tana zabgamai godiya daidai zasu shiga palourn inna Abba na fitowa Sosai gabanta ya fadi cikin dabarbarcewa ta fara kokarin kwace hannunta ya rike gam tare da galla mata harara kamar zatai kuka tace ka sakeni kara rike hannunta yayi ma .



kallon zaki gane kuranta Abba yayi mata tare da wucewarshi sosai nayi mamakin ganin Arman baiko gaishe da Abba ba saima kauda kai da yayi Abba na wucewa Arman ya gallawa Aira harara yace “ita kuma wannan rikicewar da kikayi ta mecece kamar kinga mala’ikan mutuwa “cikin muryar in ina tace yaya ab ba tsaki yaja tare da sakin hannunta ya wuce ya fasa shiga gidan inna durkushewa tayi ta fashe da kuka tasan ba karamun hukunci zata fuskanta a wajen Abba ba ga kuma shima yaya Arman din yatafi kamar fushi ma yayi da ita tana cikin kuka haidar yazo tare da daddabata ya ce “ya Aira Abba yace kizo yanzu yanzunnan ki sameshi a babban palour kika wuce minti biyar kinsan sauran..........✍🏿

Tofa meye dalilin da yasa Aira ta rikice ganin Abba ya ganta tare da Arman ????

Meye dalilin da yasa Arman bai gaishe da Abba ba????

Tukunnama wace Alakace ke tsakaninsu????

Zaku samu amsarkune ta hanyar bibiyata cikin wannan zazzafan labari

* Ta hanyar comment da sharhi tare da sharing shine abunda zaisa na gane labarin yana muku dadi ko akasin haka kuma shine babbar kwarin gwiwar da zaku bani idan kun karanta ku dinga comment tare da sharing sauran grps masoyan asali* 🤗



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/25, 00:17] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE* 📔
🅿️...............5&6

Cikin ta ne ya d'uri ruwa jin Abba na kiranta Cikin kuka ta kalli Haidar ta ce "Na shiga Ukku Haidar Abba Duka na zaiyi ko" Sai yaji yayar tashi ta bashi tausayi girgiza mata kai yayi ya ce "A a ya Aira nidai kawai cewa yayi kizo kuma kinsan Abba bayason yayi kira a bata mai lokaci ki taho muje " shahada tayi ta mik'e tare da Jan kafafunta Wanda dak'yal suke daukarta tsabar tsoro.





Sosai ta tsorata ganin Abba na safa da marwa a palour tana shiga gabanta ba abunda yake sai fad'uwa juyowar da zatayi taji Abba ya d'auke ta wani gigitaccen mari da saida hankalinta ya gushe na d'an wani lokaci kafin ta d'ago ya k'ara kifa mata mari wani irin ihu ta fasa tare da durk'ushewa ta na kuka.







Cable d'in wayar wuta ya d'auko ya nufeta tare da lafta mata daya azabar da taji ce ta saka Kara sakin wani karan "Na shiga ukku zan mutu" Mama ce ta taso hankali tashe ta rik'e cable d'in ta ce "Dan girman Allah Alhaji kayi hakuri karka daketa DA Wannan Abun" Abba ya juyo ya Kalleta ya ce "Zainab ki rabu dani wannan yarinyar bata jin magana ki barni na koya mata hankali" .





"A a Alhaji Dan girman Allah kayi hakuri ka zauna Tukunnama me tayi Abba na huci ya zauna ya dubi Aira da ta ke kuka wiwi ya ce "Had'iye kukan nan yanzu yanzu nan Dan gidanku " Cikin Sauri ta Had'iye kukan sai shshsheka da take cikin tsawa ya ce.







"D'ago ki kalleni Munafuka " Idonta jab'e jab'e da hawaye ta Kalleshi ya ce "Sau nawa Zan rabaki da d'an iskan yaron nan,ban rabaki dashi ba?tana shasheka ta d'aga kai " Bud'e baki zakiyi kimun magana "k a ra ba mu " ta fad'a a rarrabe "Fine Kinsan da haka kuma shine kika cigaba da mu'amula dashi ko Watau bakijin magana ta ko rainani ne kika yi?" Cikin kuka ta fara girgiza kai ta ce "Dan Allah Abba kayi hakuri Bazan sakeba".





