tayi mashi ba baisan lokacin da ya sakar mata murmushi ba Itama mayar mashi tayi Dan sosai yayi mata kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi da Tasha aiki fara Hafsa ce ta ce
"Ina yini Yaya" Lafiya qlau Hafsa yau a gari"murmushi tayi ta ce "Wlhko Yaya Suna mukazo tare ma muke da Mama " Aira ce ta shagwabe ta ce "Yaya bazaka fito ba wai ka hakimce a cikin mota" Dan murmushi yayi ya ce "So kike na fito a gama kalle maki ni wannan wankan nakine ke kad'ai" Dariya tayi ta ce "Wayau dai kawai cikin shagwaba ta ce " ni fa yunwa nakeji ba abunda naci tun dazu"wara idanu yayi ya ce "Subhanallahi garinya aka barmunke da yuwa" Yaya ban iyacin abincin Taro shiyasa"ai zama bai ganmu ba maza-maza shigo muje restaurant yanzunnan"
ya fad'a yana bud'e mata Kofar da yake ciki Kallon Hafsa tayi ta ce "Sis taho muje" Girgiza kai Hafsa tayi ta ce "A a kije kawai Sis Mama ta ce Zan rakata gidan Daddy su gaisa Dan muna sa ran gobe zamu koma " To shknan saimun dawo Aira ta fad'a tana shigewa batare da shakkar komai ba Restaurant mafi kusa ya kaita saida ta tabbatar da ta koshi tukwana suka fito Suna shiga mota Yaji kiran daddy yana d'agawa nan Daddy ke shaidamai akwai Wani metting da za ayi karfe Tara a Zaria kome yake ya maza ya tafi Zaria yanzu yaje ya wakilceshi da to Arman ya amsa mashi Kallon Aira yayi da take latsa Wayarshi ya ce.
"Cutie
zamuje mu saukeki a gida yanzu Tafiya ta kamani zanje zaria zan wakilci Daddy wani metting " Yaya Dan Allah ka tafi dani Daman bantab'a zuwa Zaria ba Saidai mu wuce ta cikinta in zamu wuce Dan Allah kaje dani"tafada ta na marairaicewa "Rik'e hannunta tayi ya ce " Kiyi Hakuri my cutie Amma bazaiyu na tafi dake Zaria da Daren nan ba Kuma idan munje dinma bamusan tsawon lokacin da za a d'auka ba kiyi hakuri next time idan nazo zan daukeki da kaina na kaiki kiga ko ina da rana "
"nidai Allah yaya ban yarda ba katafi dani kawai " Dafe kanshi yayi ya ce "Aira case Ce " to so kike na tafi dake na ja maki fad'a a gida Kin manta dare ne Zaiyi"Yaya wlh har muje mu dawo ba maiji ni daman b'angaren Inna nake kuma bamai sanin ma Inda naje"Ba yanda Arman baiyi ba Dan kar ya tafi da ita amma ta nace daga karshe ma kuka tasa mai hakan yasa ba yanda ya iya dole suka tafi tare tana ganin an tafi ta sauke ajiyar zuciya sai murna take daman ita tanason tafiyar mota a rayuwarta
karfe takwas da wani Abu tayi musu a Zaria Rasa Inda ma zaikaita yayi hakan yasa ya yanke shawarar kaita gidansu Wani abokinshi kafin su gama metting d'in Abokin nashi ma bai gari mamanshi ta amshesu hannu bibbiyu Daga nan Arman ya wuce wajen metting d'inshi Hankali kwance nan Aira taci abinci sai nan nan y'an gidan suke da ita Dan Arman ya ce Musu kanwar sa ce Aira ganin Har 10Arman baizoba tana ta jiranshi Har bacci yayi awon gaba da ita.
Arman ko metting d'in saida ya jasu Har 11:30 hankalinshi duk ya rabu gida biyu ga tunanin Aira daya baro.
Koda ya koma maman su abokinshi hanashi daukarta yayi ta ce su barwa safiya ba irin yanda bai yiba amma ta hana tace bazasu tunkari hanya da Daren nan ba ga kidnappers da sukayi yawa suyi hakuri su barwa safiya ba yanda Arman ya iya sai hakura yayi yaje ya kama hotel ya kwana Aira ko tana baccinta bata San wainar da ake toyawa ba saida ta farka da asuba Ta ganta a wannan gidan Kan Gado Sosai gabanta ya fad'i ta ce.
