ƙasa,idan itama bazaka iya da ita ba to saika shafi jikin gini mai tsarki kayi dashi.
Toh a wannan bayanin kaga kai zaka iya yin alwala kuma kayi sallah a zaune"
Bayan gama bayanin bai ce komai ba,amma ya miƙomin hannayensa na fara yimasa alwalar. Cikin nutsuwa nake yimasa alwalar har na gama tsaff.
Rigar dana zo da itah na taimaka masa yasaka,yanda bazata shafi ciwon ba,kafin na juyashi ya kalli gabass,magriba yafarayi wacce ake binsa kafin ya fara da rama sallahr asuba tun sanda aka jimasa ciwo.
Daki daki yake bin sallahr ina zaune ina kallonsa,daga baya daya gaji sai na koma ta baynasa ina tallafamasa. Muna daɗe a haka har akayi sallahr isha ya tsaya da ramakon yayi,ganin yana haki yagaji yasa ya tsaya dayi sai ya huta tukunna.
A bayansa nake ya jingina dani,saiji nayi ya kwanto akan cinyata,kallon fuskata yakeyi,yayinda nima na sunkuya ina kallonnasa,mun daɗe a haka idonmu a sarƙafe dana juna,saida naji hannunsa akan fuskata kafin na dawo zahiri..
Magana yafara a cikin wata murya da banyi tunanin yanada itaba.
"A ɗan zamana dake kin taka wata rawa a rayuwata,ko yaushe cikin juyewa kike da narasa taya zan misaltashi. A lokacin danake son naga kin sake dani saiki ɗankware jikinki,lokacin danazo yimiki barazana kuma saiki dake,idan nayi laushi kuma sai zama jaruma,a yau kaɗai kinyimin abinda ban taba tunani ba,kin zamemin hannun a sanda na rasa nawa,kin zamemin ƙafa da tawa taƙi aiki,kin zauna dani a wannan dokar dajin da babu kowa a ciki saini kaɗai.
Tun farkon da mahaifinki yabani ke a matsayin fansar kuɗina naga rashin dacewarsa nayin hakan,shiyasa na nesanta kaina dake,a tunanina hakan zaisa kiyi rayuwarki yanda kikeso,naƙi shiga rayuwarki saboda nasan nida ke bamu dace ba ko kaɗan,amma sai naga duk wannan koƙarin danake yatafi a banza,ke koyaushe so kike ki cusa rayuwarki cikin tawa.
Wannan ƙasa da kan da kike idan kina gabana,da kuma neman izinina a duk wani lamari na rayuwarki shine yayi babban tasiri wajen karya zuciyata,har tasaka na ajiye komai na ɗauki nauyinki batareda nasani ba. Saboda tunda nake babu wanda yazo da kansa yanemi izinina akan abu,saidai na bashi dakaina in kika ɗauke Tunga.
Sannan tun kina zuwa inda nake ina jin kin takuramin,har yazamo idan banganki ba sai zuciyata tayi ta kewarki. Sumaimah bansan mai kikayimin a rayuwata ba amma dai shigarki kinyi nasarar share wani a fili a ciki kin mamayeshi yazamo naki. Ciwon kan dana tashi a rayuwata bansan lokacin dana faraba,bai taba dainawa ba indai ba shaye shaye nayi ba sai yau,kuma dama yakan tashi ne idan na bijirewa umarnin da zuciyata tabani,saikashi yau kin karanta min wani abu naji ya tafi batareda nasha komai ba"
Tunda yafara magana ban ɗauke idona ba daga kan fuskarsa,shin anya kuwa gojen danasanine yake waɗannan kalaman,meyasa yau ɗaya naga wata nutsuwa a tattare dashi,babu wannan zazzare idon da kuma cije cijen baki..wannan gashin daya maidashi dodo duk babu shi. Kar a ji haushina idan nace yayimin kyau fiyeda mutane dayawa a garinnamu.
Hannuna nasaka akan nasa wanda yake kan fuskata,tareda sakin wani murmushi da bansan ma'anarsa..
