kuma" Murmushi tayi ta ce "Mama Aunty Aysha zan raka Unguwa" Mama tace "Tofa daga dawowa bako hutawa k'afar yawo" Mama ganin gari ne fa kawai zanyi"ta fad'a ta na ruko Aira ta gyara mata yafa Belt din nata ta ce "Yau akwai kashe hotuna sis ta fad'a suna Tafawa" Mamy ce ta ce "Aifa K'auna ta dawo Aysha da Aira tsohuwar zuma" Dariya Aysha tayi ta ce "Fad'i da k'ari Mamy Aini duk ita kadai nafi missing" .



Mama ko ta ce "Ai Halin ne yazo d'aya shiyasa " dariya Mamy ta ce "Kuma Hakane yaya Halin Aira da Aysha duka d'ayane ba abunda Aira ta rago na Aysha Dariya Aysha da Aira sukayi.



suna haka Abba ya shigo palourn Bayan ya zauna har k'asa ta duk'ursa ta gaishe da Abba ya amsa sai farinciki yake ya ce " An kammala karatu ko Aisha Allah ya miki albarka Allah baki abunda kike nema duniya da lahira yanda kika farantamun Allah baki masu farantamun miki nagode da yanda kikayi mun biyayya akan komai baki bani matsala ba karatun da na turashi shi kikayi ba tare da kin bak'antamun ko an tab'a kawomun koken ki ba Ko ki biyewa samari dukda dai ba yawo nake dake ba Naji dadi sosai Allah maki albarka"



"Ameeen Aisha ta amsa sosai tayi farinciki da Addu'ar mahaifin nata sannan ya ce " Kamar yadda Yayyunki Maryam da umar Bayan kammala Degree d'insu na kaisu Aikin Hajji da umrah insha Allahu kema ki shirya zaki Fara zuwa umrah kafin lokacin aikin Hajji yayi Allah maki albarka sosai Aysha tayi farinciki marar musaltuwa ta ce "Abba nagode nagode Allah saka da alkhairi Allah ya k'ara budi" Aira ko tana tsaye duk tayi sanyi tasan Abba da ita ya ke na cewa "aysha bata bashi matsala ba Dan haka yakece ma Aira idan yana mata fada yace " ita ce Ke neman bashi matsala cikin y'ay'anshi .



Amma hakan bai hanata taya y'ar uwarta ta farinciki ba jita ke Daman Ita "Saida Abba ya gama sanyawa Aysha albarka tukwana ya tashi zai shige ciki A hankali Aira ta ce " Ina yini Abba"ba tare da ya Kalleta ba yace "Lafiya" Dan tun sanda yaganta motar Arman Bayan dukan da yayi mata amma ta raina shi bata daddara ba yanzu ya tsaya yana tarasu ita da shi ya ga gudun ruwansu.



.sosai Aira bataji dad'in yanda Abba ya amsa mata ba saida ta Goge hawaye Aysha ma saida tayi mamaki Dan tasan yanda Abba keson Aira dukda Abba bai gwada banbanci tsakanin y'ay'anshi Amma a yanda tasani yafi nunawa Aira so saisuka Alak'anta hakan Da sunan mamansu ne da take dashi "Saida suka fito Aysha ta ce " sis ya naga Abba bai kulaki ba "Wlh nima bansaniba Aunty " .



tafada tana Goge hawayenta "makullin key Aysha ta amsa hannun driver ta tuk'a su suka tafi Aira na front seat gidan kawar Aysha suka fara zuwa basu jima ba Suka fito tukwana Suka wuce Wurin wani shak'atawa sosai Aysha tayi ta kashe musu selfie da wayarta iPhone 12 pro ita da Aira sosai suke kyau kamar wasu twins saidai kowa ya gansu yasan Aysha ta girmi Aira a shekaru Bayan nan su shiga wajen shan ice cream suna cikin sha wayar Aysha tayi ringing.



ta d'auka ita dai Aira bataji me Dayan bangaren aka ceba saiji tayi Aysha ta ce " Okay Baby ka shigo zaka ganmu da marun Abaya"bata katse wayarba suka hangoshi yana nufo su aysha murmushi ya kasa barin fuskarta harya karaso ya zauna chair din kusa da ita.