"Na shiga ukku ba dai a gidan nan na kwana ba " Sai sannan ta tuno da gida ba Wanda yasan Inda take Cikin firgice ta tashin hankali ta tashi Kanwar Abokinshice ta shigo Dan tada ta tayi salla Tazo ta isketa harta tashi Wanka Aira taje tayi ta mayar da kayan jikinta ta fito suka bata break fast mai rai da lafiya taci tana gamawa Arman yazo Godiya sosai Arman yayi musu tare da alheri Aira ma Godiya tayi musu dukda firgicin da take ciki.
B'angaren gidan su Aira basu lura da Aira bata gida ba sai wajen 11pm Inna ta rikice ta nufi part din su Mamy ta fad'a musu Aira da bata gida Nan aka shiga nemanta lungu da sak'o ba a ganta ba Sosai suka shiga tashin hankali musamman Mamy hada kukanta Har 1 ana neman Aira ba a ganta ba ranar kwanan zaune sukayi Bcci saidai barawo.
Hafsat ce da tasha baccin ta wajen Asuba ta farka Taji kamar ana neman Aira lokacin duk suna palourn Inna sunyi jugum Hankali tashe har Abba daya kasa zaune ya kasa tsaye inna ko inbanda kuka ba abunda take Hafsa dake bacci jikin mamanta ta ce "Mama Wai Aira ce bata dawo ba kowa" Duk kallonta mutanen dake palourn sukayi a tare sukace "ko kinsan Inda take ne Hafsa" Tashi tayi ta ce "Eh jiya dai da Yamma wajen magriba Yaya Arman yazo Nina rakata wajenshi tace yunwa takeji zaikaita joint taci abinci da tare zamuje saina ce Zan raka mama gidan Daddy shiyasa lokacin da muka dawo ni nazaci ma harta dawo"
"Salati dukansu sukasa musamman Mamy kuka ta fashe ta ce " Na shiga ukku Airance tabi Arman suka kwana waje"Abba ko Shi kadai yasan yanda yaji a cikin ranshi safa da marwa kawai yake yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata "Inna ko Salati ta rafka ta ce " ku bari sudawo muji dalili Dan nasan Tarbiyar Mujahed da Hajara sarai bazasuyi wani abunda bai kamata ba ni har hankali na ma ya kwanta tunda tare take da d'an uwanta"duk kallon mamaki suka bi inna dashi saikuma suka Jinjina kai Abba ko ya kasa magana sai safa da marwa da yake "Mama Halima ce ta ce
" Dan Allah yaya ka kwantar da hankalinka Tunda dai anji Inda take sai a jirari dawowarta"Cikinsu ba Wanda Abba ya tankawa shi kadai yasan Zafin da yakeji cikin ranshi.
Aira ko tun a mota take yiwa Arman kuka tasan yau Abba yasan bata kwana gida ba ta shiga ukku kasheta zaiyi tun yana Lallashinta har ya rabu da ita 7:20 tayi musu a Kano Kai tsaye gidan Inna suka isa Ba yanda Arman baiyi da ita ta fita ba amma taki sai kuka ta ke "tausasa murya yayi ya ce "
"Kinga irin haka nake guje miki shiyasa Banso kika Bini ba Amma kika dage yanzu ki kwantar da hankalinki ki shiga nasan ma bazasu Gane ba Tunda Bangaren inna kike kuma inna ba d'akinki take shiga ba shiru Aira tayi ta na tunanin kuma hakane k'ilama Allah ya rufa mata asiri basu sani ba Kallonshi tayi cikin sigar shagwaba ta ce.
"To bazaka rakani ba yaya" Idan na rakaki wani zai iya ganinmu Amma idan kikashiga ke kad'ai ba mai ganewa zaisu zaci ma kinfita ne sayan wani Abu Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Hakane Yaya to sai Anjima " Murmushi yayi mata ya ce "kije ki k'ara hutawa saimunyi waya Ko na shigo"
gyad'a mai kai tayi bata samu damar ma mayar mai da murmushinba ta nufi bakin gate a hankali ta kwankwasa mai gadi ya fito ya bud'e yana mata kallon mamaki.
