ma Abba ya bida bare ke tsirit" Aira ko kauda kai tayi ta na gunguni Saida taga wucewarta tukwana ta mik'e ta sanya k'aramar wayar a jikinta tayi bedroom d'in Mamy ta k'ara yimata ya jiki ganin d'akin da mutane ya sanya ta juya ranar duk sanda taso ta dauki jaririn hoto a wayarta ta turamai gagara tayi.









Sai washe gari wajen 11am taje gaishe da Mamy ta tarar da Ita ta na Toilet ga Alamun wanka take kuma jaririn na kan Bed shi kadai cikin Sauri ta Ruga part din inna ta ciro wayarta dake locker ta boyeta a jikinta koda ta koma tayi sa a har lokacin Mamy wanka take cikin Sauri ta fiddo wayar ta shiga d'aukar babyn hoto a snap sosai yake yin kyau.







Cikin Sauri ta bud'e data ta shiga ta turama Arman hotunan Sannan ta shiga status tayi status daman bata d'auki number kowa na gidansu ba Dan haka ba Wanda yasanma tana da waya bare har Susan tana chat tana gama dorawa ta sauka ta maza ta kira Arman tana lek'awa Kar wani ya shigo ta na kara wayar a kunne yana d'auka cikin Sauri ta ce .







"Na tura maka hoton ka hau ka gani " rikicewa tayi ganin Fitowar Mamy tayi tsaye bakin bathroom d'in ta na kallonta maza tayi cikin Rashin gaskiya ta kashe kiran Tare da Boye wayar a bayanta "Wace waya ce na gani a hannunki?ta tsinkayi muryar Mamy " .







kafin kace me idonta sun cika da hawaye ta fara in ina karya ma take so tayi abun bata saba ba ta kasa "Mamy ta daka mata tsawa ta ce " nace wayar uba waye na gani hannunki mik'omun wayar Mamy ta fad'a ta na nufota Tashi tayi tana ja da baya ta ce"I m sorry Mamy bazan Sake ba"me nace kinyi da zakice bazaki sakeba kuma wlh na k'ara magana baki mik'omun wayar nan ba zanmiki abunda baki tunani"Tuni Aira ta fara Kuka.







tsawa Mamy ta k'ara daka mata ba arziki ta mik'a mata wayar ta na yayyarfa hannu kamar wacce aka daka "jujjuya wayar Mamy ta fara cike da mamakin ganin wannan tstsadar wayar Dan taga a Instagrams ana tallarta kudinta sun haura 700k " Kallon tuhuma ta kalli Aira dashi ta ce "Wayar wacece?Tawace Mamy Dan Allah kiyi hakuri kar Abba yaji " .







ta fad'a cikin kuka "Salati Mamy ta rafka ta salamce ta ce " Na shiga Ukku ni Rahama Aira lalacemun kikeso kiyi Ki rik'e har wayar kusan 1 million a gidan nan batare da sanin kowaba Aira kunyata ni kikeson kiyi uban wa ya baki wayar wannan me tsada kuma banason kimun k'arya wlh kika kuskura kikamun k'arya saina lillisaki kuma na kira babanki na fad'a mashi maza fad'amun ubanwa ya baki yanzunnan " Tuni cikin Aira ya fara d'urar ruwa kuka ta k'ara fashewa dashi to ita me za tacewa Mamy Arman zatace ya sai mata kowa ..........โœ๐Ÿฟ



*Tofa Fans ku taimaka ku bawa Aira shawara ta shiga matsala wa zatace ya saya mata waya ๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ขgaskiya ni harta bani tausayi*



*_Miss Hajo ce_*๐Ÿค™๐Ÿฟ
[6/1, 18:30] Hajo: ๐Ÿ *NI DA YAYA ARMAN* ๐Ÿ
Hot love storyโ™ฅ๏ธ๐Ÿ”

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

๐Ÿ“š *JARUMAI WRITERโ€™S ASSOCIATION* ๐Ÿ“š

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู†

*BOOK ONE*๐Ÿ“”
๐Ÿ…ฟ๏ธ...............17&18

......Bazaki d'aga baki kimun magana ba dukanki nayi da zakumun kuka"Mamy ta fad'a cikin b'acin rai" Aira ko kuka kawai take ta na yarfe hannu Dan tasan Mamy bata fiya mata haka ba Dan bata iya b'acin raiba.