" wannan ya zama.last warning da zan k'ara ganinki da yaron can duk irin hukuncin da na yanke maki ki kuka da kanki kina jina"cikin Sauri ta d'ago ta ce "Naji Abba"ki tashi kiban wuri sakarai wacce batasan ciwon kanta ba "hada gudunta Aira ta Ruga tayi dakinsu ta na zuwa ta baje a gado taci gaba da rera kuka Amma Da Ummy su sukayi ta Lallashinta anma kamar k’ara zugata suke.





Mama ko da Mamy sosai basajin dadin wannan al'amarin nasu musamman Abba da ya fi d'aukar zafi , ba Wanda ya kumayin magana cikin su Mamy ta tashi da tsohon cikinta ta tayi d'akinta ta jima ta na hawaye tasan Duka itace silar raba wannan y'an uwa Gashi kuma batajin dad'in yanda Kullum y'arta ta zama kamar jakka akan Arman kullum Abba cikin dukanta yake amma kamarma Kara tunzurata yake Haidar ne ya shigo maza tayi ta Goge hawayen ta Kalleshi ta ce.







" Haidar jeka kiramun Hajara"to Mamy yafada yaje ya samu Aira na Kuka Amma na Lallashinta yace "ya Aira Mamy na Kiranki a d'akinta Gyada mai kai tayi ta tashi ta na Goge hawaye ta bishi ta na zuwa ta zaune gefen Gado Mamy ta kalli Haidar ta ce " Bamu wuri zamuyi magana "Yana fita ta kalli Aira ta ce " ke yanzu Hajara Haka zakiyi ta zama kin maida kanki jaka a gida ko,?kowa ya na zaune lafiya amma banda ke,tunda kika San mahaifinki bayason tarenki da shi meye na likemai Ubanki ne shi da bazaki iya rabuwa dashi ba ko kullum kinfison ke kad'ai ake jinki da mahaifinki na rasa uban me yake baki duk kinbi kin lik'emai sakarai Saikije kiyi tayi ai tunda bakison ciwon kankiba"Aira Abu dukya chunkushe mata ga Abba ya gama laftarta ga Mamy ta hauta da fad'a tashi tayi ta na kuka ta fita tayi waje ta ma bar part din gaba d'aya ta koma part din inna.







Gadon ta ta hayaye a abunda take inbanda kuka shin ya zatayi da rayuwarta ,meye laifin ta ida da Arman akan gabar dake tsakanin iyayensu ga Abba ya gama jibgarta itama Mamy zata hauta da fad'a saida ta gama kukanta harta gode Allah tace "Gashi Shima Ya Arman din yayi fushi dani ya kukeso nayi da rayuwata tafada tana wulli da pillow Ta Kara fashewa da kuka ta ce.





" Tun bansan kaina ba na shak’u da kai yaya ARMAN wacce bazan tab'a iya misalta ta da komai ba ,tun bansan kaina ba ,shakuwar dake tsakaninmu babu wanda zai isa ya rabamu koda za a dinga tsaga naman jikina ana barbada attarugu da barkono bazan tab'a iya rabuwa dakai ba " kuka ta k'ara fashewa dashi ita wai yazatayi da rayuwarta Daren ranar bacci kauracewa idanunta yayi banda kuka ba abunda take sai wajen Asuba bacci ya d'auketa.





©©©©©©©©©©©©©©©



Arman kai tsaye guest house d'inshi ya nufa kwance yake kan makeken gadonshi da komai na d'akin pink ne dakin gabaki dayanshi manne yake da hotunan Aira wasu tun tana yarinya wasu kuma da girmanta wasu tare suka dauka daga shi sai T-shirt da gajeran wando banda tsaki ba abunda yakeja ya ce "Wannan tsoron na mahaifinta da nagani k'arara a kwayar idanunta Tabbas wataran zata iya ruguza alak'armu abunda bazan tab'a jura ba kenan ko sama da k'asa zata had'e ana ruguguwar tashin k'iyama bazan tab'a yarda a rabamu ba my cutie Aira I love her so much,ina jinta har cikin kokon zuciya ta ,i can't live without her inajinta a jinin jikina,tunaninta bai tab'a barin kwakwalwata ba daidai da second d'aya why Abba yakeson rabamu me mukai musu,ina ruwan mu da rigimarsu" Chan ya numfasa saboda bai saba doguwar magana ba ya ce.





