miyah,da haka zanyi tayi ni kaɗai,tunda naso ta dunga rakoni amma ammi bata maida hankali da zancen ba,sai yanzu da tasan dole zan bar gidan ai gashinan ta haɗani da ita koh.
Jinayi an yafato hijabi nah ta gefe,dama kuma naji hayaniya a kasuwar,dan dai bana ganin mai yake faruwa ne saboda mutanen dasuke kaina.
Juyowa nayi na kalli indo wacce muke zama rumfah ɗaya,saidai ita gwaten doya take kawowa.
Idanunta a zazzare take nunamin wani waje da yatsunta.
"Ke Sumaimah kalli gacan goje agonki zai sokawa wani wuƙa"
Wani dummm gabana ya bugah,cikin firgici na kalli inda hannunnata ya nuna. Daidai kuwa lokacin da ya burma wuƙar a cikin dattijon daya cakwane wuyan rigarsa a tsakiyar kasuwar.
Wani kaɗawa hantar cikina tayi take na fara jijjiga kai kaman wata ƙadangaruwa,ba fah kuma mafarki nake ba koh,dagaskene wani a kashe a gabana akan idona.
Jini ne yafara feshi daga cikin mutumin ya wanke hannun gojen wanda yake riƙeda wuƙar a hannunsa,kowa yaga abinda ya faru,amma kuma tsoro da firgici bazai bar mutum ɗaukar mataki ba.
Bayan ya sakeshi ya faɗi kafin mutane suka riƙoshi aka nufi asibiti dashi.
Hannunsa ya yarfe yanda jini ya wankeshi sharkaf,wani ne daga gefensa ya miƙomasa tsumma,shima da alama ɗan iskanne kuma yaron sane,dan kansa sai kace gonar ayah,anyi wanann abin da suke cewa dadah.
Jikin wata katanga ya samu a gefensa ya zauna tamkar bashine ya ɗauki rayuwar wani ba,ko nace lafiyar wani.
Tabar wiwi aka miƙomasa ,wani kuma ya kunna masa ashana,buuuu hayaƙi ya turnuke fuskar tasa,baka ganin komai sai gashin kansa mai kama da ciyawa a tsatstsaye.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ai a zaune take wani satin i yanzu ƙasa ta rufemin ido,gwanda ma tun daga yanzu nafara bankwana da mutane ina neman gafarar su,danna san ana kaini gidan wannan azara'ilun duniyar tofah saidai sunana kawai dazai saura a doron duniyah.
Indo ce ta watsamin ruwa a kan fuskata,sai sannan tayi firgit na kalleta.
"Wayyo Sumaimah lafiyar ki kuwa,tun ɗazu nake tabaki amma ko motsi bakyayi,saida na zuba miki ruwa kafin kika dawo hayyacinki"
"Iyee ...uhm inaga suman zaune nayi,me...uhmmm"
Kasa ma ƙarisa maganar nayi,dama kuma bansan bai zance ɗin ba,dan gabaɗaya notin kaina ya kwance.
"Nasan mai yake yawo a cikin kanki,amma ki kwantar da hankalinki,bazai taba kasheki ba sai kwananki ya ƙare,wancan ba naji ance wai cunensa yayi ga cibiyar tsaro cewar dashi a fashin da akayiwa gidan gwamnati,amma in bahaka ba bai cika kisa akai akai ba,nina sanshi ai anguwar mu ɗayah"
"Hmmmm indo kenan,so kike nace na yarda da maganarki ko mai,kawai dai kina faɗane dan na kwantar da hankalina,saidai wannan batun babu ma shi,dan raina ya daɗe da tashi ya tsaya,inaga kuwa bazai taba sake komawa ya kwanta ba har zai sanda azara'ilu ya zare shi"
"Haba Sumaimah kar kice haka mana,ba kyau mutum yayi ta zatawa kansa mutuwa fah"
In jinta tana ta daɗin bakinta amma ban bata amsa ba,idona nasake mayarwa wajen da goje yake shida mutanensa,dan bana tunanin zansake sakewa nayi abinda ya kawoni,jikina ma yayi sanyi da zuba abincin,Asiyah ce take ta zuba Musu,dan in sunyi magana ma ba jinsu nake ba,saidai nace uhm uhmuhm.