"Okay bazaki fad'amun ba kenan tunda ni kin rainani bari na kira Abbanku saiki yi mishi bayani ta fad'a tana d'auko wayarta" Aira kamar wacce aka zabura haka ta zabura tareda Rugawa wajen Mamy ta rik'e hannunta ta na kuka ta ce "Mamy Dan Allah karki fadamashi zan fad'a maki wlh y'anzu Yaya Arman ya sayamun"


ta k'arasa fad'a ta na hawaye" Arman?Mamy ta maimaita tana mata wani irin kallo,Saurin sakin hannun Mamy tayi tare da ja da baya ta ce "Dan Allah Mamy karki dakeni bazan sakeba" Arman Mamy ta k'ara maimaitawa zaunawa bakin gadon tayi tana jujjuya wayar na y'an sakanni kafin da d'ago ka kalli Aira dake tsaye tana kuka ta ce "Shi Arman d'inne zai sai maki wannan wayar a wani dalili?Wlh Mamy shi ya sayamun".


" chabd'i Mamy tafada tukwana ta ce "Fad'amun yanzunnan wace alak'ace ke tsakaninki dashi Dan ubanki ,meye ke tsakaninku " Mamy wlh ba komai kawai zumunci muke dashi Mamy kin mance Yaya na ne fa"Ubanki ke da yayan Duka su sauran y'an gidan ba y'an uwanshi bane ko ke kad'aice y'ar uwarshi alak'ar dake tsakaninki dashi suma haka take su me yasa bai saya musu wayar ba saike kad'ai ya zab'a ya sayawa".




kasa tayi ta kanta tana hawaye ta ma rasa wace amsa zata ba Mamy "koma meye ke tsakaninku ai zamuji sannan ki gaggauta mayar mashi da Wayarshi muddin kina gujin b'acin raina marar jin magana kullum kinfison ki dinga jawomun magana yanzu da Abbankune yaga wayar nan da ni kaina basaikinjamun ba ki mayar mashi da Wayarshi ko ki kiramunshi ni nafada masa yazo ya Anshi abunshi bansan d'iyan iskanci idan kuma ba haka ba sainayi kwatsakwatsa da wayar".



cikin Sauri ta d'ago ta ce "a a a Mamy wlh bama saikin kirashi ba zan mayar masa da yadawo insha Allahu nagode da bazaki fad'awa Abba ba " Tsaki Mamy taja ta mika mata wayar tare da d'aukar jaririnta da ya fara tsala kuka Aira ko cikin Sauri ta amshi wayar ta sakata A siket ta fice daga bedroom d'in ta na fitowa palour ta tarar da Ya Umar da matarshi (Babban yayansu ss ne ya na aikine a Kebbi tare yake tafiya da matarshi khadija sai idan sunzo su sauka gidansu))cikin murna tace Lah ya yaushe kukazo"Murmushi yayi ya ce "Yanzu muka Iso little sis " sannunku da zuwa yaya Anzo lafiya ya hanya "Alhmdllh ya Rashin ji ya na nan ko yayi sauk'i " Dariya tayi ta ce "Yaya ai ni bana Rashin ji " Zadai kidaina y'ar gidan Inna "kallon Khadija tayi ta ce " .



Ina yini Aunty"Lafiya qalau "ta fada a takaice tab'e baki tayi Dan daman Chan haka halin Matar Yayan nasu take ba mutuncin kirki ya isheta ba shiyasa ma ko gidanta basa zuwa " Bari naje na fad'awa su Mama kunzo ".



"Aira tafada ta na nufar d'akin Mama da Mamy duk ta fad'a musu zuwan su ya Umar a tare suka fito su Mamy na musu barka da zuwa Suka amsa cikin sakin fuska har khadija Dan Duk iskancinta bata fiya yiwa su Mama da Mamy ba khadija ce Ta amshi jaririn hannun Mamy tare da yiwa Mamy barka tace " Allah raya "nan Shima ya Umar yayima Mamy barka Daman sunji haihuwar ne yasa suka taho Aira ganin Mamy da Mama sun d'auki hankalinsu ya Umar yasa tayi saurin fita ta nufi part d'in Inna.




bedroom d'inta ta shige tare da rufewa ajiyar zuciya ta sauke ta ce " yau na tsallake rijiya da baibai da Mamy ta fad'awa Abba Aida na shiga ukku"kiran Yaya Arman tayi kamar zatayi kuka ta fad'a mashi komai kuma Mamy ta ce Wai na maido maka wayar ta fad'a kamar zatayi kuka".