" Karfa Aje kuma ita Har yanzu Kallon yaya kawai takemun kartace kuma bata sona wulli yayi da laptop d'in dake gabanshi ya ce "Inaaaaa bazaiyuba haka yayi ta zirga zirga ya k'ulla can ya since can ganin kanshi ya fara kullewa ya tashi tare da daura alwala ya fara jera salloli duk adduarshi akan Allah ya bashi Aira Dan shi kanshi ya kasa gane wannan wace irin jarabtar so ce Allah ya d'ora mishi ta yarinyar nan........✍🏿

Hmm muje zuwa





A gaskiya ina Jin dadin comment dinku sosai masoyan asali kuma ina godiya kwarai da gaske 💃🏾💃🏾💃🏾



*Comment*

*vote*

*Share fisabilillah*#





*_Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/25, 23:13] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............7&8

Washe gari kasancewar weekend kuma basu da jarabawa yasanya bataje ko ina ba a d'aki ta yini tun Inna na tambayar me akai mata har ta rabu da ita sosai take baza ido ganin ko yaya ARMAN zaizo amma shiru hawaye ne ke zarya daga idanunta ta ce "Yaya kai kuma me nayi maka da zakayi fushi dani".



©©©©©©©©©



Zaune suke a makeken palour shida mahaifiyarshi Magana take mai amma kwata-kwata hankalinshi baya gurin saida ta dafoshi ta ce " Arman dakai fa nake magana tunaninme kake"Nothing Mummy ina jinki "Hmmm kawai ta ce sannan ta d'ora da cewa.





" Son maganar da na saba fad'a ce dai zan kuma maimaitawa Ka duba kaga ARMAN sa'anninka duk sunyi Aure wasu hada y'ay'a amma kai baka da ma niyyar yi shekararu fa ja suke Son ka duba 33years amma har yanzu baka da iyali ,ina son nima naga Aurenka naga Y'ay'anka karfa ka manta kai kad'ai ne d'ana a duniya kai kad'ai nake dashi Wanda zansamu jikoki daga gareshi ka tausaya mun ko Dan ni Arman plx".







Numfasawa yayi a ranshi ya ce "Ina wata matsalar ita ma Mummy zatazo da wata a fili kuma cewa yayi " Mummy karki damu Aure lokaci ne Idan lokacin yayi za ayi"Kullum maganar ka kenan Aure lokacine eh Aure lokaci ne amma anasa niya kaikuwa kwata kwata baka ma da niyyar ma sau nawa ina turaka kaje kaga y'ay'an y'an uwa da Abokaina karshema ka kunyatani kayiwa yaran wulakanci " .





calm down Mummynah Insha Allahu soon zanyi Aure ina da wacce nake so ita nake jira ne shiyasa" Hararar wasa ta gallamai ta ce "Kullum maganar kenan ka na da wacce kake so ,kuma kak'i fadarta mu Santa,yaushema kake kula y'an matan da har zakaso wata son kodai aljanna ta Aure ka bamu sani ba " .





Dariya maganar Mummy ta bashi sosai saida ya d'an Dara ya ce "yawwa Mummy ashe kingane aljanarce ta Aure ni shiyasa na mutu a kanta to Kinga sha'anin Aljannu sai a hankali zata rabu dani ku tayani da addua kawai Allah bani ita amma kidaina mun maganar Auren nan kinsan Aljannu da kishi karta kullaceki fa mummy".





pillow Mummy ta tillamai jin shirman na d'an ta ce " Watau Arman kadai maidani kaka ko zaka gamu dani ja iri kawai"Dariya yayi tare da gocewa pillown da Mummy ke jefamai yayi Hanyar fita yana cewa "Good bye mom saina dawo "yana fita guyd's d'inshi sukayo wajenshi dakatar dasu yayi Dan bai fiyason yawo da su ba Motarshi Fara Sol kirar Benz yahau kai tsaye gidan Inna ya nufa ya na shiga mai gadi ya bud'e mashi ya shiga A lokacin Aira na kwance saman sofa ba bacci take ba amma kallo d'aya zaka mata kasan ta na cikin damuwa.