Ajiyar zuciya Aira ta sauke ganin farfajiyar gidan ba kowa Arman ko yana ganin shigarta ya sauke ajiyar zuciya driver ya jashi suka tafi Aira ko gabanta na fad'uwa haka ta tinkari k'ofar d'akin.
saida ta tofa addu'oi tukwana ta yi bismillah ta tura kofar a hankali kamar Munafuka tana bud'ewa tayi turus ganin Duka mutanen Gidansu a palour zata iya cewa a rayuwarta bata tab'a shiga tashin hankali irin na ranar ba baya tayi da Sauri tare da Niyyar Rugawa Kafin tayi taku d'aya Abba ya chafkota cikin zafin nama da b'acin rai yayi mata wani irin
Mahaukacin ruk'o tare da d'auketa da wani gigitaccen mari..............✍🏿
*Kamar yanda na fad’a a page 30 In-Sha-Allah zamu gama book one ma ana free page kenan ku hanzarta biya tun kafin a kammala book one if you want to subscribe pay #200 katin MTN to 07026166536 hoton katin ko transfer masu Vtu suma zasu tura ta number tare da shaidar turowan amma su #300 wanda basu da buk’atar group ma ana ta pc za a tura musu suma #300 zasu biya ta number da na d’ora zasu tura y’an Niger kuma kumin magana ta wannan number +234-7026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain na 200 sai a saka ku Group karku manta book d’innan garab’asa ce babba da na sakeshi a 200 kachal Darajarshi tafi ta 1k Ni da Yaya Arman ba a fara komai ba bama a shiga wasan ba wannan duk somin tab’i ne hmmmmm wasan na nan gaba wannan shi ake kira koda kud’inka saida rabonka wannan salon na musamman ne masoyan asali ku harzarta ku biya nasan babu wanda zaizo ayi doguwar tafiyar nan batare da shiba saina jiku*💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾
*Share fisabilillah*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/4, 22:40] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚
بسم الله الر حمن الر حين
*BOOK ONE*📔
🅿️...............23&24
Aira jinta tayi cikin Wata duniyar ta daban kafin tayi ihu ya k'ara kifeta da wani marin da yafi na d'azu k'ara ta fasa cikin gigicewa Abba ko ranshi yayi kololuwar b'aci Wayar dutsin guga ya ciro Tare da wullata kanta ya bugi da Bango Nan ya hau lafta mata ta ko ina ihu take tana neman d'auki Abba ko baimasan tanayiba Dukanta kawai yake kamar baitab'a saninta ba.
Duka mutanen dake d'akin saida suka tausaya mata Dan ko jakki aka yiwa dukan nan Yagamu da azaba dukda haushin Aira da Mamy keji Amma saida ta tausaya mata Cikin kuka taje ta rik'e Abba ta ce "Dan Allah kayi hakuri Abbansu Karka kasheta" .
Bankad'eta Abba yayi Kad'an Ya hana ta fad'i cike da masifa ya ce "Ai gwara ta mutu Da ta d'auko mun magana mutuwar ta ta fiyemun rayuwarta " Cigaba da laftarta yayi Aira ko suma ce kawai batayi ba Inna ma Tana kuka ta taso ta dinga ba Abba hakuri ya kyaleta Baimasan ta nayi ba.
Dak'yal dai Mama Halima ta rik'e Hannun Abba ta ce "Dan Girman Allah Yaya ka rabu da ita wlh ta daku karka mata illa nasan bata kyauta ba da ciwo amma kayi hakuri ka zauna " Dak'yal ta samu Abba ya zauna yana huci Aira ko Wajen Aunty Aysha ta ruga da gudu ta Rungumeta ta na kuka itama Rungumeta Ayshar tayi tana kuka Dan Duk wani mai imani saiya tausayawa Aira irin bugun da Tasha.
Cikin tsawa Abba ya ce "Munafuka K'aramar karuwa Har kinyi girman da zakibi namiji kuje ku kwana waje ni zaki tozarta ki kunyata a idon al'umma ni da daraja da kimata da komai "Abba ya fad'a yana nuna kanshi" Aira ko sosai Kalmar k'aramar karuwar tayi mata ciwo Kara fashewa tayi da kuka magana ma ba kasa Mamy ma kanta saida Kalmar Tayi mata ciwo "Fad'a sosai Abba ya shigayi Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba yana cewa .
