dad'i"Tsaki Inna taja ta ce an zageta d'in ko kema bayansu d'in zaki shiga ko gobe saina zageta"Shiru mama Halima tayi Dan tasan Halin Inna ta rikice sai da lallab'o.



Aira kai tsaye gidansu ta nufa ta na kuka Mama kad'ai ta tarar a palour Mama ta ce "Lafiya Aira ya na ganki da akwati kina kuka kuma" Gidanmu na dawo ta fad'a tana kuka tare da shigewa Dakinsu na y'an matan gidan tana shiga ta saki akwatin Tare da Fad'awa Gado ta saki kuka mai ciwo............โœ๐Ÿฟ

*NI DA YAYA ARMAN book 2 itโ€™s not Free itโ€™s for sale if you wanโ€™t subscribe pay 200 only katin M t n hoton katin ko transfer #200 Naira to 07026166536 Vtu #300 Pc wanda basa bukatar a Sakasu grps suma #300 yโ€™an niger zaku iyamun magana ta wannan number +234-7026166536*

*Share fisabilillah*



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[6/7, 10:24] Hajo: ๐Ÿ *NI DA YAYA ARMAN* ๐Ÿ
Hot love storyโ™ฅ๏ธ๐Ÿ”

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

๐Ÿ“š *JARUMAI WRITERโ€™S ASSOCIATION* ๐Ÿ“š

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู†

*BOOK ONE*๐Ÿ“”
๐Ÿ…ฟ๏ธ...............27&28

....Sosai take kuka ta ma rasa Inda zata tsoma ranta taji sanyi yayyinta ba irin Lallashin da basu mata ba amma tak'iya saida ta gaji Dan kanta tukwana ranar ma da mugun zazzab'in ta kwana Wanda zazzab'in duk na tunanin Arman ne .



Washegari koda ta tashi bata lafiya sosai dak'yal ta samu tayi salla ta koma Ta lullub'e da bargo dukda zafin da ake Ba yanda su Ummy basuyi ba akan ta fito ko tea ne Tasha amma tak'iya har Ayshar mutuniyartata ba yanda batayi ba amma ta kiya.


Ganin sosai jikinta yayi zafi ya sanya su tsorata Amma ce ta je ta samu Mamy ta ce "Mamy Aira bata lafiya fa kixo kiga jikinta yayi zafi sosai" Cike da b'acin rai Mamy ta ce "me zanyi mata taje tayi ta ciwon ina ruwana" Ganin ran Mamy bace ya sanya Amma Zuwa ta fad'awa Mama Taje ta dubata taga har yanzu zafi jikinta.



Wajen Abba Mama Taje ta lallabashi akan ya fiddo mota akai Aira Asibiti Dak'yal ta lallabashi ya kira Family doctor d'insu ba ayi minti Talatin ba saiga Dr Bashir yazo tare da Abba suka shiga Mamy ta rakasu har d'akin da Aira take Haidar na gefenta Aysha na Jik'a ruwa tana shafa mata a ka dr yace meke damunta Amma tayi mai bayani dan har lokacin Aira ta kasa tashi kanta ji take kamar zai rabe gida biyu.



Kallon Dr Bashir Abba yayi ya ce "idan ka duba ta ka auni jininta Kayi mata har awon Ciki" Ciki kuma Alhaji "Mama ta fad'a cikin mamaki Duka saida sukayi mamakin maganar Abba Aira ko hawaye kawai take tasan shikenan yanzu Abba ya daina yarda dani ta fad'a cikin zuciyarta hawaye na zarya daga idanunta.




" Okay to Alhaji"Doctor ya fad'a Abba ko baiba Mama amsa ba ya fita cikin k'ank'anin lokaci Dr ya duba ta ya dauki jininta ya tafi dashi da niyyar zaije ya Auna Haidar ne yaje wajen Mamy ya ce .



"Mamy Dan Allah Kije ki duba Ya Aira wlh bata da Lafiya yanzu ma Dr yazo ya duba ta Hada Awon ciki wai Abba yace ayi mata"Cike da tashin hankali Mamy ta ce " Shi Abban naku ne ya kira Dr yace ya mata awon"Eh Mamy wlh y'anzu ma Dr ya d'auki jininta ya tafi kuma sai kuka take"Sosai ran Mamy ya b'aci fitowa Palour tayi.