"Duk abinda kake faɗan nayi aikata a rayuwarka banice nabaka wannan matsayinba,Allah ne dakansa yabaka a matsayinka na mijina,ni kawai umarnin da aka bani na nayi maka biyayya,kada nayi wani abun batareda saninka ko kuma yardarka ba,sannan na kyautata maka na kasance sassanyar inuwar dazaka zo ka hutas da gajiyarka,na kasance tamkar dare wajen rufe sirrinka,sannan na kulada kai da dukiyarka harma da dani kaina idan baka nan.....domin aljannata tana ƙarƙashin ƙafarka,sai nayi hakanne Allah zai bani izinin shiga"
A yanda nake kallon idanuwansa lokacin danake faɗomasa wadannan Kalaman,naga Abubuwa da dama wanda wasu bazan ce mesuke nufi ba. Kawai naga yashiga mamakin,shin dama ashe yanada irin wannan matsayin a rayuwar wani,kaman nasan mai yakeson faɗa na cigaba da bayanina.
"Tabbas hakane kanada wannan matsayin a rayuwata tsawon lokacinnan,koda wasu zasu gujeka suyi nesa dakai. Ni kaiɗin jigona ne,kuma mahaɗin rayuwata,wanda rayuwata ta riga ta ɗinke da taka tun lokacin da ɗauramin igiyoyin aurenka a kaina,shiyasa duk abinda zakayi wanda bai dace ba zaifi yimana ciwo nida inna sa'banin sauran mutane"
Hawayen daya zubo acikin idona ne ya sauƙa akan kumatunsa,sai sannan ya ƙifta ido,da ya tsaya tamkar wanda ya daskare a cikin ƙanƙara.
"Shin dama har haka na shiga rayuwarki,nayi tunanin dan an ɗaura aure ban kulaki ba bakomai,to idan harda waɗannan haƙƙunan da suke kanki wanda dole saikinyimin kenan nashiga rayuwarki dayawa,na rabaki da rayuwar da kike hankalinki kwance idan babu ni a ciki..kinmin abubuwa da dama,dan haka banaso ki cigaba da zama kina amsa sunan matar mutum kamanni,musamman daya kasance kinada ilimi mai yawa da kuma sanin yakamata,zalunci ne na ajiyeki a cikin rayuwata...zan sake..........".
Kiff bansan lokacin dana rufe masa baki ba ina jijjiga kai.
"Karka fara faɗin wannan kalmar,dan Allah karka furtata a gareni,da lokacin daka aka kawoni gidanka ne ka faɗaminsu zanyi farinciki da jinsu,amma a yanzu dana fahimce ka bana fatan jin wannan kalmar daga gareka,karka faɗesu ka fiddani a cikin rayuwarka"
"To amma meyasa naga......"
"Saboda na hango wata rawa danake son takawa a rayuwar taka,hmmm bazaka sani bane amma kanada wani hali da mata zasu zaga mazaje dayawa basu samu mai irinsa ba,duk da sunaso su samu ɗin. Kai tamkar zinarene a cikin duhun dare,rana bata haskashi na ballantana a gane wanne irin haske yake ɗauke dashi.....koda babu hasken rana ka bani dama nazamo fitilar dazata haska shi,ta yanda kaikanka zaka hango irin hasken da kake ɗauke dashi......dan Allah ka yarda dani,sannan ka bani damar ragamar kulada rayuwarka,kar nesanta ni daga gareka,ta hakanne zamu gano inda matsalar take kuma mu gyara.....ni har cikin zuciyata na amince dakai a matsayin mijina,kuma bana fatan naga ranar da zanyi nadama da ƙiranka da wannan sunan"
Magana nake kawai ina kwararowa abinda yake cikin zuciyata,duk da yanda muryata ke rawa saboda yanda maganganun suka tabani.
"Tunda nake ban taba yin alaƙa da wata mace ba bayan inna sai ke,a da hakan haushi yake bani,amma d kaɗan kaɗan nakejin wani abu na mannani da rayuwarki. Yanzu ma dakikaji na faɗa bawai son raina bane,saidan zanyi hakanne saboda ke,amma tunda kinji kingani ra'ayinkine zaki zauna tareda ni. Nikuma namiki alƙawarin bazan taba guje miki ba,kuma zan kyautata miki na faranta miki daidai yanda zan iya,sannan kaman yanda kika buƙata nabaki jan ragamar dukkan lamurana"
"Naji daɗin maganar ka kuma nagode,nima kuma nayi maka alƙawarin Inshaallah bazakayi danasanin yarda dani ba"
Shuru ne ya ratsa tsakaninmu,saikuma naga ya jare hannunsa daga fuskata yana riƙe kai. A yanda na kula kaman irin abinda yayi jiyane,hakanne yasa na ɗauke hannunsa na mayeshi da nawa.