" Duk cikin y'ay'ana ban haifi y'ar iskaba tun daga kan Yayyunki saike y'ar karshe_Karshe Zaki gagareni ki bani matsala Tun yaushe na rabaki da d'an iskan yaron nan baki rabu dashi ba Abu har yayi k'amari kun Fara kwanan hotel hotel k'aramar yarinya dake ni zaki daukowa magana to baku isa ba Dagake har shi har ubanshi nafi k'arfinku wlh idan kuma da kene aka had'u aga bayana to ta Allah ba takuba kinja kin fita daga raina harna Fara tantamar ma Anya Nina Haifeki kuwa".
Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Mama Da Mama Halima suka fad'a a tare Mama ta ce "Haba Alhaji wannan wace irin magana ce Kai da ranka ya b'aci baka iya control d'in bakinka wannan Maganar Ba Abun yi bace " Mama Halima kuka ta sa ta ce "Haba Yaya Wannan wace irin rayuwace kaida d'an uwanka Amma kun zama kamar Annabi da kafiri kawai kun biyewa shaid'an yayi tasiri a cikin zuciyar ku Wlh saboda ku yasa ko garin nan Banason zuwa kun Riga kun b'ata mana zumunci Kun b'ata zumuncin y'ay'anmu ".
Mamy ko Itama kukan take sosai Maganar Abba ta k'ona mata rai cike da b'acin rai Ta tashi ta sab'i d'anta ta ce "Idan ba kai bane ubanta saika fad'i uban nata kokuma da ita nazo daga gidanmu Abun kuma ya tashi daga kanta ya koma kaina sharrima Ake neman K'ullamun kenan saikaje asibiti a Auna jininka da nata idan ba y'arka bace saika nemi ubanta ka maida mai"
sannan ta kalli Aira tace " Ke kuma hankalinki ya kwanta saiki zubda ruwa a k'asa kisha kinja Anyimun wulakanci burinki yau ya cika"Ta k'arasa fad'a cikin kuka tare da barin Palourn.duk saida sukaji ba dad'i musamman Aira da ta k'arawa kukanta Volume inna ko tsaki taja ta ce “munafuka duk ba kece silar komai ba “.
Abba baiko kula mamy ba saima ya tashi ya ce zanje wajen ubanshi na Mashi warning Rikeshi Mama Halima tayi ta ce Dan Allah kayi kayi hakuri kar kaje Bari a kirashi yaya Kabir d'in yazo a sasinta tunda haka kakeso wannan Maganar Ba ta waje ba ce tukwana ya zauna yana huci.
Aunty Halima ta kira Abbansu Arman Bayan sun gaisa ta ce "Yaya Dan Allah kazo gidan Inna yanzu tana son ganinka da Sauri" Subhanalla innarce ba lfy ko wa cewar Daddy"Lafiya qalu yaya kaidai kawai kazo "To gani nan yanzunnan" Cikin Sauri Daddy Ya taho Dan a tunaninshi Inna ce ba lafiya Kafin minti Ashirin Ya Iso gidan.
Suna zazzaune Kamar y'an zaman makoki Daddy Ya shigo Security d'inshi Ya umarta su tsaya a waje Har PA d'inshi Yana shigowa ganin Inna ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ai nama zaci Inna ce ba lfy hankali na harya tashi" .
Lafiya qlau Yaya ka zauna "Bayan Daddy Ya zauna Mama Halima na kuka ta ce " Yaya Dan Allah Dan Girma Allah ku taimakemu ko ba Dan mu ba Dan Allah Kuyi hakuri ku janye wannan gabar Dake tsakaninku da tashin hankalin nan kamar Ba y'an uwa ba karku manta yaya ciki d'aya ba wasa ba ne Wlh kullum Da Bakin cikin wannan abun nake kwana nake tashi Ku taimakemu ku fahimci Juna na tabbata hatta ran iyayenmu dake k'asa basajin dad'in abun nan na tabbatar da suna raye da bazaku mana haka ba ".