Dagowar da zatayi idonuwansu suka sarke cikin na juna ganin yanda ya hade rai ya basar ya yasanya maida idanunta kasa gabanta na fad'uwa tayi Sauri ta maida hawayen da suka zubo mata Arman na zama ya gaishe da Inna ta amsa tare da cewa "Wai ni Mujahid ina mahaifinka yaje kwana biyu bai lek'o ya gaishe niba " Baya gari ne Naji Mummy tace yaje Ghana wani metting nima tunda nashigo k'asar bamu had'u dashiba"yana maganar ya na satar kallon Aira ta maida idanunta ta rufe.



"Inna ce ta ce " To Allah ya maido shi lafiya nikadai a raina nace lafiya Kabir zai kwana biyu baizo ba "shidai Arman baice komai ba sai satar kallon Aira yake inna ce ta tashi ta ce " Nidai na gaji da zafin nan bari na fita waje nasha iska tafada tare da ficewa farfajiyar wajen kamar jiran fitarta yake ya taso tare da zama kujerar da Aira take a hankali ya ce "My cutie" Shiru tayi kamar bacci take nanko ta na jinshi "Hmmmm nasan kina jina dan idonki biyu wake up zamuyi magana" badan taso ba ta tashi Dan sai yanzu take ganin me tayi mishi da zaiyi fushi da ita.





"kallon ta ya tsayayi yanda idanunta sukayi jawur ga alamar Tasha kuka cike da damuwa ya ce "Kuka kikayi ko Cutie" Kamar jira take nan take ta fashe da wani sabon kukan jin kukanta yake har cikin ranshi rungumeta yayi yana Lallashinta dak'yal ya samu tayi shiru cike da damuwa yace "wa ya tab'amun ke" Shiru tayi ta na shashsheka "ganin shaftun bulala a hannunta yayi ja abunka ga farar fata cike da damuwa ya rik'e hannun ya ce.







" Cutie Abba ya dake ki ko"Gyada mai kayi tana hawaye "sosai ranshi ya b'aci Dan a duniya ba abunda ya tsana sama da b'acin ran airanshi Har takai ga an tab'a lafiyarta wlh ba Dan shi ya haifeta ba da nikadai nasan matakin da zan d'auka cikin zuciyarshi yake maganar nan amma a fili cewa yayi "cewa yayi ki rabu da ni ko" gyada mishi kai tayi ta na hawaye "Dan son gwadata ko tsoro zaisa ta iya rabuwa da shi din yasanyashi cewa" Cutie Tunda Abba bayason mu'amularmu zan hakura na daina zuwa "wata irin zabura tayi tare da Rungumeshi tsam ta gefenshi ta zagayar da hannayenta cikinshi kamar wacce akace za a kwace mata shi tana kuka ta ce .







" kadaina cewa haka Dan Allah ni babu mai rabani dakai ko mutuwa ma tare Zata daukemu "sosai yaji dadin kalamanta cikin zuciyarshi amma Dan son Kara latsata ya sashi cewa" Bakya tsoron irin dukan da Abba yake maki banason Ana tab'amun lafiyarki shiyasa "Ni dukanshi baya mun komai nidai ka daina cewa zamu rabu daman zaka iya rabuwa dani ni bazan iya juran missing dinka ba ko Abba zai kasheni nidai ina son ganinka " ta fada tana shasheka sosai yaji dadin kalamanta A ranshi "bubbuga bayanta ya fara tare da fara Lallashinta yace.





" Sorry my cutie nima bazan tab'a iya rabuwa dakeba Kisa wannan a ranki babu mai rabamu sai mutuwa kibar kukan nan kinsan kukanki yana tab'amun Zuciya "Lokaci guda ta Had'iye kukan tayi luf jikinshi tana sauke ajiyar Zuciya kokarin Bambareta daga jikinshi yake amma ta kiya saima Kara Lafewa da tayi jikinshi tana shak'ar daddad'an k'amshin turarenshi har wani bacci bacci yake kokarin daukarta shiko bayason Yanda Aira ke rungumarshi Dan yana cutuwa amma ba yanda ya iya " A hankali ya ce "Cutie son jikinki yayi yawa " Murmushi kawai tayi ta na lumshe ido ta ce "Turarenka yanamun dad'i yaya" Ko kina so na kawo maki shi"cikin shagwaba ta ce "kamanta ka tab'a kawomun Amma ni idan na shafa banajin dad'in kamshinshi kamar ma ba shiba a jikin ka ne yake k'amshi me dadi" Murmushi kawai yayi ya ce.