Addu'o'in danayi jiya na neman sauƙi nafara karanta masa,wanda yawanci sunayen Allah ne da yayi umarnin a ƙirashi dasu,sai fatiha da kuma su QUL guda uku.
Maimaita masa nashigaba dayi bayan naji yayi shuru ma,a haka har nima bansan lokacin da baccin ya ɗaukeni ba anan zaune.

___***___


"Me kikace abbanku ya dawo?"
Hajiya Maryam tafaɗa cikeda damuwa tana kallon fatee.
"Ehh mommy yanzunnan ya shigo gidan,naga ya nufi sashensa bai shigo cikin gidaba"
Tana cikin bayanin hajiya maryam tanufi sashennasa tana tafiyar karairaya kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƙwanƙwasawa tayi,jin shuru ba'a amsaba yasa tasaka kai cikin ɗakin.
A tsaye yake a gaban window yana kallon lambun dayake bayan ɗakinnasa,kana ganinsa kasan faɗawa yayi cikin zurfin tunani.
"Me yasamu wannan babban jarumin naganshi a haka,kaddai kacemin har yanzu baku samu inda barayin sukeba,kuma sun gudu da akwatin baku kamasu ba?"
Tafada kaman mai jin tausayinsa,amma kanaki kasan ta biyu take zancen.
Zan ajiyar zuciya A.M Aliyu yayi tareda cewa.
"Maryam,waishin yaushe zaki girma ki daina wannan abunne kam iyeee,ƴaƴan ki ma bazasuyi abinda kikeyi ba,yanda kikeyi haka kikeso ƴaƴan ki suje gidan mijinsu suyi ne? Ace tsawon sati guda ba nan ina office,duk akan wani abu daya shigemin duhu,amma daga dawowata babu magana mai daɗi sai ta izgili? Shiyasa fah banshiga gida ba bare ki ganni,amma saida kika biyoni kina murnar na faɗi koh ?"
"Uhm dagajin yanda kake magana baku kamasu ba da alama,kenan wannan akwatin dayake ɗauke da bayanai masu hatsari yana hannun 'baya gari"
Juyowa yayi yana kallon hajiyah maryam,wacce take tsaye ta dan goce irin tsayuwar celebrity ɗinnan.
"Shin wai tukunnama taya kikasan cewar kundin a akwati yake,a tunani na dai bamuyi wannan zancen dake ba,kuma ko a kafar yaɗa labarai ba'a faɗa ba,taya kika sani?"
Tsareta yayi da ido tareda yimata kallon tuhuma,wanda hakan yasaka jujjuya ido tareda cewa.
"Ehh dama zaka fara yanzu,dan kasamu ma na kula dakai nazo ina tambayarka shine zaka faramin wannan kallon rashin yardar,tun batan Ahmad kakemin irin wannan kallon na rashin fahimta"
"Ohh dama 'bata yayi ba mutuwa yayi ba?"
Gum tayi da idonta tareda nemo abinda zatace.
"Mutuwa nakeso nace,kaima ai kasan mutuwar yayi tunda har gawarsa an kawo maka. Nida wannan abinda kakemin na ƙin raba sirrinka dani kokuma kana tuhumata ka daureni mana kawai ka huta iyee. Kaje cibiyar bincike kace zaka ɗaure matarka dayafiye maka"
Masifah ta cigaba dayi,ta inda take shiga ba tanan take fita,saida tayi mai isarta ta fice daga ɗakin tareda buga ƙofar.
Runtse ido AM Aliyu yayi tareda ɗora hannunsa a kansa.
Yana jin takun tafiyarta har tayi nisa.
Shin me yayi mata kuma wai itace dayin fushi,shine ya kamata ya ɗau mataki amma duk sanda yayi yunƙurin yin hakan sai yaji ya kasa.