Daga bangarenshi ya ce "bana kyauta a maido mun Kuma bana kyauta na amsa ko wani nayiwa bare ke Dan haka karma ki maidomun " To yaya ta ce fa Ta Kara ganinta Fasa ta zatayi kuma ina tsoron karta Fad'awa Abba "Arman duk Haushi ya isheshi yana jin haushin yanda iyayen Aira ke nuna mai kamar ba Wanda bai had'a komai da ita ba kamar ba kanwarshi ba Mamyn ma da yake ganin dama dama a Wajenta itama nema take ta kwatsa" .




Ya fada cikin ranshi a fili ko tsaki yaja baimasan yayi ba ya ce "Kinji dai abunda na fad'a sanin kanki ne bana magana biyu ta rage ruwanki ko ki yadda ita ko kiyi sadaka da ita ko ki fasata komai kikayi taki ce Dan haka karki k'aramun magana akan dukkan wani abu da zan baki ko na baki hope kinfahimta " Cikin sanyi Aira ta ce "Na gane Yaya yi hakuri Bazan sake ba nasan ranka ya b'aci Naji kamar kana fad'a "saiyaji ta d'an bashi tausayi yasan halinta Sarai akan wannan D'an abun saita yini ta na kuka hakan ya sashi kwantar da murya ya ce .



" raina bai b'aci ba my cutie yaya za ayi my Aira ta ta b'atamun rai Y'ar lele na ai bakya laifi "Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Uhm "Shima Uhm" din ya mayar mata yana mata Dariya ita ma dariyar tayi tanajin sanyi Cikin zuciyarta "ARMAN ne ya ce " Naga hoton k'ananmu yayi kyau naga ma kamar yaso ya sato kamannin my cutie d'ina kodan ya samu ya d'anyi farinjini wajen y'an mata ammafa my Cutie d'ina ta fishi kyau nesa ba kusa ba .




"Dariya Aira tayi sosai ta ce " Allah my yaya kace na fishi kyau"Eh mana ki daina hadamun kanki dashi ma "Dariya tayi ta ce " kai yaya Shima fa yana da kyau sosai"idan babu ke ba amma idan Dake musamman kuka Kara fuska mummuna zakiga ya koma kin manta Kyanki dishe kyan wasu yake "Dariya tayi sosai ta ce " to ni da kai kuma wa yafi kyau"Shima murmushi yayi ya ce "Ni mana Aini na taimaka maki da har kyan naki ya fito idan ba haka ba Ai kema kyan naki da baikai haka ba nine na taimaka maki"




Cikin shagwaba ta ce "Kai yaya wlh nafika kyau" Dariya yayi sosai take burgeshi idan tana shagwaba hakan yasa ya biyeta sukayi ta gardama yana mata Dariya saida suka kwashe kusan awa Ukku suna waya batare da sun gaji da Hira ba daga karshe ma Video call suka koma Dan yau Arman baida aiki yana gida Nan Aira tayi tamai labari Dan rufo d'akin ma tayi Dan kar wani ya shigo ko da zasuyi salla kin kashewa sukayi kamar suna tare Ranar haka suka yini Dukansu sai farinciki suke Dan Aira harta manta ma da Maganarta da Mamy koda zasuci abincin dinner tare sukaci Shima ya zubo nashi ita ma ta zubo nata suna ci suna kirga spoon Din da kowa yayi ta waya dukda basu da cin abinci sosai ranar saida sukaci sosai.



har wajen 11pm suna video call idan zatayi wani abun taje tayi ta dawo Shima haka Saida yaga bacci ya d'auketa murmushi yayi yana kallonta ta waya Yajima yana kallon yanda take baccin yana karajin sonta na ratsa kowani sassa na jikinshi saida yaga wayar ta birgima Alamun baccin nata yayi nisa tukwana ya kashe ganin baya ganinta ranar dukansu kwanan farinciki sukayi batare da tunanin wata damuwa ba.


