gangaro mata akan kuncinta .”wannan kuma ki qyaleshi ko yaki ko yaso abinda yake cikinki nashi ne kuma jininsa ne idan ya ga dama karya amsa mu dai mun amsa kuma muna so .”sannan duk fushi da zai yi na banza ne zai ma sauko ne ni nasan bazai iya cigaba da fushi da abinda ke cikinki ba sai dai idan bata zo duniya ba " maganar aunty tayi mata dadi ke dai ki dage da addua allah yace zai amsawa bayinsa matukar bai kosa ba ki daina cewa adduar kike kinji shiru baa cewa allah anji shiru maryam ki cigaba da yin addua,allah yana jinki kuma yana ganinki kuma zai amsa miki saboda kina da yakinin allah ya ganmu yasan mu kuma yana jinmu ,bawa zai dade yana addua amman yaji shiru har ma yaji tamkar allah bai amsa ba Aa wani lokacin abun ba alkhairi bane wani lokacin kuma Allah yana jaraba bawansa ne .”maryam tayi qasa da kanta tana amsawa da to aunty na gode in sha allahu zan sake jajurcewa ta fad’a haka a fili sai dai abani zuciyarta ta kasa samun nutsuwa .”



Washegarin da misalin qarfe 11 :00 daidai kira ya shigo wayar oga amar alokacin yana zaune a office dinsa ya janyo wayar tare da dubawa ganin wanda ya kiransa ne yasa ya d’aga da hanzari “hello !”daga can bangaren mr ata yace “amar idan kana da time kazo zuwa anjima muje gurin kanin mahaifin maryama shiru oga amar yayi kafin daga baya yace “yanzu kana ganin wannan tsarin da zaka bi daidai ne ?”ko daidai ne ko ba daidai bane ni dai kazo muje kawai “amman jiya jiya nan kace next week ?”na canza shawara .”ya fad’a yana cizan lip’s dinsa na kasa “to shikenna zan zo zuwa anjima yana gama jin abinda ya fad’a ya katse kiran ya cigaba da juyi akan kujera qarfe daya da rabi oga amar ya shigo AGC sai dai bai hau sama ba ya kira mr ata cewar yazo amman zai shiga massalaci yayi sallah “okay nima yanzu nake shirin saukowa .”daga masallaci suka wuce unguwarsu maryama shi da oga amar bayan sun kira baba gali cewar suna son ganinsa suna tafe suna tautaunawa har suka qaraso gidan su maryama lokacin da suka qaraso har baba gali ya gama shinfida ,a bangaren da suke sauke tarbon baki .”



Baba gali ya taresu cikin girmamawa yayinda mr ata sai sunkuyar da kai yake alamar nauyi da jin kunyar abinda ke tafe dashi bayan sun zauna baba gali ya mika masu hannu alamar su gaisa sai dai cike da girmamawa suka ki bashi hannu sai dai daga zaune da suke su ka d’an rusuna abinda ya kara daurewa baba gali kansa kenan “to me ya kawo haka manyan mutune haka masu daraja da arziki zasu rusuna masa lallai akwia babban alamarin daya kawo su .”Bayan sun dan zauna jimm, baba gali ya kalli oga amar yace “wallahi ranka ya dade tunda naji wayar ka na kasa samun natsuwa ina ta zullumi da fargabar ko lafiya?Oga amar ya danyi murmushi yace “lafiya qalau baba daman muna son rokon wata alfarma ce a wajenka “ Alfarma ? Wallahi kunfi karfin komai a gurina yallabai. A yanda nake jin labarinku a gari nan ban taba tabbatar wa ba sai da naga zahiri yadda kazo janaizar sadam ka bamu kudi masu tarin yawa sannna kullum cikinn taimakawa mutane dana kasa daku kukeyi jifa kwanakin baya akan maryama tayi aiki a qargashin yalla’bai kudi masu yawa aka bani a ina ake yin haka ai giramanku ya kai kusa ayi ko babu kosisi ku din na daban ne allah dai ya taimakeku .”baba komai baba mubar maganar nan haka abinda ya kawo mu muna neman Alfarmar auren maryama ne a wajenka “baba gali ya dago kanshi da sauri yana dubansu kafin muryarsa a dan rikice yace “maryama kuma ?”




Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 33

Jikin maryama na rawa tace "ban .."ban fahimci komai ba ya d'an yin sama da hannun rigarta kad'an yace "ki natsu sosai maryama ki kalleni ki fad'a min  abinda kika gani "jikinta ya sake d'aukar rawa "ni wallahi ban fahimci komai ba sir  "uhm !"ya fad'a yana sauke numfashi tare da tsurawa  pink lip's dinta idanunsa yana cigaba da shafa saman hannun ta, muryarta na rawa tace "stop sir !"stop what !"? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi "abinda kake yi ne bana so , “please stop  touching my body". ta fad’a tana danne kwalla dake kokarin zubo mata "ya kwantar da muryarsa sosai yace "bakya son ina ta'ba jikin ki? ya tambayarta yana ‘kara bin jikinta da wani shu'umin  kallo mai gigita zuciya da sauri tace "eh wallahi bana so "ta fad’a tana qoqarin zame hannunta amman ta kasa  dan yayiwa hannun kyakkywan rikon da bazata iya zamewa ba "dan Allah ka sakar min hannu sir  bana son kana ta'ba min jiki "ni kuma ina so"ya fad'a kmr bashi yayi mgnr ba, Ikc ma ya sake riko hannunta sosai  cikin nashi yana furza mata hucin numafshin sa , "shiyasa kikaji nace mai kika fahimta atattare dani kikace babu komai bayan ni nasan kin fahimci komai "ni allah ban fahimci komai ba wIh “ta fada tana fashe masa da kuka dan zuwa yanzu ta fahimci abinda yake nufi daita so yake ya lalata mata rayuwa ya cuceta ."



mamakin saurin kukanta yake , yayi notice dinta  kwatakwata kuka baya yi mata wuya"lumshe tsumammun  idanunshi yayi  yana saisaita nunfashinsa ,dan  buguwar da zuciyarsa take akanta ya wuce kaida  ,shi kad’ai yasan me yake ji a daidai
Ikc nan,  dan ji yake kamar ya fito mata da zuciyarsa taga halin da take ciki akanta ,jin taki daina kukan yasa ya bud'e idanunshi da kyar ya tsura mata kafin ahankali ya motsa lip's dinsa "me ye hk ? ya fad'a yana sake tsareta da tsumammun idanunsa "mai yasa kwatakwata baki jin kunyar kuka?"dole ne nayi kuka nidai dan allah ka daina ta'ba min jiki dan wani iri nake ji " ta qarasa mgn tana turo masa qaramin bakinta gaba, yaji kamar ya kai bakinsa kansu ya fara tsotsa a zahiri ,amman sai ya share yayi murmushin aciki dan shi yasan me take ji ajikinta kuma abinda yake bukata kenan, ta soma jin wani abu akansa shine hanya mafi sauki da zai mallaketa gabad'aya, ya sake shafa skin dinta yana sauke boyayyen ajiyar zuciya ,duk da ya san jikinsa nada tsananin taushi amma sai yaji nata kmr yafi nashi soft kai everything ma ko dan  akwai banbancin halitta ne?akwai abubawa ajikinta  dake mugun d’aukar hklsa a tare daita wanda a duk Ikc da yayi arba dashi ya kan gusar masa da hklnsa  ."



