
min a rai, dama da naga shi Sahabin ya dage ne
sai kuma suka aiko gobe azo za a daura aure sai
na hakura". Kafiin Sahura tayi magana sai Sahabi
ya doka sallama, Inna ta ce "Yauwa zo nan". Ya
nufo ta "Zauna kaji ma kunnenka". Ya rage
tsawo, Inna ta ce "Baiwar Allah ya ki ka ce?" Nan
Sahura ta soma zuga sharri, ta kara da cewa
"Yaro ina ga ma za ka san dan nawa da suke riko
Abba a ke ce masa". Cikin saurin baki ya ce, "Na
san shi". Ta ce, "To dana ne da asiri suka amshe
min shi, sai dai Allah ya isa". Ya tuna irin halayen
da Abban ke nuna mishi. Yaa jinjina kai, sannan
ya dubi mahaifiyarshi "Inna to da Kawu yayo
binciken halayan iyayenta ai ana ta yabon
halinsu". Inna ta ce, "Kin ji shi ko? To bari kaji,
kwanaki ma Tasalla da ke bayan layin nan tazo
ta fadan irin wannan matsalar ban kama ba ne
don na asanta da shegiyar karya. To kuwa an yi
biyu ba zan bari ai na uku ba, don haka a daran
ta tabbatar ma da danta an fasa gobe ya wuce
gurin Badariyya a daura, su kuma in sun ji shiru
sa ba wani can". Cike da murna Sahura ta koma
gida. * Maman Iman tayi lallashin duniya amma
Ummi ta ki yin shiru, ga zazza6i tamkar wuta a
jikinta. Sai kusan sha dayan dare sannan Maman
Iman ta rako ta gida, lokacin Umma tana ta
neman layin Abba a kashe. Ta ce, "A'a sun dawo
ne yanzun ni ke neman Abba in ji suna ina ne?"
Maman Iman ta ce, "Tun dazu tana gidanmu
zazza6i da ya rufe Ummin, na bata magani ta 'ki
sha". 47... Umma ta ce "Rabu da ita kar Allah
yasa tasha, aure dai gobe babu fashim dubi irin
yanda a ka sa gidan su yaron nan wancan karon
suka kashe kudi gurin yin girki da sauransu ba a
yi bikin nan ba. Yanzun a kuma dagawa daga
lokacin da muka samu?" Maman Iman ta ce, "Ai
ba zai yiwu ba, sai dai a bi ta da lallashi". Umma
ta ce, "Mun daina lallashinta tunda ko mun
lallasheta aikin banza ne". Maman Iman ta ce,
"To Allah ya kaimu gobem bari in shiga gida sai
mun shigo aiki da safe". Umma ta ce, "To sai da
safe". Ummi tana shiga dakin Umma taga baki
kwakkwance, ta ce a ranta "Mayu, don kalata sai
da wasu suka dada zuwa". Tana fushi da
tsohuwa amma duk da haka dakin ta nufa, ta
kwanta a bayanta don ita tuni tayi bacci. Nishin
kukanta ya farkar da Tsohuwar, kala bata ce
mata ba, sai sauka tayi ta shimfida a kasa ta
kwanta, sannan ta ce "Aniyarki ta biki Takwara".
Wannan dare gurin Ummi da Abba wani dare ne
mai cike da bakin ciki da tashin hankali, ko Sarkin
sata bacci ranar bai samu galaba gare su ba.
Dukkan su a kan kunnansu aka kira sallar farko,
Abba ya mike cikin rangaji, jin jikinshi yake yi
tamkar iska ta dauke shi saboda rashin karfi.
Ruwa ya diba ya watsa, wanka sannan yayo
alwala don yin nafila, addu'a yake Allah yasa
hakan shi ne mafi alkairi a gare shi. Da ya dawo
Masallaci kwanciya yayi amma baccin ya ki bai
fita ba sai kusan takwas. Koda yaga Bishira
zaune a tsakar gida tana karatun littafin sam bai
ji haushin rashin zuwanta gidan su Umma ba.
Nashi ganin duk wanda yaje tamkar yana murna
ne da rasa Umminshi da yayi, ita kuwa da gadara
ta fito don ya ji haushi, bata je ba yana son sanin
halin da Ummi take ciki amma ba ya ra'ayin
zuwa gidan su Umma. Shagonshi ya bude ya
shiga ya dan zauna har zuwa tara, yana kallon
lokacin da Jama'a suka yi ta dafifin shiga layinsu
don halartar daurin auran. Kurum sai ya samu
kansa da tare dan Aca6a ya hau ba tare da ya
shaida masa inda za su ba. Koda dan Aca6an ya
tambaye shi ce masa ya yi mu je. 48.... Ita ko
Ummi ranar zaune tayi sallah ta koma ta kwanta,
duk kaikawon ai da 'yan shewe-shewen da jama'a
dangi da makota tana jin su. Sai dai makoshinta
ya bushe ga zufa da ta rufeta, duk da yanayin ba
na zafi ba ne. Karfe goma daidai shi ne lokacin
daurin auran, layin ya dinke da jama'a, Alhaji
ranshi a dame don bai ga Abba ba. Ya kalli Alhaji
Karami, "Ina Abba ne?" Alhaji Karami ya ce,
"Abokan aikinshi ga su can sun zo ba a ganshi ba
son daukan daurin auran". Alhaji ya ce, "Su dauka
mana nasan yana nan tafe". Har sha daya ana ta
jiran 'yan gidan Ango shiru, su Alhaji suka tashi
dan aike gidan don a ce ana jiran wakilan ango.
Amma sai a ka dawo musu da sako wai sun fasa,
kalmar da ta rikita Alhaji ta tashi hankalinsa. Ga
jama'a an tara, Alhaji Karami ya ce wadannan
akwai kananan mutane." Daidai lokacin da muryar
wani Maroki ta ratso dodon kunnuwansu da
cewa, "Alhaji ku hanzarta Jama'a sun gaji da
jira". Alhaji ya dubi Alhaji Karami, "Aminu a daura
da Bashir". Alhaji Karami yayi shiru, can ya ce "A
daura da Abba". Alhaji Babba ya ce, "Ina zuwa".
Ya fito daga dakin Abba na da inda suke yin
shawarar, ya ratsa mutane ya ce a yi masa
magana da Suwaiba. Umma ta fito daga kicin ta
same shi a dakinsa yana tsaye yana kai-kawo ta
ce lafia? Ya
Showing 27001 words to 30000 words out of 41322 words