ta kasa amincewa da adamcy ba son yarinyar yake ba.”



Cikin tsananin tashin hankali kukan da take ,ya shiga kai kawo acikin office din hannunsa d’aya rike da kugunsa cikin haka daya daga cikin wayoyinsa ya d’auki sauti amman bai bi ta kan kiran ba ,ya sake komawa inda take wanda zuwa lokacin ta durkushe kasa tana kuka yana son hukuntata akan cika masa kunne da tai dan duk abinda zai faru akan hototunan dole zai ta’ba kima da mutuncin sa amman ya kasa sai ma ya bige da durkushewa a gabanta tare da kira sunanta cikin wata irin murya mai sanyi da kashe sansar jiki “maryama ! wanda yasa tsigar jikinta mikewa yrrr”kiyi hakuri ki yafe min nasan duk ni ne na janyo faruwar komai “.jin sautin sanyayyiyar muryarsa yasa ahankali ta d’ago shayyyun idanunta ta zuba masa batare da tace komai ba sai dai a kallon da take masa bugun zuciyarta ke qaruwa “yayinda har lokacin kira na kan shigowa wayarsa.”



ya mike ahankali ya isa inda wayar take ya d’auka yana dubawa sai daya lumshe idanunshi na second biyu sannan ya bud’e ya d’aga wayar yana cewa” hello !”kwayar idanunshi yana kanta yana kallonta yana jin kamar ya furta mata abinda ke cin zuciyarsa ko ya huta da azabar da yake sha akanta ,waya yake amman sam natsuwarsa da hanakalinsa basa kan wayar suna kanta ya kai hannu ya d’auki iPod dinsa yayi connecting dinsa da wayarsa ya manna a kunnesa wanda hakan ya bashi damar ajiye wayar akan table ya qaraso zuwa inda take durkushe “har kullum yana son ta zama jarumar mace mara rauni ,mace me qarfin zuciya Sam baya so ta zama raguwar mace domin idan ta zama mallakinsa zata fuskanci abubuwa ,idan ta cigaba da zama raguwa za’ayi galaba akanta, tsoronta zai zama rauninta hakan zai sa ayita cutar masa daita hawaye ya cika masa ido ahankali ya kauda kanshi daga kallonta .”



Ahankali ta cigaba da jiyo maganarsa cikin rauni “ki tashi ki samu waje ki zauna kafin nasan abun yi ,ta yunkura da kyar ta mike tana wani irin taku ta samu waje ta zauna dafe da kanta cikin sanyi jiki ya isa gaban fridge ya bud’e ya d’auko goran ruwan mai sanyi ya juyo zuwa inda take “have some water!” ya mika mata goran ruwa bata kar’ba ba haka zalika bata d’auke kwayar idanunta akanshi ba shima kuma bai janye hannunsa akanta ba idanunshi yana kanta har sanda ya gama wayar wani kiran ya shigo wanda ya kasance na mami ne” the way yadda yake amsa wayar yana kiran sunan sweetheart ta fahimci daita yake wayar duk da batasan abinda yake fad’a mata ba amamn hankalinta yayi mugu magun tashi yana gama wayar ya sake cewa” maryama take some water ki sha ruwa ko kad’an ne “dawa kayi waya yanzu ?”tayi magana cike da raunin zuciya” my mother ya bata amsa atakaice yana kallonta “shikenan nasan itama an tura mata hotunan ai nasan za’ayi haka nasan za’a turawa yan’uwanka da mahaifiyarka.”“ ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru” ni kawai ka fad’a min wani mataki zaka d’auka dan ni naga kamar ma baka damu da halin da nake ciki ba ,a kallon da nake maka ma gani nayi kamar dadin faruwar haka kayi.”