Mama Halima ce da Hafsa tare da Inna dayake Chan suka kwana suka shigowa yi musu bankwana zasu wuce suna zaune suna Gaisawa da Abba Mamy ta shigo ranta matuk'ar b'ace ta nufi wajen Abba tare da kama k'ugu ta ce.



"Shine har da kiran Doctor kace yayiwa y'ata awon ciki inbanda tsabar wulakanci da tonon asiri wannan ai sharri ne ma kake shirin yiwa y'arka Shi doctor d'in da ka kira Me zai d'auketa kasan abunda zaije ya k'ara ya fad'a nan gaba to Ta Allah bata mutum ba insha Allahu y'ata bazata tab'a abun kunyar da ake so tayi ba Tunda uwarta banyi ba Itama bazata tab'ayi ba"



" Cikin fad'a Abba ya ce "Wlh Rahama zanyi mugun sab'a miki karkiga kina wani zafuce zafuce ina kyaleki ba tsoronki nake jiba Ina kyaleki ne darajar Y'ay'anki inba hakaba baki isa kizo ki dinga fad'amun maganganun banza ina kyaleki ba " Tsaki Mamy taja ta ce "Karka k'ara ragamun d'in daga yau " Mama Halima ce ta ce "Haba Rahama da hankalinki da komai ki dinga yiwa mijinki Haka Ku sanyawa zuciyarku ruwan sanyi kar k'aramar matsala ta zama babba mana Kaima yaya baka kyauta ba Akan me zaka kira doctor ayi mata awon wani ciki me ya had'a Aira da ciki "



dukanku kunfini sanin abunda nakeyi ne Dan haka kar Wanda ya k'ara mun magana akan Abunda zan aikata ko na Aikata "Inna ce cikin Masifa ta ce " Kede Rahama baki da mutunci wlh Ko baki girma mashi matsayin mijinki ba Ai kin Yi karar ina wajen Y'arki d'in banza zakizo kina fafatu akanta y'ar da wahalar ta ma bakisaniba Sai in k'irga so nawa kika tab'a wanke mata kashi harta girma ke inkina da kunya kin d'aga baki kiyi magana Akan Y'arki y'arma ta fari in banda lalacewar zamani hada cewa wani y'arki Inajinma kece kika zugota jiya ta zageni Ai tunda ga Kanmu aka daina haifo mutanen kwarai wlh"




"Inna ta k'arasa fad'a cikin Masifa "Mamy bata tanka mata ba sai zama da tayi ta na girgiza k'afa Masifa sosai Inna ta shiga surfa Masifa Inda ta shiga ba tanan take fita ba ana haka Doctor Ya shigo Samun wuri yayi ya zauna Dr yace " Alhaji mungama awon ba komai ke damunta ba Maleria ce sai tunani da ya fara mata yawa Awon cikin ma ba komai Duka Maleria ce ta sanyata ciwon sannan ya mik'awa Abba result d'in da leda ya ce "ga magungunan da za adinga bata kuma yanzu zanyi mata allura insha Allahu Zata samu sauk'i"




Tashi Mamy tayi ta ce "Alhamdulilla Abunda ake son dai baifaruba akan y'ata kuma sai a tari wani sarkin" ta fad'a tare da wucewarta d'akinta duk da Kallo suka bita Girgiza kai Mama Halima tayi a ranta ta ce "Lallai Yaya Inbanda Rahama wa ya isa ya fad'a mashi maganganun nan a kwana lfy" Dr ko tashi yayi yaje Dan yiwa Aira Allurar "Inna ce taja tsaki ta ce .



" Aikin banza Ai shiyasa Tun farko na hanaka Auran Yarinyar Chan kuka dage sai ita farin ne kawai ya d'ebeku amma ni daman Nasan ba mutuncin kirki zatayi ba yanzu wa gari ya waya shidai Kabir Allah ya taimakeshi kaikuma da ka jajib'o saikaji dashi Dukta salamceka ta asirceka inaga tsoronta kakeji ma ko to ni ba kai bane ni bata salamceni ba Ai naso wlh ta Tankamun yau da taga yanda tsaffi ke Rashin mutunci Yau da saitabar gidannan dukda d'anyen jegon tunda ba gidan ubanta bane wai nan gani take ta haifi maza biyu zatawa mutane iskanci to ko Nigeria ta haife ni sai in koreta tunda bata da mutunci".