Gabaɗaya gidan mutane uku ne za'a ce daidai,daga Mammah,saleem sai Noor,su kaɗaine zaka gansu da sanyin hali. Amma Sameer kam da fatee kana gani kasan ita suka iyo. Shikuwa Ahmad lokacin dayake nan gwanda kowama dashi,domin ko sashensa a can gefe yake,bayason ana yimasa katsalandan,saidai kaima bazai maka ba.
Sannan yanada basira da sanin mai yake,komai shine yake zuwa a fari kafin sauran ,hakanne yasa kullum hankalin hajiyah maryam yana kansa,in za'ayi masa abu ma ita ke shiga da fita ta hana,shikansa yasan da hakan. Shiyasa ko sashenta baya taba zuwa sai yakama dole.
Kaman yadda AM Aliyu bai yarda da ita ba hakama Gen Ahmad,don daff da mutuwarsa ya buɗe wani file akan ta,tunda ta tafi kuma babu wanda yasake bi ta kan zancen har yau.
Tsohuwar lauyace mai zaman kanta,duk da yanzu bata aiki,amma kuma tasan takan binciken abinda take son sani sannan kuma da yanda zata gujewa mai son bincikarta. Tana da son mulki da son ganin ana mata hidima,don ko shi kansa AM Aliyu dayake shugaban sojoji bai kaita juya sojojin ba,kuma tanada mutanenta a cikinsu,wanda ko mai tace karsu faɗa babu wanda ya isa ya sakasu magana harda shi kansa uban gayyar.
Wannan abubuwan su suka sa kowa hatta ƴaƴan ta suke shakkarta inta juyo ta kansu inka cire Ahmad shikaɗai ne baya tsoronta,kuma shine ciwon idon dayake hanata bacci lokacin dayake raye,yanzu kuwa da baya nan baccinta take sha harda minshari.




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*


Mallakar SADI-SAKHNA


PROFICIENT WRITER ASSOCIATION



*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[28]



[Sumaimah a mahangar gani]


Yau kimanin sati guda kenan da zaman goje a bayan garin,kwana uku nayi ina jinyarsa sosai,dakuma kwana dashi. Dagan nanne ya hanani zama sosai,sai Tunga ne yake kwana dashi.
A iya satin kawai har yasamu sauƙi yana tashi dakans,kasancewar dama jikine yasan wahala.
Yau banje wajensa ba,gyaran ƙofar tasa nakeyi,dan jiya da naje yake cemin yau zai dawo gida.
Inna batasan yana garin ba,ita a zatonta daga can wajen aikin zai dawo,dama kuma bayason tasan halinda yake ciki.
Kayan ɗakin na fitar dukka wannan tarkacen,iyah katifarsa na bari sai sallaya da kuma akwatin kayansa,sauran shirgin da baza'ayi amfani dasu ba zubarsu nayi,wasu kuma nakaisu ɗakin gefen inna..
Wani kuwa nashashi tun safe nake har rana tayi,dana gama na ɗora girki. Yau ba makarantar safe weekend ne sai islamiyya kaɗai,itakuma banje ba.
Saida na gama abincin rana nayi wanka nayi sallah kafinnasamu na zauna,inna sai sannu take jeramin.
Kursiyyah ce ta shigo ƙofar tamu hannunta ɗauke da ɗa kwano,wanda nasan awara ce.
Bayanta ajiye kwanon abincinsu wanda muke zuba musu ta ɗauka,dan dama sun saba yanzu ko magana basayi ɗauka kawai suke....shuru kowa yana ƙofarsa ta ciki na ciki.
Sai bayan la'asar na ɗauko qur'ani kenan zanyi tilawa naji muryar Tunga shida goje,har yanzu duk sanda naji motsinsa ko kuma muryarsa sai gaba yaɗan buga ɗinnan,wanda bansan menene dalilin ba. Tun da rana nake jiran dawowar tasa,har na haƙura tukunna suka shigo.
Ban tashi daga inda nake ba inaji har suka shigo cikin ɗakin innan.
Akan kujerar da take ɗakin ya zauna,yasaka kayansa wanda yatafi dasu baƙaƙe.