A d’an rikice yace “bangane nufiki ba ?” Ai dole kace baka gane nufina ba gashi har an turawa ma mahaifiyarka aman babu wata alamun damuwa atattare da kai. yayi shiru kawai yana kallon yadda take motsa qaramin bakinta “ka fad’a min gasky an tura mata hotunanmu ko “? still dai shiru yayi kawai yana cigaba da kallonta “ an tura mata hotuna ko ba’a tura mata ba ?”wannna ba matsalrki bace ko an tura mata ko ba’a tura mata ba “to yanzu ka fad’a min matakin da zaka d’auka kafin zuciyata ta buga “what I will do is my own business it my decisions how I wil manage my hanger, duk yadda nake qoqarin kwantar da zuciyata akanki baki gani ,duk yadda nake faman rarrashinki baki gani har kina iya cewa naji dadin faruwar abinda ya faru idan naji dadi menene ribata bayan dole wad’an nan hotunan zasu ta’ba mutuncina ?”tunda nã had’u dake kullum nida kamfanina cikin damuwa muke dan haka idan kinga dama ki fad’a abinda yafi naji dadin faruwar abinda faruwa ba damuwata bace .”



nan take gabanta ya wani irin bugawa da qarfi , ta mike da sauri tana cewa “tunda ka had’u dani kullum kamfaninka da kai kuke samun matsala as how ?”me kake nufi dani sir dan bangane nufinka ba ?“idan akwai wani abu acikin ranka akaina say it directly ba wai ka dinga kwana kwana ba “what !” ya furta da qarfi yana jin kamar ya d’auketa da mari sai dai baya Jin zai iya aikata hakan akanta lip’s dinsa ya kamo na kasa yana taunawa da qarfi kafin ahankali yaja tsaki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa “kamar yadda kake tunani haka akaina nima haka nake wannna tunanin akanka,tunda na hadu da kai kullum cikin damuwa da shiga matsala nake a yau nayi dansani ,a yau nayi nadamar kasancewata acikin AGC company “matsala ba daga kamfanin bane matsala daga ke ce “what? me kace ? yana jinta ya shareta “ina bukatar na sake jin abinda ka fad’a yanzu tayi maganar tana takowa zuwa inda yake tsaye “ ke banson iskanci tunda abun naki ma wulaqanci ne na ma fasa d’aukar mataki akan abinda ya faruwa, bazanyi bincike komai akai ba kije kiyi duk abinda zaki yi idan anga dama a yad’a hotunan zuwa social media is not my own business.”cikin tsananin tashin hankali ta had’e hannuwanta waje d’aya tana jin wani irin fad’uwar gaba from no where yana shigarta “muryarta na rawa ta soma mgn “yanzu abinda zaka fad’a kenan ?I can’t say more than that ,dan haka kiyi min shiru anan ki barni .”



“me yasa zaka fad’a haka ?”wallahi ni dai abinda nasani ni ba matslar kamfanin nan bace kaine matsalar kamfaninka kuma ko kaso ko karka so ni ba matslar kamfaninka bace dan kasani kasancewata aciki cigaba ya kawowa kamfaninka aikin banza kawai Ina zaman zamana ka shigo rayuwata wanjen nuna son asaninka ka jawowa mutun shiga matsala .”“maryama how dare you talk to me like this ?me yasa kaima zaka ce nice matsalarka data kamfaninka”? sannan me yasa zakace ka fasa d’aukar mataki akan abinda ya faruwa?”me yasa bazaka yi bincike akan abinda ya faru ba “?me yasa zakace naje nayi duk abinda zanyi idan anga dama a yad’a hotunan zuwa social media is not your own business?”idan har kai ma zaka iya fad’a min haka nice bazan iya fad’a maka haka ba?wallahi kwata kwata zuciyarka bata da tausayi bare fellings kai ganinka babu wanda zai iya fad’a maka mgn ne ?”ta fad’a hawaye na zubo mata.”shiru yayi yana kallonta “wallahi da kana da fellings dole zaka zamo mai tausayin halin dana tsinci kaina a yau “duk lokacin da mutun yake cikin damuwa kai lokacin kake da damar qara ninkawa mutun damuwa akan wanda yake ciki idan ma mutun mutuwa zai yi ba ya mutu ba damuwarka bace ,”ta qarasa maganar tana kallonsa ido cikin ido .”