Shidai Abba baice komai ba Dan yasan Inna sarai inta rikice hakan yasa ya dinga lallab'ata Nan Dr ya fito yayiwa Abba sallama Mama Halima ce ta shiga d'akin da Aira ke ciki lokacin Ta tashi tana rama Sallar da batai ba "Koda ta gama sosai Mama Halima ta shiga yi mata nasiha cikin nutsuwa Akan ta yiwa iyayenta biyayya ta daina abunda basaso " Insha Allahu Mama bazan sakeba "yawwa Mamana Allah miki albarka idan iyayenki sun huce kije ki basu hakuri kinsan yanzu cikin fushi suke " tana hawaye tace



"Insha Allahu Mama zan basu hakuri" Mama ta ce "To mudai zamu wuce ai zakizomun Hutu ko tunda kun gama karatu bare kice makaranta Dan nasan halinki sarai bakison zuwa kinamun hutu" Insha Allah Mama indai Abba ya yarda zanzo".


Ranar su Mama Halima da Hafsa suka juya Aira ji take kamar ta bisu Dan gidan baya mata dadi .


Aira ita ciwon biyu yayi mata ga na Rashin jin muryar Arman kwana biyu Dan wayarta tayi mata mugun b'oye daga babbar har k'aramar.


Cikin kwana biyu Aira taji sauk'i ta warware sosai yanzu sai damuwar fushi da Iyayenta keyi da ita Dan Mamy ko magana bata mata sosai Abun yake damunta Yau tana zaune a dakinsu ganin ba kowa ya sanyata saurin d'auko wayarta Karama ta kunna ta maza ta shige toilet Dan karma wani ya shigo ta dannawa Arman Kira Saida ta gama ringing tukwana ya kira.



Muryarta cike da damuwa kamar zatayi kuka ta ce "Yaya ina ka shige kwana biyu" Bangaren ARMAN Ajiyar zuciya ya sauke Dan tun ranar da ya koma Abuja Yake cikin damuwa yasan tunda Daddy yayi wannan fushin to yasan Abban Aira ne yayi mashi Rashin mutunci yasan ba k'aramun Duka Tasha ba tsoronshi d'aya Kada Ta tsorata ta rabu dashi hakan yasa duk ya shiga damuwa gashi yayi ta Kiran layin Ta kashe



"Aira kina Lafiya ya fad'a cikin sanyi" Kamar zatayi kuka ta ce "Lfyqlau yaya sai kewarka da tamun yawa" Nima Ina nan kewarki ta addabeni My Aira Please kuyimun Alk'awarin duk wuya duk rintsi bazaki rabu dani ba idan kika rabu dani zan shiga mawuyacin hali please my Cutie"Kuka Aira ta fashe dashi cikin kuka ta ce



"Yaya bazan tab'a rabuwa dakai ba Abunda ban tab'a kawowa a kwalwata ba Dan Allah kar Daddy yasa ka rabu dani nasan Shima yanzu bayason alak'armu tunda suka sake rigima da Abba" Karki damu my cutie Daddy bazai iya rabamu ba "Bai tambayeta Abunda ya faru ba Dan bayason k'arin b'acin rai sun tab'a Hira sosai Aira duk sai taji Kashi tamanin na damuwarta ya tafi



haka Shima bangaren Arman din ta kasance Arman yace kina jina My cutie" yace Eh Yaya"Daga yanzu karki k'ara nuna muna tare karki sake wani ya lura da muna tare Ko garin nazo Bazan k'ara yarda nayi sakacin da har zai zame maki matsala banason yawan dukanki da ake Zamuyi Abotarmu cikin sirri kinji"Kamar yana gabanta ta gyad'a mai kai tace "to yaya " sannan kicewa su Abba da mamy kin rabu dani ko sun tambayeki kinji"To yaya tafada Sun Kara tab'a Hira Kad'an tukwana sukayi bankwana cike da Shauk'in k'aunar juna.


Bayan kwana biyu Aira taje ta samu Abba a lambu ta dinga bashi hakuri tana kuka tun bai kulata ba haryazo yace ya hakura amma da sharad'i saita rabu da Mujahid Goge hawayenta tayi ta ce "Abba insha Allahu mun rabu bazan k'ara mu'amula dashi ba " Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "da ko kikayi hakan da kin taimaki kanki kuma kin nemu hanyar da zamu samu Masalaha a tsakaninmu Allah yayi miki albarka" Cike da farinciki Aira ta ce "Ameen Abba nagode".