Ana jibi suna Aira na bangaren Inna wajen la asr ta fito ta nufi bangarensu tana shiga taga Yaya Aysha na fitowa daga mota driver na fito mata da akwatinta Aida gudu Aira ta Ruga ta Rungumeta Itama Aysha Rungume kanwar tata tayi cikin muryarta mai cike da iyayi ta ce "I really miss you my Fav sis " Itama cikin murna Aira ta ce Miss uh 2 my Fav Aunty da bakinan gidan ba dad'i nafi kowa rashinki "Murmushi Aysha tayi ta ce " Ai yanzu nadawo Sis mundaina Rashin juna ko"Gyada mata kai tayi ta na amsar hand bag d'inta ta rik'e mata Aysha tabs driver umarni ya shiga da akwatinta ciki tana dafe da Aira suka nufi haryar ciki Sai murnar ganin y'ar uwar tata ta ke Aira ta ce "Aunty Ya malesia d'in wai kina nufin harkun gama karatun gaba d'aya " Alhmdllh sis karatu kam mun kammala sai Kuma bautar Kasa burin Abba yau ya cika "Cikin murna Aira ta ce " Wow congratulations sis ta fad'a tana Kara Rungumeta Itama Rungumeta tayi ta ce "Thnks my sis yanzu kuma saura ku munyi waya da Ummy ai kwanaki take fad'amun kun kammala s s c e d'inku sai jiran result.




" Wlhko Aunty mungama kai wlh Aunty Ummy bata da kirki duk lokacin da nace mata ta had'ani dake ko a waya Ne wlh kiyawa take Dana dame ta ma cewa tayi "karna k'ara damunta tunda ba waya ta bace nima nayi zuciya nasayi wayar kuma wai kinma sauya layi itama bata dashi" Dariya Aysha tayi ta ce "Kai Ummy ta na nan da halin nan nata kenan Wai har yanzu Abba bai baku waya ba ki ce dai har yanzu tsautsatsauran ra ayin nan na Abba na nan na Sai an Je university idan yanzu baku fara rik'e waya ba fisabilillah yaushe zaku rik'e Baku sanin halin da duniya ke ciki Gaskiya Abba yanzu An waye y'an 10 years ma suna rik'e waya bareku ".



murmushi kawai Aira tayi batace komai ba shiyasa duk yayyinta tafi son Aunty Aysha jininsu yazo d'aya sosai ga tana mugun sonta tana tunanin yanda Aysha ta k'ara wayewa Dukda daman a waye ta tafi amma k'asar wajen nan da taje karatu ka k'ara kilewa....โœ๐Ÿฟ


*Share plx*


*_Miss Hajo ce_*๐Ÿค™๐Ÿฟ
[6/1, 22:52] Hajo: ๐Ÿ *NI DA YAYA ARMAN* ๐Ÿ
Hot love storyโ™ฅ๏ธ๐Ÿ”

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

๐Ÿ“š *JARUMAI WRITERโ€™S ASSOCIATION * ๐Ÿ“š

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู†

*BOOK ONE*๐Ÿ“”
๐Ÿ…ฟ๏ธ...............19&20

Suna isa a palour suka tarar dasu Mamy da gudu Aysha taje tayi hug d'in Mamy da Mummy tana musu iyayin tayi missing d'insu Mamy na murna tana mata oyoyo" Sai sannan Aysha ta lura da mutanen dake palourn wasu baki ta gaishe su Ganin jariri a hannun wata ya sanya ta kalli Aira ta ce "Sis wa ya haihu" .



Mamy Airata bata amsa "wow Kice nazo A daidai Allahsa dai ba ayi suna ba Kuma shine ko a fad'amun sannan taje ta amshi jaririn tace " wow ammafa yaso yayi kama da sis Aira "Haka kowa yakecewa Cewar Mamy Mama ko Kallon Aysha kawai take da shigar dake cikinta K'ank'anin kaya ne jiens da Riga danma bata da jiki hakan yasa basu d'ame ta ba ga wani uban glass da ta dageshi saman goshinta .