Abba ne Ya tashi cikin fad'a ya ce "Daman Halima dalilin da yasa kika kirashi kenan to babu wani saurin shiri tsakani na da mutumin nan Sannan ya kalli Daddy Ya nunashi da yatsa ya ce .
" Kashe ne zan maka Akan Lalataccen d'anka Jiya ya d'aukar mun y'a sun kwana waje Dan haka kajawa Dan iskan d'anka kunne ya rabu da y'ata na rabasu sunk'i rabuwa nan gaba na k'ara ganinshi da ita Zan d'auki mummunan matakin da kowa saiya koka Dan wlh ka sake d'anka ya lalatamun tarbiyar y'a ko yayi mata ciki Kotu ce Zata rabani dakai".
Cikin b'acin rai Shima Daddy Ya tashi cikin masifa ya ce "Daman saboda wannan dalilin ne kuka kirani sannan Shima ya nunashi da yatsa ya ce " Karka k'ara kiran d'ana da lalatacce y'arka ce lalatatta tunda har ka kasa bata tarbiyar da har ta bishi ta kwana Sannan kai zakayiwa y'arka kashe ba ni ba Idan ka isa da ita Kai zaka rabata dashi ba ni ba bazan rabasu d'inba Kuma da kake maganar abun Kunya ,y'a mace ke abun Kunya ba d'a namiji ba Dan haka idan ma yayi mata cikin kai da y'arka kukayi abun Kunya ba ni da d'ana ba Hope ka gane "
Yana gama Fad'ar Hakan Fuuu yayi waje Duka Wanda ke Palourn Babu Wanda bai koka ba Musamman Mama Halima da take ganin tazo kiran gyara gashi an k'ara b'arna Shima Abba cikin b'acin rai da k'unar rai ya tashi ya fice daga palourn Tabbas yau Aira ta Ja Amfad'a mashi magana masu ciwo Aira ko Sosai take kuka ita kam ta shiga Ukkunta ya zatayi da rayuwarta da gudu tayi d'aki ta haye Gado ta na kuka mai tab'a zuciya.
Yinin ranar Kowa sukuku ya yishi Haka dai akayi soye Rai duk babu dad'i musamman Mamy da zata iya cewa ranta yafi na kowa b'aci Aira ko ranar yinin D'aki tayi ko abinci bata iya ciba Tasha kukanta Har ta gode Allah ga shaftun bulalun Abba da suke mata mugun rad'ad'i.
Daddy ko cikin b'acin rai ya nufi gida yana zuwa Ya d'auke Arman da Mari Arman da jin Marin kawai yayi a sama dafe kumcinshi yayi ya tsaya yana kallon Daddy karo na farko kenan a tsawon Rayuwarshi da Daddy Ya tab'a daga hannu ya dakeshi cikin fad'a Daddy Ya ce.
"Ubanme yasa ka d'aukar musu y'a ina ka kaita har kuka kwana Waje Kaja yau an fad'amun maganganu masu zafi a saboda kai To daga yau bakai ba y'arsu na Rabaka da ita indai nine mahaifinka bakai ba ita tunda ba kanwar uwarka ba ce "Arman sosai ranshi ya b'aci Daman shi bai iya b'acin raiba " yace "Daddy daman A saboda Aira ne ka dakeni?Cikin fad'a Daddy Ya ce " A saboda ita d'in zan iya k'aramaka fiye da Wanda na maka Tukunnama fad'amun wata alak'ar ce Ke tsakaninku da bazaka iya rabuwa da ita ba "
"Daddy sonta Nake Kuma Auranta zanyi itace matata bazan rabu da ita ba kome zakuyi Saidai Kuyi Amma bazamu tab'a rabuwa da junan mu ba Fad'anku bazai shafemu ba " So Mummy da Daddy suka fad'a a tare Bai jira sun Sake cewa wani Abu ba cikin b'acin rai yayi Hanyar waje Mummy na kirashi ta na cewa
"Son dawo ina zaka kuma" Dan tasan Halin d'anta bai iya b'acin raiba musamman da har daddy ya mareshi shiyasa basusan b'ata mai rai Dan Duk maganar da
Showing 18001 words to 21000 words out of 33558 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12