Daga nan d'akin Mamy ta nufa ta isketa tana Bawa Amer madara durkusawa tayi ta bata hakuri tayi banza ta kyaleta " Kuka ta fashe dashi tare da rik'e k'asar zanin Mamy ta ce "Dan girman Allah Mamy kiyi hakuri ki yafemun bazan sakeba Mamy na tuba"Shiru Mamy tayi saikuma ta ce "




"Haba Aira tuban ki wannene bansaniba sau nawa zakiyi Abu kice bazaki sakeba karshe kizo kiyi Wanda ya linka na baya ai yanzu ni kinfi k'arfina kuma ba ruwana dake"Mamy wlh yanzu na tuba Allah nadaina bazan sakeba Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce "Tashi muyi magana indai da gaske kike bar kukan" cikin Sauri Aira ta tashi ta zauna gefen Mamy Kallonta tayi in serious talking ta ce "kin yarda kin rabu da Arman d'in koko?cikin Sauri tace.............โœ๐Ÿฟ

*Share fisabillah*

*_Miss Hajo ce_*๐Ÿค™๐Ÿฟ
[6/8, 22:32] Hajo: ๐Ÿ *NI DA YAYA ARMAN* ๐Ÿ
Hot love storyโ™ฅ๏ธ๐Ÿ”

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

๐Ÿ“š *JARUMAI WRITERโ€™S ASSOCIATION* ๐Ÿ“š

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู†

*BOOK ONE*๐Ÿ“”
๐Ÿ…ฟ๏ธ...............29&30


" Mamy na rabu dashi Shima kuma nasan Daddynshi ya rabashi dani tunda bakusan mu amulata dashi"Yawwa ko kefa Aira ki taimakamun ki fiddani kunya ki rabu dashi sannan ki daina abunda zaidinga jamun Zagi kinji"Gyada kai tayi tace "Insha Allahu Mamy Na daina" Allah sa da gaske kike na yafe maki duniya da Lahira Allah maki Albarka "



"Sosai Aira taji sanyi a ranta tace " Ameen Mamy nagode sosai"sosai Mamy ta saki jiki da Aira ta dinga janta cikin dabara ta Tambayeta ta ce " ranar da kuka tafi ina kikaje kuka kwana badai abunda yayi maki ko idan da Abunda ya faru fad'amun wlh ba maiji kuma bazan dake kiba kinji na rantse "




Nan Aira ta bawa Mamy Labarin komai Da ya faru daga karshe ta ce " Allah Mamy Gaskiya na fad'a maki ba abunda yamun ni yaya baitab'amun maganar banza ba kawai zargine kuke amma shi ba haka yake ba"wata nauyayyar Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta tabbata Aira idan ta fad'i magana haka take Dan bata karya




Sai sannan taji sanyi a ranta ta cire zargin dake ranta daman duk wannan Abun da tayiwa Abba itama akwai zargin a ranta kawai Dai abunka ga d'a da uwa ne "to yanzu shikenan komai ya wuce na yarda ki kiyaye nan gaba Dan Allah" to Mamy "sannan tace " Mamy banishi na rik'e maki ta fad'a tana mik'a hannu ta amshi Ameer tare da pidarshi ta sab'eshi a kafad'a ta fito palour Sai murna take yanzu Hankalinta kwance ta sasinta da Iyayenta.



Haka rayuwa taci gaba Aira na shan wayarta da Arman a b'oye babu Wanda ya fahimta Kullum idan Sadiq ya kira Aysha idan ta bata wayar kin amsa take ba yanda Aysha batayi da itaba amma saita k'iya tun yana kira har ya hakura ya daina kira Wanda hakan sosai yayiwa Aira dad'i.


Amma ta koma bangaren Inna kullum Inna da kewar Aira take kwana take yini Dan tayi mugun Shak'uwa da ita gashi taga Airar tayi zuciya ko bangarenta bata k'ara shigowa dak'yal a daddafe Inna ta daure tayi sati biyu ba Aira sosai kewarta ta dameta gashi Shima Arman bai sake zuwaba duk Abu ya dameta.