Har zuwa yanzu tabar hayaƙin yake shaƙa bai daina ba,saidai babu hayaƙin kaman na ɗazu,dan kana iya gano dodanniyar fuskarsa ma daga nesa.
Karaff kaman abin rashin sa'a muka haɗa ido tashi.
Wayyo bammasan mai nakeji a cikin zuciyata ba a lokacin,gashi kaman abun tsafi kokuma nace ya riƙemin idanuwa na gagara ɗaukewa,wani irin hargitsi nake ganowa a cikin idon da babu ɗigon salama a cikinsu,raina banda kuwwar neman tsira babu abinda yake.
Wata ƴar jarumtace ta gifta mun,wacce tasakani saurin ɗauke idona daga cikin nasa,wayyo nasan shikenan sai ya yanka ni,wayyo wayyo shikenan ya kamani ina kallonsa,nasan irin wadannan mutanen kuwa basaso a kallesu shikenan tawa ta ƙare.
"Sumaimah kingani yaronsa Tunga yana tahowa nan wajen,kuma da alama wajenki zaizo,dan ke yake kallo wlh".
Meee shikenan ta faru ta ƙare,indo ke tauraro mai wutsiya ce,bakya faɗan abin alkhairi.
Zuwa zayyi ya fizgeni yakaini wajensa,nima ya yankamin hanjin ciki kaman wancan mutumin.
Da ƙasan ido nake kallon wanda aka ƙira da Tunga ɗin,kuma dagaske inda nake yake nufowa babu makawa........





Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[06]



[Goje a mahangar gani]

Kwanannan ban san mai yake damuna ba,amma baƙinciki nakeji a cikin raina,duk yanda zanyi shaye shaye bana jin zafin zuciyata yana sauƙata,raina jini yake so na dunga ɗauka a koda yaushe. Hakan yake raɗamin a kowanne lokaci.
Yanzuma wannan mayaudariin daba maganinsa nayi ba yau bazanyi bacci ba,mutane gani suke kaman shune na dayayi shine yasaka na yanke masa hanji ,basu san shiɗin muna fikin ƴan fashin makwantanmu ne ba.
Zanyi fashi zan ɗau jini a garinnan,amma bazan bar wani daban yazo ya kafa tasa kujerar ba,saboda wannan garin nikaɗai ne,idan ba goje ba to kuwa ba kowa.
Duba inda nake tara dattin tabar hannun nayi,abin ya ban mamaki danaga na tara har kusan kwarkwaro bakwai,da duk yanayin danakeji daga na shata nakeji ya sauƙa,amma yanzu baya sauƙa sai nasha dayawa tukunna..
Magana naji Ragarus yanayi,banji abinda yace da farko ba,iya ƙarshen kawai na kama.
".......itace fah wacce ogah zai aura wani satin"
Inda idonsu yake kallo nima nakai nawa idon,da wata farar yarinya na haɗa ido. Abin yabani mamaki yanda ta tsaida idonnata cikin nawa,dukkuwa da yanda nau'ikan tsoro suka bayyana akan ruhinta. Ban ɗauke nawa idon ba,dama abune da bana tunanin na tabayi wa wani a rayuwata,wato ɗauke ido,bansan wata abu wai ita kunya ko tsoro ba,wannan abubuwa banida su a halittata..
Ɗauke idonnata tayi tana diriri,kaman an kama munafuki,haka kawai sainaji dabani dariyah,kana ganinta kasan tsoro ya cikata da haɗa idon da mukayi.
"Ogah barina je na siyo maka abinci a wajenta,kaga saikaji ma ko yana da daɗin da inta dafa zaka iya ci,ko ya kace"
"Zancen banza kenan kaidai kawai kace bari kaje kasamu damar yi mata magana kuma ta zubamaka na bati,kafi kowa kuma sanin banason raini. Dan haka idan kaje karma ka ambaci sunana a wajen"
Juyawa nayi na cigaba da tunanin dayake cikin kaina.
Inaji yana mayar masu yanda sukayi da ita,wai daya tambaya daƙyar ta faɗamasa sunanta saboda tsoro.