Bai san sanda yayi kusa daita sosai ba yace "fad'a min me kike ji ajikinki "wannan iskanci da kake min wallahi ji nake Kmr kana shafa min wu..."kafin ta qarasa maganarta taga ya tsareta da kwayar idanunshi  yana  jefanta da wani shi'umin kallo mai rikitarwa ,wanda yasa tayi  gaugauwar  yanke maganarta qirjinta na bugawa da sauri sauri .ba zato ba tsammanin zai doke mata baki sai jin saukar hannusa tai a saman lip dinta ya bata bal....wanda yasa tai saurin saka hannuta a daidai gurin saboda zafin da taji ya ratsata ta tsura masa idanunta tana kallonsa hawayenta na cigaba da zuba "wallahi mr ata mugu ne na bugawa a jarida ga azabar da take ji gashi yaki sakar mata hannu "dan Allah ka rabu dani nace bana so bana so kana ta'ba ni " ta fada tana bubbuga kafafuwanta a kasa hade da sakin gunjin kuka"kallo ta kawai yake without saying a word to her lallai ma yarinyar nan kurciya na mugun cinta.”
Inda mata ke nemansa ruwa a jallo idan akwai abinda yafi wanda yake mata ma suna só da zasu samu dama amman ita dan iskanci ta samun damar har kuka take tana danganta hakan da iskanci ."
hannunta ya saki  sannan  ya mike tsaye yayi taku kamar zai fita don ita a tunaninta  fitar zaiyi  sai ganin tayi  ya kashe light din office  din nan take duhu  ya mamaye office din ,nan da nan  kukan da take yi ya tsaya cak. tsoro ya ziyarceta Ikc daya hankalinta ya tashi  shayayyun idanun ta  zaro sosai cike da storo sakamakon ganin yadda yake tattaki zuwa inda take  zaune ."




da sauri ta mike tsaye  tana cewa "sir ni zan wuce gida "karki damu yanzu zamu wuce ."yanzu zamu wuce kuma ?"ta maimaita a fili zuciyarta na luguden bugu "eh zamu kai ki gida ne ko bakya so?" tayi shiru tana tunanin tare da nazarinsa "kin yi shiru ya fad'a yana dawowa gabanta ya tsaya yana kallonta ta d'an d'ago ahankali idanunta sukaci karo da sarkan zinarin wuyansa dake kwance a qirjinsa wani sabon tsoro ya kara dirar mata a zuciya wadda yasa tai  saurin sunkuyar da kanta tana runtse idanunta gam "ko kin fi so ki shiga motar hanya kuna gogayya da maza ?"numfashi kawai ta sauke batare da tace masa komai ba ."ahankali ya juya yana maida maballin rigarsa ya kwashe wayoyinsa ya nufi kofar fita tana tsaye kawai taji alamun baya gabanta dan haka tayi qoqarin bud'e idanunta taga har ya kusan ficewa daga cikin office din, tabi bayansa da kallo tana maida numfashi bata san me take ji adaidai wannan nan lokacin akansa ba .”idan tace tasan abinda take ji ko tasan abinda shi yake tattare dashi tayiwa kanta karya ta dai tasan a duk lokacin da tayi arba dashi ya kan gusar mata da hankalinta bazata ce so bane dan bazata jefa rayuwarta cikin matseefa ba dan ko soyayya ne sai tayi duk yadda tayi takicesa aranta bare ma bashi bane .”



Bazata ta’ba wannan ganganci ba shi kuma tasan yafi qarfin ya sota sai dai idan wata manufa garesa akanta idan ba haka ba ina ita ina shi hanyar jirgi dabam ta mota dabam ta sake numfasawa tana tunanin binsa ,ta bishi ne ko kuwa ta kama gaban ta ?" abu daya ne zai sa ta bishi saboda taimakon da zai mata  akan nadiya if not bazata sake ganganci binsa ba kuma tasan halinsa muddin taki baqaramin aikinsa bane yace ya fasa taimakonta ."ta kusan mintuna a haka bata motsa daga inda take ba kafin ahankali ta soma taku ta fito ta shiga office dinsu inda kusan kowa ya watse ,wasu tsirarrun maakatan sultan ne suke kai kawo ,ta kai hannunta ta d'auki jakarta dake ajiye akan table ta rataya a kafad'anta tana qoqarin fitowa daga office din wayarta ta shiga qara mara sauti,nan take ta tsaya ta ciro wayar daga cikin jakarta tana duba screen din wayar  suannsa ta gani yana yawo ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta d’aga "hello sir !"dan Allah malama ki fito karki ‘bata min lokaci .""O.."okay sir.."kafin ta rufe bakinta har ya katse kiran.”