"Ya Exam din fatan kina maida hankali" Alhmdllh yaya ina karatu sosai ai "yaya aramun wayarka nayi game" Ciro wayar yayi tare da mik'a mata "gyarawa tayi tare da d'ora kanta a kafad'arshi ta na game din da ta fad'i yayi mata Dariya ganin haka yasa suka fara yi tare yayi ci daya tayi daya idan ta fad'i yayi mata Dariya Shima idan ya fad'i tayi mishi Dariya idan kuma taci tayi ta mashi gwalo Sosai suka shagala Aira harta manta da wani abu waishi damuwa Dan ita daman b'acin rai bai zama cikin zuciyarta.





"Ummy ce ta shigo ita da Amma Duk.kallon Mamaki suka dinga kallonsu dashi Ummy dai tab'e baki tayi ta zauna Amma ko mamakin irin taurin kai iri. Na Aira take " Amma ce ta gaisheshi ya amsa yana mata dariyar ya fad'i Inna ce Ta shigo tsaki taja ta ce "Ohni Halima ina ganin rayuwa yaran zamanin nan baku San ta ido ba wlh ayi yara baku da aiki sai Rungume Rungume da tab'e tab'e kai nidai Na kusa korarku wlh a daina shigomun Bangare ehe akanme" ta k'arasa fad'a tana zama tare da Mike kafa "yi sukayi kamar bada su take ba saima cigaba da game d'insu sukayi " inna Haushi ya cikata ta tashi tace "ku tashi ku fita tare da nuna musu hanya turo baki Aira tayi ta ce " kedai tsohuwar nan baki son zaman lafiya me aka miki kuma"Ubanki akamun ku tashi ku fita nace "Bazamu fita dinba ki daukemu ki fiddamu ta fad'a tana murguda baki "





Salati inna tayi tare da Goge hawaye ta ce "Ni kike zagi Hajara kai albasa batai halin ruwa ba baki biyo halin mai sunan ki ba Y'ar uwata ba haka take ba kai amma ma wlh an cuceta da aka saka mata sunanki kaico Adda Jaru Allah ya jikanki yasa kina cikin rahama ke kuma bari inje nafadawa ubanki kina zagina " Jin hakan ya sanya Aira saurin tashi tare da ruko hannun Inna Dan tasan ta kaita wajen Abba ta kade Ta ce .





"Haba my lovely grandy wasan jika da kaka ne fa ni ina ni ina maki Rashin kunya waya haifeni a garin nan" Inna ta tsuke baki tace "ba wani dad'in baki da zakimun " ta kama hanyar fita tayi Sauri ta bita Tare da ruko ta ta ce "Inna dawo zan baki Zumar turawa wlh ai kina so ko" Lokaci guda Inna ta saki fuska ta ce "da gaske kike y'ar nan " Eh mana inna da gaske Amma saikin dawo saikin fasa zuwa"juyowa inna tayi tana washe baki ta ce "Daman ai wasa nake maki y'ar albarka ai duk cikin d'iyan Habu ke kika fita zakka ba kamar waccen Zakalkalar bata da aiki sai latsa waya Ko y'ar halawa bata tab'a kawomun ba .





" ta fad'a ta na kallon Ummy Aira ko Dariya hada rik'e cike jin an tabo ummy itako Ko kallon Inda inna take bataiba saima cigaba da chat d'inta da tayi Arman dukda bai fiya Dariya ba saida ya d'an dara jin irin dramar da inna da Aira sukesha Bayan Aira ta kawowa inna coculate din Arman ya tashi ya ce "Cutie zan wuce " Kamar zatayi kuka ta ce
Showing 3001 words to 6000 words out of 33558 words