Aysha black beauty ce tana da kyau ba fara ba ce Amma bata da bak'i sosai irin choculate colour d'innan amma daga ganinta kasan akwai iyayi da malle " ita Mama duksai kunya ma ta kamata Ganin da mutane itako Aysharma ko a jikinta hakan yasa Mama ta fara aika mata da Harara ganin batasan da ita ba yakeba ya sanya Mama kyaleta saida tagama iyayinta tukwana taja Aira sukayi Bedroom d'insu .



koda su Ummy da Amma suka ganta suma sai murna suke suna daka tsalle suna murnar ganinta Aira tace "Su daina karsu b'alla mata yaya" suna haka Mama ta shigo ta kalli Aysha ta ce "Ke yanzu Aysha ba kunya haka kika ketaro tundaga wata k'asa kikataho a haka kamar ba y'ar musulmi ba " Aysha na tubure fuska ta ce "Haba Mama daga dawowata Ko Sannu da zuwan kirki fa bakimun ba zaki fara mun fad'a me shigar nan tayi kuma" .



Mama ta girgiza kai ta ce "Ai daman Nasan sai Abunda yayi gaba a nan ma ya aka k'are bare anturaki wata k'asar da ba uwa ba uba ba mai tsawatar maki dole likkafa taci gaba shiyasa tun farko banso Alhaji ya tura ki wata k'asa karatu ba to wlh mu nan ba Chan bane Dan haka kar in Kara ganin kinyi wannan shigar kinfito wannan shigar ko tsakar gida Inda kunya kinyita bare waje idan kin gama hutawa kije abincinki na dining Mama ta fad'a tare da barin d'akin.



Aysha gunguni tayi kasa_kasa saida Mama ta fita ta ce " Aifa nadawo wlh su har yanzu sunk'i su waye mu Chan ba ruwan wani da wani ina laifin wannan shigar ta fad'a tana tab'e baki "(nikam hajjo nace ikon Allah Ayshar nan za Aje da ita ).




Bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin Wata doguwar Riga (Abaya)mai shegen kyau maron kallonta Aira tayi ta ce " Wow My Aunty kinyi kyau"Lakutar kumatunta tayi ta ce "Thnks kanwa Sannan ta fiddo wata irinta ta mik'awa Aira ta ce " ga taki nan daman tare nayi mana Anko ki shirya kafin na gama cin abinci zamu fita outing ".



Tsalle Aira ta daka tare da Rungumeta ta ce " Thnks Aunty shiyasa nake sonki da yawa tukwana ta maza ta cire kaya ta d'aura towel tayi bathroom danyi wanka Amma ce da Ummy suka hade baki wajen cewa "mu ina namu" Bansayo da kuba da gani sai Besty na zamuyi ankon"Amma tace "Aifa kindawo yanzu za a fara gwada mana wariyar da aka saba Ummy ko taja k'aramun tsaki ta ce " ko kunya wai wani bestynta k'anwarta ta Ukku amma kamar wata sa arta duk saisun rainaki".




murmushi Aysha tayi ta ce "Kede kina nan da halin nan naki na shegen son girma to meye a ciki kanwar tau ta ukkun saime ke nan gani kike kinma girmi kowa To nidai karkimun Rashin kunya tunda ba a girmanba " Tab'e baki Umny ta yi ta ce "Ni mancewa ma nake kingirmeni Duka shekara biyun da wani Abu sannan ked'in mate Dina ce Ke bare kice kinfini aji nima dai yanda kika gama Degree d'innan nan da sati Ukku zan kammala saime banbancin kinje Malesia ne ni kuma ina B U K saime a ciki".




Dariya kawai aysha tayi ta wuce parlou ta ce "Kanki akeji ta na fita ta tarar da bak'in duk sun tafi kai tsaye dining ta nufa taci abinci me rai da lafiya Aira ko cikin Sauri ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar Riga irin ta Aysha sosai tayi mata kyau ta fito kamar wata balarabiya sai baza k'amshi take hoda da kwalli kawai ta shafa sai lipstick sosai tayi kyau ta dansa madaidaicin takalmi marar tsawo ta yafa k'aramun belt din Rigar kwantaccen gaban gashinta ya fito wa iya zubillahi zo kuga yanda Aira tayi kamar wata balarabiya Tana fitowa ta tarar da Aunty Aysha ta kammala cin abincin kallonta tayi ta ce ".



wow my kanwa kinganki kuwa "Sai sannan su Mamy suka Kalleta Suma sunga tayi kyau Mama tace "wannan gayu haka sai ina
Showing 12001 words to 15000 words out of 33558 words