jiki a sanyaye ta qarasa fitowa daga office din tana d'aga qafafuwanta da kyar,  a tsaye ta ganshi ajikin had’addiyar motarsa bmw fara sol hannayensa duka suna  cikin aljuhun won dashi , ganinta yasa ya bud'e mata murfin kofar baya sannan yayi mata alama ta shiga da kwayar idanuwansa,wani yrrr taji  a gaba d'aya ilahirin jikinta ahankali zuciyarta ya dinga bugawa da sauri sauri "wannan shine karo na biyu da yayi mata haka ,kuma a gaban masu tsaronsa da direbansa ,ba ita ba hatta masu tsaronsa da direban sa a ruwa sun dasa ayar tambaya akanshi dan duk tsawon lokacin da suka d’auka tare dashi suna masa aiki babu wanda ya samu wannan matsayin bayan mahaifiyarsa gashi karo na biyu kenan yana bud’e mata murfin mota .”ahankali maryama tayi kasa da  kanta tana d’ora hannunta d’aya akan d’aya tana d’an jujjuya jikinta alokacin da yake sake  mata alamar ta shiga, tai tsam da zuciyarta dake tsinkewa tana sake nazarinsa da kyau."



alamunsa da abubuwan da yake mata suna nuna mata kamar  só ne saboda duk yadda mutun yake sonta tana ganewa  amman kuma shi nashi salon ne yazo dabam shi yasa ta kasa fahimtarsa da kyau
Idan yayi wani abu kamar só sai kuma yayi wani abu kamar sha'wa ,za dai tafi ajiye abun a matsayin shaawa dan ina mutun kamar shi zai sota ?" "me mutun kamarsa zai yi daita ?"wace ce ita ?"waye ubanta a duk fadin kasar nan da har zai sota ita data kasance  jinin talakawa ,me yasa zai sota?"kai wanan ma ba abune  mai yuwu ba, akwai dai abinda yake nema a wajenta wanda ba sai ta tsaya wahalar da kanta ba tuni tasan me yake so atare daita gara ta kama mutuncin kanta zai fiyye mata alkhairi kuma har abada bazata yarda ta banzatar da budurcinta ba duk wuya duk runtsi tana tare da abunta .”cike da natsuwa ta shiga ta zauna bangaren daya bud’e mata tana mai ra'be jikinta tare da kamkame kayan jiknta tana kallon bangaren da take zaune tana jinsa ya shigo ya zauna a kusa daita bai ra’beta ba sai dai taji idanunshi ajikinta suna yawo wanda ke qara saka zuciyarta tsinkewa tare da mummunar bugu .”




ahkl  mota biyu suka fara fita sai motar da suke ciki tabi bayansu sai kuma mota biyu dake biye dasu a natse direba ke jansu, motar tayi shiru yadda bai ce mata qalla ba itama bata waigo inda yake ba bare ma ita bata da abinda zata ce masa ,dan kusan shi ke takalota da magana har suka isa titin Liverpool bai ce uffan ba , anan taga motocin gabansu sun d’auki wata hanya haka ma motocin bayansu yayinda motarsu ta sauka zuwa kasan bridge din Liverpool ahankali direban ke jansu ,tukinsa bai yi slow ba hakazalika ba mugun gudu yake shararawa ba a haka har suka shigo unguwarsu still babu wanda  ya cewa danuwansa wani abu ,a ruwa yayi parking a inda yayi jiya yana cewa “ranka ya dade mun qaraso mr ata bai ce masa qala ba illa ya rankwafo zuwa jikinta yana qoqarin bud'e mata murfin motar daga cikin “ya rabbi ta furta tana saisaita numfashinta sakamakon abinda taji ya tsarga mata ai yana barin jikinta tayi wuf ta fito daga mota adaidai lokacin daake kiran sallahr isha'i kafin tayi tattaki ta tsallaka ta karya kwanar da zata shigar daita dogon layinsu taga ya fito bata tsaya ba ta soma tafiya.”