"Aira dai na kallonsu kawai take Shima ba laifin yana da kyau gashi Daga gani kamar akwai Naira Aysha cikin farinciki tace" Nayi missing naka my baby Tunfa sanda ka kawomun ziyara rabon da muga juna kusan 5months ta fad'a tana shagwaba "Shima cikin so da k'auna ya Ce " Miss you too my prince's kinsan yau ba cikin k'aramun farinciki nake ba na ganinki sannan ya kalli Aira da take kallonsu ya ce .




"Dear ko ita ce k'anwar tamu da ake ji da ita " Aysha tace "Eh baby itace " Aira ko "yafada yana kallon Aira murmushi tayi ta ce " Eh ina yini "Lafiya qalau kanwarmu y school gsky yayarki Naji dake fa kusan kullum saitayimun maganarki" murmushi Aira tayi ta ce "Ai nima ina ji da ita sosai " Aira najin Aysha da Saurayinta na zuba love ita dai cikin ranta mamaki take daga karshema barin wajen sukayi suka koma Dan nesa da ita tana nan zaune rik'e da wayar Aysha taji wani yayi mata sallama ba tare da ta d'ago ba ta amsa .


"zan iya zama Hajiya" Ba matsala ta fad'a ta na kauda kai"y'an mata bazaki kalleni ba "yafada yana murmushi kamar bazata d'ago ba sai kuma ta d'ago ta ganshi wani dogo mai matsakaicin jiki ya sha shaddarshi me kyau.




kauda kai tayi yana b'ata rai Dan bata son takura " ina yini Hajiya Sannu da hutawa"Lafiya "ta fad'a ta na kauda kai" Kamar bazai magana ba saikuma ya ce "Tun d'azu na hangoki ina son nayi maki magana kikamun kwarjini na kasa Sai yanzu dak'yal nayi shahada na taho Dan na fad'a maki abunda ke cikin zuciyata Gaskiya tunda nake bantab'a ganin macen da ta burgeni ba sama dake nayi yawo wurare da dama Amma bantab'a cin karo da macen da sace zuciyata kai tsaye ba idan ba ke ba fatan baza a watsamun ruwa a k'asa ba za a amshi tayi na hannu bibbiyu" .





Aira ji tayi kamar ta shakeshi Dan Haushi tace "d'an naci a zuciyarta amma a fili cewa ta yi" Kayi hakuri ni bana soyayya a gida an hanani"Saiki fara a kaina na tabbatar zan sanyaki farinciki "tsaki taja cikin ranta ta ce " maye "Nan yayi ta mata magana da magiya tayi banza ta Kyaleshi Suna Haka Aysha ta dawo ita kad'ai ga Alamun saurayin nata ya tafi Tana ganinta Aira ta mik'e ta ce " Aunty Aysha mu tafii".



Kallon Aysha saurayin yayi ya ce "Auntynmu ina yini" murmushi Aysha tayi ta ce "lafiya qlau brk da hutawa" yawwa Aunty gwarama da Allah ya kawomun ke nasan zaki taimakamun ki shawomun kanta tun d'azu nake nan amma ank'i bani dama gimbiyar tawa dai ga alama akwai mulki "Dariya Aysha tayi ta ce " karka damu Insha Allahu zanmata magana haka take "kai amma nagode Wlh Aunty kinyi taimako amma ya sunan gimbiyar tawa" Hajara Amma ana ce mata Aira"wow so sweet name "nikuma suna na ABUBAKAR YUSUF MADUGU”ni D’an sokoto ne nazo bikin aboki na ne ni bakone a garin nan.




Ah Babban suna sunan Abbanmu"cewar Aysha " kice ina da manyan y'ay'a to yanzu Aunty yaza ayi naga kamar Sauri kuke zaku wuce ko zaki taimakamun da number ta"wlh bata da waya yanzu kam"to Dan Allah kozaki taimakamun da taki saimuyi magana"ba matsala Aysha ta fad'a tare da karantomai number ta.




rafar y'an 500 ya Aje musu Aysha taki amsa dak'yal ya samu ta amsa tare da mashi Godiya ya wuce "Aira ko duk Haushi ya isheta saitajima mutumin duk ya bata Haushi ga haushin Aunty Aysha da ta biye mai.