"Sumaimah"
Na maimaita a raina danaji ya faɗa,hmmm ina tausaya mata inta shiga shirgina,indai zata kama kanta to babu ruwana da itah.

Ƙarar jiniya naji na ƴan sanda,ina jin su Tunga suka tashi  tsaye,so suke nace musu mu tafi kaman koyaushe,saidai yanda na jingina da jikin katangar banason na tashi.
Muryar DSP ce ta ziyarci dodon kunnena,hakanne yasaka ni dagowa na kalleshi.
"Goje abubuwan da kake a garinnan kare bazai ciba,dan haka ka biyomu ofishimmu yanzunnan kaida yaranka,dolene ka fuskanci hukunci,sannann kuma ka biya tarar mutumin daka buɗewa ciki. Babu wanda yafi ƙarfin doka duk shu'umancin sa"
"Hannu ɗayane kawai ya soka masa wuƙa,kuma wannan hannun na gojene,dan haka a dokance iya gojene zai biku kawai koh,don haka muje.
Kai Tunga ko zata mutu ko kuma tayi rai to a ƙaddamar,in kunji lafiya ku sama ta gora kawai"

Murmushi nayi lokacin dana shiga motsar ƴan sandan,idon DSP yayi zuru zuru,da alama ya ankare da saƙon dana aikawa su Tunga.
Kishingiɗa nayi a cikin mota kafin a isa,har bacci ya fara ɗaukata.Duk daren duniyata yanda naga ranar haka nake ganin daren,musamman ma idan na taimaki wani,kokuma wani yayimin abu ban ramaba,narasa mai yasa nake haka,shin kowa haka yake ko kuma ni kaɗaine tawa halittar daban.
Amma yau kam tunda nayi abinda rannawa yakeso to da alamar zan iya samun bacci.
Saida naji motar ta tsaya kafin na tashi zaune,dama bacci nake so nayi inda wadancan yaran bazasu takuramin ba,haka ma inna a gida,tunda zan kwana a wajen sai nayi ta bacci babu wani shedule a kaina.
Suna buɗe bayan motar na nufi ɗakin danake zama idan na biyosu,babu wanda yafi doka injisu da faɗa,to gashi na kawo kaina amin hukunci.
Maganar DSP naji yana yiwa wani ɗan sanda da muke tafiya tareda shi,hmmm su gama abinsu ma,daga ƙungiyar BC(black cobra) sun dawo gobe da yarjenjyata ta shiga ƙungiyarsu,to bazasu sake gani na ba ma,nasan zuwa lokacin nafi ƙarfin wannan kurkunnasu,duk da yanzu ma zancen manyan garine yasaka nake biyosu,amma wannan shine na ƙarshe,shiyasa nazo nayiwa wajen bankwana.
"Kai copur wannan abinda ake yi masa ya ƙare daga yau,ku kaishi cell ɗin da ake saka mai laifi irinnasa,sannann gobe a miƙashi ga kotu,dan ƴan uwan wanda ya sokawa wuƙa sune suka kawo ƙara,kuma sunce kotu zasu kai ƙarar"
Da nayi niyyar na ƙyalleshi na wuce,saidai kuma zuciyata bazata iya ba,in ba gargaɗi nayi masa to bazanyi baccin danake mararin yi ɗin bama
Dawowa nayi da baya har zuwa inda yake tsaye,da wani tulelen cikinsa a cikin rigarsa,an bubbunka haram ciki ya nuna alama.
"DSP sambo in kana cin ƙasa kasani  ka kiyayi ta shuri,babu ruwana da wata ƙara dazasu kai,abune ya haɗani dashi shiyasa nayi masa hukunci,da kunsan abinda yake muku a garinnaku ma da godiya zaku min.
Sannan da kake wani tada ƙayar baya nasan biyanka kuɗi sukayi koh? In mutum yasamu kuɗi kuma iyalansa yake tunkara dashi. To in kanaso suci wannan kuɗin cikin lumana,ƙaramin yaronnan ya dunga zuwa makaranta da ƙafafunsa,sannan wannan ta gidan kar ta haihu lokacin ta bayyi ba.