still dai shiru yayi kawai yana kallonta “ai bazaka ta’ba jin tausayin wani acikin ranka ba saboda zuciyar dutse gareka,” ka wani zuba min ido kana kallona baka da wani bambamci da dutse still kallonta kawai yake yana jin kamar ya kamota ya soma yaryarfa mata mari “da fatan kaji abinda na fad’a yanzu there’s no difference between you and stone” yadda dutse yake da qarfi haka zuciyarka take da qarfin da rashin Imani da rashin tausayi dan ..”enough maryama !”ya furta da qarfi yana dukan glas cup din dake kan table, nan take cup din ya fashe tare da ruwan ciki aiko nan take hannunsa ya yanke sai ga jini ya fara zuba wani irin qara ta saki mai sauti tare da yowa kanshi tana kiran “sir me yasa zaka yi haka ?kaga irinta ba ?kaga irin abinda zafin zuciyarka ya janyo ?” kalli yadda kajiwa kanka ciwo ?ta kai hannunta zata ta’ba shi yayi saurin katseta ta hanyar cewa “karki soma kai hannunki jikina stay a waya from me “dan Allah ka ..” nace banason go and do your work matsowa tayi kusa dashi sosai muryarta na rawa tace “a halin yanzu babu wani aiki da zan yi wanda ya wuce na duba hannunka “mar..”dakatar dashi tayi ta hnayar d’aga masa hannunta “ka barni nayi abinda ya dace” ta fad’a tana haki “maryama there’s no need for this kinsan zaki damu me yasa kika ‘bata min rai “sir babu ruwana da abinda ya bata maka rai ka zauna kawai “ ta fad’a tana zubar da hawaye yaki zama kamar yadda ta bukata .”gashi zafin zuciyar da yake cinsa yasa jinin ke qara zuba .”



“please sir site !”shiru yayi kawai yana sauke numfashi kafin ahankali ya samu waje ya zauna yana cizan lip’s dinsa ko zai rage masa azabar zafin da yake ji ,”muga hannun ta fad’a cike da tsananin damuwa kin bari yayi taga hannu, ta kai hannnuta ta riko hannun ta qarfin tsiya tana kallon ciwon da yaji shima kallonta yake tana hura masa iskar bakinta a ciwon wanda yayi sanadiyar da ya dinga jin wani sanyi na bin lungu da sako na sansar jikinsa lumshe tsumammun idanunshi yayi” tabbas maryama ta kamu da tsananin sonshi batare datasan tana yi ba,” ta d’ago kanta ahankali idanunsu ya tsarke cikin juna cike da zafin zuciyata tace” ka tsaitsata zuciyarka, dan zafin da zuciyarka take yayi over shi yasa jinin yaki tsayawa, mutun bashi da wani aiki sai zafin rai please ka tsaitsaita kanka “maryama banason damuwa please ki sakar min hannu ki kama gabanki.” numfashi ta shiga saukewa sama sama tana jin wani irin a gabdaya ilahirin jikinta” i saida leave my office now ya sake fad’a yana nuna mata kofa .”tai mugun zuba masa shayayyun idanunta tana kallonsa hawaye na gangaro mata batare datayi yunkurin mikewa tsaye ba .”







Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 41


Ahankali maryama ta d’auke kwayar idanunta akanshi zuwa hannunsa ganin yadda jini yake bin yatsun hannunsa ya mugun d’aga mata hankali .”hawaye ne sosai yake zuba daga idanunta tunanin inda zata samo abinda zata d’aure masa hannun take amman sam ta rasa .”tana cikin tunane tunane taga ya mike tsaye cikin sanyi jiki tayi saurin riko d’ayan hannunsa mara ciwo cike da zafin nama ya fixge hannunsa yana mata gargad’i da kwayar idanunshi “ki tashi ki bar min office idan kuma ni kike son na bar miki sai ki bari nasani.”ya fad’a yana mai kawar da fuskarsa daga kallonta .”d’ago idanunta tayi ta cigaba da kallonsa gani tayi yanayinsa ya sake sauyawa ya wani maida kanshi gefe yana huci tmkr wani zaki tana kallonsa ya d’auki d’aya daga cikin wayoyinsa ya nufi d’akin dake cikin office din ,da idanu ta rakashi har sai da taga shigarsa sannan ta iya sauke numfashi da ajiyar zuciya atare sai dai kamar yadda ya bukata haka tayi jiki a sanyaye ta mike ta fita daga office din tana daidaita natsuwarta dan kada ‘yan office dinsu su fahimci wani abu .”



tana fita ko cikakken minti biyar batai ba mr ata ya fito ya samu waje ya zauna yana sauke numfashi tare da tokare hannunsa mara ciwo a kugunsa yayinda hannunsa mai ciwo ya ajiye akan ciyarsa yana kallo irin raunin daya ji. yana zaune doctor dinsa ya nemi izinin shigowa da kyar ya bud’e baki ya bashi izinin shigowa ya shigo a natse ya gaishesa cike da girmamawa sannan ya ajiye jakar kayan aikinsa ya soma had’a kayan aikin da zai bukata yana cewa “ranka ya dade garin yaya ka samu irin wannan raunin haka .”?shiru mr ata yayi masa dan bai san me zai ce masa ba .”doctor ya janyo kujera zuwa gabansa ya zauna yana masa sannu cike da kulawa ,kanshi kawai ya gyada, a natse ya d’auki bandage ya had’a da d’an digon wani farin ruwa mai d’auke da sinadarin akai ,hannunsa ya kai ya riko hannun mr ata ahankali ya soma goge masa ciwo da auduga wani irin zafi ya ziyarci sansar jikinsa yayi saurin runtse idanunshi tare da cije labbansa da qarfi adaidai lokacin maryama ta kai idanunta office dinsa inda ta hango doctor zaune yana treatment din hannunsa naunauyen ajiyar zuciya ta sauke da qarfi sannan ta mike ta fito .”



Ahankali ta tura kofar ta shigo ta tsaya akanshi sake rike hannunsa doctor yayi cike da kulawa ya cigaba da goge masa yayinda mr ata ya sake cije lips dinsa yana qoqarin zame hannunsa muryarta a raunane tace “sorry sir da zafi ko ?kayi hakuri a wanke maka shine zai sa ciwo ya bushe numfashi kawai ya sauke dan sosai yake Jin zafin ruwan da yake sawa yana goge masa ciwon sake kama hannun doctor yayi yadda maryama taga ana wanke masa ciwo ya sake d’aga mata hankali hakan yasa ta fara kuka tana cewa doctor yayi masa ahankali kalmominta ne sukai nasarar d’auke masa ciwo “sorry sir da zafi ko ?kayi hakuri a wanke maka shine zai sa ciwo ya bushe
ya runtse idanunshi sosai ana wanke masa ciwo tana kuka har sanda doctor ya gama wanke ciwon tsab sannan ya nada masa bandage.”
Doctor ya kalli innocent face din maryama had’e da jin mamaki sannan ya saki murmushi “ya shi ake wankewa ciwo amman kece mai kuka?to ki bar kuka haka .amman banda kuka maryama babu abinda take kwayar idanunta sunyi ja sosai fuskarta kuwa duk tayi face face da ruwan hawayen wasu magunguna doctor ya bashi sannan yayi masa sallama shima mr ata ya mike ya shige ya barta tsaye taji kamar ta bishi sai dai tsananin tsoro ya hananta .”