A mota Aira ta kalli Aysha ta ce " Aunty wannan Wanda yazo wajenki d'azu waye"baby Abdulkarim kenan Boy friend d'ina ne kuma mijina insha Allah tafada tana murmushi wara idanu Aira tayi cike da mamaki ta ce "To Aunty yaushe har kuka hadu keda kika tafi karatu kuma nasan kafin ki tafi Abba baya barin kowa zance " Dariya Aysha tayi ta ce "Aira kenan kede kawai ayi sha ani amma ni tun ina s. S three nake soyayya ta a b'oye kawai dai ina nunawa Abba ne amma soyayya ta nake ke yanzu fa kai ya waye akanme ace Y'an mata gand'ama gand'ama damu ace ba samari yaushe garin zai waye my Abdul a Airport muka had'u dashi tun lokacin tafiyata karatu ta farko tun daga lokacin muke soyayya ina sonshi sosai Shima haka yana ziyarta ta chan akai akai munshaku sosai Dan tun bayanzu ba yakeson muyi aure na ce yayi hakuri ya jira lokacin da Na gama karatu gashi yanzu kuma alhmdllh yanzunma maganar ce mukayi nace ya samu Abba yanzu ba wannan maganar ba Wannan Sadiq din yana da hankali wlh sosai ga nutsuwa ki nutsu Kuyi soyayyarku saina dinga had'aku kinji kanwata baki da matsala dani ba meji".




Turo baki Aira tayi ta ce "Ni Gaskiya Aunty kibar zancenshi ni baimun ba bama wannan ba kinsan Abba ya hanamu nikuma bazanyi Abunda ya hanaba Gaskiya gwara Na hakura nayi karatuna kawai yanda yakeso din"galala Aysha tayi tana kallonta tana tuki ta ce "Amma wlh Aira baki da wayo to maza kiyi sakakka irin na Aunty Maryam ta biye Dokar Abba harta gama Karatu bata da saurayi Abba ya had'ata da d'an Abokinshi dukda ba wani sonshi sosai take ba ta hakura danma yanzu suna son juna Amma ai Kinga batayi mata dad'i ba b'ata auri Wanda takeso ba To wlh kika biye kema haka zakuyi nidai ba ruwana tunda na kama My Abdul Dina" .



Tab'e baki Aira tayi ta ce "Uhm Aunty yaya Arman fa Yama hanani kula samari fa kuma nayi mashi alkawari bazan kula kowa ba " galala aysha tayi ta na kallonta ta ce "Ke amma sakaraice ma Hajara har wani Arman ne zai hanaki kula samari to idan baki kula samari ba ubanwa zai Aure ki ko Shi Arman d'inne zai Aureki iyeeeeee kujimun ikon Allah " Aira daram Gabanta yayi irin mummunan fad'uwa jin Kalmar Aunty Aysha ta k'arshe "Ko shi Arman d'inne zai Aure ki?????!!!!!..............✍🏿



*Ni da Yaya Arman Book1 ne Free Book2 Ba free book ba ne Na kud’ine Book one zai k’are ne daga Page 30 daga nan za mu shiga Book two kai tsaye Ba tare da Gargada ba zaku iya fara biya tun kafin a k’are Book one zaku turo katin MTN #200 ta wannan number 07026166536 tare da shaidar biyanku ta 07026166536 y’an niger kuma ku bini pc ta number nan dana d’ora +2347026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain a ciki*

_Normal group = #200_

_PC = # 300_

_V t u # 300_

*Sainajiku masoyan asali na tabbata bazaku tab’a nadamar sayan littafin nan ba darajarshi tafi ta #200 kachal na barshi ne hakan kawai saboda kauna da soyayya ga masu buk’atar a tallata musu hajarsu su tuntub’eni kai tsaye a number wayata kamar haka 07026166536 zamuyi ciniki cikin sauk’i insha Allahu sainajiku Masoyan asali na tabbata bazakuso ayi zazzafar doguwar tafiyar nan babu ku ba*👯‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/2, 09:31] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............21&22

Sosai gabanta ya fad'i sai yanzu ma ta tuna da Dan ayi Aure ake soyayya Shiru tayi ta na ta sak'e sak'en a ranta Tanajin Aysha nayi mata fad'a tayi mata banza ta kyaleta Har suka isa gida Suna isa Aira kai tsaye Part din Inna ta nufa Dan lokacin har Angama kiran magriba.