Gaisawa suke da inna amma kana ganin kasan yasha wahala a tafiyar da suka iyo ɗin,yana daurewa ne kada ya nuna rauninsa.
Shi Tunga tun a tsakar gida ya koma,wanda nasan goje yace masa ya tafin.
Ido muka haɗa dashi ya kashemin ido guda ɗaya ,ɗauke idona nayi tareda ajiye qur'anin nafita daga ɗakin.
Kofarsa na nufah nasake gyara komai,ruwa na kai a jug mai sanyi wanda shine dama bankai ba kada yayi ɗumi.
Hucin numfashinsa nafara ji a bayana,dan dama najiyo takun sawunsa.
A gadon bayana ya kwantar da kansa tareda saƙalo hannayensa ta cikina,tsayawa nayi daga tashi tsayen ina sauraran numfashinsa wanda yake fitar dashi kaman mutum yayi gudu.
"Kinsan nagaji meyasa kika taho kika barni a ɗakin inna,daƙyar fah na iso wajennan"
"Hhhhh sannu toh,a mashin kukazo ne daga can?"
"Uhmm a gashi duk gonakin mutanene a hanyar,sai jijjiga ni Tunga yake tayi a hanya,wajen ciwo yakemin kaman yanzu nayi raunin"
Jin abinda yafaɗa yasa nafara ƙoƙarin cire hannunsa daga kunkumina,amma kuma sai ya sake riƙeni kaman zai maidani ciki.
"Kace wajen yana ciwo,yakamata a duba kar ko ya buɗe,sannan ka haɗa gumi yakamata kayi wanka kaci abinci,saika sake shan maganin"
Cikin nuna damuwa nake maganar,ai yayi ƙoƙari ma da nice da wannan ciwo bazan iya tashi ba.
Tashi yayi daga bayannawa ya dawo kan katifa ya zauna,ɗakin yake ƙarewa kallo baki buɗe.
"Wow dama ɗakinnan yanada girma kaman haka,ban taba saniba saboda shirginsa,gaskiya kinsha aiki sosai na gyarashi"
Ƴar dariya nayi tareda matsawa na cire masa canvas ɗin ƙafarsa.
"Tohh yanzu abinci zaka faraci kokuma wanka zakayi?"
"Uhm bari naci abincin,dan yunwa nake ji sosai,sannan inason shan magani,saboda tafiyar danayi wajen yana min ciwo sosai"
Yaƙarisa maganar harda lumshe ido yana maida numfashi. Ganin yanda yake bansan lokacin dana kai hannuna ba na bude maballin rigar,wajen da ciwon yake nake kallo,hatta fatar cikinsa ma tayi ja,saidai bayyi jini ba alama yafara kamewa kenan.
"Uhm take it easy mana madam,sauri kike har haka ne?"
Yanayin magana na kulada yanda na ɗora hannayena akan cikinsa,saurin janyewa nayi tareda matsawa baya. Me yake damuna ne haka,yaushe na fara ɗaukar taba jikinsa ba komai bane ba.
Dariya yakeyimin tareda ƙarisa cire rigar gabaɗaya ya ajiye a gefe.
"Uhm nagode da kulawarki,hakan yana yimin daɗi idan naga kin damuwa da halinda nake ciki,sannan karki damu bazan ɗauki komai ba dan kin taba jikina,ya hallata a garekine ba shiyasa kika taba ba uhm?"
Ohh kunya ce takamani naji kaman na nutse a ƙasa,maza fa daman sun iya zarar zance.
"Yawwa yanzu naji kayi turanci dama ka iya ne?"
Nayimasa tambayar dan ya manta da waccar maganar,kaman hakan kuwa yayi tasiri,dannaga ya tafi tunani.
"Turanci kikaji nayi,uhm zai iya yiyuwa,dan wani lokacin mutane kan faɗa cewar inayi,ko karanta rubutu danake kawai gani nayi ina rubutawa,amma ban tuno makarantar danayi ba kuma"
"Taya ya hakan zai kasance toh?"
"Uhm ta haka mana,zubamin abincin naci inason shan maganinnan"
Zancenne yaƙare a haka na zuba masa abincin kaman yanda ya buƙata.
Har yashiga wanka ya fito ina zaune a ɗakin,dan cewa yayi kada na tafi na jirashi,daga shi sai gajeran wando ya shigo yana goge kansa da,wani ƙaramin ƙyalle.