Shi dana sokeshi ya rayu bari muga in muka mata tiyatar cikinta zata rayu?....."
Cikin sigar jan kunne na ƙarisa maganar ina jaddada masa gargaɗinnawa da idanuna,aikuwa hakan yayi aiki,dan lokaci ɗaya gumin tashin hankali ya lullube jikinsa sharkaff..
Bansake bi takansa ba na nufi ɗakin dana ke sauƙa innazo,har copur ɗin ya buɗemin ƙofah.
Ai wannan mutumin dan basu san sharrinsa bane da kuma makircin daya haɗamin harma da garin gabaɗaya,dana kasheshi ma da sai hakan yafimin daɗi.wawaye duk a zatonsu harda ni a lalatacciyar satar da aka yi musu,sun raina aikina ma da alama.
Mutum yayi sata a garinnan ko ya kwashi tsiya,inda ma kajine ko akuyah idan za'ayi gashi da sauƙi,amma kuɗi kan basuda wannan arziƙin..
Ina nan kwance akan katifar ɗakin har bacci ya ɗaukeni.

           __***__


Tarin bola ce tsiri guda kaman zata dabo sama,da alama duk faɗin birnin garin anan suke tara tarkashen sharar.
A can cikin bolar saika kula ga hango motsin mutane ledodi sun lullubesu,suna nan kwance har yanzu basu tashi daga suma ko baccin wahala ba.
Malam audu ne yafara buɗe idonsa tareda ture ledar da take kansa,waya sani ma kota kashi ce.
Tashi yayi daƙyar ya zauna yana nishi,saboda tsamin da jikinsa yayi.
Gabas ya kalla kana da yamma,mai kuma suke a tsakiyar bola da ranar Allah.
Zaro ido yayi lokacin daya tuno izayar da suka sha a jiya a gidan dasuke aikin.
Gefensa ya kalla inda gaji ke kwance shame shame akan wasu tsummokara,saikace mahaukaciyah.
Ƙoƙartawa yayi yakai hannunsa ya kwaɗa mata duka a kunkuminta,aikuwa ta saki azababben ihu tana wangale baki.
"Wayyo wayyo kunkumina ku taimakeni jama'a zai cire"
"Ke dallah tashi mubar wajennan idan zamu iya tashi,waɗancan dangin fir'aunan bayan gari suka kawomu cikin bola"
"Bola kuma wacce iri"
Itama ta yunƙura tana kallon tsummokaran da take kai"
Motsin Atika da sukaji a gefensu ne ya sakasu waiwayawa,kuma gaji ta fasa faɗin abinda yazo bakinta.
Kuka take tanan kururuwa kaman a cikin bacci,da alama abinda yafaru jiyanne yake dawo mata.
Jijjigata gaji tayi cikin baƙin ciki,dan koma mai yafaru ai ita ta jawo musu,da yanzu sun gama aikace aikacen gidan suna karyawa da lafiyayyen abinci.
"Shegiyar yarinya mai ɗuwawun bin maza,ai gashinan abinda kika jawo mata,in sonsa kike tun farko da ki faɗamin mana asan surkullen da za'ayi,amma daga ke har ubannaki dayake garorine ku kagu jimanaye kunga kuɗi,sai karba kawai kuke bakwa tunanin mai ya faru. Ban tashi sanin mai yake faruwa ba sai ranar dazan sha duka tukunna.
Sai ku tashi mu tafi ai .......ahhh......."
Shuru tayi tana jujjuya kunkumi,dan dama sojan kunkuminnata yayi ta sambaɗawa kulƙensa.
Hararar malam audu tayi dayayi mata sannu,yunƙurawa tayi ta shi kana ta tashi sauran yaran wanda suke baccinsu hankali kwance.
Bayan sun tashi a wajen tafiya suka farayi zuwa tasha,kowa sai komaɗewa yake yana tafi kaman horon cikin film ɗin mayu.
Duk inda suka wuce kallon su ake,amma ko a jikinsu,tsamin da ƙashushuwansu suke ma ya isa.
Sa'ar da sukayi daga inda suka zubar dasu bashida nisa da tasha,saidai kuma ba a nan gizo yake saƙar ba kuɗin motar komawa garinnasu ne aiki.