"Bayan tayi salla a palourn zaune tayi tana lazumi kafin ta tashi innace ta shigo ta na fad'a tana cewa " Haba nidai wlh ana wahalshe dani ace Dan kinibibi Kamar Rahama god'ai god'ai da ita Bata iya wankan jariri ba koma ta iya Dan iskanci batayiwa d'anta wanka ba saini to zanga Ranar da babuni ubanda zai dinga musu ai duk gani na ne ya kawo hakan malalata kawai tun daga zamaninmu aka dena haifo mutanen kwarai Wai kamar Rahama da in Auren k'auye ake y'arta ma saita Aurar da Y'a Amma tsabar iskanci sai an wahalshe dani ".




Aira na jinta tayi mata banza Dan ba kowani fad'an inna take tankawa ba " Tsaki Inna taja ta kalli Aira Dan ta tsani tana fad'a a mata banza in ba a bata hakuri ba gwara ko tankawa kayi ta ce "Ke kuma y'ar gidan malalaciya Daga gidan ubanwa Kike Rabonki da nan tun azahar ina kikaje " Tsaki Aira taja tare da tashi tayi bedroom d'inta ta na jin Inna na cewa "Uwarki da ubanki kikayiwa tsaki ba niba fitsararriya mai ido a tsakar ka " Murmushi kawai tayi dan yau ba y'an fad'an take ba shiyasa bazata biyewa inna ba ta na shiga d'akin ta kulle Dan yau batajin ko dinner zata iyayi sbd ciye ciyen da sukayi a waje.




Ta na zuwa Sauri tayi ta cire kaya ta fad'a toilet ta yi wanka tana fitowa tasa kayan bacci ana kiran isha I nan ta tada salla saida ta gama ta tashi ta ninke hijab ta d'auko k'aramar wayarta da babba ta baje kan Gado wara idanu tayi ganin missed call d'in Arman rututu a k'aramar wayarta cikin Sauri ta Danna mashi kira saida ta katse tukwana ya kira cikin Sauri ta d'aga ta ce "Hello my Yaya ina yini" Ajiyar zuciya taji ya sauke daga bangarenshi ya ce "Nayi ta kira Baki d'auka ba ina kika shige" Sorry yaya wlh Aunty Aysha ce tazo shine na rakata unguwa"Yaushe tazo?Dazu "da ina da ina kikaje" gidan kawarta muka fara zuwa daga Chan muka wuce wajajen shakatawa amma waje biyu kawai mukaje muka dawo"Ita Aysharce daga dawowarta zata d'aukanmunke ku tafi yawo me yasa da zaku tafi baki fad'amun ba kafin nan ma wasu kaya kika fita da su?





"sorry yaya na manta ban fad'a maka ba Bansa matsatsun kaya ba wlh doguwar Riga ce a ma baje take Aunty Aysha ta sayo mana Nida ita idan kana soma saina turo maka hoton ka gani"ba sai kituroman ba na yarda Amma fad'amun Gaskiya akwai saurayin da yace ya na sonki?gabanta ne ya fad'i sai sannan ta tuna da Sadiq



cikin y'ar in ina ta ce "ya ya ba kowa" Aira kenan a tunaninki Idan kikayimun k'arya bazan gane ba baki saba karya ba Dan haka duk sanda kikayi ganewa nake oya fad'amun Gaskiya"Kamar zatayi kuka ta ce "To yaya bazakayi fad'a ba " Eh bazanyi ba gsky kawai nakeson ki fad'amun"




Ajiyar zuciya ta sauke nan ta bashi labarin had'uwarsu da maganarsu da Aunty Aysha bata b'oye mashi komai ba "Sosai ranshi yayi mugun b'aci cikin fad'a da masifa ya ce " Ita Aysharce daga zuwanta har zata fara koya miki biye-Biyen Samari,"


"yaya Dan Allah kayi hakuri "Tafada kamar zatayi kuka " Cutie bakiyimun komai ba Amma Aysha tayi mugun bani mamaki Yazama dole gobe na shigo garin na kad'e mata warning Sannan duk sanda ya kirata ta baki ko kika bashi number ki kukayi mu'amula ko soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba kinsan dai Mahimmancin Allah ya isa sarai(😆😂oh ni Arman hada Allah ya isa sai kace ubanta).