Yau Aira y'an gidan su duk suna zaune a palour ana hira da misalin Tara na dare har Abba da su Mamy Amer na Bayan Aysha ta goyashi Inna ta shigo Aira na ganin shigowarta ta kauda kai Wajenta Inna ta nufa ta ce "Haba y'ar lelena daman zaki iya fushi dani Duka ina duniyar take bare mu dake cikinta biko nazo ki taho mu koma gidan duk bayamun dad'i da kika tafi" Turo baki Aira tana zunbura Baki ta ce



"Keda kika koreni ni ba Inda zani kije Chan takwarartaki ta dinga tayaki kwanan ni bazan koma ba"Inna ta Goge hawaye ta ce " Haba Hajara Dan Kinga ina sonki shiyasa kikemun wulakanci to wai ba na baki hakuri ba ki taho mu tafi "ba Inda zani ni ki tafi " Sudai su Mama suna gefe suna Dariya kasa kasa Dan Inna da Aira sai Allah haka zasuyi fad'an kuma inna tadawo tana bata hakuri"cike da Masifa Inna ta juya ta kalli su Mamy ta ce




"ku yanzu cikinku ba mai bata hakuri Kunajina kukayi banza dani Dan kun rainani ke Rahama ba y'arki bace Baki isa kice tayi hakuri kodan daman Nasan ai ke kike zugata shiyasa yanzu ta gujeni kiwon d'an makwarwa ne nayi " tafada tana Goge hawaye "Cikin ladabi Mamy ta ce " kiyi hakuri Inna ni wlh banzugata ba Dan kar nayi magana kuma kice ina ruwana shiyasa amma kiyi hakuri sannan ta harari Aira ta ce "Tashi ku tafi" Turo baki Aira tayi ta ce "Mamy itafa da kanta ta koreni har cewa tayi karna k'ara zuwan mata" Inna tace



"Kai Hajara banda sharri a ina na koreki " Abba ne ya ce "Mamana tashi ku tafi banson doguwar magana" Tashi Aira tayi ta ce "To Abba a ranta sosai taji dad'i Dan daman kamar a k'aya take bata samun damar shan waya da Arman Yanzo ko gidan Inna ko kwana zatayi tana waya dashi ba mai sani d'akinta ita kad'aice kawai ta gwada batasone Dan inna tasan Taji Haushi Akwatinta ta d'auko wayoyinta daman suna ciki ta fito ta harari Inna ta ce .



" To muje kuma wlh kika k'ara korata ko kika zagi Mamy na taho har abada bazan koma ba"To y'ar lelena Inani ina Kara korarki ni daman Chan ban zagar maki uwa ba Rahama ai y'ar kirkice bakiji sunan ba Rahama duk Inda kikaji an ambaci Rahama ai andace bakiga ba ko mutum mutuwa yayi ba Rahama ake nema mashi "Dariya Aira tayi sosai hada rik'e cike tace " To shikenan My Inna muje suma su Abba Dariya sukayi sosai Har Mamy wai yau itace Inna ke yabo .


Su Aira na fita Mamy ta tashi ta cewa Mama"Yaya saida safe "To Auntynsu Allah tasheni lafiya Mama ta fad'a " Mamy ta kalli Aysha da murmushi fuskarta ta ce "Yau ko tayin bacci zai miki" Dariya Aysha tayi ta ce "Mamy muje saina kwantar dashi Dan karya tashi suna zuwa d'akin Aysha kwantar da Amer Sannan ta kalli Mamy ta na Sosa kai ta ce " Uhm Mamy Dan Allah wani taimako zakiyimun"Mamy tace "inajinki Aysha fad'a kai tsaye insha Allahu indai zan iya zan maki shi"



Cike da kunya Aysha ta bawa Mamy labarin Saurayinta Abdulkharim da hadu Airport daga karshe ta ce "Shine yanzu yace yanason yazo ya gaishe da Abba shine nake tsoron yiwa Abba magana Dan Allah Mamy ko zaki fad'a masa nasan ke zai fahimce ki " Murmushi d'auke da fuskar Mamy ta ce "Ah masha Allah kice munkusa shan biki amma gsky Naji dadi karki damu Insha Allahu zanyi mashi magana ba matsala" Godiya sosai Aysha tayiwa Mamy Dan tasan daman itace zata fad'awa Abba direct yayi na'am.



Mamy Bayan ta fito daga wanka jikinta daure ta towel ta dauki amer tana cikin sauyamai kaya Abba ya shigo kauda kai tayi kamar batasan yashigo ba Dan tun sanda sukayi rigima ta ke fushi dashi cikin kwantar da murya Abba ya ce "Haba sarauniyar mata Farar mace alkyabbar mata wai har yanzu baki huce ba Fushin nan ya isa Haka kinsan bazan jureba Airar ma data had'amu na yafe mata".




" hmmm kawai mamy tace taci gaba da abunda Take Abba ya ce "To wai ba nace kiyi hakuri ba Haba my
Showing 24001 words to 27000 words out of 33558 words