Tun safe suke tashar har yamma,ganin bazasu samu mota ba yasa suka samu wani waje a tashar suka zauna.
Hayam hayam kowa sai baza hamma yake kaman zaici babu,idonsu yayi zuru.
"Yanzu kana gani zamu mutu bazaka nemo mana abinda zamuci ba,huhulahu kawai"
"Wai nikam gaji meyasa tunda kika shi a cikin bolar nan ni kike sauƙewa tujara,ya isheki fah haka,wlh zan sake mangareki ba ruwana da ciwukan da suke jikinka"
"Hehehe to ko sun duka ƙwalƙwalwarka ne take faɗa maka zaka iya dukana iyeee,kalleka fah kaima a doddoken kake ba iya ni kaɗai ba,ƴan ƙafafunka ma daƙyar kake ɗagasu sai kace lagwani. Kaff danginku haka kuke sai kace ƴaƴan kunika,zama dakai yasa duk ƴaƴana haka suke ƙafafu kaman liƙo cikin kuwa kaman randa,ni ba abinna zagesu ba kaima haka kake. Shiyasa nake mamakin ya akayi goje yakeda ƙira da ƙarfi,ubansa da uwarsa ba haka suke ba,har Addu'a nake ko ƴaƴana zasu iyoshi,na huta da aikin kashinsu da yawa,yaro in ka haifeshi bazayyi tafiya ba sai ya shekara uku tukunna wani abin ma..........."
"Dan Allah gaji kiyi shuru haka,dan Allah ku bar faɗannan sai munje gida,kowa sai kallon ku yake"
Kaman tayiwa dutsi magana ko kallonta basuyi ba,wata harara malam audu ke yiwa gaji kaman idonsa ya fito,dan yaji zafin wannan wankin babban bargon da tayi masa a tasha.
"Hmmm ke yanzu har zakice ma danasanin aure na kikeyi,daɗinta ma mu gidanmu ba mayu bane bama tanɗe kuruwar mutane,kowa yayiwa wannan ubannaki shaidar ko tsuntsune ya gifta da kan gidanku sai ya tanɗe kuruwarsa. Bandama ƙaddara data haɗani take,kaff abokaina da ƴan uwana babu wanda yayi na'am da aure na dake,nima kaina bansaniba ko tanɗeni kikayi"
"Hhhhhh narasa mai zan tanɗa inma maitarce sai kuruwarka,ko ban tanɗe ta bama a tanɗen take,dan daga ganinka yanda kake haka ma kuruwar taka take"
Tashi atika tayi tabar wajen,kowa sai kallonsu yake amma su babu ruwansu,ina zatakai wannan abin kunyar,wai dama haka auren yakene,kowa na ganin hanjin kowa,shiyasa fah ta tsani aurenma ita a rayuwarta,tafiso kawai a hole in holewar tazo a wuce wajen.
Tana cikin tunaninne taji muryar wani ɗan garinsu. Juyowa tayi suka haɗa ido da tasi'u,shima da yace yana sonta,kayan gwari yake kawowa daga garinnasu zuwa nan,dama sana'arsa kenan.
"Lahhh tasi'u kaine"
"Ehh nine atika mai kike anan wajen ga jikinki duk ciwo?"
Inda inda tafara na ƙaryar dazata yimasa,can kuwa wani abu ya faɗo mata a rai.
"Uhmm dama gida zamu tafi to shine jiya barayi suka shiga mana gida,bayan sun ƙwace komai kuma suka yimana duka"
"Innalillahi garin ya haka,in su malam ɗin suke,dama tafiya gida zanyi ko zakuzo mu tafi kawai,saidai zamuyi dare a hanya saboda motar tawa batada gudu"
"Babu komai hakanma mun gode,barina ƙirasu toh"
Wajen iyayennata ta koma,zuwa yanzu sun daina faɗan kowa ya karyar da kai yana nishi na wahala da yunwa.
Lokacin data faɗamusu yanda sukayi da tasi'un ba ƙaramin murna sukayi ba.
Biredi ya siya musu da zobo irinna ɗurawar nan ganin sun fita hayyacinsu.