Sosai Aira tayi mamakin kalaman Arman wai Allah ya isa Amma dayake tasan idan ranshi ya b'aci saida lallab'o tafi kowa iya zama dashi shiyasa ta ce "To Yaya Bazanyiba Goben da gaske zaka zo" ta fad'a ta na son sauya maganar "Eh cutie zanzo Amma kwana biyu zanyi na juya" Cikin murna Aira ta ce "Amma Naji dad'i my yaya Allah ya kawomun kai lafiya" Ameeen my Cutie ya fad'a tare da cewa Good night kiyi bacci yanzu nasan kingaji"murmushi tayi mai cike da so da k'auna ta ce "Have a nice dream yaya saida Safe".



Tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita washegari Suna Yaro yaci suna Abdullahi za ana cemai Ameer sosai gidan ya cika ranar da mutanen Arziki Kanwar Abbansu Aira ma dake Aure a Kaduna Mama Halima tazo tare da y'arta Hafsat sa'ar Aira ce kuma kawarta ce sosai Ranar Aira jinta take cikin Farinciki duk inda tayi Hafsat na biye da Ita Da misalin k'arfe biyar na yamma sosai Aira tayi kyau cikin Wani tsadaddan lace black and blue sai ratsin pink sosai ya amshi farar fatarta batayi wata make up kamar koda yaushe hoda da kwalli kawai ta shafa




Sosai tayi kyau kamar ka saceta ka Ruga a lokacin ta na bedroom d'inta dake d'akin inna Bayan ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turarruka masu k'amshi drawer gefen gadon ta ta bud'e cike yake choculate kala kala kamar kaje Kanti duk Wanda yaya Arman yake saya mata ne manya biyu kawai ta d'auko ta fara sha Dan yunwa takeji sosai tunda safe rabonta da abinci Dan ita daman haka take batacin abincin sabga




Nan Tasha hotunan ta sosai tana gamawa tayi status a what's app tana ganin amfara comment akan hoton ta maza ta kashe datar ta sauka wayarta ce k'arama tayi ringing ganin Yaya Arman ne ya sanyata picking cikin Sauri ta ce "Yaya Badai har kazo ba " Daga bangarenshi ya ce "Yanzu haka ina bakin gate d'in gidan Inna " Tsalle ta daka ta safko daga Gado ta ce "Wow Sannu da zuwa yaya ka shigo mana" bazan shigo ba cutie Naga akwai mutane a wajen kinfi kowa sanin ban fiya son taron mutane ba Kidai fito Kawai "



"to yaya ga ni nan "ta fad'a ta na saurin Saukowa daga gadon cikin Sauri ta boye babbar wayarta a locker ta rik'e k'aramar takalmi da gyale ta zira tayi Sauri ta fito a palour ta tarar da mutane gaishesu tayi ta fita A farfajiyar gidan ta gamu da Hafsat Hafsat ta ce " Aira ina zuwa naga kina shirin fita"Taho ki rakani wajen YAya Arman zani"



Dariya hafsa tayi ta ce "Ah koda nace wannan show d'in kice love za a sha wannan k'auna keda Yaya Arman har yanzu akwaita kenan" Murmushi Aira tayi tanajin dadi har cikin ranta ta kama hannun Hafsa ta ce "Ai kauna ta na nan Hafsa *NI DA YAYA ARMAN* Mutu ka raba Dariya Hafsa tayi ta ce "



Allah yarda ni daman najima da sanin soyayya kuke wlh"wara idanu Aira tayi ta ce "Rufamun Asiri waya fad'a maki soyayya muke kawai dai k'auna ce muke " Uhm idan tayi tsami dai maji cewar Hafsa suna fita suka tarar dashi a cikin mota back seat driver na gaba Zage glass din motar yayi ya tsaya kallonta sosai ta tafi dashi ba k'aramun masifar kyau
Showing 15001 words to 18000 words out of 33558 words