Ɗauke kaina nayi,amma sai naji ya zauna a kusadani har muna gogar juna...ohh wannan sabon hali na goje na kasa gane kansa sam.
Mai yasaka na miƙo masa yafara shafawa,shuru mukayi dagani harshi babu wanda yace komai.
Tashi nayi zan tafi ya riƙo hannuna,
"Ina kuma zakije,ni kaɗai zaki tafi ki bari a ɗakin?"
"Uhn zan ɗora girkin dare,Sannan ba kace bacci zakayi ba?"
"Oh na tuna,to ki dunga zuwa kina leƙowa akai akai harna tashi"
"Hhhh to shikenan yanzu na tafi?"
Ɗaga kai yayi kaman baya so,wai dama wannan bawan Allah haka yake ne,kokuma yanzu ya koyi waɗannan abubuwan..
Bayan na fito inna tayi mamakin daɗewata a wajen gojen,amma batace komai ba,nima kuma banyi maganar ba.
Ina cikin jajjaga kayan miya naga ya fito daga ɗakinnasa ya fita,ƙananan kayane a jikinsa yana tafiya normal ba wannan bubbuɗawar. Ko ciwonne yasakashi oho..
Tsayawa nayi daga abinda nake na zubawa bayansa ido yana tafiyar,saida yaje saitin zaure ya juyo muka haɗa ido.
Kunya ce ta rufeni ganin yakamani ina kallonsa,da hannu yayi min alama nazo,fuskarsa ɗaukeda murmushi.
Zatona wani abu zaicemin,sai kawai ji nayi ya sumbaci goshina,tareda ɗallamin yatsarsa kuma a wajen duk lokaci guda.
Shafa wajen nayi tareda turo baki.
"Meyasa dana juyo kika ɗauke idonki kaman wacce nakamaki kina laifi?"
"Dama zaka iya fita ne?"
"Silly girl na kula wani lokacin idan bakyason bani amsa saiki yimin tambaya koh"
Hannu yakawo zai sakeyimin ɗall amma wannan karon na koma gefe ina dariyah,shima murmushi yayi tareda cewa.
"Zanje wajen su dunga ne karsuga shuru bayan sunsan nadawo"
"Banda bawa mutanen gari tsoro"
Nafaɗa ina komawa cikin gidan da sauri,yanda nasan bazai dawo ya kamani ba.

__***__


"Wayyo Allah nah"
Wani yaro yasaka kuka ana cikin karatu a aji. Malaminne ya tsaya da karatu tareda juyowa yana kallon yaran ajin,wanda yayi kukan ya kalla tareda tambayarsa mai yafaru.
"Kai tashi,miye kake yiwa mutane kuka a aji?"
"Malam Deejah ce ta sokamin wani abu a wuyana"
Tun kafin malamin yayi magana tayi caraff tace.
"Malam bacci yakeyi a aji kana karatu"
Jijjiga kai yayi tareda riƙe kai,ya akeso yayine da wannan tantiriyar yarinya,duk ajin yarane masu shekaru biyar zuwa bakwai,amma ita shekararta kusan sha uku,dukka tafi yaran aji girma. Shi ba abin yace akaita aji sa'anninta ba babu abinda ta iya,in yayi kokarin cewar a koreta kuma abokinsa Musbahu ne ya roƙeshi akan ya barta a ajin.
"Zo nan kizo ki tsaya a gaban aji"
Yafaɗa a zuciye,tahowa tayi tana kallon ƙasa kaman wata ta Allah.
"Karanta min Kul'azubi rabbin nass naji,tunda shi bacci yakeyi ke ai idonki biyu ina"
Wuri wuri tafara da ido alamar bata ma san mai yakecewa ba,sai wuss wsusss takeyi kawai ta bakinta.
Bulalar hannunsa ya ɗaga ya zambaɗa mata a gadon baya,sake zura mata yayi,aikuwa take ta kwarara ihu.
Ƴan ajinne suka sheqe da dariyah ganin yanda take tsalle tana dadare.
"Malam aradu ya isheka,dan kaga abokaina basa biyoni
Showing 51001 words to 54000 words out of 60324 words