Kaman almajirai kuwa haka suke turawa a cikinsu,kowa so yake yayi maganin yunwarsa. Banda ruwan albarka babu abinda suke masa,kaman basune sukayi masa cin mutunci ba dayace neman auren atika,a ganinsu shi ba sa'anta bane,yanzu gashinan babu kunya suke masa godiya daya taimakesu.
(Shiyasa a duniya ba'a son kaci mutuncin mutum ko ya yake kuwa,saboda Allah ne kaɗai yasan ranar da zai maka rana,a lokacin da bakayi tsammani ba. Allah yasa mu dace dai.)
Daff da magriba suka kamo hanyar garinnasu,tunda suka tafi wata shida sai yau zasu koma,dama ance in daɗi bai kawoka gida ba wuya ai zata kawo ka.
Shuru sukayi a cikin bodin motar a tsakiyar kayan miyan da bai siyar ba,sai wulla ido suke,ga motar batada gudu ko kaɗan,ko yaushe zasu isa oho.
Kaman a sama sukaji muryar tasi'un yana tashinsu,abin kunya sunyi bacci duk sunyi rugu rugu da tumatir ɗinsa,wani abinma hadda taruhu da tattasai,gasu da ɗanyen ciwo a jikinsu.
Banda mutsu mutsu da nishin azaba babu abinda suke.
Motar ba wani tudu bane da ita,amma saida sukayi dagaske kafin suka iyah fitowa,ko tsayawa yimasa kyakykyawar godiya basuyi ba suka shige gida,dan basa cikin hankalinsu.
Lokacin gari duru duru yake ana shirin ƙiran assalatu.
Inna mairo ta fito da butarta zata shiga banɗaki sai ganin mutane tayi sun shigo gidan,salati tafara jiki yakama karkarwa,dan tayi zaton gamo tayi,saikuma ta kula ashe su gaji ne
"Gaji kuma?"
Tafaɗa cikeda mamaki.



Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[07]


Butar hannunta ta ajiye tana kallonsu,sune kuma da gaske,tayiwa kanta wannan tambayar.
"Gaji kune da asubar nan haka,mai ya faru kukayi wujiga wujiga haka?"
Bude baki tayi zatai magana ƴar ta ƙarama ta rigata,tunda su ba ciwo a jikinsu.
"Yaya ce tayi soyayya da Alhaji,shine wasu sojoji sukayiwa su baba duka suka jefarmu a bola"
Kunya ce takama su kaman zasu nutse a wajen.
Saurin wayancewa inna mairo tayi,musamman ganin yanda gaji ke kallon ƴar tata farida kaman zata cinyeta ɗanye.
"Ohh to Allah ya tsare gaba,yanzu kuzo ku zauna,barina fito daga banɗaki na haɗamuku ruwan wanka kuyi mamatsa jikinku."
Cije baki gaji tayi,so take tayi magana amma kuma tana tsoron kar inna mairo ta hana su ruwan kaman yanda tayi niyya.
Kafin gari ya waye duk sun wanke jikimsu sun sanja kaya wanda inna mairo ta ɗauko musu a sashennasu,dan ko ɗakinta basu bariba tun asubar,bare su taka cikin gidan suga mai ya sauyah.
A daren tayi musu abinci mai sauƙi sukaci,hankalinsu ya dawo kansu.
Da safe kuma tasiyo musu burofen da masu shago suka buɗe.

Gaji ce tafito daga ɗakin tana kallon gidan,babu abinda ya sauya a cikinsa,saima fess da yayi kaman bashine sansanin shirgi ba lokacin da suke nan. Ƙofarsu ta nufah domin taga mai ya sauya,tun kafin ta ƙarisa tajiyo kukan saniya,abinne yabata mamaki,saniya kuma a ƙofarsu?.
Turus tayi ganin kewayen ƙofar tata cikeda abincin saniyar da kuma kashinta,wajen sai kace kewayen dabbobi.
Cije baki tayi tareda ƙiran sunan goje da ƙarfi har ƙasan maƙoshinta.
"Gojeeeeeee!!!"
"Na'am"
Taji ya amsa a bayanta.
Wani dum ƙirjinta ya doka saboda firgici,dan
Showing 9001 words to 12000 words out of 60324 words