ahankali  ya biyo  bayanta, idanuwanshi na kanta haka ya dinga binta yana bin  duk wani takunta da kwayar idanunshi  tamkar wacce  ke rangaji haka take ajiye takunta a nutse duk ilahirin jikinta na juyawa ,duk jin kan maryam  daya  sani  da nuna ita wa tace  wajen iya gayu da sanyin murya  tare da iya tafiya bai ta'ba ganin tayi  irin salon maryama  ba kai bai ma san mata nada irin wannan salon ba ko don bai kallon mata ne sai maryam din data zame masa dole kuma da ita kad’ai ya zauna   bai sani ba , dan shi bai san komai da ya shafi shirgin mata ba tsakaninshi dasu a wajen aiki ne  kuma tsakani da Allah shi baya kallon tafiyarsu ."
"Wait" ! Kunnuwanta suka jiyo mata muryarsa mafi soyuwar sauti domin dai ko tana so ko bata só zuciyarta ta aminta yana da sanyin murya mai dadi da shiga jiki ,ta tsaya cak ta kasa juyowa zuwa garesa sakamakon abinda ke nukurkusan zuciyarta da ganganr jikinta a natse ya qaraso zuwa gareta ya tsaya a gefenta yana had'a kafad'anta danashi "ta d'an matsa kad’an aranta tace "matsalarsa kenan son jikin matseefa”.



ya motsa lip's dinsa ahankali "karki mata tambayar da nayi miki d'azu a office ,tana jinsa amman tayi shiru "zan baki lokacin nan da qarshen watan nan ina son ki natsu kiyi tunani akaina, bana son idan na tambayeki ki tsaya min inda inda ko kice baki fahimci komai ba ,ko kuma kizo min da wannan banzar kukan naki I can't take it "yana gama fad'ar haka yace zaki iya wucewa zuciyarta na bugawa da matsanancin qarfi ta soma d'aga qafafuwanta wanda take jin sun mata nauyi kamar yadda maganarsa suka mata  nauyi acikin kwakwaluwarta ,tana tafiya amman still tana jin idanunshi na biye daita a duk inda tasa qafarta sai dai ta kasa juyowa taga halin da yake ciki a haka ta shige gidansu bazata iya cewa ga adadin lokacin daya d'auka a kofar gidansu ba ."kai tsaye bangaren umma ta shiga kamar koda yaushe Sai dai duk jikinta yayi wani iri umma ta hango zaune ita kad’ai a parlour’n hannunta rike da casbaha da alamun idar da sallarta kenan .”
assalamu alaikum “ta furta tana mai qoqarin qarasawa inda take, umma ta amsa mata tana kallonta da kulawa “maryama kin dawo ?”na dawo umma sannu da gida .”yauwa !”ta amsa tana dubanta maryama tayi shiru tana jingina bayanta ajikin kujera har lokacin zuciyarta taki daina bugawa inda ita kuma so take ta saisaita ta dawo normal .”




“Lafiya kuwa maryama naga duk kinyi wani iri “?hawaye ya d’an gangaro a gefen idanunta amman tayi dabarar gogesa “haka fa jiya kika shigo min nayita tambayarki abinda ya samu hannunki kika
yi ta wasa da hankalina batare da kin fad’a min ba yau ma gashi kin shigo min wani iri anya kuwa maryama kina son kwanciyar hankalina “?nafi kowa son kwanciyar hankalinki ,babu
Showing 108001 words to 111000 words out of 176292 words