Kamar d’azu haka ta fita da sanyi jiki tana goge hawayenta sai dai duk bayan second sai ta Kai kallonta zuwa office dinsa gbdy ta kasa aiwatar da komai tana zaune a office dinsu ya fito yana zare yar saman suit dinsa ya ajiye had’e da qarasa wa inda fridge yake ya d’auki goran ruwa ya kafa a bakinsa sauke goran qasa yayi had’e da fitar da numfashi itama numfashi ta sauke ta fito daga office dinsa ta wani office din dake kallon nasu domin ta kira masu tsaftace waje suzo su gyara masa office .mr ata ya fito yana magana akan waya har ya kai kofar fita adaidai lokacin da maryama ta kunno kai zuwa office dinsa sukai karo dashi tayi baya zata fad’i yayi saurin kai hannusawa duka ya tallafo bayanta yayinda ita kuma a gigice ta kai hannunta d’aya saman rigarsa daidai saitin zuciyarsa dake luguden bugu ta dafe cikin tsananin tashin hankali da jin tsoron abinda zai mata .”



ido cikin ido suke kallon juna kowannensu fuskrsa d’auke da tarin damuwa saurin zare jikinta tare da gyara tsayuwarta tayi still suna kallon juna batare da sun cewa juna qala ba muryarta cike da rauni tace “kayi hakuri please” ya gyada mata kai kawai batare da yace mata uffan ba “sir ko zamu koma ciki ina son nayi magana da kai .”bai mata mutsu ba ya juya ya koma ciki ta biyosa tana jin wani irin fad’uwar gaba, ta karaso inda yake tsaye ta sunkuyar da kanta kasa “ka zauna !” kiyi maganrki “amm daman hakuri zan baka akan maganaguna sam banji dadin abinda ka fad’a min ba haka zalika nima banji dadin reaction dina ba amamn kayi hakuri da abinda na farfad’a maka”.tai maganar tana fashewa da kuka kayi hakuri bansan dalilina ba ,ban ta’ba tsammanin zan iya fad’a maka haka ba am very sorry sir .”



yay gyran murya yana cewa “is okay “!.yanzu ya kake Jin hannunka ta fad’a hawaye na sake wanke mata fuska tsaki yaja batare daya amsa mata ba “.shi kam wannan zubar hawayen na matukar yi masa ciwo ace mutun baya gajiya da kuka kalli yadda kwayar idanunta suka canza “kuka na menene haka ?”ya jefo mata tambaya d’ago kanta tayi ta zuba masa sosai adaidai lokacin da wani guntun hawayen dake makale acikin idanunta ya samu damar gamgarowa a fakaice ya kalleta “Ina ganin zaki iya wucewa gida dan ni yanzu gida zani ya fad’a cikin halin ko in kula yana mai latsa wayarsa dake rike a hannunsa.”hawaye ne suka shiga gangarowa daga idanunta kamar an bud’e famfo muryarta a raunane tace “ka taimakeni ka fad’a min zaka d’auki mataki akan issues dinmu ?”shiru yayi “dan Allah ka taimakeni kar ‘yan gidanmu suga hotunan mu most especially aunty hasana da aunty salma idan suka ga hotunan nan na shiga uku babu abinda zan fad’a su yarda dani bazan sake d’an d’ano wani abu wai shi farin ciki ba ka taimakeni banason mutuncina ya zube tuni wasu hawaye suka wanke mata fuska ..”



Tunda ta fara magana bai d’ago ya kalleta ba sannan kuma bai daina abinda yake ba sai a yanzu ne da sheshekar kukanta ya cika masa kunne ya d’ago kansa daga latsa wayar da yake “wace irin yarinya ce ke mai son kanki dayawa magana d’aya taki ci taki cinyewa ke mutuncinki kad’ai ne abun dubawa?”ni rayuwata acikin duhu take shi yasa kaga na damu da mutunci…. tun kafin ta Kai ga qarasa maganarta ya juya ya nufi kofar fita biyosa tai da gudu tana kiransa “sir !”bai tsaya ba har ya isa kofar shiga lifter ya shige koda ta
Showing 138001 words to 141000 words out of 176292 words